”Dargazu ya kasance ɗa ne ga sarkin yaƙin wannan birni mai suna Darmusa, kuma a tarihin zuriyarsu ba’a taɓa samun rago ba ko macece ko namiji ne. Duk wanda ya fito daga gidansu dole ne sai ya kasance sadaukin gaske idan kuwa abinda aka haifa ya kai shekaru biyar ba tare da ya nuna wata babbar alama ta jarumta ba, su da kansu ‘yan ahalin suke kashe shi da hannunsu. Babu iya ƙoƙarin da masu sihiri da masu bincike ba su yi ba domin ganin sun gano sirrin zuriyarsu da kuma yadda za’a samu galaba akansu amma abu ya faskara. Wani abin mamaki dangane da zuri’ar su Dargazu shi ne, basu taɓa jagorantar rundunar yaƙi aka fita ba tare da an samu nasara ba, kuma ba a taɓa kashe ko da mutum ɗaya daga cikin zuri’ar tasu a fagen yaƙi ba, sai dai cuta ta kwantar da shi har ya mutu ko kuma kawai a wayi gari ya mutu ba tare da an san dalili ba. Bayan Sarkin yaƙi Darmusa ya mutu ne aka naɗa babban ɗansa wato Dargazu a kan karagarsa ta sarkin yaƙi. A kowace shekara a ƙalla dargazu na kashe kimanin mutum arba’in daga cikin fursunonin wannan kurkuku haka nan kawai ba tare da wani laifi ba sai don tabbatar da wata tsohuwar al’ada ta wannan ƙasa. Yanzu gashi ka jawo mana wani tashin hankalin ta hanyar takalar shi da rigima. Yanzu shi kenan ka ja min mutuwa tun kafin lokacina ya yi, kuma shikenan burina na ganin na kawo canji a cikin zuri’ar mu ba zai tabbata ba. Kai! Gaskiya ni dai bani da wani amfani!”
Imran ne ya yi wannan furuci yayin da ya ɓarke da kuka mai ratsa zuciyar duk wani mai imani.
Wani gwauron numfashi na sauke ina tunanin amsar da ya kamata in bashi. Domin a wannan lokaci jikina ya yi sanyi matuƙa da jin wannan labari, don haka sai na shiga rarrashinsa ina mai cewa,
”Ya kai abokina, ka kwantar da hankalinka, babu abinda zai same mu face abinda Allah ya ƙaddara mana, kuma za mu mutu ne kawai idan lokacinmu ya yi. Kuma ka sani cewa matuƙar ina nan a raye na yi maka alƙawarin zan taimaka maka har ka kuɓuta daga wannan ɗaurin da aka yi maka bisa zalunci da izinin Allah.”
Ko da na zo nan a zancena, sai na ga Imran ya ƙura min ido kawai ya yi kasaƙe ba tare da ya ce komai ba. Da na ga haka, sai na tambaye shi dalilin da yasa yake min irin wannan kallo. Maimakon ya bani amsa, sai shi ma ya jefo min wata tambayar da cewa,
“Me yasa ka yi alƙawarin za ka taimake ni bayan ba ka sanni ba, ta yaya za ka taimake ni bayan kaima kamo ka aka yi, kuma shin kai mabiyin wane addini ne?”
Ko da najie waɗannan tambayoyi nashi, sai na yi murmushi sannan na gyara zama na ce da shi,
“Ya kai Imran, ba na buƙatar sai na san mutum tukunna kafin in taimaka mishi matuƙar ina da halin yin hakan, domin addinin mu ya koyar da mu kyautatawa mutane da taimaka musu ko da ba mu san su ba. Sannan kada ka manta cewa ka karɓe ni a matsayin aboki da shigowata wannan wuri ba tare da ƙyamata ba, ka ga kenan ko ba komai kai abokina ne kuma abokai an san su da taimakon juna a koyaushe. Amsar tambayarka ta biyu kuma ita ce, shi mai rai baya taɓa cire tsammani. Sannan kamar yadda aka kama ka ba tare da ka yi laifin komai ba, nima hakan ne ya faru da ni, domin har yanzu ban san dalilin wanzuwata a birnin Sahara ba, abin da kawai na sani shi ne lallai jikina na bani cewa zan fita daga wannan birnin lafiya. Amsar ka ta ƙarshe kuma ni mabiyin addinin Musulunci ne.”
Ko da jin wannan batu nawa, sai Imran ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya ce,
”Da fari dai na ji daɗin wannan bayani naka sosai, kuma na gode da karamcinka. Amma ina so ka sani cewa, maganar fitar mu daga nan fa ba wai bada labari bane kawai, magana ce ta jarumta tare da nuna isa da kuma ƙarfin mulki wanda kai baka da ko ɗaya daga cikin su, tayaya kake tsammanin za ka iya taimaka min har in fita daga wannan wuri? Shin ka ma san birnin nan ne balle ka iya yin wani abu? Ko da ganin irin shigar ka ma dama na san kai ba ɗan nan bane, kuma baka san irin mutanen nan ba, kashe mutum a wajensu ba komai bane.” Imran ne ya yi wannan batu fuskarsa cike da damuwa.
”Imran ka sa ranka a inuwa, kai dai kawai ka yarda da ni, domin nasan abinda ba ka sani ba kamar yadda kai ma ka san abinda ban sani ba.” Na bashi amsa ina mai murmushi.
”Kai kuwa mene ne ka sani wanda ban sani ba? Imran ya sake tambayata cike da mamaki.
Ni kuwa sai na dafa kafaɗar shi sannan na ce da shi,
”Kada ka damu Imran, lokaci zai baka amsar tambayoyinka, abinda kawai zan iya faɗa maka shi ne, Allah na taimakon duk wanda ya nemi taimakonSa. Kuma na yi imani da cewa zai taimaka mana.”
Ko da jin haka, sai Imran ya sake tambayata da cewa,
“To wai shi wannan Allahn da kake ta kiran sunanshi wanene shi ɗin? Kuma ta yaya zai iya taimaka mana? “
“Allah Shi ɗaya ne, bashi da mahaifi, bashi da mahaifiya, bashi da wa ko Ƙani, Ya ko ƙanwa, hakanan kuma bashi da ‘Ya kuma bashi da ɗa. Shi ba haihuwarSa aka yi ba, kuma Shi bai haifi kowa ba, amma dukkan wasu halittu da suke cikin duniya Shi 5ne Ya halicce su daga ƙudurarSa. Shi ne Ubangijin Musulunci, Shi kaɗai nake bautawa saboda shi kaɗai ne wanda ya cancanci a bauta masa. Kuma duk wanda ya maida lamarinsa gareShi, to zai taimake shi ta inda bai yi tsammani ba”. Na bashi amsa a taƙaice.
Yayin da Imran ya ji wannan bayani nawa, sai ya yi shiru yana tunani sannan daga baya yace,
“Ai kuwa in haka ne lallai ya kamata mu nemi taimakonSa, to amma a ina za mu ganshi har mu nemi taimakon nashi?”
Ko da na ji wannan tambaya tasa sai na yi murmushi sannan na bashi amsa da cewa,
“Ai Shi Allah buwayi ne gagara misali, Yana ko’ina kuma yana ganin komai sannan yana jin komai, babu wani mahaluƙi da zai iya ɓoyewa daga gare Shi m, kuma yanzu haka ma yana jin duk abinda mu ke tattaunawa ni da kai.
“Kai Haidar?!
Imran ya faɗa cike mamaki tare da zaro ido sannan ya ci gaba da cewa,
“To ya fito mana kawai mu ganshi in ya so sai mu yi magana da shi kai tsaye mu ji shi kuma mai yake so a maimakon taimakon da zai yi mana?”
Daga nan kawai sai Imran ya miƙe tsaye ya fara magana da ƙarfi yana cewa,
“Allah gamu! Ka taimake mu, mu samu abinda muke so mu kuma za mu yi maka duk abinda kake so!”
Da ƙyar na samu na shawo kansa ya zauna sannan na ci gaba da yi masa bayani kamar haka,
“Ya kai Imran, ka sani cewa Shi Allah wadatacce ne daga dukkan wani abun buƙata, baya buƙatar komai a wajen kowa, amma kowa da komai suna buƙatar komai a wajenSa. Bugu da ƙari, idanuwan mutane sun yi kaɗan su ga zatinSa, Kunnuwa sun yi kaɗan su ji muryaSa. Amma bari ka ji kaɗan daga cikin zantukanSa,
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinƙai.
Lalle ne, Muminai sun samu babban rabo.
Waɗanda suke a cikin sallarsu masu tawali’u ne
Kuma waɗanda suke, su daga barin yasassar magana, masu kau da kai ne.
Ka ji kaɗan kenan bawa.
“Amma kuwa kalaman suna da tsari mai kyau tare da daɗin saurare, a ina ka samo su to tun da kace ba a iya jin muryaSa?”
A nan ne na yi wa Imran gamsashshen bayani dangane da Allah maɗaukakin sarki tare da yi masa taƙaicetaccen bayani akan Musulunci da kuma bayyana masa wanene Annabi Muhammad (S.A.W), tare da sauran abubuwan da suka shafi addini har dai ya amintu kuma ya nuna sha’awarsa na shiga cikin wannan addini. Cikin murna da jin daɗi kuwa na biya masa kalmar shahada ya maimaita.
Ai kuwa yana gama maimaitawa sai wani irin baƙin hayaƙi ya soma fitowa daga bakinsa, bayan wani ɗan lokaci sai hayaƙin ya daina fitowa, kawai sai gani muka yi Imran ya koma siffarsa ta asali a maimakon ta tsoho da yake da ita sakamakon aikin sihirin da aka yi masa ya koma siffar kyakkyawan saurayi majiyin ƙarfi.
Ganin wannan al’amari ne fa yasa Imran ya wangame baki yana kallon jikin shi tare da shafa fuskar shi da sauran jikin shi kamar ranar ya fara ganin kanshi, ya kai kusan daƙiƙu goma yana kallon jikinshi kafin can daga baya kuma sai ya dube ni cikin mamaki sannan ya ce,
“Kai Haidar! Wannan wane irin sihiri ne ka aikata haka a gare ni na koma kamar yadda nake da.”
Ko da jin haka, sai na sake yin murmushi cike da farinciki sannan na ce da shi,
“Wannan ba aikin sihiri bane, ikon Allah kenan! Abinda ka faɗa shi ne ya jawo sanadiyyar karyewar aikin sihirin da aka yi maka. Cewa ka yi ka yarda cewa babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma AnnabinSa Muhammad lallai bawanSa ne kuma manzonsa ne.”
Ko da jin wannan batu nawa, sai Imran ya rungumeni cikin farinciki yana mai cewa,
“Lallai wannan Allah kuwa da girma yake, yanzu-yanzu daga shiga addinin har ya yi min irin wannan gagarumin abin alheri haka?”
Ni kuma sai na bashi amsa da cewa,
“Alherin Allah ya da girman zatinSa sun buwaya. Ai wannan ma kaɗan kenan ka gani daga cikin ikonSa. Daga nan sai na ci gaba da yiwa Imran bayanin dokokin addinin Musulunci da abinda shari’ar musulunci ta ce akan muhimman abubuwan da suka shafi rayuwar kowane musulmi. Muna cikin wannan tattaunawa ne wayata ta fara kiran sallah, hakan ya tabbatar min da cewa lokacin Azahar ya yi. Don haka sai muka bugi ƙasa muka yi taimama ina mai nunawa Imran yadda ake yin komai har muka gama sannan na ja mu sallah muka gabatar da ita a cikin wannan ɗaki na kurkuku. Bayan mun kammala mun yi addu’o’i sai na ji wata irin nutsuwa ta sauko min a cikin zuciyata, sannan wannan so da nake ji game da Sadiya sai na ji ya ragu ya koma daidai yadda yake a da, wato so irin na Yaya da ƙanwa.
Haka muka ci gaba da rayuwa a cikin wannan faffaɗan ɗaki da ke cikin kurkuku Birnin Sahara ni da Imran har tsawon kwanaki uku. A ɗan wannan zama da muka yi da shi ne shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninmu da shi. Kuma ta hakan ne na fahimci cewa Imran yana da wata irin baiwa ta ban mamaki. Wato duk abinda na faɗa masa sau ɗaya shikenan ya riƙe shi kamar dama can ya san shi. A cikin waɗannan ‘yan kwanaki da muka yi da shi tare muke yin sallah ina kuma ci gaba da yi mishi bayani dangane da addinin musulunci. Wani abun ma koya mishi nake yi a aikace domin ya fahimta da kyau, haka muke yi tun daga safiya har zuwa dare. Sai da ya zamana Imran ya haddace izu biyar na Alƙur’ani mai girma gyam a cikin kwanaki ukun nan. Ko da yake jin harshen larabcin da yake yi ya taimaka mishi sosai wajen fahimtar karatun da sauri, na yi mamaki matuƙa da irin yadda ƙwaƙwalwarsa ke saurin ajiye abu. Haka in muka shiga fagen tambayoyi da amsoshin su, in da ya dinga min tambaya ni kuma ina bashi amsa tare da yi masa bayani akan duk wani muhimmin abu da ya kamata a ce sabon shiga addinin Musulunci ya sani gwargwadon sani na. Kullum akan kawo mana abinci da ruwa sau ɗaya ne kawai.
A rana ta uku da daddare, bayan mun idar da sallar Isha’i mun zauna muna ci gaba da tattaunawa har dare ya raba, sai muka ji ƙarar takun sawayen wani ya nufo ɗakin da muke ciki. Ba tare da wata fargaba ba muka miƙe tsaye dukkanmu tare da zuba ido akan ƙofar ɗakin don ganin waye shi kuwa da tsakar daren nan ya zo wajenmu? Kuma me yake nufi da mu?
Ba mu jima a cikin wannan hali ba sai muka ga wata mace kyakkyawa sanye da kayan bayin gidan Sarautar Birnin Sahara ta nufo ɗakin da muke ciki, biye da ita a baya kuma wasu narka-narkan ƙarata ne guda uku suna ta muzurai kamar sa ci babu. Ko da wannan baiwa ta zo dai dai bakin ƙofar da muke wacce aka yi ta da zunzurutun rodi, sai ta tsaya sannan ta yi wa dakarun da ke biye da ita alamar su ɗan koma baya. Bayan dakarun sun ja da baya sai ta nuna ni da ɗan yatsanta sannan ta yafito ni da hannu alamar in zo. To kun san ni wani lokacin da zafin rai, sai na ga kamar wannan ai rainin wayo ne, don haka kawai sai na basar kamar ban ganta ba na koma na zauna abina na juya mata baya.
Ganin wannan abu da na aikata ne yasa Imran ya tsugunna sannan ya dafa kafaɗata ya ce,
“Ya kai Haidar, kada ka ɗauki wannan al’amari da zafi, ka je gareta ka ji abinda ke tafe da ita.”
Jin yadda ya tausasa murya da kuma mutuncinsa da nake gani sakamakon shigowarsa cikin addinin Musulunci ne kaɗai suka sa na amince da batunsa ba don raina yana so ba. A Sanyaye na miƙe ina tafiya kamar ba zani ba har na je daf da bakin ƙofar na tsaya, sannan na dubeta ido cikin ido da nufin in daka mata tsawa tare da tuhumarta kan dalilin da yasa ta zo gare ni cikin wannan dare.
Sai dai kafin in aiwatar da wannan nufi nawa, tuni wannan kuyanga ta matso gare ni cikin wani irin zafin nama ta toshe min baki da hannunta. Mamaki ya hana ni cewa komai, bayan ta toshe min baki da hannun nata sai kuma ta yi amfani da ɗayan hannun nata ta yi min alamar in yi shiru sannan ta ɗaga kanta da alamar ‘Ka gane?’ nima sai na ɗaga mata kai da alamar ‘Eh Nagane’
Daga nan sai ta saka hannunta a cikin wani ɓoyayyen aljihu da ke cikin rigarta, ta zaro wata takarda ta miƙo min. Na amshi takardar jikina a sanyaye na warwareta domin ganin ko menene a ciki, aikuwa ina buɗewa sai na ga rubutu kamar haka,
‘Daga Sarauniya Nadiya ta birnin Sahara. Zuwa ga Haidar cike da yarda da aminci. Ya Kai Haidar, da ɗari dai ina mai baka haƙuri a bisa abinda ya faru, ka sani cewa ba da son raina na yi hakan ba, amma a matsayina na Sarauniya mutanena suna sa ido a kaina domin ganin na yi abin da ya dace. Kuma idan har kana so ka fita daga cikin wannan birni a raye, to ya zama dole a gareka ka bi duk umurnin da zan baka a gobe idan an zo da kai fada kana mai nuna cikakkiyar biyayya a gareni, ta haka ne kawai zan iya ƙoƙarin tseratar da rayuwarka da ta sadiya. Ka taimake ni kada ka bani kunya Haidar.”
Daga Sarauniya Nadiya.
Ko da na gama karanta abinda wannan takarda ta ƙunsa, sai nan da nan na ji kaina ya fara ciwo, domin miliyoyin tunanuka ne suka yi caa a cikin ƙwaƙwalwata a wannan lokacin. Mafi girma daga cikin su kuma tambayoyi ne waɗanda amsoshinsu ba masu samuwa bane a wannan hali. Menene dalilin da yasa Nadiya ta ke so ta cece ni? Kuma me yasa har take roƙona? Menene sirri da kuma ribar biyayyar da take so in yi mata a gobe? Waɗannan da ma wasu tambayoyin makamantansu ne suka taru su ka yi min kane-kane a cikin ƙwaƙwalwata. Ina cikin juya zancen a zuciyata ne kawai sai na ji an girgiza ni, nan fa na dawo cikin hayyacina ba shiri, ashe wannan baiwa ce ta girgiza ni sakamakon daɗewa da na yi ban ce mata komai ba.
Ko da muka haɗa ido da ita sai ta kaɗa kanta tana mai min alamar ‘Ka amince?’ cikin sanyin jiki na kaɗa mata kai nima da alamar ‘Eh na amince’ Daga nan sai wannan baiwa ta fizge takardar daga hannuna ta jefata cikin bakinta ta tauneta kamar ta samu buredi, bayan ta lamushe takardar sai kuma ta risina ƙasa cikin girmamawa ta yi min alamar godiya sannan ta juya ta tafi, dakarun da su ka rakota su ma sai su ka rufa mata baya, kafin ka ce kwabo har sun ɓace daga ɗakin.
Munajiran babi nagaba🤩
Munajiran babi nagaba🤩
Na gode sosai. Yana nan tafe.
Yana tafe in sha Allah.
Good job
Fatan Alkairi Allah 👍👍👍👍👍👍
Na gode sosai.
muna jindadin littafinnan
Madalla, ina godiya sosai.
Gdy ta musamman domin wan nan littafi yana bada citta
Na gode sosai.
Allah yayi Tai mako
Amin. Jazakallah Khair.
Bari kuma mu je shafi na gaba mu ji yadda za a yi
Na gode sosai.
Wow! This is amazingl!
Thanks
Dakyau. Labarin nan yayi fa.
Na gode sosai
Masha Allah. Allah ya ƙara hazaƙa.
Amin. Jazakallah Khair
Wannan Labari Yayi
Na gode sosai.
#haimanraees
Ma Sha Allah.
Thank you.