Skip to content
Part 4 of 17 in the Series Birnin Sahara by Haiman Raees

Bayan sun tafi sai na koma inda Imran yake na zauna jikina a sanyaye ba tare da na ce komai ba. Bayan wani ɗan lokaci sai ya dafa kafaɗata ya ce,

“Ya kai ɗan uwana me yake faruwa ne?” 

Har na buɗe baki zan bashi amsa sai na ji kamar wani abu na motsi a kusa da bakin ƙofar ɗakin da muke ciki, don haka sai na laɓaɓa na je kusa da ƙofar na daka tsawa da cewa, 

“Waye ne a nan?” 

Aikuwa faɗin hakan ke da wuya sai ga wani sirrin mutum wanda jikinsa babu komai sai bante ya yi fitar burtu daga wani saƙo ya ruga a guje kamar zai bar duniyar. Daga nan sai na koma inda Imran yake na labarta masa duk abinda ya faru tsakanina da wannan baiwa da kuma abinda Sarauniya Nadiya ta faɗa a cikin wasiƙarta, ko da ya ji wannan batu nawa sai shi ma jikinsa yayi sanyi. Bayan ya daɗe yana tunani sai ya ce dani, 

“Ya kai Haidar, ka sani cewa akwai wasu maganganu guda biyu da kakana yake yawan faɗa min sa’adda yake raye a duk lokacin da ya ga na shiga cikin irin halin da kake ciki a yanzu, a duk lokacin da ya faɗa min su yakan barni ne da su a matsayin linzamin da zai taimaka min wajen yanke hukuncin da ya kamata da ni.” 

Ko da na ji wannan batu nasa sai na ce da shi, 

” Ya kai Imran su kuwa waɗannan wasu irin maganganu ne haka? Kuma shin ko za ka iya faɗa min su in ji?”

Da jin waɗannan tambayoyi tawa, sai Imran ya ce da ni, 

“Maganganu ne guda biyu, na farko a duk lokacin da na zo mishi da batun na samu wani abu na ci gaba, to yakan ce da ni 

‘Ya kai jikana, ka sani cewa a duk lokacin da ka ga wani ci gaba ya tunkaro ka, to ka sani cewa cikin biyu dole ne a samu ɗaya, ko dai lokacin samun ci gaban naka ne ya zo, ko kuma tarko ne ake so ka faɗa ciki.’

Magana ta biyu kuma yakan faɗa min ita ne yayin da ya ga na shiga damuwa saboda neman mafita dangane da wani al’amari da ya dame ni, yakan ce dani, 

‘Ya kai jikana, ka sani cewa duk amsar da kake nema tana cikin zuciyarka, mai yiwuwa kai ba za ka yarda da kanka ba, amma amsar duk da kake nema tana cikin zuciyarka.’

Yayin da Imran ya zo nan a zancen sa, sai na yi shiru na rasa me zan ce, daga baya dai sai na tambaye shi da cewa, 

“To amma in banda abinka, ta yaya waɗannan maganganun za su taimaka min wurin yanke hukuncin abinda ke tunkaro ni?

Da Imran ya ji tambayata sai ya yi murmushi sannan ya ce, 

“Ka yi tunani.” 

Daga nan kawai sai ya kwanta abin shi ya barni nan ina ta tunanin abinda ya faɗa min. Ina nan zaune ina tunanin waɗannan maganganun da Imran ya faɗa min har na ji barci ba neman ya kwashe ni, don haka ma yi addu’o’i sannan na kwanta. Ban tashi ba har sai da sanyin alfijir ya keto ya tashe ni, daga nan na tashi Imran muka yi taimama muka bada farali. Da gari ya waye sosai, sai muka ga an kawo mana abinci mai rai da lafiya har da abubuwan sha. Da fari Imran kamar ba zai ci ba wai saboda kada ya zo an zuba guba mu ci mu mutu, ai da naga haka sai na ce ina zuwa kawai na yi Bismillah na hau cin abincin ba tare da wata fargaba ba, da dai ya ga haka shi ma sai shi ma ya sa hannu muka ci gaba da ci a tare. Nan dai muka ci muka sha muka gode wa Allah.

Ba mu fi daƙiƙa talatin da gama cin abincin ba sai ga dakaru sun zo ƙofar ɗakin da mu ke ciki, Babba daga cikin su ya nuna ni da yatsansa ya ce, 

“Sarauniya Nadiya na buƙatar ganinka a fada yanzu.”

Daga nan sai ya sa mukulli ya buɗe kwaɗon ɗakin ya yi min alamar in fito. Har na kama hanya zan fita sai na waiga na kalli Imran wanda tuni alamomin damuwa sun ziyarci fuskarsa na ce,

“Kada ka damu ɗan uwa, babu abinda zai same ni in sha Allah.” Ko da Imran ya ji haka, sai ya saki fuskar sa, amma duk da haka sai ya ce da ni, 

“Amma dai ina fatan kana da mafita dangane da batun nan ko?” Ko da na ji wannan tambayar sai na yi wani irin murmushi ta gefe ɗaya, wato irin murmushin nan da ake kira na mugunta sannan na ce da Imran, 

“Kada ka damu abokina, ina da mafita, kuma in sha Allah babu abinda zai same ni.” 

Daga nan muka yi sallama na fita daga ɗakin. Ina fita kuwa suka maida mukulli suka garƙame ƙofar ɗakin sannan suka sani a tsakiya muka fara tafiya. Kimanin dakaru ashirin ne suke bayana, sannan sai wasu kamar su a dama da hagu na, sai kuma biyar a gabana suna mana jagora. Haka muka ci gaba da tafiya ba tare da na san ina muka nufa ba. Wani abu da ya bani mamaki shi ne, sam babu wanda ya damu da cewa ba a ɗaure nake ba daga cikin dakarun. Haka dai muka ci gaba da tafiya muna wuce wurare iri daban-daban. Ga dukkan alamu dai a ƙarƙashin ƙasa muke domin bana iya ganin komai face inda nake takawa da kuma saman kaina, kuma ina iya jin kururuwar da sauran fursunonin gidan yarin suke yi.

A haka dai muka ci gaba da tafiya har muka fito fili inda ina iya ganin sararin samaniya. Daga nan sai aka ɗaura ni a kan wani ƙaton keken doki muka ci gaba da tafiya. Tsawon lokaci muna wannan tafiya babu wanda ya ce da wani komai. Can sai na dubi wani ɗan siriri daga cikin dakarun da ke tare da ni na ce da shi, 

“Amma abokina kai ya naga ka yi rama da yawa ne? Ko baka samun abinci isashshe ne?” 

Maimakon ya bani amsa, sai kawai ya yi banza da ni kamar ma bai ji ni ba. Da dai na ga haka sai na taɓa kafaɗarsa domin in sake maimaita tambayata. Haba ai kuwa sai gani na yi ya kawo min wani wawan naushi, ba don na ankara da wuri na goce ba da tuni na zama dameji. Wannan abu sai ya ɓata min rai don haka sai na matso da ƙarfina na ce, 

“Wai ku wasu irin mutane ne da ba ku san wasa ba? Ku shikenan komai mutum yayi sai ku kai duka da ƙoƙarin naƙasa shi… ban gama faɗan abin da ke raina ba sai kawai na ga kowanensu ya juyo kaina ya saita ni da makamin da ke hannunsa. ai kuwa ban yi wata-wata ba na tsuke bakina, don na ga alama waɗannan ba wasan suke so ba.

Haka dai muka ci gaba da tafiya akan wannan keken doki muna ratsa sahara. Sai dai bana iya ganin komai sakamakon zagaye ni da waɗannan samudawan suka yi. Tafiya muke yi zamu ba zamu ba dai har muka shigo cikin gari, na fahimci hakane ta hanyar jiyo hayaniyar jama’a da na yi da kuma dogayen gine-gine da nake iya gani ta saman kaina. Bayan mun taɓa ‘yar tafiya a cikin garin sai na ji keken dokin da nake ciki ya tsaya. Daga nan kuma sai waɗannan dakarun suka sauko sannan suka bani umurnin nima in sauko. Bayan na sauko sai suka sake yi min rumfa kamar yadda suka yi min da fari, sannan suka iza ƙeyata a gaba muka ci gaba da tafiya a ƙafa. Wani rufaffen wuri na ji alamar mun shigo yayin da a lokaci guda kuma na ji ƙarar wata ganga ya doki kunnuwana. Ba mu yi nisa da tafiya a cikin wannan wuri ba sai na ga waɗannan dakaru sun tsaya cak wanda hakan yasa nima na tsaya. Can kuma sai na ga sun rabu zuwa gida biyu suna masu samar da hanya a tsakiya. Ko da ganin haka, kawai sai na bi ta cikin wannan hanyar na fito fili inda zan iya ganin komai da ke wurin. Ai kuwa sai na yi arba da abin mamakin da ban taɓa gani ba a rayuwata. A ƙofar wata ƙasaitacciyar fada na tsinci kaina. Fada ce da ta ƙawatu matuƙa ta yadda idan na ce zan misalta muku ita, to tabbas sai kun ce sharata kawai nake yi, amma dai bari in ɗan yi muku bayani a taƙaice.

A ƙalla tsayin fadar daga ƙasa zuwa sama zai kai kimanin tsawon itacen dogon yaro guda biyu da rabi, ga wasu murtuka-murtukan dirkoki da suka tokare fadar waɗanda ƙarti biyar da wahala su iya ritsa guda ɗaya, faɗin fadar kuwa ba a cewa komai. Ƙasan fadar kuma an yi masa daɓe ne da wasu irin duwatsun wuta masu canja launi lokaci zuwa lokaci. Gaba ɗaya bangwayen fadar an yi musu wata irin kwalliya ne da ɗanyen gwal, ga wasu fitulu na lu’ulu’u ɗirka-ɗirka masu matuƙar haske suna lilo a sama, duk da yake safiya ce a wannan lokaci, hakan bai hana su nuna hasken su ba. A jikin bangon fadar da kuma waɗannan dirrkoki, rubutu ne da bana iya fahimtar ko me suke nufi da kuma hotunan mutane da dabbobi iri-iri. Fadar tana da zubi ne da yayi daidai da harafin turanci na V, daga can tsakiyar fadar wata ƙasaitacciyar karagar mulki ce wacce ko karagar sarki Lu’umanu na birnin Teheren albarka. Sai kuma wasu matsakaitan kujerun sarautu guda goma sha uku da ke jere a dama da haunin karagar. Na ci gaba da tafiya har na zo tsakiyar fadar sannan na tsaya ina ci gaba da kalle-kalle kamar yaro ha shiga kasuwa. 

Zaune akan wannan ƙasaitacciyar karaga kuwa, Sarauniya Nadiya ce ta ci ado da wasu irin kaya masu ruwan ƙasa da ƙyalƙyali tare da ɗaukar ido, ga wani takalmi shi ma mai ruwan ƙasa ta saka a ƙafarta, sai dai irin mai tudun nan ne da wasu irin mata ne kaɗai ke sawa. Sai kuma kambun Sarauta da ke bisa kanta wanda shi kuma kalar ruwan gwal ne da shi, ga kuma rubuce-rubuce da wasu rubututtuka da suma ban san abinda suke nufi ba. Wato na daɗe da sanin cewa Nadiya kyakkyawar mace ce ta gaban kwatance, amma wannan kwalliya da ta yi yau, yasa na ƙara tabbatar da cewa in zan yi wata biyar ina tunanin a wane rukuni ya kamata in aje ta a sahun kyawawan mata, gajiya kawai zan yi, domin ko a matakin farko na ajiye ta nasan na yi laifi don ta wuce nan. Wani irin matsewa da buɗewa na ji zuciyata na yi a wannan lokaci da ko kaɗan bana so, amma ita zuciyar tana so. 

A tsai-tsaye a bayanta kuma wasu lafta-laftan ƙarti ne guda biyar kamar shanu, haka ma sauran kusurwoyin fadar duk jarumai ne a tsaitsaye da kayan faɗa a hannayensu. A dama da hagun Sarauniya Nadiya kuwa, zaune akan waɗannan kujeru masu kyawun gaske guda goma-sha-uku-uku fadawa ne da sauran masu faɗa a ji na masarautar. A kujerun farko da ke dama da haunin Sarauniya Nadiya wasu mutane ne guda biyu masu sanye da jajayen riguna a zaune. Dukkansu za su kai kimanin shekaru saba’in a duniya. Kuma kujerunsu suna kusa da na Sarauniya Nadiya ne. A hagu da mai jar rigar da ke hagun Sarauniya Nadiya kuma Dargazu ne zaune tare da wata matashiya wacce ta yi kama da shi cikin shigar yaƙi na baƙaƙen kaya, fuskokin su babu alamar fara’a ko kaɗan.

A dama da mai jar rigar da ke daman Sarauniya Nadiya kuma kujera ce wadda ita kaɗai ce babu kowa akanta a duk cikin kujerun fadar. Gaba da ita kuma wani mutum ne mai siffar bokaye zaune a kan wata baƙar kujera wacce ita kaɗai ce mummunan abu da idona ya kai kansa a fadar. Shi ma fuskarsa babu alamar fara’a. Ragowar kujerun kuma duk suna ɗauke ne da sauran masu muƙamai a fadar. 

‘Me ya sa waccan kujerar ita kuma na ganta wayam?’ 

Na tambayi kaina a cikin zuciya ta 

‘To kai kuma ina ruwan ka?’

Wata murya daga wani ɓangare na zuciyata ta faɗa. Nan dai na kori tunanin wannan kujera daga zuciyata.

Gani na da sauran jama’ar fadar suka yi na fito fili sosai ne yasa suka fara ‘yan maganganu kowa na faɗin albarkacin bakinsa. A yayin da suke waɗannan ‘yan maganganu hankali na baya kansu. Ina can na hangame baki ina kallon wannan kyakkyawar fada wacce ko a mafarki ban taɓa ganin irin ta ba. Ƙarar wata ganga da aka buga ce ta sa hankalina ya dawo jikina. Ni dai ban ga wannan ganga ba amma dai da jin ƙarar na san ta ganga ce, domin ƙarar ta ne na ji tun farkon shigowar mu wurin. Sai dai ban ga wanda ya buga gangar ba kuma ban fahimci sautin daga ina yake fitowa ba. Lokaci guda kawai dai sautin ya bayyana a kunnuwana. Shiru ya ɗan biyo bayan wannan sauti yayinda fadar ta yi tsit kamar mutuwa ta gifta.

Can sai wani ɗan figigin mutum ya miƙe tsaye daga kan ɗaya daga cikin kujerun dake hagu da Sarauniya Nadiya ya fara takowa zuwa tsakiyar fadar, hannunsa na ɗauke da wata ‘yar madaidaiciyar ganga wacce a ɗazu hankalina bai kai kanta ba. Yayin da ya zo tsakiyar fadar, sai ya fara doka wannan ganga tasa cikin wani irin sauti mai daɗin gaske wanda yasa ni har na fara karkaɗa ƙafa ba tare da na sani ba ina mamakin yadda aka yi wannan ‘yar ƙaramar ganga ke bada sauti haka. A taƙaice dai gwani ne wannan.

Wani ɓangare na zuciyata ya ce, 

‘Hmm wa ya ga su jikan Dujal’

‘Shiru!’ 

Ɗayan ɓangaren ya faɗa. Kafin in sake yin wani tunanin, sai kuma wani mutumin ya tashi ya fara rero wata waƙa mai daɗin gaske yana jinjinawa Sarauniya Nadiya da kuma sauran jama’ar Birnin Sahara. Wani abin ban mamaki shi ne, yayinda yazo daidai gaɓar da yake yabon Sarauniya Nadiya, sai na ji haushinsa ya turnuƙe min zuciya. Wani ɓangare na ƙwaƙwalwata sai ya ce, 

“Kai hamago ina ruwanka da ita? Kana fa da budurwa, Sadiya hamago, Sadiya!” 

Gaba ɗaya wannan fada da kayan alatun da ke cikinta sun sa har na manta ma da maganar Sadiya. Ni dai ban san me ke faruwa ba, amma ji na ke yi a wannan lokaci kamar son Sadiya ya ƙara raguwa a zuciyata yayin da na Nadiya kuma ke ƙara ƙaruwa. Me ke faruwa da ni ne wai?

 Na tambayi kaina a zuci, sai dai ba ni da amsar da zan ba wa kaina.

Ganin da na yi wa wannan fada yasa na fara shakkar anya kuwa zan fita wurin nan lafiya? Ga shi ban ga Sadiya ba a cikin fadar, ko dai sun kasheta ne? Wani ɓangare na zuciya ta yace, 

‘Ka daina wannan mugun tunanin’ Daga nan sai na ƙudurta a raina cewa lallai zan yi duk yadda zan yi don in samu damar barin garin nan. Sai dai duk da wannan ƙuduri da na ɗauka, na san cewa in aka yi min wani rainin hankalin komai na iya faruwa, wataƙila ma abinda ya sa Sarauniya Nadiya ta lallaɓe ni kenan, tunda ta san halina sarai.

Bayan wannan mawaƙi ya gama rero waƙarsa, sai fadar ta sake yin tsit, daga nan kuma sai mutanen da ke fadar suka fara fitowa ɗaya bayan ɗaya suna bayyana ƙwarerwarsu a fannoni iri-iri. Shi dai Dargazu jarumta ya nuna, yayinda wannan mutum mai shiga irin ta bokaye kuma ya tabbatar min da abinda nake tunani ta hanyar yin tsafe-tsafe iri-iri a gaban kowa. Nan fa aka ci gaba da nuna bajinta iri-iri, abin gwanin ban sha’awa. Bayan an gama sai kuma kowa da ke fadar ya risina bisa guiwarsa guda ɗaya ya yi gaisuwar ban girma ga Sarauniya Nadiya. Sai da ya zamana ni kaɗai ne a tsaye cikin fadar. Bayan wani ɗan lokaci, sai Sarauniya Nadiya ta yi gyaran murya. A sannan ne duk jama’ar fadar da suka duƙa ƙasa suka miƙe sannan suka koma kan kujerunsu suka zauna.

Bayan kowa ya zauna ne, sai wani lafcecen badakare ya daka min tsawa da cewa, 

“Kai don ƙaniyar baka iya gaisuwa bane?” 

<< Birnin Sahara 3Birnin Sahara 5 >>

16 thoughts on “Birnin Sahara 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×