Skip to content
Part 8 of 17 in the Series Birnin Sahara by Haiman Raees

Nan fa na yi tsuru-tsuru ina raba ido kamar an ƙure ɓarawo ba tare da sanin me zanyi ba. Ba zan ɓoye muku ba, a wannan Lokaci gaba ɗaya kasa magana na yi. Can sai na ji muryar Boka Wajagi yana cewa, 

“Ƙarya kake ya kai wannan baƙo, baka isa ka zo ka ce zaka gaje mana sarautar birninmu ba, har abada ba zan taɓa yi maka mubaya’a ba…”

Kafin ya gama wanna zance nashi sai na tare shi da cewa, 

“To wa ya faɗa maka na zo nan ne domin in gaje muku sarauta? Kuma wa ya gaya maka ina buƙatar mubaya’arka?”

Ko da Boka Wajagi ya ji waɗannan tambayoyi nawa sai ya yi kururuwa tare da zunduma ashar yana cewa, 

‘Halaka ta tabbata a gare ka ya kai maƙiyin birnin mu, dakaru ku kamo min shi…” 

Maimakon dakarun da ke cikin fadar su yo kaina su kama ni, ko ɗaya daga cikin su babu wanda ya nuna alamun ma ya ji maganar shi balle ya motsa. Nan fa dariya ta ƙule ni na yi kamar in dara amma sai na danne. Bayan haka, sai na nufi inda Sarauniya Nadiya take a durƙushe na ce, 

“Ya ke Sarauniya Nadiya, ki yi haƙuri ki miƙe tsaye kada mutanen ki su yi tunanin wani abu, ke fa Sarauniya ce.” 

Ko da na zo nan a kalamaina, sai Sarauniya Nadiya ta ɗago daga durƙuson da ta yi. A wannan lokaci idanuwanta sun cika da ƙwalla, amma kuma ga murmushi nan ya bayyana ƙarara a fuskarta. Wai menene matsalar Nadiya ne? Na tambayi kaina, saboda Wannan abu ya matuƙar ɗaure min kai. Sai dai kafin in yi mata wannan tambayar, kawai sai ji na yi ta kama hannuna a karon farko tun bayan haɗuwar mu ta ɗaga sama sannan ta fara magana da cewa, 

“Ya ku jama’ar Birnin Sahara, ga yariman ku Haidar ɗa ga tsohon sarki Hammadi ɗan Hantsi ina mai gabatar muku da shi! A gaban idon ku ya hau karagar mulki ba tare da wani abu ya same shi ba, kuma a gabanku ya bayyana sunan shi da na mahaifin shi, lallai na yarda da sahihancin zancen shi don haka zan barshi ya je zuwa ga ahalin shi, idan har ya rayu to zai halarci zaman taron duk shekara wanda za’a yi a babban ɗakin gani nan da wata uku, duk wanda yake da tantama ko ƙorafi dangane da wannan hukunci nawa, yana iya gabatar da ƙorafin shi yayinda aka taru a bikin gani mai zuwa, na sallame ku.”

Na san cewa da yawan ku za ku iya tunanin; ‘Dakyau ! Wannan abu ya yi, ko kuma ‘shikenan Haidar ya samu sarauta.’ amma ina. Abinda ya fara fitowa daga bakina tambaya ce, 

“Me kike nufi da in na rayu?” Na tambayeta cikin alamun damuwa. “Za ka gani da idon ka, ta bani amsa tare da sakin hannuna. A wannan lokaci ne mutanen da suka halarci fadar suka fara watsewa, dakarun da ke tsaron fadar ne kaɗai suka tsaya. Ba tare da jiran komai ba, sai Sarauniya Nadiya ta bada umurnin a kwance Sadiya kuma a kawo ta inda nake.

Ko da Boka Wajagi ya zo fita daga cikin fadar, sai ya zo inda nake ya kalle ni ido cikin ido ya ce dani, 

“Ya kai wannan baƙo, ka sani cewa tabbas daga yau ka samu maƙiyi mai suna Wajagi, maƙiyin da ba zai taɓa hutawa ba har sai ya ga bayanka.” 

Yayin da ya zo nan a zancensa, sai Sarauniya Nadiya ta buɗe baki da nufin ta bashi amsa amma sai na dakatar da ita, bata so hakan ba, amma babu yadda ta iya. Daga nan nima sai na fuskance shi ido cikin ido na mayar mishi da amsa da cewa, 

“Ni kuma daga yau ka sa a ranka cewa ka samu maƙiyin da a kullum zai ta buɗe maka sabbin ƙofofin da za ku iya zama abokai, maƙiyin da zai ci gaba da hana ka bacci amma kuma zai iya ceto rayuwar ka a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso, lallai za ka gwammace mutuwa da yin gaba da ni, domin daga yau ka bar ƙara samun nutsuwa har sai ranar da ka cire ni daga cikin maƙiyanka.”

Yayinda na zo nan a zance na, sai Boka Wajagi ya turɓune fuska kamar an goyo biri a keke, sannan ya ɓace bat daga gabana yana mai dalla min harara. 

“Amma dai ina fatan ba haka kake nufi har a cikin zuciyarka ba ko?” Sadiya ce ta yi min wannan tambaya cikin alamun damuwa. Gaba ɗaya tausayi take bani ma ni, ta jigata ƙwarai da gaske da ƙyar ma take iya tsayuwa bisa duga-duganta. Na yi mata murmushin ƙarfin hali tare da cewa, 

“Kada ki damu.” 

Ina rufe baki sai ga sarkin yaƙi Dargazu ya zo gaban mu, ya dubi Sarauniya Nadiya cikin fushi ya ce, 

‘Nadiya, wannan wane irin ɗanyen aiki ne haka kika shuka? Me kike nufi da ƙaddamar da wannan baƙo a matsayin yarima?”

Kafin ya gama maganar sa, sai Sarauniya Nadiya ta tari Numfashinsa da cewa, 

“Kana iya yin duk waɗannan tambayoyi a ranar taron gani, Dargazu.” 

Wannan amsa da ta bashi ba ita yaso ba, amma sai ya yi shiru, can kuma sai ya ce, 

‘Koma dai menene kike shiryawa, ki sani cewa ba zai taɓa yin tasiri ba, da yardar abar bauta.”

 Daga nan kuma sai ya kalle ni, sannan ya ci gaba da cewa, 

“Bar ganin ka bar ‘yata da ranta, kada hakan yasa ka yi tunanin gabar mu ta yanke kenan, ƙaruwa ma ta yi, ita kuma Dardira zata bayyana min yadda aka yi har ɗan tatsitsin mutum kamar ka ya samu galaba akanta cikin sauƙi haka.” 

Ko da ya gama rattabo zancensa, sai na yi murmushi sannan na ce da shi, 

‘Kada ka damu, nima haka na ɗauke ka, amma ‘yarka ta yi ƙoƙari domin jaruma ce ta gaban kwatance, sai dai ta kasa samun abinda ya kamata ace ta samu, wannan shi ne matsalarta.” 

Dargazu ya yunƙura da nufin ya mazge ni, kawai sai gani muka yi wata katangar gilashi ta raba tsakanina da shi, ko da ya bugu da jikin wannan katangar gilashi, sai ta yi mishi shokin kamar wutar lantarki, dole ya ja da baya, sannan ya ja Dardira suka wuce.

Shi kuwa wannan mutumin na huɗu wanda bai duƙa min ba, kallona kawai yayi ta yi har ya fita ba tare da ya ce min komai ba. Bayan fitarsa ne sai Sarauniya Nadiya ta waigo gare ni ta ce da ni, 

“Ka yi haƙuri Haidar, wannan ba ita bace haɗuwar da na yi tsammanin zata faɗo mana a rayuwa, sai dai masu iya magana dama sun ce, ƙaddara ta riga fata, ka yi haƙuri da duk wani irin ƙalubale da za ka fuskanta, ina tare da kai komai wuya komai rintsi, kuma na yi maka alƙawarin goya maka baya akan ko me ka zo da shi, saboda zan iya yin komai saboda kai.” 

Waɗannan kalamai na Sarauniya Nadiya sun sa jikina ya yi sanyi kuma na faɗa kogin tunanin ma’anar maganarta. Ban kai ga samo komai ba, sai na ji tana cewa wannan baƙuwar jarumar, 

“Ki kula min da shi, kada ki bari ya mutu!” 

Ita kuma sai ta yi murmushi sannan ta ce, 

“Zan yi iya ƙoƙarina, amma ki sani, Haidar fa ba ƙaramin ɗan jarfa bane, da wuya ya yi tsawon kwanaki uku ba tare da an kashe shi ba.” 

Ko da ta zo nan a zancenta, sai Sarauniya Nadiya ta yi mata godiya sannan ta ƙara baiwa Sadiya haƙuri, ganin haka yasa nace, 

“Barka dai Sarauniya, gani nan fa da raina, ya naji kuna ta maganar mutuwa ta ne?” 

Sarauniya Nadiya ta yi tattausan murmushi a gareni sannan ta ce, “Ɗan uwa, na yi matuƙar kewar ƙiriniyarka, ka kula da kanka.” Daga nan ba ta sake cewa da mu komai ba sai kawai ta wuce ta bar mu a tsaye. Har ta yi nisa sai na tuna da wani abu mai muhimmanci, don haka sai na kira sunanta, hakan yasa ta tsaya sannan ta waigo. Na ƙarasa wajenta a hanzarce sannan na bayyana mata buƙatata ta a saki Imran mu tafi tare da shi. Ba tare da nuna wata damuwa ba ta sa wasu dakaru suka je suka kawo Imran. 

Bayan an kawo shi ne sai wannan baƙuwar Jaruma ta yi mana jagoranci zuwa ga wani ƙaton keken doki da ke ƙofar fadar wanda wasu manya-manyan dawaki guda huɗu ke ja. 

Daga nan sai muka shiga cikinsa mu huɗun duka, wato ni, Sadiya, Imran da kuma wannan baƙuwar jaruma, wani bawa wanda yake gaban keken dokin ya ja akalar dawakan muka fara tafiya zuwa inda Allah ne kaɗai ya sani.

Masu karatu kafin in kai ku da nisa, zan so a daidai wannan gaɓa in baku ɗan taƙaitaccen tarihi na, wataƙila hakan zai sa ku fahimci wasu al’amura dangane da ni a cikin wannan labari nawa me ban mamaki. 

*****

Wane Ne Haidar Ɗan Hammadi?

Kamar dai yadda kuka sani, sunana Haidar kuma sunan mahaifina Hammadi. Ni haifaffen garin Kaduna ne. Mahaifina ya kasance hamshaƙin ɗan kasuwa kuma attajirin gaske. A ƙalla yana da shaguna kusan guda sittin a cikin garin Kano kawai, banda sauran jahohi da kuma wasu rassan kasuwancinsa da ke ƙasashen da ke maƙwabtaka da ƙasar Nijeriya. Matarsa ɗaya ce jal a duniya, wato mahaifiyata mai suna Murjanatu.

Hammadi Enterprises shi ne asalin sunan kamfanin mahaifina, kuma kamfanin na siyar da kaya iri daban-daban tun da ga talakalma har zuwa sauran kayan amfanin gida da na gini da dai sauransu. Ni kaɗai iyayena suka haifa, hakan yasa na samu cikakkiyar gata a wajen su, ko me nake so ana yi min. Kayan sawa kuwa, idan aka yi min wanki da guga sai in yi watanni biyu ina sakawa ba su ƙare ba. A taƙaice dai babu abinda na nema na rasa a duniya. Sai dai kuma in da matsalar take shi ne bana maida hankali a karatu ko kaɗan. An canja min makaranta ya fi sau ashirin, ga ni da zuciya. Yaro ko kallon banza ya yi min yanzunnan sai in kama shi in bashi kashi. In kuwa malami ya sake ya doke ni ko kuma ya bani wani horo, sai in narke mishi in ce bani da lafiya a yi ta kace-nace. Wani lokaci kuma in tayar da hayaniyar duk makarantar sai kowa yasan an taɓo ni. Wani babban abu kuma shi ne, bana jin nauyin faɗa wa babba magana komai girman shi, domin bana shakkar kowa tunda na san muna da kuɗi kuma su ke magana. Na zama dai taƙadari lamba ɗaya. Duk wani abu da ya shafi ƙiriniya ko rashin jin magana ina wurin.

A haka har na fara girma amma ban daina ƙiriniyar ba, ko da yake na ɗan fara maida hankali a kan karatu, rikici da mutane fa kam babu sauƙi sai na Allah. Yau in daki ɗan wannan, gobe in mari wancan. Har dai abin ya damu mahaifina. Don haka, watarana lokacin ina ɗan shekara goma sha huɗu sai ya kirani yana min nasiha da cewa, 

“Ya kai ɗana, haƙiƙa na so ace ka zamo wani irin mutum na daban saɓanin irin wanda kake ƙoƙarin zama a yanzu, na so ace ka zama hamshaƙin malami, ɗan kasuwa ko kuma wani ƙwararre a ɗaya daga cikin fannonin ilimin zamaninka. Wannan yasa nake ta iya ƙoƙarina wajen ganin ban tauye ka ta kowane fanni ba. Sai dai kash! An yi rashin sa’a, hankalinka ba anan yake ba. To ka sani cewa, ba zan yi maka baki ba, kuma ba zan hana ka zama irin mutumin duk da kake son zama ba, amma ka sani cewa, kowane irin mutum kake so ka zama a duniya yau sai ka tashi tsaye, domin Hausawa suna cewa ‘Himma bata ga rago.’ 

Ko da mahaifina ya zo nan a zancen sa, sai na yi shiru ban ce komai ba. Bayan wani lokaci sai na kalle shi sannan na ce, 

‘Abba ban fahimci abinda kake nufi ba, shin ko za ka yi min bayani domin na fahimta?

Yayin da ya ji wannan kalami nawa sai ya yi murmushi, sannan ya ce, 

“Shin ba kai rigimamme bane? Shin ba kai taƙadari bane? Kai mara ji ko? Kai fitinanne ba? To ka sani cewa, kai ba komai bane face ɗan tatsitsin mara ji wanda bai kai a tsaya ma a kalle shi ba, a taƙaice dai, da za a kwatanta ka da sauran taƙadiran zamaninka, to za ka samu cewa kai ba komai bane face ɗan ƙaramin kifi a cikin teku. Lallai ne in kana so ka zama taƙadari sai ka canja salonka, don ba zan amince da ɗana ya zama komai ba a kowane fanni face gagara-ba-dau. Don haka zan taimaka maka ka zama fitinanne da wataƙila babu kamar sa a cikin wannan zamani naka, amma bisa sharaɗin cewa za ka bi duk umurnin da na baka ba tare da gardama ba.”

Ko da mahaifina ya zo nan a zancensa, sai hankalina ya tashi na rasa wace amsa zan bashi. Domin ni ko a tarihi ban taɓa jin labarin mahaifin da ya taɓa nunawa ɗansa amincewarsa kan rashin jin da yake yi ba, balle ma har ya ce zai taimaka masa wajen zama gagararren da babu kamar sa. Eh, tabbas nasan cewa ni mara ji ne, tun da kusan kowa ma haka yake faɗa, akwai wuraren da ma in na je ana ganina sai ka ji ana cewa ‘amma da ganin wannan baya jin magana’ saboda ko tafiyata ka gani kasan akwai magana. Wasu ma har cewa suke yi ina da aljanu. Sai dai kuma fa, tabbas zan ji daɗi idan aka ce na zama wanda ya fi dukkan sauran marasa ji kangara, domin ko ba komai dole a girmama ni,wannan shi ne tunani na a wancan lokacin.

Don haka sai na ce,

“Abba kana nufin kenan zan iya yin dukkan abinda na ga dama, kuma ba za ka yi fushi da ni ba?”

Kun san yaro, musamman mara jin magana, babu abin da ya fi so sama da ya samu ‘ƴancin yin abinda ranshi yake so, don haka wannan shi ne abinda ya fi damu na a wancan lokacin. Yayin da mahaifina ya ji wannan tambaya tawa sai ya yi dariya sannan ya ce da ni, 

“Tabbas za ka samu damar yin duk abinda kake so, amma ba yanzu ba, dole sai bayan na kammala baka horon da nake so tukun, don haka shin ka amince da sharaɗina?” 

Na sake yin shiru ina tunani, wata zuciyar na ce min ‘kawai ka amince, wataƙila ma horon da za a bama ka bai wuce shara ko gugan leda ba ka ga daga nan sai ka je ka yi duk abinda kake so’ yayin da wani ɓangare kuma na zuciyata ke yi min gargaɗi da cewa ‘kada ka sake ka amince, wa ya sani ma ko wani aiki ne mai wahala za a sa ka?’ Daga Ƙarshe dai na bi shawara ta farko, wato na ce na amince. Kaico! Babban kuskuren da na fara yi kenan a rayuwata. Domin sai da na yi da na sanin ma fara yin ƙiriniya a rayuwata.

Albishir na farko da mahaifina ya fara yi min bayan na amince da sharaɗinsa shi ne daga wannan ranar ba zan ƙara zuwa makaranta ba, sannan an sa min dokar hana fita na tsawon wata uku. Na san wasu daga cikin ku in suka ji wannan maganar za su yi murna da cewa ai wannan cin banza ne tun da za su zauna a gida su yi abinda ransu ya ke so, ayya! abinda ba ku sani ba shi ne, wannan duk ‘somin taɓi ne.’ 

Tun daga wannan rana na fara shiga tashin hankali da bala’i kai ka ce ba sona mahaifina ke yi ba. Da fari dai an fara ne da abu kamar wasa, domin washe gari mahaifina ya kira ni falonsa, bayan mun gaisa sai ya ce in zauna kusa da shi. Bayan mun zauna sai ya saka mana wani fim ɗin Amurka mai suna DISTURBIA. Bayan mun gama kallo sai ya ce in je in yi mishi sharhin fim ɗin tare da bayyana abinda na fahimta a cikin fim ɗin kuma kada ya gaza shafuka shida na turanci da na Hausa. Nan fa ido na ya raina fata, saboda bana son rubutu a rayuwata. Fim ɗin yana magana ne akan wani yaro mara jin magana, amma da na je yin bayani sai gashi na kakare. Wai ni nan mai wayau, kawai sai na je na yi wasu ‘yan surutan banza kawai na kawo. Haba ai ko da na kawo ya karɓa ya gani sai ya ajiye littafin akan teburin da ke gaban shi, sannan ya miƙo min wata jarida da na taras yana karantawa ya ciro shafuka shida ya ce in je in kwafe rubutun da ke jiki tsaf daga bango zuwa bango. kwana huɗu nayi ina kwafe wannan rubutu, kai in taƙaice muku zance ma dai sai da hannuna ya yi ruwa kamar zai daina aiki, ya dinga min ciwo, amma ba tausayi hakanan sai da na kwafe rubutun jaridar nan tas! Daga nan kuma sai ya ɓullo da wani sabon salo, kullum zamu kalli fina-finai guda uku, kuma kowanne sai na yi mishi sharhi na kawo ya sa hannu.

Daga nan kuma sai ya fara sani ina karanta littafai, ko na turanci ko na Hausa. Su ma kuma duk wanda na karanta sai ya sani na yi sharhi tare da jiggan bayanai akan labarin littafin. Mai yiwuwa ka yi mamakin jin duk mahaifina yana lura da ni yayinda na ke gudanar da waɗannan ayyuka da yake saka ni, kada kayi mamaki domin tun daga ranar da muka yi wannan magana mahaifina ya daina zuwa kasuwa. Kasancewarsa hamshaƙin ɗan kasuwa kuma mai kuɗin gaske, sai ya sakarwa yaransa ragamar kasuwancinsa gaba ɗaya, hakan yasa kusan ko da yaushe yana gida tare da ni. Sallah kaɗai ke fitar da ni waje, ita ma tare muke zuwa kuma tare muke dawowa ba halin yin magana da kowa. Ita kuwa mahaifiyata, dama bata faye yawan surutu ba, bata ce mana komai sai dai kawai in ta nishaɗu ta zo ta zauna tana kallon mu ko kuma itama ayi kallon da ita. In kuwa ba haka ba, to tana ɗaki tana ibada, karatun ƙur’ani mai girma, ko sallah ko wuridi. Idan kuwa wata magana za su yi ko za su fita wani waje to mahaifina zai tabbatar da cewa ya bani ƙasurgumin aikin da har su dawo ba zan iya gamawa ba kafin su fita.

Kamar fa wannan bai isa ba, sai iyayena kuma suka koma koyar dani karatu da kansu, amma kullum darasi biyu kawai ake min, na addini da na zamani. Sai dai fa a biyun nan babu wani alamun sauƙi a cikin al’amarin. Kullum sai an haɗa ni da aikin aji da na gida. Sannan ga maganar sharhin fina-finai da na littatafai. Ga kuma wata tsirfa da mahaifina ya ɗauka na cewa kullum sai na karanta manya-manyan jaridun ƙasar da ke fita. Kullum bani da wani takamaiman lokacin hutu. Ana bani awa ɗaya da rabi in yi bacci da rana a kullum, daga nan sai aiki kawai. In dare ya yi bana bacci sai ɗaya da rabi, kuma ban isa in kwanta ba sai na yi sallar dare. Azumin Litini da Alhamis kuwa wannan dama dole ne.

Duk abinda nake so, da zarar na yi magana za’a siya min saboda akwai kuɗin. Da na ce abu kaza nake so nan take za’a je a kawo min. In kaya na ce ina so take mahaifina zai hau yanar gizo ya ya buɗo su in zaɓa waɗanda nake so ya siya min su, sai dai kawai a kawo min su har gida. In kuwa na sake aka bani wani umurni ban yi ba ko na nuna gazawa ta, to a wannan rana sai na gwammace kiɗa da karatu.

Kafin watanni ukun nan su cika a ƙalla ba zan iya bayyana yawan fina-finai ko littafan da na karanta ba, amma a hankali sai na fara fahimtar cewa, dukkan fina-finai da littafan da mahaifina yasa ni nake kallo ko karantawa suna ƙunshe ne da labarai na matasa ko yara marasa jin magana irina, tare da irin ƙalubalen da suke fuskanta da kuma irin hanyoyin da suka bi har suka kai inda suka kai, da kuma irin kura-kuran da suka biyo bayan wasu zaɓuɓɓuka nasu da dai makamantansu. A sannan ne na fara fahimtar ashe lallai ban ma san mecece duniya ba, ban ma san waye ni ba. Ban san menene ma taƙadiranci ba.

Kalle-kalle, karance-karance, rubuce-rubuce da kuma darussan da mahaifana ke koya min a kullum suka sa kafin ƙiftawa da Bismillah na fara zama irin mutumin nan da turawa ke kira GENIUS! Bayan dokar ta ɓacin da aka saka min ta rashin fita ta ƙare, sai mahaifina ya siyo min wata waya mai kyau ‘yar yayi. Shi da kanshi ya nuna min yadda ake amfani da ita, da yadda zan buɗe adireshin Imel da duk wata kafar sadarwa da ake iya amfani da ita. Ya kuma sa min Alƙur’ani mai girma da kuma sauran manyan littatafai da karatuttukan manya da ƙananun Malamai. Suma in kuka ji yadda na sha azaba a kansu sai kun tausaya min. Daga nan kuma sai ya fara fita da ni zuwa wajen harkokin yau da kullum. Idan yau muka ziyarci mahauta, gobe sai mu ziyarci ‘yan koli, jibi kuma mu je wajen masu wasa da maciji ko wani abun dai can daban. Duk inda muka je muna yi musu wuni ne, idan muka dawo kuma a sani yin sharhi akan abinda muka gani ko muka ji.

A taƙaice dai masu karatu, sai da ya zamana na samu ilimummuka masu yawa daga yawace-yawacen da muke fita da mahaifana fiye da littatafai ko fina-finan ma da nake karantawa ko kallo. Domin Hausawa na cewa gani ya kori ji. Wannan dalili yasa na fara canja ra’ayina na son ganin na zama gagararre, fitinanne ko mara jin magana, domin zuwa wannan lokacin kuma na fara fahimtar cewa ruwan fa ba tsaye.

Wataƙila wasu daga cikinku su yi mamakin yadda ra’ayina ya sauya haka cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, to kada ma ku yi mamaki. Domin ni kaɗai na san me na hango a sanadiyyar darussan da na koya. Idan wani ya ji wannan labari, mai yiwuwa yace lallai Haidar ka ga abubuwa da yawa a rayuwa, ayya! ai wannan in ka ji wasa fara girki kenan! Domin kamar yadda nake sa ran cewa izuwa yanzu kun fara sanin irin salon mahaifina, wannan duk bai isa ba, don haka sai ya sake fito da wani sabon salon.

Wannan sabon salo kuwa ba komai bane face atisaye, wato motsa jiki. Kamar yadda na faɗa muku a baya, mahaifina ƙasurgumin attajiri ne, don haka ba ma matsalar kuɗi. Da fari dai ya fara jana fita gudu ne a kowace rana, daga gida in muka fita ba ma tsayawa sai munyi kamar awa uku muna gudu. Haka nan da yamma ma sai mun sake waɗannan awoyin. Ashe duk wannan fitar yana ɗan fara koya min ne kawai. Watarana da safe, bayan mun dawo daga masallaci, mun shirya tsaf domin fita gudun da muka saba, sai na ga ya ja ni zuwa wani ɓangare na cikin gidan mu wanda na daɗe ban je wurin ba, saboda ba lokaci. A iya sanina da wannan waje ba komai face wata tsohuwar mota mai siffar kwaɗo da mahaifina ke so sosai ya ajiye ta a wurin yana zuwa kallonta lokaci bayan lokaci, sai kuma tarin yashi da aka tara da nufin yin wani aiki da ban san ko na menene ba, amma bisa mamakina, ko da muka ƙaraso inda a da wannan mota take, sai na ga wani ƙaton gini ya bayyana a wurin. To yaushe aka yi wannan ginin? Na faɗa a raina 

Ginin ya yi matuƙar ƙeruwa, bene ne hawa ɗaya an yi mishi zubi irin na yayi. Har na buɗe baki domin in tambayi mahaifina yadda aka yi wannan gini ya wanzu a wannan waje, amma sai na yi shiru. Domin a daidai wannan lokaci ne ya kama hannu na muka shiga cikin wannan waje. Shigar mu ke da wuya sai na saki baki ina kallon ikon Allah. Ba komai na gani ba face wani jibgegen falo wanda ban taɓa ganin falo mai faɗinsa ba, domin ya yi girman garejin mota. Cike da falon nan kuwa ba komai bane face kayan motsa jiki kala-kala, wasu ma ko labarin su ban taɓa ji ba. A gefe kuma sai na ga wani mutumi a zaune, ko da mutumin ya ganmu sai ya taso ya tarbe mu da fara’arsa. Bayan mun gaisa da shi cikin harshen turanci, sai kuma suka canja yare shi da mahaifina. Bayan sun daɗe suna tattaunawa, sai mahaifina yake sanar da ni cewa wannan mutumin likita ne babba a ƙasar jamus, kuma ya zo ne musamman domin ya duba lafiyata kuma ya bamu shawarwari dangane da yadda ya kamata mu fuskanci horaswar da ke gaban mu.

Bayan likitan ya yi min gwaje-gwaje iri daban-daban kamar ba zai daina ba. Sai ya buƙaci da in je in hau ɗaya daga cikin injinan motsa jikin da ke cikin wannan tafkeken falo, bayan na motsa jikina na tsawon mintuna talatin, sai kuma na dawo likitan ya ƙara yin wasu gwaje-gwajen. Daga nan sai su lka yi sallama da mahaifina ya shige cikin wani ɗaki da ke dama da tsakiyar wannan falo. Nan shi kuma mahaifina ya fara zagayawa da ni yana min bayanin kowane inji da ke cikin falon da yadda yake aiki da kuma amfanin shi , sai a wannan lokaci ne na fahimci cewa ashe wurin motsa jiki mahaifina ya haɗa a cikin gidanmu.

Daga nan kuma sai ya kai ni hawan da ke sama inda can ma sai da na saki baki saboda ƙawatuwa da wajen yayi, a nan ne yake bayyana min cewa daga ranar komai nawa zai dawo nan har zuwa ƙarshen wannan shekara, anan zan dinga kwana a nan zan dinga komai nawa. Da farko na yi tunanin ko na fara samun ‘yancin kaina ne, amma ina, ko kaɗan!

Tun daga wannan rana, sai mahaifina ya canja min irin abincin da zan dinga ci bisa shawarar likitan sa. Motsa jiki kuma babu kama hannun yaro, ɗaga ƙarfe, gudu, tsalle-tsalle da sauran su kullum aikin kenan! A kowane ƙarshen mako kuma wannan likitan yakan zo ya duba lafiya ta. A ƙalla kullum ina samun horaswa na tsawon awa takwas. Kada fa ku yi tunanin wai zancen ya ƙare daga nan! Mahaifina sai kuma ya ɗauki salon koya min salon faɗa iri daban-daban. Kokawa ne, dambe ne, kareti ne, Judo, Kung Fu, Jujitsu da ma dai sauran su waɗanda tsayawa ma bayyana sunayensu bashi da wani muhimmanci domin zamu iya kwana ba mu gama ba. Na yi matuƙar manakin yadda ya iya wasu abubuwan don ban taɓa tunanin ya iya ba saboda yanayin sanyin jikinshi a mafi yawancin lokuta. Abu ɗaya ne jal mahaifina ya ƙi koya min, shi ne faɗa da makami. Ko kaɗan ya ƙi yarda da in taɓa makami.

Ganin cewa na iya salon faɗa iri-iri sai ya sani na fara jin kaina da cewa ni wani ne, don haka bani da wani burin da ya wuce wani ya takale ne mu gwabza, kamar mahaifina ya fahimci hakan sai ya fara jana izuwa majalisin malamai daban-daban muna zama muna ɗaukar karatu, a irin wannan hali ne na samu damar haɗuwa da manya-manyan malaman ƙasata, ciki kuwa har da waɗanda aka kashe yanzu basa raye, da fatan Allah Ya jiƙansu Amin.

Wa’azozin da muke saurare a kusan kullum sai suka sa ni kuma na fara gudun duniya, domin a duk lokacin da na ji wani wa’azin da ya shafi mutuwa, sai in ga rayuwar ba’a bakin komai take ba. Bayan an samu kimanin wata shida muna haka, sai kuma mahaifina ya sake fitowa da wani sabon salon. Shi ne, Watarana kawai sai ji na yi yace min in shirya zamu je wani ƙauye ziyara. Na haɗa kayana kuwa muka shiga mota. Sunan wannan ƙauye da muka je Fanturawa, kuma manoma ne mutanen garin sosai ba kaɗan ba. Bayan mun sauka a gidan wani abokin shi mai suna Shitu. Sai mahaifina yake bayyana min cewa zai bar ni ne a garin in ɗan yi wasu kwanaki.

Haka kuwa aka yi, bayan mun yi kwana ɗaya a garin sai mahaifina ya koma gida ya bar ni a wannan garin. Nan aka fara zuwa da ni gona, dama lokacin damina ne, ga shi shuka ya fara girma. Kullum za mu je gona da sauran yaran malam Shitu, su ne ma suke koya min harkokin sha’anin noma. Har ma ya zamana mu kan yi wata waƙa mai daɗi kamar haka:

Yabanya ta yi shar-shar

Furanni sun yi luf-luf

Damina ta kankama

Muna godiya wurin sarki. 

<< Birnin Sahara 7Birnin Sahara 9 >>

12 thoughts on “Birnin Sahara 8”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×