Abu wasa-wasa dai sai da na yi wata uku a wannan ƙauye ba tare da mahaifina ya ziyarce ni ba, sai dai lokaci bayan lokaci muna yin waya da shi. To a wannan garin ne muka haɗu da Nadiya, tun daga ranar da na ɗora idanuwana akanta duniyata ta canja, domin tun daga wannan lokaci murmushina ya ƙaru saboda ita. Wasu halayen da ban taɓa tunanin zan koye su ba sai gashi ina yinsu kamar dama can halina ne. Komai nata ya yi min daidai, mu sammaan idanuwanta da ke ɗauke da wasu sirrika da babu yadda ban yi ba wajen ganin na gano su amma na kasa. Babban abin da ya fi jan hankalina game da ita shi ne irin yadda take iya isarwa da mutum saƙo ba tare da ta furta ko da kalma guda ɗaya ba.
A wancan lokacin ta bayyana mana cewa ita ɗaliba ce da take karantar ilimin Noma da Kiwo don haka aka turo ta wannan ƙauye domin ta fahimci al’amuran noman karkara in yaso sai ta haɗa shi da ilimin da ta yi na zamani domin fitar da shawarwari dangane da yadda za a inganta noman mutanen karkara. Kasancewar bata jin Hausa sosai (a yadda ta nuna a wancan lokacin), kuma aka ci sa’a ni ina jin turanci, sannan kuma a gidan malam Shitu ta sauka, Wannan dalili yasa muka shaƙu da ita sosai, har dai abin ya kai ga na bayyana mata abinda nake ji dangane da ita a cikin zuciyata, amma sai ta maida abin wasa tare da nuna min cewa a matsayinta na kirista(kamar yadda ta faɗa), ba lallai bane iyayenta su amince da ni da dai wasu dalilai makamantan haka. Sai dai kuma hakan bai hana mu shaƙuwa da juna a matsayin abokai ba.
Muna cikin wannan hali ne mahaifina ya zo domin ya maida ni gida. Babu yadda banyi ba domin Nadiya ta bani ko da lambarta ne domin mu dinga gaisawa amma ta ƙi, a taƙaice ma dai baran-baran muka rabu saboda na matsa kan sai ta bani lambar. Wannan shi ne ƙarshen gani na da Nadiya, amma fa har yanzu sonta bai gushe ba daga cikin zuciyata.
Bayan mun dawo gida bai fi da wata biyu ba sai cutar ajali ta kama mahaifina, har ya zamana an kwantar da shi a asibiti. Likita ya tabbatar mana da cewa ciwon hanta ne ya kama mahaifin namu, kuma abu ne mawuyaci ya rayu, sai dai wani hukuncin Allah kuma.
Maimakon hankalin mahaifinmu ya tashi, sai na ga ko gezau ma bai yi ba, amma ita mahaifiyata gaba ɗaya rikicewa ta yi, da ƙyar na samu na lallaɓeta. Sai dai ni kaina a wannan lokacin hankalina a tashe yake, amma bana iya bayyanawa a fili. Bayan kwana uku da kwantar da mahaifina a asibiti, watarana ina zaune a gefen gadonsa muna hira. Sai ya ɗago kai ya ƙura min ido ƙuriii kamar ba zai daina ba. ganin hakan yasa jikina ya yi sanyi, amma sai na yi ta maza na tambaye shi da cewa,
“Abba da akwai wani abu da kake buƙata ne in kawo maka?”
Ko da mahaifina ya ji wannan tambaya sai ya yi murmushi sannan ya ce in tayar da shi zaune. Bayan na zaunar da shi tare da sa masa matashi a bayansa ta yadda zai ji daɗin jingina. Sai ya ce min in zauna kuma in natsu da kyau zai faɗa min wata magana mai muhimmanci, a daidai wannan lokaci kuma zuciyata tana riya min cewa wannan ce maganata ta ƙarshe da za mu yi da mahaifina.
Bayan na zauna, sai ya sake kallo na da kyau sannan ya ce da ni,
“Ya kai ɗana, ka sani cewa maganar da za mu yi da kai a yanzu, ta fi duk wata magana da muka taɓa yi da kai muhimmanci, don haka ina so ka natsu da kyau ka ji abinda zan faɗa maka. Kafin dai mu yi nisa, ina so ka sani cewa wannan magana da zamu yi yanzu ita ce nasiha kuma wasiyyata a gareka, don haka bana so ka ɓata min zance na da kuka ko wani abu makamancin haka, domin yanzu kai ba yaro bane, kuma dukkanmu mun san cewa mutuwa tana kan kowa. Da farko ina so ka sani cewa ina matuƙar alfahari da kai a matsayinka na ɗana, sannan ina mai godiya ga Allah da ya bani ɗa irin ka. Domin ko ba komai ka yi min biyayya matuƙa gaya, irin biyayyar da a farkon rayuwarka in wani ya ce za ka yi min irin lta ba lallai bane in yarda, haƙiƙa ina matuƙar alfahari da kasancewarka ɗana, Allah ya maka albarka.”
Bayan ya ɗan numfasa, sai ya ci gaba da magana da cewa,
“Ya kai ɗana, ka sani cewa na yafe maka duk wani laifi da ka yi min bisa kuskure ko kuma da gangan, kuma nima ina fata za ka ka yafe min duk wani laifi da na yi maka ko kuma wani abu da na gaza yi maka a rayuwa a matsayina na mahaifinka, haƙiƙa Allah ya sani, na yi iya abinda zan iya yi maka, sai dai kuma ɗan Adam ba a iya masa, mai yiwuwa na tauyeka ta wani Fannin ba tare da na sani ba.”
A wannan lokaci idanuwana sun cika taf da hawaye, jira kawai suke su fito. Har na buɗe baki domin in bayyana mishi cewa ni bai taɓa yi min wani laifi ba sai ya dakatar da ni ta hanyar ɗaga min hannu. Sannan ya ci gaba da cewa,
“Ya kai ɗana, ka sani cewa na fuskanci ƙalubale iri daban-daban a rayuwata, amma jikina yana bani cewa za ka fuskanci ƙalubale a rayuwarka ta gaba irin wanda ko ni ban taɓa fuskanta ba. Na samu jin daɗin rayuwa fiye da mafi yawancin mutanen zamani na, amma jikina yana bani cewa zaka samu fiye da haka, na samu tarin dukiyar da ni kaina ban san irinta ba, amma jikina yana bani cewa nan gaba sai ka ninka ni kuɗi sau ba iyaka. Na samu shahara da ɗaukaka matuƙa, amma jikina yana bani cewa za ka samu ɗaukaka irin wacce ban taɓa samun irin ta ba. Wannan yasa na ke so in baka wasu ‘ƴan shawarwari da za su iya taimaka maka yayin da ka tsinci kanka a cikin irin wannan matsayi, domin ba lallai ne in yi tsawon rai ba balle in sa ka a hanyar da ta dace.”
“Abu na farko ina so ka yarda da Allah, ka yarda da duk wata ƙaddara da ta same ka, ka yarda da cewa Shi ne ke da ikon komai, Shi zai kare ka kuma shi kaɗai ne zai iya baka duk abinda kake nema. Ka zama mai maida komai naka zuwa gare Shi, ka zama mai dogaro da Shi, ka zama mai miƙa duk al’amuranka gareshi, tabbas Shi kuma zai yi maka komai a rayuwar ka. Abu na biyu, ka kiyayi hassada, lallai ita cuta ce mai wuyar magani, don haka ina maka gargaɗi da ka guje ta. A duk lokacin da ka ga wani mutum da wani abu wanda kake so, to ka roƙi Allah ya baka wannan abun idan har alkhairi ne a gare ka, in kuma ba alkhairi bane ya musanya maka da mafi alkhairi. Sannan ka sani cewa, ka fi wani shi ma wani yafi ka, kuma ba za ka taɓa samun dukkan abinda kake so ba. Abu na uku, ka zamo mai tausayi da kuma kyautatawa jama’a iya ƙarfinka, domin rayuwar nan bata da tabbas, kuma duk abin da ka tara watarana za ka tafi ka barshi, duk matsayin da ka kai dole watarana zaka sauka, a ƙarshe dai kamar yadda ake binne kowa a ƙasa, kaima a cikin ƙasar za a binne ka.”
“Sannan ina horon ka da ka zamo mai gaskiya a dukkan lamuranka, lallai ita ƙarya tana jawo bala’i iri-iri a tsakanin mutane. Ka da ka raina ilimi, ka da ka raina kowa kuma kada ka yarda kowa ya raina ka. Ka da ka cuci kowa, kaima kuma kada ka yarda wani ya cuce ka. Kada ka haɗa kanka da kowa. Ka da ka zamo mutum mai yawan tsammani, ka yarda cewa komai na iya faruwa a ko’ina kuma a koyaushe. Ka tausaya wa na ƙasa da kai, kuma ka girmama na sama da kai. Ka guje wa son zuciya, musamman a yayin yanke hukunci. Ka zamo mai yawan yi wa mutane uzuri tare da basu dama a karo na biyu, kuma ka kiyaye saurin zargi ko yanke hukunci. Lallai in ka yi koyi da waɗannan abubuwa, ina sa maka rai cewa al’amura za su yi maka sauƙi, amma fa ka sani, tabbas rayuwa bata da sauƙi, musamman ga mutumin da ya kasance mai nasaba da suna irin naka.”
“Suna irin nawa kuma? Kamar yaya kenan Abba?”
Na tambaye shi cike da mamaki.
Mahaifina yayi murmushi har sai da na manta na ɗan wani lokaci cewa bashi da lafiya, sannan ya ce,
“Haidar, sunan ka yana nufin zaki, zaki kuwa a koda yaushe ana alƙanta shi ne da abubuwa masu wahala guda biyu, su ne jarumta da da mulki. Sai dai ina so ka sani cewa jarumi ba ya nufin mutum mai ƙarfin damtse ko mai taurin rai kawai. Jarumi shi ne mutumin da ya ke iya yin murmushi da dariya a lokacin da yake cikin baƙin ciki, Jarumi shi ne mutumin da yake iya yafe abin da aka yi mishi na ɓatanci ko da kuwa yana da damar ramawa, Jarumi shi ne wanda yake miƙawa wanda ya bashi guba nunanniyar tuffa domin shi ya ci ya rayu cikin ƙoshin lafiya duk kuwa da cewa shi wancan ɗin ya nufe shi da mutuwa. Jarumi shi ne wanda yake cika alƙawari idan ya ɗauka, Jarumi shi ne wanda baya juyawa nashi baya komai rintsi da tsanani, Jarumi shi ne mai miƙawa maƙiyinsa hannu domin su yi musabaha ko da kuwa shi maƙiyin nasa ya jefo shi da mashi ne. Lallai ka tuna da wannan.”
Shi kuwa mai mulki, baya nufin shugaba kawai wanda zai ce a yi kaza a bar kaza. Shugaba shi ne wanda yasan haƙƙin na ƙasa da shi kuma yake ƙoƙarin kare mishi wannan haƙƙin ta ko’ina. Shugaba shi ne wanda ya damu da damuwar waɗanda yake shugabanta fiye da damuwar kanshi. Shugaba mutum ne wanda ke sadaukar da komai nashi domin al’ummar shi.”
“Abu na ƙarshe, ka sani cewa daga yau, baka buƙatar sai na ce maka yi kaza ko bar kaza, daga yau ka samu cikakken ‘yancin da za ka iya yin duk abinda ka ga dama, amma kada ka manta da nasiha ta, kuma kada ka manta da ko kai waye. Abu mafi muhimmanci kuma shi ne kada ka manta da Allah a duk inda kake.”
Da wannan kalami ne mahaifina ya yi shiru ba tare da ya ƙara cewa komai ba. Nan fa na ji kaina yayi dumm! Maganganun da ya faɗa min suka fara safa-da-marwa a cikin Ƙwaƙwalwata. gashi dai yau burina ya cika na samun ‘ƴanci da damar yin duk abinda na ga dama, amma a wane irin farashi? Ina cikin wannan tunani ne sai mahaifiyata ta shigo ɗakin da mu ke, dama ta je kawo mana abinci ne daga gida. Ko da shigowarta sai na tashi na gaisheta jikina a sanyaye sannan na bata wuri ta zauna. A wannan lokaci ne ta ce in je cikin mota in ɗauko mata kayan da ta zo da su . Da fitata ko minti biyu ba’a yi ba na dawo, amma ina shigowa me zan gani? Mwhaifiyata ce take lulluɓe jikin mahaifina da mayafi yayinda take furta Inna lillahi wa Inna Ilaihir raji’un yayin da hawaye kuma suke zubowa a fuskarta. Ban san sa’ilin da na saki kayan da ke Hannuna ba na nufo inda suke cikin firgicin da ban taɓa shiga kamar sa ba.
In taƙaice muku labari dai, a wannan rana ce Allah Ya yi wa mahaifina rasuwa, a gabana aka suturce shi tsaf har aka binne shi. Haƙiƙa mahaifina ya tara mutane waɗanda ko da ace gwamna ne yake biki, to sai haka. Ba shi da ‘ƴan uwa, haka mahaifiyata ma bata da ‘ƴan uwa, amma saboda zaman lafiya da taimakon jama’a da ya wanzu yana yi a rayuwarsa, wannan yasa tun daga almajirai har shuwagabannin yankin mu sai da suka halarci jana’izarsa.
Lallai Ɗan Adam ba komai bane a wajen Allah, ko me ka tara, ko wani irin matsayi ka kai, a ƙarshe dai mutuwa za ka yi kuma babu wanda ya isa ya hana afkuwar hakan. Ya Allah Ka jiƙan mahaifina da rahama. Bayan rasuwar mahaifina ne sai mahaifiyata ta sake nisanta kanta da duniya, bata yin komai face ibadarta, abinda duk kuwa nace ya kamata a yi bata min musu ko jayayya kawai zata ce in yi kai tsaye. Hakan yasa nima na fara shiga ‘yar damuwa, domin na saba da in karɓi umurni ne ba wai in bada ba. watarana sai take bayyana min cewa ba zata iya ci gaba da zama a wannan gida da muke ciki ba, domin zai dinga tayar mata da hankali ne a duk lokacin da ta tuna da mahaifina,kuma gidan ya yi mata girma yanzu da babu shi. Hakan yasa muka siya wani ɗan ƙaramin gida a wata unguwar talakawa da ke nan cikin garin Kaduna muka zauna. Mun tare bai fi da wata biyu ba, sai wata maƙwabciyar mu mai suna Ikilima ta buƙaci mahaifiyar mu da ta ɗauke ta aiki domin ta dinga yi mata ‘yan aikace-aikace. Da ta nemi shawara a wajena sai ni kuma na amince, Ikilima ita ce mahaifiyar Sadiya, wannan dalili ne yasa muka saba da ita har ma akan zolaye mu da maganar soyayya, amma babu ko da wani abu makamancin hakan a tsakanin mu.
Kasancewa na ɗa ɗaya tilo da mahaifina ya haifa, hakan yasa kusan komai na harkar kasuwancinsa da kamfanoninsa suka dawo hannuna, amma ni sam basu dame ni ba. Don haka na bar ragamar kamfanin a hannun ma’aikatansa kawai, duk kuwa da cewa ni ne shugaban kamfanin a yanzu, in ba taro ya zama dole sai na je ba ne, bana ma maida hankalina ta kanshi. Hakan yasa na zama tamkar wani ɗan basaja, dalili kuwa shi ne, in dai ba taro zan je na manyan mutane ba, bana wani sa kaya masu tsada, bana hawa mota ko mashin, Keke kawai na siya nake hawa in je uzurina. Hakan yasa mutane da yawa ma ba su san ni ne ɗan gidan hamshaƙin Attajiri Hammadi ba, domin in da za ka ganni a hanya ma kana iya wucewa in wuce ba tare da kayi min kallo a karo na biyu ba. Ni kuma hakan ya fi min alheri domin bana son hayaniya.
Hakan ne ma yasa na koma ina amfani da sunan Kabir don in ɓadda sawu. Daga baya ne na nemi aiki a wani gidan biredi na fara aiki da su. Aka ɗauke ni a matsayin ma’aikaci. Ba neman kuɗi ya kaini ba domin ina da kuɗin siyan gidan biredin ma gaba ɗaya, kawai dai ina sha’awar aikin ne. Saboda duk kuɗin da na samu a wurin aikin ma kafin in dawo gida na rabar da ninkin su. A can kuma babban gida in da muka taso, na yiwa ma’aikatan ƙarin albashi sannan nace su ci gaba da aikinsu, bana komai a ciki face lokaci – lokaci da nake zuwa in motsa jiki in fice abina.
Kusantar mutane da nayi yasa na fahimci irin halin rayuwa da ake ciki a wasu wuraren. Hakan ya sa duk in da na ji ana buƙatar taimako nan da nan zan tura da tawa gudunmuwar a ɓoye ba tare da kowa ya sani ba, batun rashin ji kuwa? Manta ma kawai da wannan kaji, kawai dai lokaci bayan lokaci nakan taɓa saboda mutanen duniya wasu sai da hakan. Sai dai na ɗauki wata sabuwar ɗabi’a, ita ce barkwanci da zolaya, shi ma hakan na yi ne domin in lulluɓe damuwata da fara’a.
To ana cikin wannan hali ne fa, watarana muna ƙulla biredi a wajen aikin mu kawai sai na ji kamar an fisge ni haka, daga nan ban san me ke faruwa ba, kawai sai farkawa na yi na tsinci kaina a Birnin Sahara.
Duk wannan labarin na tunano shi ne yayin da muke tafiya a cikin wannan keken doki tare da su Imran, Sadiya da kuma wannan baƙuwar jaruma. Sai a wannan lokacin ne na lura da cewa wannan baƙuwar jarumar zuba min ido kawai ta yi tana kallona, Yayinda ita kuma sadiya ta zuba mata ido tana kallonta. Ganin hakan yasa na yi gyaran murya sannan na dubi wannan baƙuwar jaruma na ce da ita,
“Shin ko za ki iya faɗa mana sunanki tare da yadda aka yi har muka zama ‘yan uwan juna ni da ke?”
Ko da jin wannan tambaya, sai jarumar ta yi murmushi sannan ta ce,
“Sunana Sanafaratu, kuma ni ce ‘ya ta uku a wajen mahaifiyata, ina nufin matar mahaifinmu ta farko.” Daga nan sai ta yi shiru. Bayan wani ɗan lokaci sai ta numfasa sannan ta ci gaba da cewa,
“Tun ba yauba dama na sha faɗawa mahaifiyarmu cewa za ka zo, amma sai ta ƙi amincewa da batuna, yau gashi abinda nake faɗa ya zama gaskiya, wataƙila daga yau zata fara yarda da maganganu na.”
Yayinda na ji wannan batu nata, sai na sake cika da mamaki, har dai na gaza haƙuri na tambayeta da cewa,
“Shin ke kuwa ta yaya aka yi kika san da wanzuwata kuma har ki ka san da zuwa na?”
Ko da Sanafaratu ta ji wannan tambaya sai ta sake yin murmushi sannan ta ce,
“Abin bauta Khonsu ne ya albarkace ni tun ina ƙarama.” ta faɗi maganar ba tare da nuna wata alama ta cewa wasa yake yi ba.
Cikin rashin yarda Sadiya ta ce,
“Abin bauta kwanso kuma?”
Nan take Sanafaratu, ta galla mata harara, sai dai kafin ta kai ga cewa komai sai na yi maza na bata amsa da cewa,
“Ba kwanso take nufi ba, in na fahimta tana nufin Khonsu ne, shi ɗin yana daga cikin ababen bautar birnin Misra tun sama da kimanin shekaru duba ɗari uku da suka gabata, shin hakane?”
Na tambaye ta yayin da na maida hankali na gareta kacokan. “Tabbas hakane maganar ka, tun ina ƙarama na taso da baiwa ta mafarki, duk abin da na yi mafarkinsa to tabbas cikin biyu zai zamo guda, ko dai abin ya riga ya faru ko kuma yana kan faruwa. Bana iya gani ko mafarkin abinda zai faru, amma ina iya ganin abinda ya faru ko kuma yake kan faruwa matuƙar dai zan kwanta bacci, sai dai hoton ya bayyana a gareni ƙarara idan ya zamana akwai hasken farin wata, kuma duk abinda na ji ko na gani bana manta shi komai daɗewa. Wannan dalili ne yasa bayan na fara girma sai na fara bin tafarkin abin bauta Khonsu. A cikin irin waɗannan mafarke-mafarke nawa ne na dinga bibiyar rayuwarka tare da ta mahaifinmu har zuwa lokacin mutuwarsa. Daga sannan ne na daina ganin al’amuran da suka shafe ka sosai, face ‘yan kaɗan, amma a koda yaushe jikina yana bani cewa za ka zo. Wannan dalili ne yasa tun a safiyar yau da na samu labarin an samu baƙon haure da ya shigo ƙasar mu kuma na ji za’a kai shi fada na yo shiri domin ina da tabbacin cewa kaine.”
Ko da jin wannan batu sai mu ka sake yin shiru na wani tsawon lokaci, ba tare da wani ya ce komai ba. Ni dai tunanina a wannan lokacin shi ne, ‘idan har Sanafaratu Khonsu take bautawa, ina ga sauran mutanen ƙasar?’ Domin jikina yana bani cewa ƙalubalen da zan faɗa ciki ya wuce duk inda na ke tunani a wannan birni. Daga can dai sai na yi ƙarfin hali na ce da ita,
“Ya ke wannan mituniyar kirki, shin ko zan iya samun ƙarin bayani dangane da birnin nan tare da ababen bautarsu, kuma shin ko zan iya sanin tarihin asalin birnin nan tare da yadda akayi har mahaifina ya rabu da birnin Sahara duk da kasancewarsa sarki?”
Ko da Sanafaratu ta ji waɗannan tambayoyi nawa, sai ta yi ajiyar numfashi tare da sunkuyar da kanta ƙasa. Bayan wani ɗan lokaci sai ta ɗago kai sannan ta fara bani labarin tun daga farko.
Masha Allah!
Allah ya kara basira
Amin, Jazakallah Khair.
Masha Allah
Allah y kara basira
Amin. Jazakallah Khair
Fatan Alkairi Allah yatemaka sir
Amin. Na gode sosai
Masha Allah.
Shukuran