Shopping Cart

Close

No products in the cart.

Birnin Sahara by Jamilu Abdulrahman 2

Birnin Sahara | Babi Na Bakwai

<< Previous

Kamar haɗin baki kuwa, sai ni da Dardira muka sake nufo juna da wani sabon azababben gudu, muka tari juna tare da fara sabuwar fafatawa. Nan fa faɗan ya zamo sabo, ya zamana muna kaiwa juna muggan hare-hare. Sai da muka kwashe sama da daƙiƙa ɗari da sittin muna wannan fafatawa amma Dardira ko lakutar hanci na bata samu damar yi ba, yayinda ni kuma gaba ɗaya na rikitata da duka da sandata. A ƙalla na yi mata ƙwararan bugu guda shida a manyan gaɓoɓin jikinta. Hakan yasa da ƙyar take iya tsayawa da ƙafafunta, kuma da ƙyar take iya kare farmakin da nake kai mata.

Da dai na fahimci cewa ta yi tiɓis, sai na kai mata wani wawan duka a kai, ta sa takobinta ta kare, kafin ta ankara na daki ƙafafuwanta guda biyu a tare, nan fa tayi taga-taga zata faɗi, tun kafin ta kai ƙasa na rarumeta mu ka yi ƙasan tare. Ya zamana ta faɗi akan fuskar ta, Yayinda ni kuma na jawo hannayenta baya tare da taɗiye ƙafafuwanta a cikin nawa kamar ɗan kokawa, ya zamana ta kasa ko da motsin kirki. Nan fa fadar ta ƙara yin tsit. Na kalli Dardira da kyau ina haki na ce, 

“Ki miƙa wuya mu bar yaƙin nan.” “Ba zan taɓa miƙa wuya ba!” ta faɗa cikin ƙaraji. 

“Ba burina bane in kashe kowa, kawai ki miƙa wuya ni gida nake so in koma.” na sake faɗa mata ba tare da na saketa ba. 

“Kawai ka kashe ni tun da ka yi nasara.” ta faɗa ba tare da nuna damuwa ba. 

“Ahalinki suna buƙatarki, kuma kina da amfani ga mutanen ƙasar nan, ki miƙa wuya kawai!” na sake maimaitawa a karo na uku. 

Daganan sai shiru ya ɗan gudana a tsakanin mu, bayan wani ɗan lokaci sai Dardira ta aje wani gwauron numfashi sannan ta ɗaga kai alamar ta amince. Nan take na saketa sannan na matsa gefe ina haki. Sai a wannan lokaci ne na fuskanci mutanen fadar waɗanda da yawansu sun miƙe tsaye tare da wangale baki suna kallona, wasu cikin mamaki wasu cikin firgici. Ita kanta Sarauniya Nadiya sai da ta tsaya kawai tana kallona cikin rashin sanin me ya kamata ta ce. A daidai wannan lokaci ne kuma Dardira ta miƙe tsaye, ta kalle ni da kyau, sannan ta yi min gaisuwar bangirma ta hanyar risinawa kaɗan, sannan ta koma bayan mahaifinta kanta a sunkuye ta tsaya ba tare da ta ce komai ba. Shiru ya ɗan ƙara gudana aka rasa wanda zai ce ƙala a fadar gaba ɗaya. 

Da dai na ga kowa yayi tsit, sai na maida dubana zuwa ga Sarauniya Nadiya na ce da ita, 

“Ya ke wannan Sarauniya mai karamci, ina mai roƙon ki da ki gabatar min da jarabawa ta gaba.” 

Wannan kalami nawa ne ya dawo da gaba ɗaƴan mutanen da ke cikin fadar hayyacinsu, nan take Boka Wajagi ya nufo ni yana mai cewa, 

“‘Wannan abu akwai ƙwange a ciki, a ƙa’idar irin wannan fafatawa dole ne ɗaya ya kashe ɗaya sannan ya wanzu a matsayin mai nasara…” 

Kafin ya gama rufe bakinsa sai nan take Sarkin yaƙi Dargazu ya Katse Shi da cewa, 

“Kana nufin ka ce da ya sani ya kashe ‘yata kenan ko yaya?” 

Boka Wajagi sai ya juya gare shi yana cewa, 

“Amma kai ma ka san haka wannan dokar take…” 

Nan dai suka fara kace-na-ce a tsakanin su. Da dai na ga abin nasu ba mai ƙarewa bane sai na yi gyaran murya sannan na ce, 

‘Idan ba za ku damu ba, wannan matsalar ku ce, na zaɓi in barta da ranta ne don ni ba rigima nake nema da ku ba, kuma kashe mutane baya cikin tsarina, don haka ku ji da ni tukunna, daga baya sai ku ci gaba da gardamar taku.”

Cikin ɓacin rai Boka Wajagi ya juyo gare ni yana magana cikin fushi, 

“Kai kuma wa ya kasa da kai? Kai har ka isa manya suna magana kana saka musu baki…”

Ai kafin ya gama maganar nima tuni zuciyata har ta fara tafasa don haka na maida mishi da martani da cewa,

” Ai gani na yi manyan sun koma wasan yara, don haka na ga ya dace in yi magana.”

“Kai ni ka ke gayawa magana?”

Boka Wajagi ya tambaya cike da mamaki.

“To sai me don an gaya maka maganar? So kayi ɗayan mu ya mutu kuma hakan bai faru ba kawai shi ne kake jin haushi, kenan ko dai ka tsaneni ko kuma ka tsani ahalin sarkin yaƙi shi yasa kake so ɗayan mu ya mutu.” 

Hayyasa, ashe na tono tsuliyar dodo, nan take Boka Wajagi ya jefe ni da wata wuƙar tsafi, na yi sauri na goce, kafin in ankara sai gani kawai na yi wasu kibiyoyi guda biyar sun fito daga cikin yatsun shi sun nufo ni a fusace. Na sa sandar da ke Hannuna na kaɗe kibiyoyin gaba ɗaƴa, nan take suka zube ƙasa suna huci tare da narka shatin inda suka faɗo.

Ko da ganin haka sai Boka Wajagi ya nuno ni da yatsun hannunsa yana mai karanta wasu ɗalasiman tsafi, nan take sai wata ƙaƙƙarfar iska ta tunkaro ni a fusace. Tun kafin ta iso gare ni na fara jin hucinta, wani abun mamaki sai na ji jikina ya ƙame na kasa motsa ko da yatsan ƙafata. Nan dai na zubawa sarautar Allah ido kawai na tsaya ina jiran abinda zai faru da ni, domin na san cewa sai yadda ta yiwu a wannan hali. Ko da ya rage bai fi taku uku a tsakanina da wannan iska ba, kawai sai naga wata Jaruma sanye da wasu kaya masu ruwan ƙasa waɗanɗa suka rufe gaba ɗaya jikinta idanuwanta kawai ake iya gani ta diro gabana sannan ta sa wata garkuwa da ke hannunta ta tare wannan iska. Ko da wannan iska ta bugi wannan garkuwa, sai nan take ta koma da baya a fusace ta ɗaga Boka Wajagi sama ta buga shi da ƙasa, take ya faɗo magashiyan baya ko iya ko motsi. Nan fa kowa yayi Cirko-cirko ana kallon-kallo yayinda jarumai suka fara zare makamansu da nufin su kaiwa wannan jaruma hari, ita kuwa sai ta tsaya ƙyam a gabana ba tare da ta yi wani ƙwaƙƙwaran motsi ba. Ganin haka yasa Sarauniya Nadiya ta miƙe tsaye tare da umartar waɗannan dakaru da su dakata.

Bayan dakarun sun dakata daga kai wa wannan baƙuwar jaruma harin da suka yi nufi, sai Sarauniya Nadiya ta tako da kanta ta zo gaban wannan jaruma, kasancewar ina bayan wannan jaruma ne a tsaye, ina iya ganin yanayin fuskar Sarauniya Nadiya, sai dai bana iya ganin yanayin na ita wannan Jaruma. A wannan lokaci Sarauniya Nadiya bata nuna wata alama ta rashin jin daɗi ko murnar bayyanar wannan jaruma ba, amma ina iya ganin alamun damuwa rututu a cikin ƙwayar idanunta. Bayan sun ƙarewa juna kallo na wani ɗan lokaci sai Sarauniya Nadiya ta dubi wannan jaruma da kyau ta ce, 

“Shin ko zan iya sanin dalilin da ya fito da Damisa daga maɓoyarta?” 

Ba tare da jarumar ta yi wani motsi ba sai ta ba wa Sarauniya Nadiya amsa da cewa, 

“Damisar ta biyo bayan ɗan marayan Zaki ne, kuma tana fata za a barta ta tafi da shi ba tare da ja-in-ja ba.’

Ko da jin wannan furuci sai alamun rashin fahimta suka yi dirar mikiya a fuskar Sarauniya Nadiya, don haka sai ta sake tambayar wannan jaruma tana mai cewa, 

“Shin dama akan samu alaƙa ne tsakanin wuta da ruwa?” 

Yayin da jarumar ta ji wannan tambaya sai ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce, 

“Tabbas waɗannan halittu ne da ba sa jituwa da juna, amma alaƙarsu anan ita ce dai irin alaƙar da ke samuwa a duk lokacin da wani ya yi nufin amfani da su. Misali, Yana iya dafa abinci da wuta kuma yana iya shan ruwan hakanan don biyan buƙatar shi, sannan yana iya kashe wutar da ruwan ko kuma ya dafa ruwan da wutar don biyan wata buƙata tashi.”

 Wannan kalami da jarumar ta yi ne ya sa kyakkyawar fuskar Sarauniya Nadiya ta ƙara faɗawa cikin yanayin damuwa, nan fa ta fara kaiwa da komowa tana tunanin hukuncin da ya kamata ta yanke. Ni kuma na yi kasaƙe… Ina kallonta. Su ma sauran jama’ar fadar sai suka yi tsit, Yayinda suka zubawa wannan jaruma ido kawai ba tare da ɗayansu ya ce komai ba. Da dai na ga abin na yi ne, sai na buɗe baki na ce, 

“Ku yi haƙuri da kutse na, ina godiya mai tarin yawa a gareki yake wannan jaruma, amma idan ba za ki damu ba zan so ki bari sarauniya ta fara sallamata tukunna, in yaso daga baya sai ku ci gaba da zancen naku.” 

Ko da na zo daidai nan a zancena sai wannan jaruma ta juyo ta fuskance ni sannan ta buɗe baki cikin sassanyar murya ta ce da ni, 

“Kada ka damu ɗan uwa, komai zai yi daidai, ka ɗan ƙara haƙuri kaɗan.” 

Ko da na ji wannan batu ya fito daga bakin wannan baƙuwar jaruma da ban santa ba sai tunanina ya dagule, hankalina ya dugunzuma har ma na fara yi wa kaina wasu tambayoyi sababbi waɗanda su ma kamar kullum bani da amsar su. Shin ita wannan baƙuwar jaruma wacece ita? Menene alaƙarta da sarauniya Nadiya? Kuma me yasa ta tausasa kalami a gare ni har ta kirani da Ɗan Uwa? Lallai ina buƙatar sanin waɗannan amsoshi, ko da yake ban san me yasa nake son sanin su ba, balle in san ta yaya zan same su. Ina can ina wannan zancen zuci, sai na ji muryar Sarauniya Nadiya yayinda ta ci gaba da magana tana mai cewa, 

‘Yake ‘ƴar uwa , na kasa ajiye maganganun ki a kowane bigire na ƙwaƙwalwata, domin duk inda na nufa da zancen, sai in ga bai dace da wajen ba, don haka zan so ki warware min zare da abawar kafin in yanke hukuncin da ya kamata.’

 Ko da Sarauniya Nadiya ta zo nan a zancenta. Sai na ƙara shiga wata sabuwar damuwa, shin wane hukunci Sarauniya ke son yankewa? Kuma me yasa ta kira wannan baƙuwar da ‘Yar Uwa? ni dai a iya sanina da ita, bata da wata ‘yar uwa mace, asali ma ita kaɗai mahaifinta ya haifa, sai dai ko in ƙarya ta yi min, tunda bata taɓa faɗa min cewa ita Sarauniya bace. Ko da na zo daidai nan a tunanina, sai wata ƙaramar murya daga cikin kaina ta ce dani, 

‘Amma kai ma dai ka cika soko, shin abubuwa nawa ne Nadiya ta faɗa maka waɗanda daga baya ka gano cewa ba gaskiya bane? Kuma abubuwa nawa ne bata gaya maka ba da yanzu kake ganin su a zahiri?’

Eh kuma fa hakane, don haka sai na kauda wannan zance daga cikin raina.

Wannan baƙuwar jaruma sai ta ƙara yin ajiyar zuciya a karo na biyu sannan ta ce, 

“Wannan abu ne mai sauƙi, ɗan uwanmu ne ya dawo gida.”

Ta faɗi tana mai nuna ni da hannuwanta biyu. Ko da jin haka sai Sarauniya Nadiya ta ɗago kai da sauri cikin alamun mamaki ta dube ni sannan ta sake duban wannan baƙuwar jaruma, kai da ganinta a wannan lokaci ka san cewa lissafi take yi a ƙwaƙwalwar ta, domin alamun damuwa ne tare da fahimtar girman halin da ake ciki suka bayyana a ko’ina na jikinta. Bayan wani ɗan lokaci sai ta ce, 

“Shin ko kina da dalilin da yasa kika faɗi hakan?

Ko da jin wannan tambaya sai wannan Baƙuwar jaruma ta ce, 

“Ni kuwa ke da dalilai, da fari dai, babu wata hujja da zata iya bayyana mana yadda aka yi har ya iya shigowa cikin wannan birni namu face kasantuwar shi ɗan asalin wannan birni, sannan kasancewar ya samu damar shigowa tare da wani bayan shi hakan na bayyana mana cewa shi ahalin sarauta ne. Sanin kanki ne kuma cewa babu wani sanannen mutum a raye a duk faɗin Birnin Sahara da ya iya salon faɗan da wannan baƙo yayi a yau ɗin nan face mahaifina tsohon sarki. Abu na ƙarshe, Shin kin yi tunani dangane da ma’anar sunan shi, kuma shin ko kin san ma sunan mahaifin shi?”

Ko da wannan baƙuwar jaruma ta zo nan a zancenta, sai na ga Sarauniya Nadiya ta zaro ido cikin matuƙar firgici tana mai kallona cikin alamun tuhuma. In faɗa muku gaskiya? Ban taɓa ganinta a cikin tashin hankali irin wannan ba. yayinda na ga irin wannan kallon tuhuma da Sarauniya Nadiya ta ke yi min ya yi yawa, sai na tari numfashinta tun kafin ta fara magana na ce, 

“Ehem.. kun ga, ina ganin dai an ɗan samu matsala ne, yake wannan baƙuwar jaruma ina mai matuƙar godiya a gareki bisa taimako na da ki ka yi, ban san ta wace hanya zan iya saka miki ba. Duk da cewa ban san yadda aka yi ki ka san sunana ko ma’anar sunana ba, amma zan so ki sani cewa ni ba jarumi bane, asali ma dai ni ba kowa bane face ma’aikacin gidan biredi, don haka in ma kina tunanin ni wani ne to ga dukkan alamu an ɗan samu kuskure. Yake wannan Sarauniya, ina fata dai ba so ki ke ki aminta da maganar wannan baƙuwar jaruma ba dai ko?” 

Na ƙarasa magana ina mai duban Sarauniya Nadiya cikin alamun tambaya.

Nan fa ta sake yin shiru kawai tana wani sabon tunanin, can bayan wani ɗan lokaci sai ta ɗago kai ta ce da ni, 

‘Yaya sunan mahaifinka?”

“Mene?” 

Na tambayeta cikin alamun rashin yarda da jin abinda ta faɗa. 

“Cewa na yi yaya sunan mahaifinka?” 

Sarauniya Nadiya ta maimaita tambayarta wannan karon cikin nuna isa. Hakan ya sa babu yadda na iya face na bata amsa da cewa, 

“Hammadi, sunan mahaifina Hammadi shikenan hankalin kowa ya kwanta ko…” 

Ai kafin in rufe bakina kawai sai gani na yi gaba ɗaya mutanen fadar sun yi zumbur sun miƙe daga kan kujerunsu, wasunsu ma har leƙowa su ke yi don su ganni da kyau, wasu kuma suka kaure da sabuwar muhawara a tsakankanin su. Ita kuwa Sarauniya Nadiya kawai ƙura min ido ta yi cikin alamun mamaki mara misaltuwa, yayin da fahimtar gaskiyar abin da ke faruwa ke zama mata a ƙwaƙwalwa. 

Can bayan wani ɗan lokaci sai ta yi gyaran murya, take fadar ta yi tsit kamar mutuwa ta gifta. Bayan kowa ya natsu sai ta kalli wannan baƙuwar jaruma cikin alamun rashin fahimta ta ce, 

“Me ki ke so?” 

Ko da jin wannan batu, sai wannan baƙuwar jaruma ta sake yin murmushi sannan ta ce, 

“Abubuwa guda biyu kawai nake so a gare ki. Na farko dai shi ne ki bar wannan baƙo ya zauna a kan karagar mulki domin ki tabbatar da cewa maganata gaskiya ce, abu na biyu kuma shi ne ki bani shi domin in kai shi zuwa ga ahalin shi in ya so daga baya sai mu jira hukuncin ki.”

Yayinda wannan baƙuwar jaruma ta zo nan a zancenta, sai nan take na ji zufa ta fara tsatstsafo min a goshi, a zuciyata na ce anya wannan kuwa ba mahaukaciya ba ce? Me ya sa ta ke so in hau karagar mulkin ƙasarsu? Kuma me take so ta tabbatar? Su waye kuma ahalina?

“Amma kin san in aka samu matsala dai mutuwa zai yi ko?”

wannan magana da sarauniya Nadiya ta yi ce ta dawo da ni cikin hayyacina. Don haka firit! Sai na shiga tsakaninsu na ce, 

“Kun ga, ya kuke cinikina ne bayan gani a gaban ku? Ni fa ba na zo nan bane don in hau wata karaga, ban ma san ya aka yi na zo nan ɗin ba, kuma ban shirya mutuwa ba, baya ga haka duka-duka shekaruna Ashirin da ɗaya a duniya, don me zan tura kaina zuwa ga halaka ina ji ina gani? Kuma menene ma dalilin da zai sa in hau wata karag….”

Ban samu damar ƙarasa wannan maganar da nake yi ba saboda tsabar ruɗun da na shiga. A karon farko na rayuwata yau na tsaya baki buɗe na kasa cewa komai ba tare da ance in yi shiru ba. Ba komai ne yasa na gaza ci gaba da magana ba face wani abu da wannan baƙuwar jarumar ta aikata. Ba komai wannan baƙuwar jaruma ta aikata ba kuwa face yaye mayafin da ya rufe mata fuskarta. Nan fa na saki baki sototo… Kawai ina kallonta. Nasan da yawan ku yanzu za ku yi tunanin ‘Haidar ya ga kyakkyawar mace ne shi yasa ya kasa cewa komai. Haƙiƙa tana da kyau sosai, sai dai ba tsabar kyawunta ne ya sa na tsaya ina kallonta ba face tsabar kamannin da muka yi da juna. Komai nata irin nawa sai dai kawai ta fini tsayi kaɗan da alamun shekaru, hancinta yafi nawa tsayi kuma ta fini hasken fata. Babban abinda ya raba mu kuwa in har za’a yi magana akai shi ne ƙwayar idanunta ruwan ƙasa ke gare su kuma da ka gansu kasan ba wasa a tare da su. Ko da ta yi murmushi a gare ni, sai naga idanun nata suna wata walƙiya irin yadda na mahaifina ke yi, kumatunta kuma ya ɗan loɓa kamar yadda nawa yake yi. hakan yasa na ja da baya kaɗan cikin alamun mamaki da tsoro.

Ko da baƙuwar jarumar nan ta ga haka, sai ta sake yin murmushi sannan ta tausasa murya a gare ni tana mai cewa,

“Kada ka damu ƙanina, babu abinda zai same ka kuma zan baka amsar duk wata tambaya da ka ke da ita, amma da fari ina so ka zauna a kan wancan karagar mulki tukunna.” 

Waɗannan kalamai nata ko kaɗan basu sa hankalina ya kwanta ba, domin har izuwa wannan lokacin ji na ke yi tamkar mafarki nake yi. Can dai na tuna cewa nifa Haidar ne, kuma tarar aradu da ka ɗaya ne daga cikin fitattun abubuwan da na yi suna a fagensu, don haka kawai sai na yanke shawarar bari kawai in zauna akan wannan kujera in yaso ayi wadda za’a yi. 

Ko da gama wannan tunani nawa, kawai sai na nufi wannan karaga ba tare da wata fargaba ba. Ko da naje in da karagar ta ke, sai nayi bismillah sannan na zauna. Zamana kan wannan karaga ke da wuya sai wani abun mamaki ya faru. Ba komai bane abin mamakin face wani ƙaƙƙarfan haske da ya fara fitowa daga jikin wannan karagar mulki wanda ya haske gaba ɗayan fadar. Bayan wani ɗan lokaci kuma sai hasken ya gushe, komai ya koma daidai kamar tun dama can wannan haske bai taɓa wanzuwa ba.

Nan fa fadar ta sake yin tsit yayinda kowa ya ƙura min ido don ya ga mai zai faru. Bayan na samu kamar daƙiƙa goma da hawa wannan karagar mulki ba tare da wani abu ya faru ba, sai na yi zumbur na miƙe tsaye sannan na nufo inda Sarauniya Nadiya take tsaye tare da wannan baƙuwar jaruma domin in yi musu magana. 

Maimakon su bani damar yin magana, kawai sai na ga Sarauniya Nadiya ta yi wani abu wanda nan take yasa ma’aikatar sadarwar ƙwaƙwalwata ta tafi yajin aiki. Ba komai Sarauniya Nadiya ta yi ba face duƙawa bisa guiwarta guda ɗaya tare da faɗin, 

‘Ina miƙa gaisuwata tare da mubaya’a ga Haidar ɗan Hammadi, yariman Birnin Sahara!

Ko da rufe bakin Sarauniya Nadiya, sai na ga ita ma wannan baƙuwar jaruma ta kwaikwayeta, daga nan kuma sai ɗaya bayan ɗaya mutanen da ke fadar suma suka fara durƙusawa bisa guiwoyinsu tare da furta kalmar mubaya’a a gareni. A ƙarshe dai sai da ya zamana mutum huɗu ne kacal a cikin fadar waɗanda ba su durƙusa ba. Su ne Dargazu, Dardira, Boka Wajagi da kuma wani tsohon mutum da ban san ko wanene ba.

Next >>

6 thoughts on “Birnin Sahara | Babi Na Bakwai

  1. Masha Allah lbr yy Kuma ya bada ma’ana muna maka fatan alkhairi marubuci Allah ya Kara basira Kuma Allah ya daukakaka

Leave a Reply

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.