Shopping Cart

Close

No products in the cart.

Birnin Sahara by Jamilu Abdulrahman 2

Birnin Sahara | Babi Na Shida

<< Previous

Yayin da Dargazu ya zo inda Sarauniya Nadiya take, sai ya yi mata gaisuwar ban girma, sannan ya juya zuwa ga sauran jama’ar da ke fadar ya fara magana cikin muryar shi mai kama da ƙarar tashin jirgi da cewa, 

‘Ya ku mutanen Birnin Sahara, a karo na farko tun bayan hawan Sarauniya Nadiya karagar mulki, yau za’a gwabza yaƙi, kuma a karo na farko tun bayan kafa wannan birni, yau za’a gwabza tsakanin jarumin wani gari can daban da kuma namu na nan kuma a cikin wannan fada ta ƙasarmu mai daraja, lallai wannan faɗa da za’a yi ya kamata ya zama ɗaya tamkar da dubu a cikin tarihin wannan birni namu. Don haka a matsayina na sarkin yaƙin wannan birni kuma jarumin da babu kamar sa, na zaɓi ‘ƴata Dardira a matsayin wacce zata gwabza da wannan baƙon turmi… Au ina nufin jarumi, domin a tantance jarumtarsa.”

Ai ko da jin wannan batu na Dargazu sai na ji hantata ta kaɗa, Sarauniya Nadiya kuwa komawa ta yi kan karagarta kawai ta zauna cikin alamun karayar zuciya, su kuwa jama’ar fadar sai suka ɓarke da sowa suna murnar faruwar wannan al’amari, a taƙaice dai suna murnar mutuwata tun gabanin na mutu. Ita kuwa Dardira sai ta fito filin fadar tana tafiya cikin rangwaɗa, izza da jiji da kai a lokaci guda, mutane na tafa mata da yi mata kirari. Ba kowa bace face wannan mace da na ga sun yi kama da Dargazu kuma take zaune kusa da shi tun shigowata fadar. Yayin da ta fito filin fadar, sai Dargazu ya kalle ni cikin murmushin mugunta sannan ya kalli Dardira cikin alfahari ya ce, 

‘Shin ko akwai wata wasiyya da za ku bayar ko da ɗayan ku ya mutu a sanarwa da ‘yan uwansa?”

Ko da jin haka, sai caraf Dardira ta karɓe da cewa, 

‘Bana buƙatar in bar wata wasiyya don na san babu yadda za’a yi wannan ɗan tatsitsin ya yi nasara a kaina balle har ya kashe ni.” 

Ko da na ji wannan zance sai raina ya ɓaci, zuciyata ta harzuƙa, tabbas ido ba mudu bane amma yasan ƙima, ko da ganin irin ƙirar jikin Dardira na san ba sai an gaya maka jaruma bace, amma duk da haka bai kamata ace tana wannan cika bakin ba, don haka sai nan take zuciyata ta kwaɗaita min son ganin na yi nasara akanta ko don inga inda wannan jiji da kan nata zai kaita. To amma ta yaya zan iya yin nasara akan ta? A zahiri dai in tsagwaron ƙarfi ake magana to manta ma kawai, nasan ta wuce tunanina, sai dai sa’a da dabara. Yauwa dabara! To amma wacce dabara zan yi mata?

A dai dai wannan lokaci ne wata shawara ta faɗo cikin raina, sai dai abu ne mai wahala in yi nasara da ita, amma in na yi sa’a, tana iya zamar min abin alfahari, in kuwa banyi sa’a ba, zata sa in zama bahamage lamba ɗaya. Nan fa na fara tunanin in yi amfani da ita ne ko kuma in sake wata? Ina cikin wannan tunani ne kuma sai ga wata shawarar ta faɗo min daga inda ban taɓa tunanin zata zo ba. Wannan shawara kuwa ta fito ne daga bakin wani shahararren jarumin fim, na sani cewa za ku yi makakin ace ina cikin wannan yanayi amma ina tunanin wani jarumin fim. To, kada ku damu da wannan, abu mafi muhimmanci shi ne, shawarar shi ta zo min a dai dai lokacin da nake buƙatarta, ga abinda ya taɓa cewa, 

‘Ka tari aradu da ka a rayuwa, in ka yi nasara za ka ji daɗi, in kuma ka faɗi ka ƙara ilimi.’ 

Haƙiƙa tarar aradu da ka shi ya fi dacewa da ni a dai dai wannan lokaci tare da fawwalawa Allah komai. Don haka yayin da Dargazu ya nemi jin ta bakina dangane da wasiyyar da zan bari sai kawai na yi murmushi sannan na dube shi ido cikin ido na ce, 

“Amma kai dai kam Dargazu kana da ban mamaki, a cikin mutane biyu na kasa tantance wannene kai, tabbas ko dai kai ne jarumin da ban taɓa ganin irin shi ba, ko kuma hamagon da ban taɓa ganin irin shi ba.” 

“Me kake nufi da kalmar hamago ne?” Dargazu ya tambaya cikin alamun rashin fahimta.

‘Kada ka damu da wannan, abinda nake so in tambaya a nan shi ne, shin wane irin uba ne zai tura ‘ƴarsa cikin gasar rai ko mutuwa? Idan har jarumtakarka ta gaskiya ce me zai hana ka gwabza da ni? Amma ai cin zarafi ne a gare ni ka haɗa ni faɗa da mace, su mata ababen so ne, ababen sha’awa ne kuma ababen killacewa ne tare da nunawa kulawa, ba wai ababen turawa inda za su iya rasa rayukansu ba, ko ka gaji da ita ne kake so ka share ta daga doron ƙasa ta hanyar haɗa ta faɗa da ni? Shin wai ma kasan ko ni wanene kuwa?”

Waɗannan kalamai nawa sai suka sa fadar ta ƙara yin tsit kamar an yi mutuwa, shi kam Dargazu kasa cewa komai ya yi saboda rikicewa, ‘yar dariyar da yake yi ma a ɗazu yanzu babu ita, ita kuwa Dardira ranta ƙara ɓaci ya yi idanuwanta suka kaɗa suka yi jawur kamar an saka ƙarfe a wutar maƙera, Boka Wajagi da ke kusa da ni sai ya min raɗa a kunne da cewa, 

“Taka ta ƙare yaro!” 

A’aha! Wai me na yi wa mutanen garin nan ne ya zamana kusan kowa na son ganin mutuwata? Maimakon wannan magana da Boka Wajagi ya faɗa min ta sa na karaya, sai ma ta ƙara min ƙwarin gwiwa, don haka sai na tafi zuwa ga Sarauniya Nadiya na ce mata, 

‘Ranki ya daɗe kin san dai irin yadda na ke mutunta mata, bai kamata a ce wai an rasa namijin da za a haɗa ni faɗa da shi ba a duk faɗin birnin nan sai mace, ki taimaka ki ce wani abu mana.”

Yayin da na zo nan a zancena sai fadar ta sake yin tsit, kowa ya zubawa sarauniya Nadiya idanu don jin abinda zata ce, ni kuma a zuciyata sai na ce (da kyau) ya zuwa yanzu dai komai na tafiya yadda nake so. Bayan shiru ya ɗan gudana sai Sarauniya Nadiya ta ce, 

‘Sarkin yaƙi Dargazu shi ke da alhakin zaɓen wanda za ku kara da shi, idan har ya zaɓi Dardira a matsayin wacce za ka kara da ita, bani da wani ƙorafi, fatan nasara wa mai sa’a.”

Da kyau, na faɗi a raina, su kuwa jama’ar fadar ba ƙaramin jin daɗin wannan hukunci da Sarauniya Nadiya ta yanke suka yi ba, don haka sai su ka sake ɓarkewa da sowa tare da murna, nima a wannan lokaci murnar nake yi duk kuwa da cewa a zahiri kowa na ganin cewa mutuwata ta ƙarato.

Daga nan sai Dargazu ya ce in zaɓi irin makamin da nake so in yi faɗa da shi. kasancewar mahaifina sam baya barina in yi amfani da duk wani abu da aka ce ƙarfe ne saboda wasu dalilai da shi kaɗai ya sani, babu wani makami da na iya sarrafawa a rayuwata face sanda, sandar ma a duk lokacin da zai koya min kari ko duka sai ya bani sandar da ta yi min girma sosai ko kuma wacce ta yi min kaɗan, a duk lokacin da na yi masa ƙorafi sai yace in yi haƙuri, lokaci zai zo da zan fahimci komai, amma har yanzu lokacin bai yiba. Don haka sai na cewa Dargazu sanda nake so a bani a matsayin makamin da zan yi faɗa da shi. Ko da faɗin hakan sai gaba ɗaya mutanen fadar suka sake fashewa da dariya saboda ganin sakarcina, Dardira da Dargazu da Boka Wajagi kuwa har suna kifewa saboda tsabar dariyar mugunta, ita kuwa Sarauniya Nadiya yayinda mu ka haɗa ido sai ta yi min wani irin kallo mai kama da ‘Ka yi hauka ne?’ 

Ni kuwa a wannan lokaci babu abinda nake faɗa a zuciya ta face, 

“La’ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalumin.” 

Nan dai aka sa wasu bayi suka kawo min wata doguwar akwatu cike da sanduna dogaye, gajeru da kuma matsakaita don in zaɓi irin wacce nake so. Ko da na nufi inda wannan akwatu ta ke , sai na ji wasu kalamai da mahaifina ya daɗe yana faɗa min su suna zuwa cikin ƙwaƙwalwata,

‘Kada ka taɓa raina maƙiyinka komai ƙanƙantarsa, domin zai iya baka mamaki, kada ka taɓa nunawa maƙiyinka ƙiyayya a fili hakan zai sa ya kasa fahimtarka, kada ka gaza taimakawa maƙiyinka a duk lokacin da ya buƙaci hakan, matuƙar ka taimaka mishi daga ranar ka zama surikin shi.’

Haka dai na ci gaba da tafiya a hankali har na je gaban wannan akwatu, da zuwa sai na yi Bismillah sannan na kai hannu da nufin na ɗauki sandar da ke layin farko, kwatsam sai na ji kamar an janyo ni izuwa cikin wannan akwatu, nan take na faɗa kan akwatun yayin da hannuna kuma ya riƙe wata sanda tam. Mutanen fadar suka ƙara fashewa da dariya, ina jin Dardira tana cewa,

“Kalli yadda yake wani abu sai ka ce akuya mai ciki.” 

Aka ƙara fashewa da dariya. Har ga Allah na ji kunya, to amma sai na wayance kawai na ɗago daga kan wannan akwatu cike da ƙwarin gwiwa, hannuna kuma riƙe da wannan sanda.

Bisa mamaki sai na ji wannan sanda ta yi daidai da ni, ban taɓa riƙe wata sanda da ta yi daidai da ni ba sai wannan. Wani ƙarin abin mamaki shi ne, gashi dai ga dukkan alamu ba da ice aka haɗa sandar ba amma bata da wani nauyin kirki, daidai ni ɗin dai. Nan fa na tsaya ina kallon wannan sanda cikin mamaki domin ban taɓa tsammanin za a samu wata sanda wacce za ta min daidai a hannu kamarta ba. Ita dai wannan sanda ba wani tsawo gare ta ba, kuma bata da kauri sosai kuma kamar yadda na faɗa, bata da nauyi. A hankali kuma sai na fara fahimtar cewa akwai wasu ƙananun rubutu a jikinta. Kafin in tantance zan iya karanta wannan rubutu ko ba zan iya ba, sai na ji an sake buga wannan ganga mai ƙarfin sauti, take fadar ta ƙara yin tsit, daga nan sai Dargazu ya bada damar a fara wannan faɗa a tsakanina da Dardira.

Dardira ta ja tunga ta yi tsayuwa irin ta manyan jarumai riƙe da wata sharɓeɓiyar takobi wanda saboda tsabar ƙyallinta har kashe min ido ta ke yi. A nawa ɓangaren kuwa, kasantuwar wannan sandar a hannuna ba ƙaramin ƙwarin gwiwa ya bani ba, amma saboda in ci gaba da shirin da na fara, sai na yiwa sandar riƙon sakarkari kuma na yi wata tsayuwa irin ta cikakkun dolaye. Hakan yasa Dardira ta yi min wani murmushin mugunta sannan ta ce, 

‘Sai ka yi bankwana da masoyiyar taka kafin ka mutu.” ta faɗa tana nuna ƙofar shigowa fadar da bakinta. Ko da na kai dubana wajen ƙofar, sai na ga wasu dakaru suna shigowa da Sadiya cikin fadar a ɗaure. Har yanzu ban daina mamakin yadda na ji sonta ya fice min a rai ba saɓanin da da farko yadda nake jinta tamkar ita ce rayuwata. Maimakon in ce mata wani abu kawai sai na yi mata murmushi, sannan na juya zuwa ga dardira nace da ita, 

‘Ina matuƙar tausayin wannan kyakkyawar fuskar taki, domin zata tafi lahira ba tare da ta shirya ba.”

Haba, ashe wannan kalami nawa ya ɓata mata rai fiye da yadda na yi tsammani, don haka kawai sai ta nufo ni da wani irin azababben gudu cike da fushi ta fara kaimin muggan hare-hare ta ko’ina.

Maganar gaskiya duk inda ake neman mace jaruma mai ƙarfin damtse da zafin nama Dardira ta kai, domin kai min sara da duka take yi ta ko’ina, ni kuwa a nawa ɓangaren babu abinda nake yi face gocewa da kuma kare muggan hare-haren da take kawo min. Dardira tana da matsala guda ɗaya wacce ga dukkan alamu bata san da ita ba, matsalarta ita ce bata da dabarar yaƙi, tsabar ƙarfin damtse da kuma zafin Nama kawai take taƙama da shi, na fahimci hakan ne ta hanyar irin hare-haren da take kawo min ina gocewa tare da kare kaina ba tare da ni na kai mata hari ko sau ɗaya ba, a taƙaice dai ita mai kai farmaki ce. Wani wawan sara da ta kawo min na goce ne yasa muka yi cirko-cirko muna kallon juna. 

Nan take wasu kalaman mahaifina suka ƙara kawo min ziyara, 

‘Cikakken jarumi shi ne wanda ya ƙware a kowane irin salon yaƙi, kai hari, kare kai ko taimakawa abokan yaƙinsa. Wanda duk ya ƙware a kai hari kawai, to ba zai iya kare kansa ba idan abokin karawarsa ya fishi ƙarfi. Shi kuwa wanda ya saba da kaiwa abokan faɗan shi ɗauki, abu ne mai wahala ya yi nasara a faɗan ɗaya da ɗaya. Shi kuwa wanda ya ƙware a kare kai kawai abu ne mawuyaci ya mutu a yaƙi, kuma da wahala ya yi nasara, don haka kana buƙatar ka haɗa duka ukun, kuma kada ka sake maƙiyinka ya gane ka ƙware a fannonin duka, ya zama yayinda zai gane hakan, tuni har ka yi nasara a kanshi.’

Hmmmmm na yi ajiyar zuciya tare da yin murmushi. 

“Allah Ya jiƙanka baba, kana kabari amma kana ci gaba da koya min darussa.”

 Na faɗi haka a zuciyata. A dai-dai wannan lokaci ne kuma Dardira ta kawo min wani mummunan sara a saitin wuyata na yi maza na kare, kafin in ankara ta kawo min wani wawan hamɓari da ƙafarta a ƙirjina, nan take na ji kamar an buga min guduma a ƙirji. Ƙarfin dukan ne yasa na yi wata ‘ƴar ƙaramar tafiya daga inda nake na je na bugu da wata dirkar ginin fadar, nan take kaina ya fashe jini ya fara zubowa.

Ko da na shafo kaina na ga jini, sai nan take zuciyata ta harzuƙa, raina ya ɓaci. Zumbur na miƙe tare da goge wani ɗigon jini da ke ƙoƙarin shiga min idanuwana. A daidai wannan lokaci ita kuma Dardira ta koma kefe kawai tana kai-komo tare da jiran ganin na taso. Daga nan sai na yi wani abu wanda ni kaina sai da ya bani mamaki.

Wata Irin tsayuwar yaƙi na yi wacce ta fi kama da tsugunno, ita dai irin wannan tsayuwa ita ce tsayuwar salon yaƙi na ƙarshe da mahaifina ya koya min kafin ya rasu, kuma har ya rasu ban gama ƙwarewa a irin yadda yake so ba. Ina ganin yadda yake yi kuma ina jarabawa amma bana iya yinta kamar yadda yake yi. Wani irin salon faɗa ne wanda mukan yi wa juna dariya akan shi a wasu lokutan saboda sunan da muka sa mishi na ‘Malam buɗe mana littafi.’ Shi irin wannan salon yaƙi, mutum yakan tsuguna ne kamar yana kan babur, ƙafarsa ɗaya tana gaba ɗaya tana baya. Hannuwansa ma haka, sai dai hannun gaba zai kasance ne a ƙasa-ƙasa, hannun baya kuma a sama. A haka, abokin karawarka zai kasa tantance da wannene za ka kai mishi hari, in ya yi can kai sai kayi nan, in kuma yayi nan sai ka taro shi ta can.

Wato wannan salon faɗa ba ƙaramin wahalar koyo yake da shi ba, balle kuma ace a ƙware a kanshi. Mahaifina ya faɗa min cewa shi kanshi ya ɗauke shi tsawon shekaru kafin ya ƙware kuma yakan yaba min ma dangane da ƙoƙarina domin yakan ce na fishi saurin ɗaukar abu idan aka koya min. Bugu da ƙari, duk iya karance-karancena, bincike-bincikena, da kuma kallace-kallacena ban taɓa cin karo da irin wannan salon yaƙi ba.

Don haka yin wannan tsayuwa a daidai wannan lokacin sai ya zamo abin mamaki a gareni, musamman duba da cewa ban gama ƙwarewa a kai ba. Sai dai bisa ga mamakina, wannan tsayuwa da na yi ta yi matuƙar firgita Dardira tare da Sauran mutanen fadar, domin Dardira sai da ta ja da baya cikin firgici kafin daga baya ta koma yadda take. Ina kallon wasu daga cikin mutanen fadar ta gefen ido na ga suma sun mimmiƙe, amma na ƙi yarda in waiga gare su domin Dardira tana iya kawo min hari a kowane lokaci.

Next >>

5 thoughts on “Birnin Sahara | Babi Na Shida

Leave a Reply

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.