Skip to content

Babban Kalubalen da na samu a rubutu shi ne rashin iya daidaitacciyar Hausa – Nana Aicha Hamissou

Filin tattaunawa da fitattun marubuta na Hikaya a yau ya samu yin tattaki har ƙasar Niger inda muka zaƙulo muku matashiyar marubuciyar nan kuma hazika, Nana Aicha Hamissou. Ga yadda hirar ta kasance:

Tambaya: Da farko muna son jin taƙaitaccen tarihin baƙuwar tamu.

Amsa: Sunana Nana Aicha Hamissou Abdoulaye, an haife ni a ranar Laraba ashirin da bakwai ( 27) ga watan Yuli na shekarar dubu ɗaya da ɗari tara da casi’in da huɗu (27/07/1994) a unguwar sabon gari ta jihar Maraɗi, Jamhuriyar Nijar. Na fara karatu a ɓangaren addini a Madarassatul Hizibur Rahim da ke unguwar Zaria ta 2 a nan garin Maraɗi. A lokacin da na cika shekara shida a duniya aka saka ni a makaratar boko a shekarar 2000 a wata primary mai suna Ecole sabon gari a nan garin Maraɗi, na gama a shekarar 2006 inda kai tsaye na ɗora karatuna a wata ƙaramar Sakandire mai sunan CEG Rauda, bayan na gama na wuce babbar sakandare mai suna Lycée Ɗan Baskore. A lokacin ne kuma Allah Ya albarce ni da saukar Alkur’ani a shekarar 2013.

Bayan na gama Sakandire na samu gurbin karatu a jami’ar Gwamanti mai suna Université DanDicko DanKoulodo de Maradi (UDDM) a shekarar 2015. Sakamakon yajin aiki ban gama ba sai a watan Yulin 2020 inda na samu kwalin digiri a fannin Etude d’Impact Environnemental (Nazarin Tasirin Muhalli). A ƙarshen watan Disambar shekarar na ɗora master a jami’ar Abubakar Ibrahim International University a ɓangaren Gestion de L’environnement (Yadda za a kula da Muhalli). Wani uzuri mai girma ya ɗan tsayar da ni, da tun bara na gama Master ɗita. A taƙaice dai da izinin Ubangiji na kusa gama digiri ta biyu in Sha Allahu.

A ɓangaren addini ma har yanzu ina neman ilmi, inda a halin yanzu ina karatu a madarassatul Imamul kisa’i, Al’islamiyatul Tahfizul Qur’an da take nan garin Maraɗi.

Aicha Hamissou
Marubuciya Nana Aicha Hamissou da Award dinta na Gasar Hikayata ta BBC a shekarar 2021 

Tambaya: Me ya ja hankalinki har kika fara rubutu?

Amsa: Ban taba zaton zan zama marubuciya ba! Abu guda na sani, ina karance-karance duk da ban yi karatun littaffai ba na takarda amma na yi karatun littafai online wanda in na ce zan ƙirga su to zan yi ƙarya don ban san adadinsu ba. Kwatsam wata rana ina zaune sai na fara wani rubutu mai kama da ɗanɗano sai na tura a wasu group biyu da nake ciki na Rahma Kabir da Asma Baffa. Sai mutane suka yi ta ce mini in ci gaba ai littafin zai yi daɗi har Rahma Kabir ita ma ta ba ni ƙwarin gwiwar farawa a akwatin sirri. Na ce mata ba zan iya ba saboda ban iya Hausar Nijeriya ba. Sai ta ce mini zan iya, in yi typing in turo mata za ta gyara min. Babu ƙyashi babu hassada na turo mata shafi na farko ta gyara mini haɗe da fitar mini da gyararrankina, sannan kuma na sake wani shafin ta sake gyara mini. Daga nan na fara typing na yi wa kaina editing ina turawa. Wannan shi ne mafarin zamana marubuciya.

Tambaya: Wanne littafi ne ki ka taɓa karantawa da ya fi burge ki?

Amsa: Suna da yawa ga wasu daga ciki:
1. Ɗan Adam na Rufaida Umar
2. Tamanin da tara na Abdullahi Hassan Yarima
3. Da Ma Sun Faɗa Mini na Jibrin Adamu Jibrin Rano.

Tambaya: Idan za ki yi rubutu, shin ki kan tsara komai da komai ne kafin ki fara ko kuwa kai tsaye ki ke farawa?

Amsa: Ya danganta daga yanayin rubutun, idan dogon labari ne nakan yi ƙwarangwal kafin na ɗora alƙalamina. Idan kuma gajere ne ina iya tsara shi a ƙwanyata na ɗora alƙalami ko kuma shi ɗin ma nakan yi masa ƙwarangwal wani lokacin. Ya dai danganta daga yanayin labarin.

Tambaya: Ya kike yi idan wani tunani sabo ya zo miki game da wani rubutu na daban alhalin kina tsakiyar rubuta wani. Ki kan saki wancan ne ki yi wannan sabon ko kuma sai kin gama da wanda ki ka fara?

Amsa: Ka san ba a yi wa rubutu hawan ƙawara, idan har wani tunani ya zo mini daban nakan nemi takarda na rubuta abin da labarin ya ƙunsa. Alabarshi sai na ci gaba da wanda nake yi gudun rikita kaina da kuma masu bibiya ta.

Tambaya: Ki kan ɗauki kamar tsawon wane lokaci kina bincike kafin ki fara rubutu, kuma daga nan yakan ɗauke ki tsawon wani lokaci kafin ki kammala rubutun littafin?

Amsa: Ya danganta daga yanayin labarin da kuma inda za a yi bincike. Kawai dai nakan sa a raina abin da zan yi mai muhimmanci ne don haka ina mayar da hankali ga abin da na sa gaba. A da can ina wata uku ko biyu in gama labari guda, amma yanzu gaskiya ina ɗaukar lokaci har shekara guda sukutum.

Tambaya: Wacce hanya ki ke bi wajen samun jigon labarinki?

Amsa: Ko a hanya na ga wani abu da ya ba ni mamaki, birgewa ko haushi nakan yi saƙe-saƙe a raina yadda zan iya rubutu a kansa da tunanin zama darasi ga mutane. Ni abu kaɗan zan gani ya busa mini ruhin rubutu, samun jigo bai ba ni wahala. Matsala guda ce rashin mayar da hankali da nake da shi wurin rubutu.

Tambaya: Wacce hanya ki ke bi wajen fitar da halayen taurarinki tare da ba su sunan da ya dace da su?

Amsa: Idan na yi ƙwarangwal, nakan samu feji guda na rubuta sunayen taurarin labari tare da matsayin kowane da kuma irin rawar da zai taka.

Tambaya: Shin ko kin taɓa amfani da wani ɓangare na tarihin rayuwarki a cikin rubutunki?

Amsa: Ko sau ɗaya.

Tambaya: Wanne littafi ne ya fi ba ki wahala daga cikin dukkan litattafan da ki ka taɓa rubutawa?

Amsa: Kundin Bincikena.

Tambaya: Wanne irin ƙalubale kika fuskanta a bangaren rubutu?

Amsa: Ƙalubalen da na fuskanta a lokacin da na fara rubutu ba su da yawa gaskiya. Zan iya cewa ba su wuce na rashin iya daidaitattaciyar Hausa ba.

Tambaya: Litattafai nawa kika rubuta? Kuma za mu so mu ji sunayensu.

Amsa: Na rubuta littafi bakwai ni kaɗai:
1. ‘Yar Aikin Gidana
2. Da Wa Na Dace?
3. Rayuwarmu Ce Haka
4. Soyayyar Gaskiya
5. Laila Hafsat
6. Inuwa Daya
7. Kundin Bincikena.

Sannan na yi rubutun haɗaka sau uku: na farko shi ne Sai Na Ɗauki Fansa tare da ƙawata Aisha Abubakar Mrs Bb da kuma ‘yar’uwata Maryam Nasir (Manab ‘Yar Baba), sai rubutu na biyu tare da marubutan kungiyarmu ta Kainuwa mai suna Hannu Ɗaya Ba Ya Ɗaukar Jinka, sai na uku shi bai fita ba wanda muke sa ran bugawa in sha Allah mai suna Da Jininsa A Jikina tare da fasihan marubuta guda goma.

Na rubuta gajerun labarai da dama. A cikin su akwai:

  1. A Sanadin Mijinta
  2. Wani Jinkiri…
  3. Kuskuren Da Na Tafka
  4. Na Yi Nadama
  5. Hoton Mijina
  6. Tun A Duniya
  7. Rai da Ƙaddara
  8. Kala Biyar
  9. Butulci
  10. Wanda Bai Ji Bari Bari Ba
  11. Ramin Mugunta
  12. Sanadin Bikin Salla
  13. Wata Rayuwa
  14. An Ƙi Cin Biri…
  15. Akwai Bambanci
  16. Da sauran su.

Tambaya: Wanne littafi ne Bakandamiyarki, kuma me ya sa?

Amsa: ‘Yar Aikin Gidana, kasancewar shi ne mafarin samun duk wata nasara da na yi a harkar rubutu.

Tambaya: Shin kema kin amshi sauyin da zamani ya zo da shi na rubutu a waya?

Amsa: Eh na amshi wannan sauyin saboda ana saurin isar da saƙo cikin wayar. Ba tare da ko sisi ba ka karanta littafi ka ƙaru da darasin ciki. Don akwai waɗanda suke karanta littafi ba tare da sun siya data ba, a facebook wato freemode.

Tambaya: A duk cikin Taurarin labaran da ki ka rubuta wanne ki ka fi so, kuma me ya sa?

Amsa: Fatima ta cikin labarin Butulci wanda na yi nasara a gasar BBC da shi. Dalilin zaɓenta a matsayin wacce na fi so saboda yadda ta kuɓutar da kanta daga masu garkuwa da mutane ta hanyar amfani da hikimarta.

Tambaya: Akan samu wani lokaci da kan marubuci ke cushewa har ya kasa rubuta komai. Shin kin taɓa shiga irin wannan yanayin? Kuma ta wace hanya ki ka bi wurin magance hakan?

Amsa: Ban taɓa shiga ba. Abin da na sani shi ne ina tsintar kaina a gajiye idan na jima ina rubutu ko na so takura wa kaina. Abin da nake yi shi ne ajiye alƙalami na fita hanyar rubutun sai an kwana ko a wuni ban bibiyi labarin ba.

Tambaya: Mene ne abin da ki ka fi so game da rubutu?

Amsa: Ya zamana idan ina karanta labari in ji tamkar gaske ne abin da yake faruwa da taurarin labarin da nake karantawa ko nake kallo ko saurare.

Tambaya: Me ki kan yi a duk lokacin da ki ke da sarari?

Amsa: Abubuwa da yawa:
Karatu
Shiru tare da nazari
Hira da masoyana ds.

Tambaya: Wace karin magana ki ka fi so? Kuma me ya sa?

Amsa: Mai haƙuri yakan dafa dutse ya sha romo. Saboda duk wanda ya yi haƙuri a rayuwa zai yi nasara da ƙarfin ikon Allah..

Tambaya: Da rubutun online da na littafi wanne ya fi ma’ana da saurin isar da saƙo?

Amsa: Duka suna da ma’ana gaskiya kuma suna saurin isar da saƙo yadda ya kamata. Amma a ganina littafan takarda sun fi ma’ana saboda babu tarkace a cikin su, duk da online ma akwai ƙwararrun marubuta waɗanda littafansu suke da daɗi da ma’ana. Sannan littafan waya sun fi saurin isar da saƙo saboda da waya kana iya karatu ba tare da ka biya ko sisinka ba ko kuma ka fita waje siye. In har za ka karanta littafi mai ma’ana na online to ya fi na takarda saurin isar da saƙo.

Tambaya: Wanne tasiri marubuta suke da shi a cikin al’umma?

Amsa: Marubuci mutum ne mai isar wa al’umma saƙo, mai warware masu matsalolinsu ba tare da ya yi tozali da su ba, ta hanyar ƙirƙirar wata duniya ya ƙawata ta da wasu mutane masu ɗauke da irin matsalolin mutanen zahiri ko makamancin haka. Ko iya haka na tsaya na san za ku fahimci girman tasirin marubuci a cikin al’umma. Yana yin rubutu saboda abubuwa da dama kamar : Samar wa al’umma mafita, wa’azantarwa, adana tarihi, wayar da kai, Yada ilmi, nisaɗantarwa, sanar da halin da duniya take ciki, ds.

Wa’azantarwa : Yana rubutu domin yin wa’azi ga mutane, wani lokaci ma sai ka ga an yi wa mutum wa’azi ya ƙi ɗauka amma sai a yi rubutu ya jijjiga shi silar iftila’i ko wani abu da ya faru da taurarin labari.

Yaɗa ilmi: marubuci yana yin rubutu domin yaɗa ilmi a cikin al’umma. Kamar misalin littafin gwanata Hauwa Shehu na Harin Gajimare. A hikimance ta yaɗa ilmin cybercriminal kuma ta isar da saƙonta cikin sauƙi ta hanyar rubutu.

Adana tarihi : marubuci yana bayyana ainihin yadda rayuwar alumma take ciki, marubuta. suna yin rubuce-rubuce su faɗi hali da lokacin da ake ciki.

Wayar da kai : Marubuta suna wayar da kan al’umma. Kamar misali a hikimance marubuta suke yin rubutu a kan illolin auren dole, ko kuma shaye-shaye, kula da lafiya ds.

Nishaɗantarwa: Marubuta suna rubutu domin nishaɗantarwa, kamar misalin fim ɗin Gidan Badamasi, a zahiri labarin nishaɗi ne amma idan aka natsu za a fahimci tarin darussan da suke ƙunshe cikin shi.

Sanar da halin da duniya ke ciki: marubuta suna rubutu domin sanar da duniya halin da ake ciki. Kamar misalin labarin Rai da Cuta na Maryam Umar da ya lashe gasar BBC a 2020. Duk wanda ya karanta shi komai nisan shekaru idan bai san cutar Corona ba to zai yi tambaya game cutar a faɗa masa.

Tambaya: Shin ko akwai wani labarin da ki ke rubutawa a yanzu haka da masoyanki za su yi tsumayin fitowarsa?

Amsa: Na’am. Har ma na gama shi, za a buga shi in Sha Allahu. Sunansa Kundin Bincikena.

Tambaya: Wane ne tauraronki a cikin marubuta?

Amsa: Muntasir Shehu.

Tambaya: Tsakanin Fim da littafi wannene ya fi saurin isar da saƙo?

Amsa: Ban sani ba gaskiya don ban cika kallon fim ba. Na jima ma ban kalle shi ba.

Tambaya: Wanne kira za ki yi wa masu rubutu na kauce hanya?

Amsa: Kira na farko a gare su shi ne su ji tsoron Allah, su ji tsoron Allah, su ji tsoron Allah.
Kira na biyu da zan yi masu shi ne su sani rubutun batsa ba abu ne mai kyau ba, in har suna yin shi ne don su samu mabiya ko su zama celebrity to wallahi tun wuri su farka da mumunnan mafarkin da suke yi. Masu rubuta abin alkairi ma ba kowa ne yake tunawa da su ba in suka daina rubutu ko kuma suka je hutu, wata ɗaya wata biyu an gama yayin mutum an kama wani.
Kira na uku a gare su da su zubar da makamansu na rubutun batsa don ni dai ban ga wata fadakarwa da yake ba su kama rubutun da zai amfani al’umma musamman a wannan lokacin da muke ciki wanda cin hanci da rashawa ya yi yawa, matsalar tsaro ta yawaita, bangar siyasa ta zama ruwan dare gama duniya, media ta zama dandalin musayar ra’ayi, harkar ilmi ta taɓarɓare. Akwai jigogin labarai da yawa da ya kamata a ce an yi magana a kansu amma a banza sai shirme kawai suke yaɗawa.
Duk wata marubuciya mai rubutun batsa ina yi mata addua’a Allah Ya shirya ta shiri na addinin Musulunci.

Tambaya: Waɗanne nasarori kika samu a rubutu

Amsa: Nasara ta farko da na fara samu ita ce haɗuwa da mutane na gari waɗanda suka zame min ‘yan’uwa har nake alfahari da su, waɗanda nake jin su tamkar ‘yan’uwan da muka fito jini daya da su.
Nasara ta biyu kuma ita ce alkairi, na samu alkairi mai yawa sosai. Kullum cikin samun alkairan marubuta nake yi. Ga girmamawar da nake samu daga wasu mutane. Ina matuƙar son girmamawa shi ya sa duk wanda ya girmama ni ina jin daɗin hakan a raina. Wannan ma yana cikin nasarar da na samu.
Na uku na koyi rubutu, na fara gane rubutu, ina kan gane rubutu, ina fatan na ci gana da gane rubutu. Wannan ma wata nasara ce da na samu.

Bayan su na samu wasu nasorori da suka haɗa da:

1: A shekarar 2021 na yi nasarar zama gwarzuwa ta biyu a gasar Hikayata ta BBC. Silar wancan nasarar na samu wasu nasarori kamar haka:
A. Nasarar karramawa daga ƙungiyarmu ta Madubi.
B. Nasarar karramawa daga mamallakin jami’armu Dr Muhammad Abubakar Ibrahim, inda aka shirya taro na musamman a karrama ni, a wurin taron aka yafe mini kuɗin karatun shekara biyu Masters ta 1&2 waɗanda za su kusa kimanin miliyan guda na sefa.
C. Kafin karrama ni sai da ya kai ni wurin magajin gari shi ma dai ya ɗan zura hannu a aljihu haɗe da ba ni wani abu.
D. Watarana ina zaune na ga kira da wata baƙuwar lamba. Bayan na ɗaga mutumin yake ce mini Shugaban Alliance Française ne, ya kira ni yake shaida mini taro ne za su shirya a ranar Francophony, ya sa a nema masa marubuta biyu daga Nijeriya su karanta masu gajeran labari sai ake sanar da shi ai akwai wata ‘yar Nijar ma ‘yar ma Maraɗi da ta ci gasar BBC shi ne ya samu lambata ya kira ni.
2. Na zo ta 10 a gasar Ɗangiwa2022.
3. Na kuma samu nasarar kasancewa cikin waɗanda aka buga labaransu a Mujallar Tantabara mai taken Hausa da Hausawa a wannan shekarar.

Aicha Hamissou
Marubuciya Nana Aicha Hamissou tare da Senator Uba Sani a yayin bikin lashe gasar Hikayata ta BBC Hausa a shekarar 2021 | Hakkin mallakar hoto: BBC Hausa

Tambaya: Wacce shawara za ki bawa sabon marubuci ko marubuciya?

Amsa: Zan ba su shawarar da su je su koya, ko kuma su fara siyen littafan ƙa’idojin rubutu da karin magana. Sannan su nemi masana su fara koyar da su. Abin da yake da amfani sosai wanda in aka bar shi an bar daɗin labari shi ne ƙa’idojin rubutu. Daga rubutu ya cakuɗe to fa zai fara gundarar mai karatu Musamman in waɗanda suka san sirrin ƙa’idojin rubutu ne.
Bayan sun fara koyon ƙa’idojin rubutu sai su fara tuntuɓar wani ya koyar da su yadda za su fara rubutu. Zan yi masu nasihar su nemi jigon labari mai ma’ana su fara yi da shi. Sannan bayan sun fara su kasance masu haƙuri da juriya don dole in har kana son ka cigaba ko kuma ka zama wani to dole sai ka haɗa da hakuri. Zan ba su shawarar su kasance marasa ƙorafi game da makaranta. Zan yi masu fatan alkairi daga karshe.

Tambaya: Wanne kira za ki yiwa mutane masu kallon rubutu a matsayin hanya ce ta ɓata tarbiyya?

Amsa: Kafin in amsa tambayar bari in ce wani abu a kai. Ni fa in har wata ta ce mini ta lalace sanadin karatun littafin kuma marubuciya ce silar lalacewarta, ra’ayina ita ce babbar mai laifi.
Me ya kai ta karantawa? Dole aka yi mata?
Shafin farko da za ki karanta in bai yi maki ba sai ki aje shi ki nemi tsari a wajen Allah ya hane ki da son ƙara karantawa.
Shawarar da zan ba su ita ce, kai tsaye zan ce ƙarya ne bai ɓata tarbiya sai wacce ta so ta lalace.
Sannan kuma zan ce masu akwai marubuta waɗanda suka amsa sunansu masu ilmi da fasaha waɗanda in har ka karanta littafansu za ka ji daɗin karantawa har ba ka son a zo ƙarshen labarin. Kuma zan ce masu da yawan masu karatu in sun karanta littafansu har suke gyara matsalarsu. Saboda wata rayuwa ta littafi exactly wani zai ce rayuwarsa ce, wani zai ce da shi ake ma. Kenan ta wannan hanyar ma wani yana iya gyara wata matsalarsa. Don haka kai tsaye zan ce ba gaskiya ba ne.

Tambaya: Wanne irin cigaba harkar rubutu ta ke samu a yanzu?

Amsa: Gaskiya an samu cigaba sosai ta fuskar bunƙasa shi ma yadda marubuta suke sarrrafa basirarsu cike da ƙwarewa suna rubutu.

Tambaya: Shin wanene ubangidanki a harkar rubutu?

Amsa: A da idan abu ya shige min duhu ina tambayar Almu Dakata ko Bamai. Sai kuma mutanen ƙungiyarmu mutanen amana. Yanzu dai malamaina biyu ne , Malam Jibrin Adamu Jibrin da kuma Malam Sadik Abubakar.

Tambaya: Mene ne burinki a harkar rubutu?

Amsa: Saƙon da na isar ya amfanar da al’umma.

An yi wannan hira da Nana Aicha Hamissou ne a ranar Talata, 13 ga 10 Oktoba 2020 kai tsaye. An kuma tace tare da sabunta tambayoyin a ranar 27 ga watan Mayu 2024.

Tsara tambayoyi da gabatarwa: Maryam Haruna tare da Hauwa’u Muhammad.

Tacewa da sabuntawa: Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page