Skip to content
Part 1 of 2 in the Series Inuwa Daya by Nana Aicha Hamissou

SHIMFIƊA

Kowanne ɗan’adam yana da tarin burika damfare a ma’adanar sirrinsa, dogon buri ko kuwa kishiyarsa. Dalilin da ya sa muradan mutane suka bambanta, ko da kuwa ciki guda suka fito. ‘Yan’mata da yawa burinsu auren wanda suke so mai kuɗi ko mai rangwame matuƙar yana da sana’a, saɓanin Fadila wadda burinta auren mai hannu da shuni ne, ba taɓa kallon talakan saurayi da gashin ido ba balle har ta ji shi a ranta da sunan soyayya. Duk da kasancewarta ba ‘yar kowa ba, amma zanen ƙaddara ya haɗa ta INUWA ƊAYA da masu kuɗin, ta rikiɗe ta zama tamkar su har ma ta fi mai kora shafawa. Kullum maganarta guda sai mai kuɗi, matar gaban mota ce. Duk wanda ke rayuwa a INUWA ƊAYA da ita ya san wannan burin nata, tsabar yadda take yawan maimaita wa mutane shi har na tare da ita sun haddace shi.

Tafe take cikin motarta Rap4, waƙar Ado gwanjo take saurare wacce aka yi wa laƙabi da war. Murmushi ne kwance bisa allon fuskarta wanda yake da nasaba da sirrin zuciyarta, masu azanci kan ce labarin zuciya a tambayi fuska. Haka ne kuwa, domin daɗi ya mamaye zuciyarta a duk lokacin da ta tuna burinta yana gaɓ da cika.

Cike da ƙwarewa take tuƙa motar, tana bin waƙar tamkar a bakinta aka fara rera ta. A daidai ƙofar wani gida mai ƙaramar ƙofa ta faka motar tata. Fita ta yi tana taƙu ɗaiɗai makuli riƙe a ɗayan hannunta yayin da jakarta ke ɗayan hannunta. Sallama ta rafka a gidan, ba tare da an amsa mata ba ta ɗora da faɗin,

“Hajiyata!”

Hajiya Zali wadda ke zaune saman saman tabarma a tsakar gida ta amsa sallamar Fadila, tana ɗora wa da faɗin, “Fadila ke ce war haka… yau babu makarantar ne?”

“Ni ce Hajiyata.”

Ta tsahirta haɗe da zaunawa saman kujerar roba da ke ajje tsakar gidan, kafin ta ɗora da,
“Makaranta! Ai na gama karatu Hajiyata, wanda na yi Allah Ya sa masa albarka. Matar manya ce ni fa ko kin manta?”

Ta ƙarashe tana sakin murmushi haɗe da duba agogon da ke ɗaure saman tsintsiyar hannunta.

Hajiya ta ja numfashi kafin ta ce,

“Anya Fadila… wai daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaƙi?”

“A rashin tayi akan bar arha. Ko kin manta ne na tuna miki?”

Murmushi kawai Hajiyar ta yi tana kallon Fadila wacce ta ci gaba da cewa,

“Duk da kin san burina, amma bari na yi miki tuni!”

Ta tsahirta tana sakin ƙaramin murmushi kafin ta ɗora da,

“Babban burina a doron ƙasa na rayu a INUWA ƊAYA da mai arziki, ko da kuwa babu son shi a zuciyata matuƙar yana so na, na ci alwashin zan saka almakashi na tsaga zuciyata in cusa son nasa da ƙarfi da yaji na rufe ta ruf. Komai tsufan mutum kuwa! Komai shekarunsa; ko da kuwa ya kai sa’ar kakana matuƙar yana da kuɗi zan iya auran shi. Tun da na gane akwai aure tsakanina da mutumin da na ɗauke shi matsayin a uba, na ɗaukar wa kaina alƙawarin mallakar shi a matsayin uban ‘ya’yana.” 

Ta kaɗa baki haɗe da buɗe idanuwanta sosai tana kallon Hajiya Zali kafin ta ɗora da faɗin,

“Na shirya fuskantar kowaɗanne irin kalubale matuƙar zan rayu a inuwa ɗaya da baba a matsayin ma’aurata, kalarsa nake muradi a matsayin mijin aure, irin shi na jima ina nema a matsayin abokin rayuwa. A daidai lokacin da sirrin ɓoye ya fito fili na ɗora ɗamarar cim ma burina, sai na auri babana ko da kuwa Ummi za ta mutu a kan na auri mijinta, ko da kuwa duniya gabaɗaya za ta yi alawadai da ni, amma ba zan taɓa damuwa ba matuƙar na cika burina.”

Tana dire maganarta, Hajiya Zali da take fuskantar ta, ta fara tata maganar tana cewa,

“Na jima da sanin muradinki auren mai kuɗi Fadila, amma ban taɓa zaton lokaci guda za ki aminta da auren Alhaji ba. Amma me za ki ce wa duniya?”

Fadila ta kaɗa baki sannan ta furta, “Duniya fa kika ce! Ki daina damuwa da duniyar wasu, ki fuskanci duniyarmu ko kuwa na ce duniyata. Kada ki manta ni fa mace ce.”

“Na fi kowa sanin ke mace ce Fadila amma…”

“Amma me? Alwashi na ci sai na aure shi tun da har kika kwaɗaita mini mayar da burikana a kansa. Kamar yadda kika ce za ki fara aikinki, ni ma zan fara aikina yanzu ba sai an jima ba.”

Tana gama faɗin haka ta zari jakarta haɗe da mikewa tsaye tana faɗin,

“Na tafi gida sai na sake waiwayo ki, da ma daga unguwa nake na biyo mu gaisa.”

Kafin ta yi taku biyu Hajiya ta katse mata hanzari ta hanyar cewa,

“Shin kina ganin bingida za ta saɓu a ruwa?”

“Me zai hana ta saɓuwa matuƙar aka saka ta? Bingidar ma ai suna ta tara! Wata ko cikin ruwan acid akan iya saɓa ta.”

Tun kafin ta kai aya Hajiya take kallon ta cikin wani irin yanayi na mamakin furucinta, tana dire maganar ta ɗora tata da faɗin,

“Ta yaya Fadila?”

“Ta yadda ɓera ya yi satar daddawa. Ke fa kika ƙwaɗaita mini! Don haka kin fi ni sanin yadda ake haihuwa a ragaya.”

Tana gama faɗin haka ta yi gaba, har ta yi taku huɗu, ta kuma juyowa haɗe da kallon Hajiya Zali sannan ta ce,

“Na manta abu guda mai matuƙar muhimmanci! Muradin kasancewa da shi zan so ya zamana yana cikin hayyacinsa. Ina nufin duk cikin abubuwan da za ki wanzar kada ki ziyarci boka; malamin tsubbi ko ɗan bori, don burina na mallake shi har ƙarshen numfashina, watau fitar rai daga gangar jiki ce kaɗai nake so ta raba ruhinanmu.”

“Da har ina tunanin…”

“Kada ki soma! Billahillazi mutuwa za ta ziyarce ni a lokacin da komai ya wargaje don aikin boka ba dawamamme ba ne. Ni kuma burina ni da shi wani ya yi wa wani wankan gawa. Na bar ki lafiya Hajiyata.”

Ba ta jira amsar Hajiya Zali ba ta fice daga gidan cikin takun kasaita.

Babi Na Daya

“Idan na fahimci bayaninki Alhaji yana son ƙara aure ne don ya tafi da matarsa wurin aiki nasa, saboda kun tara ‘ya’ya ba zai yiyu ya dinga tafiya da ku ba.”

Hajiya Baratu ta faɗa tana fuskantar aminiyarta Hajiya Amina wadda ta gama labarta mata matsalar da take ƙoƙarin tunkaro su.

Ajiyar zuciya Hajiya Amina ta sauke kafin ta furta,

“Haka ya faɗa mana aminiya, har ce masa na yi ya tafi da Hajiya Ikilima, ni zan kula da nata ‘ya’yan amma ya ce ba zai yiyu ba wai aiki zai min yawa. Gara ya ƙara auren, kuma wai budurwa zai aura.”

Hajiya Amina ta faɗa cike da taikaci.

“Budurwa! Tabdijam! Alhajin ne zai auri budurwa don rashin sanin inda ke masa ciwo… da waɗannan shekarun nasa?”

Faɗin Hajiya Baraatu tana kama haɓa.

“Ke ma abun ya ba ki mamaki ko? Ai ni sai da na kusa masassara tsabar tashin hankali. Auransa bai dam ni ba budurwar ce tashin hankalina.”

“Me ya sa ba ki ba shi shawarar auren bazawara ba? Ko ke kina iya haɗa shi da wata, ina nufin cikin ƙawayenki da ba su da aure. Sai ki duba wanda kika aminta da ita ki haɗa shi da ita ya aura don abun kunya ne Alhaji ya auri budurwa.”

“Kina ganin zai yarda da wannan shawarar? Kodayake ba nan gizo ke saƙa ba wacce zan zaɓa masa ɗin ce ban sani ba.”

Wani irin kallo Hajiya Baratu ta yi wa Hajiya Amina kafin ta kaɗa baki haɗe da faɗin,

“Ki je ki yi shawara mana! Kina iya shawara da ‘ya’yanki. Ban ce ki yi shawara da Hajiya Ikilima ba, don ita ma tana iya zaɓa masa cikin kawayanta daga baya su haɗe maki kai, watakila ma sun kora ki daga gidan.”

“Wannan ma shawara ce, kuma maganarki abar dubawa ce. Na gode sosai aminiyata, samun aminiya kamar ki a ɗoran ƙasa sai an tona. Zan yi tunani a kai kamar yadda kika ce, kuma duk yadda na yanke za ki ji ni.”

Hajiya Amina ta faɗa wacce sai a lokacin ne kaɗai ta saki murmushin yaƙe, don ba ta fatan maigidanta ya auro musu budurwa. Ko mace biyu zai aura a rana guda su zama su huɗu tana maraba da hakan, amma ba za ta so a ce mijinta ya rayu a inuwa guda da sa’ar ‘yarsa ba. 

Daga haka suka ci gaba da tattaunawa kafin Hajiya Baratu ta yi wa Hajiya Amina sallama. Tana barin gidan cike da kudiri daban-daban a ranta. Bayan fitarta daga gidan ta furta a fili,

“Ba zan taɓa barin wata mata ta sake kasancewa da Alhaji ba matuƙar ina raye, don irin mijin da na jima ina nema ne a doron ƙasa. Na shirya fuskantar kowaɗanne irin kalubane matuƙar zan rayu a inuwa ɗaya da shi. Wallahi wallahi wallahi ko ina yawo tsirara sai na mallake shi in ya so duniya ta zage ni don na auri mijin ƙawata, kodayake damuwata ba kallon da duniya za ta yi mini ba ne, damuwata ita ce rashin mallakar mijin ƙawata a karo na biyu.”

Salularta ta ciro daga jaka, ta kira wata lamba. Bayan an ɗaga kiran ne ta kwashe da wata irin dariya haɗe da faɗin,

“Shashashar can ba za ta taɓa gane kudirina a kan mijinta ba, ni kuma ba zan taɓa nuna mata shi ba, ina so lokaci ya nuna mata shi haɗe da nusar da ita asalin wace ce ni, na dai ba ta shawarar ta nema masa cikin zawarawan kawayenta mace guda. Dalilina na yin haka kuwa don duk cikin kawayen nata ni ce kaɗai bazarawa. Ina son ganin in da gaske ni ɗin aminiyarta ce kamar yadda take iƙirari.”

Ta tsahirta haɗe da sauraren abin da ake faɗa mata a ɗayan ɓangaren kafin ta ɗora da,

“In kuma ta ƙi zaɓe ta a matsayin matar mijinta dole na fara ziyartar bokaye ko da kuwa zan ƙarar da duk abin da na mallaka a duniyar nan don ba zan taɓa yarda wata mace ta aure shi ba.”

Tana gama faɗin haka ta tari mai adaidaitasahu ta bar unguwar tana ayyana abubuwa daban-daban a ranta game da mijin ƙawarta.

*****

Hajiya Amina ta tara yaranta gabaɗaya a babban falonta, tana labarta musu auran da babansu yake son ƙarawa, ta kuma sanar da su kudirinsa na auren budurwa. Tana neman su ba ta shawara yadda za ta ɓullo wa lamarin, ko kaɗan ba ta son ya auri budurwa, tana tsoron ƙaramar yarinya ta zo ta ɓata musu farincikinsu, ta yi musu rashin kunya a gaban yara. Tun lokacin da ya sanar da ita zai ƙara aure ta susuce ta rasa me yake yi mata daɗi saboda rashin nutsuwa, ko kaɗan ba ta son hayaniya a rayuwarta. Ba ta jin idan maigidanta ya auri budurwa za a haifar musu ɗa mai ido, don ta runtse ido ba ta ga kyan makanta ba, musamman idan ba a yi dacen da yarinyar kirki ba, mafi yawan lokuta yaran sun sauya tunanin mazajensu. Wannan ne dalilinta na labartawa aminiyarta Hajiya Baratu matsalar da take ƙoƙarin tunkaro su, ita kuma ta ba ta shawarar hira da ‘ya’yanta. A ranar ta faɗa musu halin da ake ciki kasancewar duk ba su san dawan garin ba, don aminiyar tata kawai ta san abin da yake faruwa.

Kallonta ta mayar gare su tana jiran abin da za su ce,  su ɗin ita suke kallo musamman yadda ta susuce lokaci guda kamar ba ita ba. Cike da tausayawa Mujahid ya kalli mamarsu yana faɗin,

“Mama don Allah ki daina damuwa da maganar auran nan, ke fa babba ce idan kina tayar da hankalinki yarinya ƙarama za ta shigo ta raina ki. Tun da ya ce da ita zai tafi ki sanyaya zuciyarki, ki nuna masa kamar ba ki san yana yi ba. Don Allah mama ki cire damuwa a ranki kar abun nan ya taɓa ki, kar ki mance kina ɗauke da hawan jini kar damuwa ta yi miki illa.”

Fatima ta yi caraf ta ce,

“Yaya kana goyon bayan auren baba ke nan?”

Wani kallo ya wurga mata kafin daga bisani ya furta,

“Goyon bayan auren baba ko rashinsa ba shi ne damuwata ba. Damuwata halin da mahaifiyata take ƙoƙarin saka kanta saboda auren.”

“Ni dai ba ni goyon baya, na san Aisha da Maryam ma haka.”

Aisha da Maryam duk suka gyaɗa wa Fatima kai alamar maganarta gaskiya ne, yayin da Muhsin babban ɗan Hajiya Amina yake kallon su ba tare da ya furta komai ba. Shi kansa bai son auren da babansu zai yi, amma ba zai zama mai son kansa ba saboda muradin uwa ya tauye na uba ba, dukkansu yana son abinda suke so, don haka sai dai ya lallaɓa mamarsu kar jininta ya hau saboda damuwa. Sai da ya yi jim kafin ya fara magana yana cewa,

“Ki yi haƙuri Ummita! Don Allah kar ki sa damuwa a ranki game da lamarin nan. Kishi bai tsufa a zukatan masoya duk tsufansu, amma a shekarunki ya kamata ki saka wa baba ido a kan abin da zai yi. Dukkanmu ba mu son auren auren amma tun da ya bijiro da shi dole za mu haƙura da shi mu rungume shi hanu bibbiyu.”

“Wai me ya sa maza duk halinku guda… maimakon ku ba Ummi shawara sai ku zo kuna ba ta haƙuri?”

Cewar Fatima ta ƙare maganar tana buga tsaki.

“Kamar yadda ku ma mata halinku guda. Ke don kaniyarki haka ne kike zaune gidan aurenki da wannan banzan kishin?”

Cewar Muhsin wanda yake jifan Fatima da wani irin kallo tun da ta fara magana.

“Yo ni ya isa ma ya ce zai ƙara aure!”

“Fatima!”

Hajiya Amina ta kira sunanta da kakkausar murya, kafin ta ɗora tata maganar da faɗin,

“Ba don wannan shirmen na kira ki ba. Abin da nake so da ku daban amma abin da kuke ce mini daban. Shawararku nake buƙata, shin wa ya kamata na nema wa babanku cikin ƙawayena ya aura, ba na so ya auri budurwa sam!”

“Kina goyon bayan ƙarin auren ke nan Ummi?”

“Ke dan ubanki tashi ki bar gidan nan kafin na saɓa miki. Ban san ranar da kika lalace da shegen kishi ba.”

“Amma yaya…”

“Na ce ki bar gidan nan kafin na ci ubanki!”

Muhsin ya faɗa a tsawace yana huci.

Fatima ta fara gunguni, ganin yana shirin zuwa inda take ta ruga a guje wajen Hajiya Amina tana faɗin,

“Ummi wallahi ki ce kar ya dake ni. Kawai daga faɗar ra’ayina sai cibi ya zama ƙari, ƙari ya zama kababa.”

Ta ƙare sannu-sannu tana goya ɗanta. Tana shirin fita daga falon ya kalli Maryam haɗe da wurga mata harara kafin ya ce,

“Ke uban me kike jira da ba za ki bar gidan nan ba?”

“Shi zai zo ɗauka ta.”

Ta faɗa tana sadda kai ƙasa

“To ku bar falon nan duka tun da na ga alamar duk ba ku da hankali, kuna shirin saka mahaifiyarku cikin tashin hankali. Duk Yarinyar da na ƙara ganin ta ba Ummi gurguwar shawara sai na je har gidanta na ɓalla ‘yar iska. Na ga kanku na shegen motsi don kun yi aure.”

“Aure wasa ne! In fitsari banza ne kaza ta yi!”

Mujahid ya tari numfashinsa tana hararar Muhsin.

“Faɗa masa dai yayana mai sanyin hali.”

Fatima ta yi maganar ƙasa-ƙasa yadda ba zai jiyo ta ba. Daga nan suka fice daga falon ya rage daga Umminsu sai mazan yaran nata.

Cikin kwantar da murya Muhsin ya fara magana yana cewa,

“Da farko ina mai ba ki haƙuri korar yaran nan da na yi ba tare da an samu matsaya ba akan abin da ya tara mu. Ko kaɗan yaran nan ba su san ciwon kansu ba balle su ba ki shawarar kirki.”

Inuwa Daya 2                       >>

19 thoughts on “Inuwa Daya 1”

  1. Ma sha Allah ƙawata, labarin nan ya tafi da imanina, kai daga karantawa kasan ba karamin 6arin basira aka yi ba, Allah ya kara basira da fasaha , muna biye dake

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×