Skip to content
Part 2 of 2 in the Series Inuwa Daya by Nana Aicha Hamissou

Muhsin ya ci gaba da cewa, “Duk halin da ɗan’adan ya tsinci kansa ya kamata ya miƙa lamurransa ga Ubangiji, Shi Zai yaye masa dukkan damuwarsa.” Ya tsahirta yana sake kallon ta kafin ya ɗora da, “Ummita don girman Allah ki kwantar da hankalinki, ki fita sabgarsu, ki nuna tamkar ba ki san abin da ke faruwa ba. Ki mayar da komai ba komai ba.”

Tsit ɗakin har aka ɗauki wasu daƙiƙu ba tare kowa ya ce ƙala ba, kafin daga bisani Hajiya Amina ta ja numfashi tana ɗorawa da,
“Na sani ɗan Hajiya, har yanzu ka kasa gane manufar tara ku da na yi a nan. Shawararku nake nema game da auren da Alhaji ya bijiro da shi. Shin wa kuke ganin ya kamata na zaɓa masa ya aura cikin ƙawayena? Ko kaɗan zuciyata ba ta muradin rayuwa a INUWA ƊAYA da yarinya ƙarama sa’ar ‘ya’yan cikinsa. Na tabbatar idan na nema masa zai yarda da zaɓina. Ai da baƙi ƙirin gara baƙi sau dubu.”

Tana aja aya Mujahid ya magantu, cikin nutsuwa ya fara cewa,
“Ummi kamar yadda Muhsin ya ba ki shawarar fita daga sabgar auren baba, to yana nufin har da nema masa mata kar ki saka hannunki ciki. Me kike tunanin zai faru idan kika nema masa da kanki ba a dace ba? Kar mu tafi da nisa ma, shin kina tunanin zai amince da zaɓin naki…ko kuma kina ganin ba shi da zaɓinsa ne. Mu ƙaddara ma ba shi da zaɓin nasa to idan an dace ba kya tsammanin wacce kika zaɓar masa ɗin ta juya miki baya, idan kuma aka yi rashin dace aka yi auren-je-ka-ka-dawo tabbas baba da ke zai yi kuka. Kin ga an ɓata goma biyar ba ta samu ba, garin shan kunun bayar ludayi kin kifar da na ciki.”
Ya yi shiru yana sake nazarin fuskarta da karantar yanayinta kafin ya ci gaba da cewa,
“Ɗabi’ar ‘yan adam ba kowane mutum ne ya san hallaci ba. Akan kai mutum a inuwa, maimakon ya zauna tare da wanda ya kai shi ɗin, a’a zai yi iya yinsa domin tura shi a rana. Wannan ita ce babbar ɗabi’ar mutane, sun rama hallaci da sharri. Ba a taɓa yi gane halin mutum komai kusancinku sai kuna tarraya akan abu guda sannan halin kowa zai bayyana…”

“Ƙwarai kuwa Mujahid! Ka fahimci duk abin da nake nufi. Ina tare da bayaninka ɗari bisa ɗari. Tun da shi da kansa ya nuna sha’awar ƙara auren ta zuba masa na mujiya. Wannan shi ne kawai abin da ya fi dacewa.”

“Kuna nufin in bar shi ya auri budurwar kamar yadda ya nace?”
Hajiya Amina ta faɗa tamkar wacce aka aiko wa da sakon mutuwa, yadda fuskarta ta yi ƙicin-ƙicin kamar ba ta taɓa sanin wata aba dariya ba balle murmushi.

“Shi ne mafita Ummi.” Cewar Muhsin yana kallon Mujahid da yake faman gyaɗa masa kai kamar kadangare.

“Sai nake ganin budurwa za ta ɓata farincikin gidan nan,
Sai nake ganin babban abin kunya ne Alhaji ya auri budurwa,
Sai nake ganin ku kanku abun kunya ne a ce mahaifinku ya auri budurwa,
Sai nake gani ku kanku za ku zama abun gulma cikin gari,
Za ku zama tamkar jirgin sama, kuna wucewa ana daga kai ana kallon ku.”

Ta tsagirta tana kallon su kafin ta ci gaba da cewa,
“Wannan ne babban dalilin da ya sa na kasa jurewa har na nemi tsokacin Hajiya Baratu, ita kuma ta ba ni shawarar nema masa cikin ƙawayena gudun samun matsalar daga nake hangowa daga wurin hudurwa. Ni kuma kaina ya cushe, ƙwaƙwalwata ta tafi hutun wucin gadi, zuciyata ta yi ammana da shawararta. Na ga ya dace na tuntuɓe ku nema mini mafitar wadda kuke ganin dacewarta da abbanku.”

Dukkaninsu shiru suka yi, kowa da bikin da zuciyarsa. Musamman kalamanta na sanyo ƙawarta Hajiya Baratu, sun samu matsaguni a zuciyoyinsu. Kallon ta Mujahid ya yi yana son yin magana amma bai son ranta ya ɓace, saboda maganar da zai yi allura tana iya tono garma, amma dai zai bi yadda take so don yana son kawo ƙarshen abotar mamarsu da Baratu. Da ma can ba ta wani kwanta masa a rai ba yadda take yawan zuwar musu gida. Abub ya ishe shi bai son mace da yawo sam a rayuwarsa.
Ta kashe aurenta ba ta nan, ba ta can, ta rasa mai kwasar ta shi ne ta ba Umminsu shawarar nemo wa babansu bazawara. Saboda ta ga mahaifiyarsu ba ta da matsala kuma ita ce mamar tasu take yawan kira da ƙawarta saboda jimawarsu a tare. A ganin ta idan mamar tasu ta yi shawara da su ita ɗin ce za su zaɓar mata saboda kusancinsu. Wannan shi ne hasashen da ya darsu a zuciyarsa ko da ya ji bayanin mamar tasu. Ita kuma ga dukkan alamu ba ta gane komai ba.

Lallai yanzu ya sake tabbatarwa mace idan tana neman mafita kowa kan iya ba ta shawara kuma ta ɗauka, ba tare da la’akari da wasu abubuwa ba da kuma zurfafa bincike. Ba don haka ba tun a wancan lokacin ya kamata mamarsu ta gane manufar Hajiya Baratu. Kodayake ba lallai ba ne tunaninsu ya zama ɗaya ba, kowane mutum da inda ya sa gaba. Amma shi kai tsaye ko da ta faɗa masa haka, ya gane manufar Baratu, so take ta yi jifan tsuntsu biyu da dutse ɗaya. Da kyar ya samu dama furta mata,

“Kin san wa Hajiya Baratu take so ki zaɓa wa baba?”

“A bayyane yake mana! So take a zaɓar miki ita matsayin abokiyar zama. Ni tuni na fahimci wannan karatun.”

Muhsin ne mai maganar yana kallon Mujahid, shi ma shi yake kallo cikin mamakin kalamansa da suka zam irin guda da tunaninsa. Wannan shi ake ce wa na riga ka da zuci ka riga ni da baki. Watau hasashensu ɗaya da shi ke nan.

“Kai ba ni son shashanci! Ka san me za ka faɗa mini kuwa? Ko asiri aka yi Baratu ba za ta auri Alhaji ba balle tana cikin hankalinta. Ka san wace ce ita kuwa… ka san shekararmu nawa tare da ita kuwa… ka san abotarmu tun ta yaushe ce… me ya sa ana maganar gaskiya kana sanyo mana tatsuniya?”

“Ba tatsuniya ba ce Ummi, zahirin gask…”

“Ku tafi na sallame ku, kar ku tayar mini da hawan jini.”

Duk yadda suka so su yi mata bayani ƙi ta yi a cewarta sun fara kawo mata shirme. Ban da shirme ta yaya za su dubi tsabar idonta su ce mata Hajiya Baratu tana son Alhaji… ai ko a garin mahaukata da maciya amana hakan ba za ta taɓa faruwa ba.
Babu yadda suka iya suka fice daga falon suna ba ta hakuri saboda tausayin ta da suke ji. Da ma abin da Mujahid ya yi gudu ke nan, shi ya sa ya kasa faɗa mata abin da yake hangowa wanda ba lallai ba ne ita ta hango shi. Ga shi ta ƙi ba su haɗin kai balle su yi mata bayanin yadda za ta fahimta. Da wannan tunanin suka yanke shawarar yadda za su yi wa abin tufkar hanci don suna ganin yadda mamarsu ta rikice tamkar ba ita ba.

*****
A nata ɓangaren ba ta wani ɗauki maganar tasu da wani muhimmanci ba, shirme ko wasan kwaikwayo ta ɗauke ta. Ba ta hango ta yadda za a yi al’amarin da suka faɗa mata ya yiyu ba. A ganin ta ko wasan kwaikwayo ne wacce ta fito matsayin Baratu sai an yi mata alawadai balle a zahirin gaskiya. Don haka ta tattara maganganunsu ta watsar ba tare da samun wani matsuguni a zuciyarta ba.

Sai ta mai da hankalinta kacokan ga tunanin yadda za ta nema masa bazawara, tun da ‘ya’yan nata sun ƙi mai da hankali ga batun nata. Ta kwashe lokaci mai tsayi tana tunani har dare ya yi mata ta kasa tabuka komai.

Tana nan zaune ta yi zurfi a tunani Alhajin ya shigo ɓangarenta ba tare da ta sani ba, sai da ya taɓo ta ne ta ankara da shi. Sannu da zuwa kawai ta yi masa ta ci gaba da sabgarta don ba ta buƙatar doguwar hira da shi matukar ba ta fasan auren budurwa ba ce. 

Shiru ya ratsa ɗakin na lokacin mai tsayi, kowa da bikin zuciyarsa tsakaninsu.

“Amina me yake damun ki?”

Muryarsa ta fasa dodon kunnenta da wani amo mai ɗaci. Wani tuƙuƙin baƙinciki ne ya taso mata jin kalaman maigidan nata gare ta. Watau bai ma san shi ne damuwar tata ba ko? Har yake da bakin da zai dubi idonta ya furta mata tambayar abin da yake damun ta? Sai da ya sake tambayar ta, ta buɗe baki da kyar tana furta,
“Ba komai.”

Tana gama faɗin haka ta fice daga falon zuwa ɗakin baccinta tana jin ciwo a zuciyarta.

Bin bayanta ya yi da kallo yana mamakin sauyawar ta lokaci guda daga bijiro da maganar aurensa. Ko lokacin auren Ikilima ba ta nuna ƙin aurensa ba sai yanzu da girma ya kama ta, kuma ba ita za a yi wa kishiyar ba.

‘Koda yake ta faɗa mini ba ta damu da aurena ba matuƙar bazawara zan aura.’
Ya raya a zuciyarsa. Kafin daga bisani ya  furta a fili yana cewa,
“Mata rigima!” Ya ƙarashe maganar da bin bayanta a ɗakin. Da kyar ya samu ta yi masa magana bayan an kai ruwa rana yana rarrashin ta.

“Me ya sa ba za ka haƙura da auren nan ba?”

Ta yi furucin ba tare da ta kalle shi ba, domin ita kaɗai ta san abin da take ji a ranta.

“Amina me ya sa kika damu kanki da aurena fiye da Ikilima, wacce ita za a yi wa kishiya?”

“Saboda yaranta manya maza ne. Ni kuma nawa mata ne waɗanda suke munzalin aure, kuma sa’annin wacce ka buga kai da ƙasa ka ce ita za ka aura. Da a ca ba ni da ‘yan’mata ko kallo aurenka bai ishe ni ba balle na damu da shi. Ina tsoron ta shigo gidanka ta ɓata mini tarbiyar yara. Me kake tunanin zai faru idan ‘ya’yanka mata suka ga rayuwar da za ka yi da sa’anninsu?”

“Tun farko na faɗa miki makasudin auren nan. Ba nan garin zan zauna da matar ba balle wani abu marar daɗi ya faru da ba a fatan shi.”

Ba ta ce masa komai ba ta haye gadonta tana jan bargo. Ita har ga Allah ba ta son ya yi auri budurwa ne saboda kar a ɓata mata yara, wasu ‘yan’matan da suke auren tsofin maza rawar kan tsiya ce da su. Wasu ba su da kirki kowacce irin badala yi suke yi gaban ‘ya’yan miji, babu ruwansu da kunyar ‘ya’yan miji mace ko namiji.  Tana tsoro a auro budurwa ta mai da mata miji yaro, ya dinga yin abinda bai kamata ba gaban ‘ya’yansa. Abubuwa marasa daɗi da ba ta fatan faruwar su su fari. Wannan ne abin da ya ɗaga mata hankali ta kasa jurewa, har sai da ta bayyana wa ƙawarta sirrinta wanda sam bai kamata ba a zamantakewar yau da kullum ta mata da miji mace ta dinga barbaɗa sirrinta komai ƙanƙantarsa ga mutanen gari. Amma yaya ta iya da samarin kakaninta? Ko yanzu sai ta kuma komawa wajen Baratu neman shawara domin waɗanda take ganin za su taimaka mata da ita sun kasa ba ta haɗin kai, don haka gobe za ta kuma neman Baratu ko za ta iya hango mata wacce ta dace da mijinta.

*****

“Akwai wata babbar giwa da nake miki fatan dacewa da ita, idan ta faɗi za a sha romo kuma a ci nama sosai. Babban abin birgewa tana da kyau da ɗaukar ido ga duk wanda ya yi tozali da ita.”

Hajiya Zali ce mai maganar, yayin da Fadila ke kwance ta yi filo da ƙafafuwanta.

Ɗago kai Fadika ta yi tana kallon ta kafin ta furta,

“Wannan kurman zancen fa Hajiyata!”

“Kar ki damu da kurmancinsa, abin da nake son sani shin har yanzu wancan burin naki da muka hardace yana nan? Saboda giwar da nake magana tana yanayi da burinki. Sai dai shekarunta sun ja, za su yi ukun naki ban sani ba ko hakan zai kawo miki cikas wajen mallakar ta ba. Shi ne nake tunanin ko za ki so ta duk da akwai…”

“Ki yi mini gwari-gwari yadda zan fi fahimtar karatun naki.”
Fadila ta katse ta da sauri domin ta ƙagu ta ji asalin labarin.

“Wani lokaci mamaki kike ba ni tamkar ba Bahaushiya ba. Turawa duk sun ɓata ku, komai sai sai an yi muku dalla-dalla matuƙar aka yi amfani da Hausa, da yaren masu jajayen kunnuwa ne da tuni har an wuce wajen.”

“Hausar ce tamu da wahala sosai. Yanzu baje mini karatun faifai yadda zan fahimci sakon da kike son isarwa. Don na matsu na ji wace ce giwar da kike magana.”

“Hmmmm!” Hajiya ta ja numfashi kafin ta ɗora da,
“Aka ce babanku aure yake son yi?”

“Haka nake jin labarin ni ma.” Ta tsahirta kafin ta ci gaba da faɗin,
“Amma muna maganar giwa me ya kawo zancen babanmu? Ni fa na matsu na ji bayanin da za ki yi mini.”

“Ina ba ki kina roko! Me kike ci na baka na zuba?”
“To na yi shiru. Ba zan ƙara roko ba.”
Ta faɗa tana sakin murmushi, ita ma Hajiyar martanin murmushin ta mai da mata kafin ta ci gaba da cewa,

“Babanku ne giwa! Ki je ki yi nazarin maganganuna sai ki dawo mu ɗora sabon darasi. Na ga alamar ba kya fahimtar karatunki da kyau.”

“Baba kum…”

Ba ta ba ta damar nisa da zancenta ba ta katse ta,
“Ki yi shiru, sannan ki yi nazari za ki gane komai. Matsalar rashin nazari ne kafin amsa tambaya shi ya ke sa a kasa gane komai.”
“Na kasa gane komai fa.”
“Fadila ke nan! Wa ya ce miki sha yanzu magani ake yi?”
Ba ta kuma cewa kala ba ta shige ɗaki tana sake nazartar kalamanta.

*****

“Sun ƙi ba ni haɗin kai aminiyata. Duk yadda na so su taya ni nema wa Alhaji mata abun ya ci tura. Haƙuri kawai suka ba ni wallahi, wai in bar shi ya zaɓa da kansa na fita ma sabgarsa. Halin maza duk iri ɗaya ne wallahi, sai dai wani ya ɗara wani.”

“Maza kuma! Ina su Fatima da A’isha? Su ma goya wa baban nasu baya suka yi?”
“Ina fa! Neman haukace mini suka yi ma da suka ji zai auri budurwa. Ban son saka su a sabgar nan, su ji da gidajensu.”

“Kamar yaya?”

Baratu ta faɗa tana jin haushin kalaman Amina, tamkar tuwan kwantowa a bakinta, zafin su tamkar ana zuba mata ruwan dalma a kunne. Ji take tamkar ta shako wuyan Hajiya Amina ta rufe ta da duka, tun da suka yi waya da Aminar ta faɗa mata janyewar ta daga sabgar nema masa aure take jin haushi kuma ta kullace ta sosai. Wani yanayi ta shiga da ba za ta isa faslita shi ba, har ma ta kasa ba ta wani haɗin kai a wayar shi ne ta isko ta har gida domin su zanta.

“Kamar yadda kika ji na faɗa miki a waya ɗazu,to babu wani abu da ya sauya!”
Ba tare da Baratu ta ce komai ba, Hajiya Amina ta kwashe yadda suka yi da ‘ya’yanta ta faɗa mata, abi guda ne ta ɓoye mata watau zancen su Majahid da suke ikirarin Baratu so take Alhaji ya aure ta.

<< Inuwa Daya 1

3 thoughts on “Inuwa Daya 2                      ”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.