Skip to content

Sharhin littafin ‘Alkalamin Kaddara’ 1 & 2 na Lubna Sufyan

Sunan Littafi: Alƙalamin Ƙaddara (1&2)

Marubuciya: Lubna Sufyan

Inda aka Buga Littafi: Bakandamiya Hikaya (Online)

Shekarar Bugu: 2022

Yawan Babi: Littafi na ɗaya: 11, Littafi na biyu: 41; Jimilla: 52

Mai Sharhi: Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)

Manufar Sharhi: Bunƙasa Harshen Hausa da ciyar da adabi gaba

Gabatarwa

Akan ce ka gode wa Allah a kowane irin yanayi ka tsinci kanka, saboda komai ƙuncin da kake ciki wani ya fi ka. Haka kuma komai jin daɗin da kake ciki shi ka wani ya fi ka. Kuma masu iya magana na cewa ‘Ƙaddara ta riga fata’ wato abin duk da Allah ya ƙaddara zai same ka, to baya yake da abinda kowa zai yi maka fatan ya same ka. Kowa da irin wannan tasa ƙaddarar, in ka ci ta wani ta fi taka daɗi, ta wani kuma in da za ka ji sai ka yi kuka. Shin da wacce irin tawada alƙalamin ƙaddarar mu ya yi mana rubutu, wacce irin ƙaddara ce ke kan kowannen mu, ya za mu yi idan muka wayi gari wata mummunar ƙaddara ta afka mana? Waɗannan da ma wasu tarin abubuwa duk suna nan a ƙunshe cikin wannan hamshaƙin littafi mai suna Alƙalamin Ƙaddara.

Tarihin marubuciyar a taƙaice

Marubuciya Lubna Sufyan an haife ta ne a ƙaramar hukumar Ingawa da ke birnin Katsina. Fitacciyar marubuciyar ta fara karatun addini tun tana ƙarama kuma ta yi karatunta na Firamare ne a garin Katsina, daga baya ta koma garin Kano inda ta yi karatun Sakandire har ta gama. Bayan ta gama ne sai ta koma Katsina in da ta yi karatun Diploma a ɓangaren zanen taswirar gidaje. Daga baya kuma ta ci gaba da karatu a mataki na gaba, wato babbar Diploma wadda da turanci ake ce wa Higher National Diploma (HND) a Kaduna.

Kamar mafi yawancin marubuta, marubuciyar ita fara rubuce-rubuce ne tun tana makaranta, kuma ta kasance ɗaya daga cikin fitattun marubutan online na wannan zamani, domin abu ne mai wuya ka faɗi sunanta a duniyar marubuta da makarantan wannan zamani ba a samu wanda ya santa ba. Zuwa yanzu marubuciyar ta rubuta litattafai sama da guda goma sha ɗaya. Wasu daga cikin litattafan da ta rubuta sun haɗa da;

  • Rai Da Ƙaddara
  • Wata Bakwai
  • Akan So
  • Rayuwar Mu
  • Abdulƙadir
  • Mijin Nobel
  • Martabar Mu
  •  Alƙalamin Ƙaddara da dai sauransu

Har’ilayau kuma, marubuciyar ta kasance mai son girke-girke ce sosai. Kuma baya ga rubutu, marubuciyar tana yin fassara daga harshen Turanci zuwa Hausa, wannan aiki na fassara ne ma ya zama sanadin yin aikinta da kamfanoni da ƙungiyoyin gwagwarmaya masu zaman kansu a lokuta daban-daban a kuma kan batutuwa iri daban-daban kamar su GiveNorthEducation, WomenInArewa, WomenInFinance da dai sauransu. Sannan kuma, marubuciyar ta sha yin aiki da makarantun Islamiyya da bloggers wajen fassara musu aiyukansu. Haka kuma ƙwararra ce wajen  haɗa ɗuwatsun ƙawa na adon mata. Sannan kuma tana aikin juyar da bayanan murya zuwa rubutu (transcription). A taƙaice dai, duk in da aikin rubutu yake, to a nan marubuciyar ta fi ƙarfi.

Marubuciyar kuma na ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar marubuta na Fikra Writers Association. Lubna Sufyan ta yi aure a shekarar 2022, kuma tana zaune ne a garin Kaduna yanzu haka.

Labarin a Taƙaice

Mahaifin Tasneem mai suna Muftahu wanda aka fi sani da Abba, wani mutumin kirki ne talaka mai neman na kanshi domin ganin ya rufa wa kanshi da ahalinsa asiri. Amma matarsa Bara’atu wacce ake kira da Ummi irin matan nan ne da basu da godiyar Allah. Duk abinda ya kawo bata godewa, kuma sai ta fita ta je inda take so ba tare da ta tambaye shi ba, yaran kuwa bata kula d su yadda ya kamata. Kullum cikin maula take tare da kiran babu. Bisa wannan dalili ne har ƙaddara ta kai Tasneem wani gida a matsayin ‘yar aiki har yaron gidan ya yi mata fyaɗe. Wannan ne ya jawo silar da ta fara biye-biyen maza domin ta kula da ƙannenta.

Hankalin Tasneem ya yi matuƙar tashi sakamakon asirinta da ya tonu tun a daren ta na farko da auren Rafiq. Domin kuwa Ya gano cewa bata zo gidan shi da budurcinta ba Wannan yasa ta shiga tashin hankalin da har zuwa ƙarshen littafi na biyu bata fita daga cikin shi ba.

Alhaji Mustafa Shettima wanda tsohon lauya ne, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa ya kasance yana iya yin komai don ganin ya cimma burikansa na siyasa. Ciki kuwa har da yi ‘yarsa auren dole ta hanyar roƙonta da ta auri wanda bata taɓa gani ba, ita kuma ta amince saboda biyayyarta, duk kuwa da cewa tana da wanda take so wato Muneeb.

A gefe kuma ga Altaaf da matarsa Majida waɗanda ke neman haihuwa ruwa a jallo amma basu samu ba. Kwatsam! Sai Altaaf ya gano cewa yana da yara ‘yan biyu a wani ƙauye waɗanda Nuwaira ta haifa ba tare da ya sani ba bayan ya mata fyaɗe shekaru da dama da suka wuce.

Ashfaq, wanda mutuwar mahaifansa da ta ‘yan uwanshi har guda biyu tare da ɓacewar ƙanin shi ɗaya suka sa shi neman kuɗi ido rufe domin kauce wa ƙaddarar talauci kuma na kwance yana jinyar raunin harbin da aka yi mishi da bindiga sakamakon harƙallar miyagun ƙwayoyi da ta haɗa shi da wasu. Ga kuma ƙaninsa watau Tariq wanda shi kuma yake fama da jarabar shan kayan maye wadda ya kasa dainawa, duk kuwa da cewa har gidan nahaukata ya taɓa zuwa a dalilin hakan.

Rafiq na cikin tashin hankali na sanin cewa matar da ya aura ta san wasu mazan a waje, sai kuma wani sabon tashin hankalin ya faɗo mishi, domin kuwa baya iya tuƙi sai dai a tuƙa shi, duk kuwa da cewa yana iya tuno lokacin da yake tuƙin da kanshi. A gefe kuma ƙanwar shi da aka yi wa auren dole ta kira shi tana neman ya zo ya ɗauke ta sakamakon azabar da take sha a gidan mijin ya ishe ta. A daidai lokacin da ya gano cewa hatsarin mota ne da ya yi ya sa ya manta rayuwarsa ta baya, a daidai wannan lokacin ne kuma ya gano cewa wannan hatsarin ne ya yi sanadiyyar mutuwar matarsa da ‘yarsa waɗanda ya kasa tuno ko da sunan su balle rayuwar da suka gudanar a tare.

Jigo

Ko daga ɗan taƙaitaccen bayanin da aka yi dangane da labarin a dunƙule, na san cewa mai karatu zai iya fahimtar cewa babban jigon wannan labari shi ne ‘Ƙaddara’ kamar yadda sunan littafin ma ya nuna. Dalilin faɗar wannan magana kuwa ba ɓoyayye ba ne, saboda kusan duk taurarin da ke cikin labarin an fi maida hankali ne akan irin yadda ƙaddarar su ta kasance daga farko, tsakiya da kuma ƙarshen labarin. Kuma batun ‘Ƙaddara’ shi ne wanda aka fi magana a kai.

Wasu na iya ganin soyayya a matsayin babban jigon Alƙalamin Ƙaddara. Wannan za ta iya kasancewa. Saboda an dabaibaye labarin cikin harkokin soyayyar da ta kasance tun farko a tsakanin Rafiq da Tasneem, Rafiq da Samira, Fadila da Nawfal, Zafira da Muneeb inda ta ƙare da da soyayyar ɓangare uku wadda ta wanzu a tsakanin Hamna, Tariq da kuma Tasneem duk kuwa da cewa ita Tasneem ɗin bata san cewa Tariq ɗin yana sonta ba.

Bayan wannan babban jigo da na yi bayani, marubuciyar ta yi amfani da ƙananun jigogi masu yawan gaske waɗanda su ne suka haɗu suka goya wa labarin baya ta hanyar koyar da darussa da dama a cikin wannan labari. Ga wasu kaɗan daga cikin su kamar haka:

• An nuna mana irin yadda soyayya take da ƙarfin canza rayuwar mutum gaba ɗaya, da kuma irin yadda rashin masoyi ka iya jawo dagulewar rayuwar mutum. Misali, dubi yadda Muneeb yake bayyanawa Zafira irin yadda yake ji a ranshi da ya ji za ta auri wani, “Bazan iya ba, na kasa tuna yadda rayuwata take ba tare da soyayyarki ba, wallahi bansan ya duniyata zata kasance babu ke a ciki ba…” (Littafi Na 1, babi na 11)

Dubi kuma yadda aka bayyana wata ɓoyayyiyar soyayyar da ke tsakanin Tariq da Hamna,

‘kuma kullum sai ta mishi text ɗin gaisuwa da safe, da dare kuma ta sake tura mishi wani, duk da ba kullum take samun amsa ba, bata damu ba, a kalar son da take ma Tariq bata jin wani sauran aji a tare da ita, wani lokaci cikin dare takan farka haka kawai da tunanin shi manne a zuciyarta da yake hanata sukuni, haka zata ƙare daren da yin salloli da neman mafita. (Littafi na 2, babi na 38)

• Matsalar sangarta yara da iyaye ke yi saboda mugun so tare da kauda kai akan laifukansu, musamman iyayen mu mata ba sabon abu ba ne amma yana da hatsarin gaske. Domin kuwa shi ya jawo lalacewar Altaaf har ya ɗauki mugayen halaye waɗanda har suka kai shi ga aikata munanan laifuka, ciki kuwa har da fyaɗe. Ba laifi ba ne don iyaye sun so ‘ya’yansu, amma in soyayyar ta yi yawa sai gata ta yi yawa, hakan kuma ke jawo matsala mai girman gaske. Kuma marubuciyar ta yi ƙoƙari sosai wajen fayyace irin yadda iyaye masu irin wannan tunanin suke ji kamar yadda ta bayyana da cewa, ‘..tunda ya bar gidanta kuma ta shiga ɗaki ta kwanta don zazzaɓi take ji ya rufeta, tunani take tunda ya fita daga gidan na lokacin da rayuwar Altaaf ɗin ta gurɓata haka bata sani ba, tunanin inda ta yi kuskure take yi ta rasa.  (Littafi na 2, babi na 30)

Da kuma inda ta ce,

‘Ba za ta ce ga asalin abinda take ji akan ƙaddarar da ke faruwa da Altaaf ba, tana kula da kallon da Baba yake mata jiya kamar laifinta ne abinda yake faruwa da Altaaf ɗin yanzun. In tambayar ta yayi ba za tai mishi musu ba. Amma kuma bata jin dana sani a ƙasan zuciyarta, bata san ko don Altaaf ɗin ya canza ba ne ba yanzun. Abu ɗaya ta sani, in za’a bata damar komawa baya, ba zata sake abu ɗaya akan yadda ta taso da Altaaf ba, bata dana sanin gatan da ta nuna mishi ko kaɗan, in zata iya mishi fiye da wanda take bashi a yanzun zata yi . Wannan kalar ƙaunar kawai ta sani. Yanzun ma da zata iya ɗauke mishi damuwar da take bayyane akan fuskar shi zata ɗauke ya samu sauƙi. (Littafi na 2, babi na 33)

• Talauci ba hauka ba ne, kuma in da kwaɗayi to fa akwai wulaƙanci. An nuna mana irin yadda illar kwaɗayi da son abin duniya suke akan mahaifiyar su Tasneem, domin har ta kai ga tana zagin ‘yarta tare da tursasa ta akan ta fita yawon siyayya da wani don ta samu abin duniya ba tare da duban matsalar da hakan ka iya jawowa ba. Kamar yadda a littafi na 1, babi na 1 take cewa,

“Ke wacce irin yarinya ce marar rabo? Arziƙi na binki kina runtse ido? In ke halin ƙuncin da muke ciki ba ya damunki sai aka ce miki ni ba ya damuna? Don ubanki yaushe za ki yi hankali?”

• Mutuwa mai tonon silili! An nuna mana yadda mutuwa iya tarwatsa ahali gaba ɗaya, domin kuwa mun ga yadda hakan ya wanzu ga su Ashfaq bayan mutuwar iyayen su.

Sannan mun ga yadda mutuwar mahaifi ta ƙara jagula rayuwar su Tasneem da ƙannenta.

• Rashin tsayayyen namiji a gida ba ƙaramin abu ba ne, kuma mun ga irin illar da ke cikin hakan a rayuwar Altaaf. Shi kanshi Altaaf ɗin daga baya sai da ya fahimci matsalar da ke cikin hakan kamar yadda marubuciyar ta bayyana da cewa,

‘A tsawon rayuwar shi ba wai ya damu da Baba bane, asali ma komin shi Ammi ce, kuɗin kashewa, kayan sakawa, matsalar makaranta, ba zai tuna rana ɗaya da Baba ya ɗauki kuɗi ya bashi ba, ko ya bashi kaya a matsayin wannan shi ya siya mishi. In ma yana yi ɗin sai dai ko ta hannun Ammi hakan ke faruwa kuma bata taɓa faɗa mishi ba. Maganar da ta wuce minti sha biyar bata haɗa shi da Baba. (Littafi na 2, babi na 30)

• Marubuciyar ta fito da illar da ke cikin zuwa gidan miji ba tare da  budurci ba ga ‘ya mace. Domin ta bayyana yadda duk soyayyar da ke tsakanin Rafiq da Tasneem ta fara barazanar tarwatsewa tun a farkon labarin. (Littafi na 1, babi na 1)

• Biye-biyen mata ba aiki ba ne nagari. Kuma marubuciyar ta nuna mana haka a wurare da dama a cikin labarin, musamman akan rayuwar Altaaf.

• An kuma nuna mana illar shaye-shaye akan rayuwar Tariq da cewa,

‘Idanuwan shi kafe suke akan kwalaben kodin ɗin da ke gabanshi. Hannuwan shi da suke a dumtse har ƙaiƙayi suke mishi na son ɗaukar kwalbar. Zai iya rantsewa har kan harshen shi yana jin ɗanɗanon haɗin da yake cikin kwalbar da ya fi komai tafiyar mishi da damuwa. (Littafi na 1, babi na 1)

•  Soyayyar ‘yan uwa tana girma da muhimmanci sosai, kuma marubuciyar ta nuna yadda hakan ya yi tasiri akan Rafiq da ‘yan uwan shi, watau fawzan, Aroob da Zafira. Kamar yadda ta nuna akan Su Tasneem da ƙannenta da kuma Altaaf da ƙaninsa Aslam da kuma Ƙanwarsu Barrah. Su ma su Ashfaq hakan ya yi tasiri sosai akan tasu rayuwar tun daga farko har ƙarshen labarin.  Dubi dai yadda hankalin Rafiq ya tashi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci a littafi na 1, Babi na 2 akan rayuwar Fawzan.  “Na zo gida ne, babu kowa sai Asabe. Ta ce Fawzan yana nan, kuma ɗakin shi a kulle. Ban san ko meye ba… Kawai bana jin yanayin na min daɗi.”

• An nuna irin yadda auren dole ke wargaza wa ‘ya’ya mata rayuwarsu akan Zafira sakamakon aurenta da Omeed. Dubi hujjojin da mahaifin Zafira ya yi amfani da su wajen bayyana mata dalilin shi na son ta auri wanda ya zaɓa mata,

“Ba ƙaramin gida bane ba, yaro ne da ya fito daga gidan mutunci…”

“…Ina son ki sani yana da matuƙar muhimmanci a wajena, zan rasa abu da yawa in baki amince ba, a karo na farko ina roƙonki da ki amince Zafira…”

“Ina son ki auri ɗan gidan Alhaji Yusuf Modibbo ne…”

“Auren ki da shi na da muhimmanci a wajena. Karki ce a’a Zafira. Na riga na amsa musu…”

(Littafi na 1, babi na 11)

To dubi kuma yadda aka bayyana kaɗan daga cikin matsalar irin wannan auren, wanda shi ne rashin barin matar ta ziyarci danginta a littafi na 1, babi na 2 da cewa,

“Duk sanda kaso kake zuwa ka ga naka ‘yan uwan… Ban san me yasa kake hanani zuwa ganin nawa ba.”

• Haƙiƙa fyaɗe wani abu ne da ya zama ruwan dare a wannan zamanin. Kuma marubuciyar bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen bayyana irin yadda hakan yake da illa ga rayuwar ‘ya’ya mata ba. Domin ta bayyana yadda hakan ya zama silar lalacewar Tasneem ta fara bin maza, da yadda Nuwaira ta kasa samun mijin aure, da kuma yadda ya zama silar mutuwar Arifa.

• Tsakanin mata da miji sai Allah. Wannan littafi ya ƙara tabbatar da wannan maganar ta hanyoyi da dama. Dubi yadda Tasneem ke ƙoƙarin kwantar wa da Rafiq hankali duk da cewa ciwon zuciya da tashin hankali na damunta.

“In kuka za ka yi ka yi, in wani abu kake son fasawa ka tashi in raka ka akwai abin fasawa da yawa a gidan… Ko me kake jin yi, idan akaina za ka huce ka yi, ka yi ko me kake tunanin zai sama maka sauƙi Sugar, don Allah, ganin ka haka na karya min zuciya…” (Littafi na 2, babi na 29)

Da kuma inda aka nuno Majida wadda duk da fushin da ta yi da Altaaf bayan ya bayyana mata cewa yana da yaran da ya samu ‘yan gaba da Fatiha take ƙoƙarin ganin ta kwantar mishi da hankali bayan ta sauko da cewa,

“Mi za mu yi yanzun? Yaran fa?” (Littafi na 2, babi na 35)

• Zina mummunan aiki ne da ke kawo matsalolin da Allah kaɗai yasan yawansu a cikin Al’umma. Marubuciyar ta yi ƙoƙari sosai wajen nuna illar hakan akan tauri irin su Altaaf, Tasneem da Fadila. Amma kuma an nuna yadda kowa ƙaddarar shi ke canzawa domin Wadata da su Yaks basu shiga irin wannan hali ba duk da cewa suma sun yi. Hakan ke nuna cewa in Allah ya so sai ya yafe maka kuma ya rufa maka asiri, ko kuma ya bari sai ka koma gare shi tukunna

• Wani Muhimmin ɓangare da marubuciyar ta taɓo kuma shi ne irin yadda masu Makarantun kuɗi ke shiga ƙalubale a ƙoƙarin su  na ganin sun farantawa yaran mai kuɗi ko dai saboda kwaɗayin abinda suke samu a wajen iyayen yaran ko kuma don ganin yaran basu bar makarantar ba. Kamar yadda marubuciyar ta bayyana da cewa,

‘Numfashi Principal ta sauke. Kanta har ya fara ciwo, sosai ta gaji da Altaaf a makarantar ta, babu yadda zata yi ne kawai shi yasa. (Littafi na 2, babi na 12)

• An nuna mana yadda yin zaɓi mummuna ke sa watarana mutum ke ƙarewa cikin da na sani da nadama. Kalli yadda aka bayyana halin da Altaaf ya shiga da cewa,

‘…tun lokacin da yaima Nuwaira abinda yai mata yake neman hawaye ko zai samu sauƙi amma ya rasa su, haka lokacin da Wadata ya ce baya son ganin shi, da lokacin da yai ma Ashfaq abinda yai mishi, da duk wani lokaci bayan ya gane yayi kuskuren da ba duniyarshi kawai zai taɓa ba har lahirarshi. Kuka yake yau na abinda ya rasa, kuka yake na yadda zaɓukan da yayi a rayuwarshi suka jefa kokwanto a cikin lahirarshi. Kuka yake na komai da komai. (Littafi na 2, babi na 30)

Dubi kuma yadda Tasneem ta tsare Ummi take cewa,

“Na faɗa miki idan aurena ya mutu a daren farko ke ce, ke ce Ummi, tun a daren ya mutu bai faɗa min ba ne sai yau. Kin rasa surikin da kike mafarkin samu Ummi, bazan yafe miki ba kamar yadda Abba ma ba zai yafe miki ba…” (Littafi na 2, babi na 31)

Ga kuma halin da Ummi ta shiga biyo bayan wannan maganar,

‘Zuciyarta na fara wata irin dokawa kamar zata fito daga ƙirjinta. Yadda lokaci ya ƙure mata take gani, bango ta kama tana miƙewa, da gudu ta ɗauki buta tana zagayawa banɗaki don cikinta ya kaɗa. Tana da tabbaci babu abinda zai hanata dakuwa a hannun mala’iku saboda laifukanta masu girma ne, tana tsoron mutuwa, amma bata taɓa jin tsaronta irin na yau ba.’

‘Saboda ba wai rasuwar shi take ma kuka ba a wannan lokacin, ɗan abinda yake kawowa da zata rasa shi ne matsalarta. Yanzun kuma sosai take kukan rasuwar shi, take kukan yadda bata da tabbacin ya yafe mata laifukan da ta dinga yi mishi da ƙuncin data dinga saka shi, bata ma taɓa ganin laifinta ba balle ta yi tunanin ta bashi haƙuri. (Littafi na 2, babi na 31)

Shi kanshi mahaifin Altaaf yayi tashi nadamar kamar yadda marubuciyar ta bayyana da cewa,

“Ina amsa sunan mahaifinka ne kawai, amma ban taɓa zame maka shi ba. Wannan kuskurena ne, bazan ɗora shi akan kowa ba. Duk da na sha gaya ma kaina ɗan Ammin shi ne fiye da yadda yake ɗanka… Ko ba komai ya kwanta a cikin ta, ƙaunar da ke tsakanin su abune da ba za ka taɓa fahimta ba…” (Littafi na 2, babi na 33)

Ammi, wacce ta yi sanadiyar lalacewar Altaaf ma ta yi tata nadamar,

‘Amma yau cikin idanuwa Barrah ta kalleta tana faɗa mata ta cuci Altaaf, cikin su ma ba kowa ba sai Altaaf, yaron ta da take jin in aka bata dama zata kwashe sauran shekarun da suka rage mata a duniya ta miƙa mishi, yau shi Barrah take faɗa mata ita ce sanadin duk wani abu mummuna da ya same shi, ba wannan ba ne yasa hawayenta suke zuba yau, gaskiyar maganar Barrah ɗin, miƙewa Ammi ta yi daga falon saboda zazzaɓin da take ji ya saukar mata, ɗakinta ta koma ta kwanta, har lokacin hawayen takaici ne suke zubar mata, a karo na farko a tsawon lokaci da take kuka da idanuwanta, a karo na farko a rayuwarta da da na sani ya kawo mata ziyara, yanayi ne baƙo a wajenta, rufe idanuwanta ta yi ko zata samu sauƙi, amma sai duk wani abu da ta yi ba dai-dai ba a farkon aurenta da duk wani abu akan tarbiyar yaranta suka soma kawo mata ziyara suma. (Littafi na 2, babi na 38)

Bayan waɗannan kuma akwai ƙananan jigogi da dama da marubuciyar ta taɓo a cikin wannan littafi domin su koyar da mai karatu darussa da dama irin su ƙalubalen rayuwar mata a jami’a, illar mugayen abokai, matsalar taɓuwar ƙwaƙwalwa da dai sauran su.

Salo da Sarrafa Harshe

Marubuciyar ta baje basira iya basira wajen bada labarin wannan littafi. Domin ta yi amfani da salo iri daban-daban kuma duk masu burgewa wajen isar da saƙon labarin a sauƙaƙe.

Misali:

• Salon Koyarwa: Babban salon da marubuciyar ta yi amfani da shi a cikin wannan littafi shi ne salon koyarwa, domin ta yi amfani da wannan salo a kusan kowane shafi na littafin. Ta koyar da darussa da dama da suka shafi zaman rayuwa ta yau da kullum, zamantakewa a tsakanin ma’aurata, yadda zaɓi mai kyau yake da muhimmanci a rayuwa da yadda zaɓi mummuna ke da tasiri wajen rugaza rayuwa. Duk wannan ta yi shi ne cikin harshe mai sauƙi yadda mai karatu zai fahimta ba tare da wata wahala ba.

• Salo Mai Armashi: An yi amfani da salo mai jan hankali da armashi sosai da sanya nishaɗi ga mai karatu ta hanyar kawo misalai masu jan hankali, motsa zuciya da kuma sa mai karatu dariya da nishaɗi a wasu lokutan.

Salon Tafiyar Kura: An yi amfani da salon tafiyar kura ne a cikin wannan littafi, inda marubuciyar ta fara ba da labarin daga tsakiya sannan ta ci gaba da warware shi a hankali a hankali ta hanyar komawa baya ta kawo wani batu sannan ta dawo ta ci gaba daga baya kuma ta sake komawa ta kwance wani a baya kafin ta kuma dawowa ta ci gaba. A zahiri ma, ta kwashe kusan dukkan littafi na ɗaya ne wajen kawo matsalolin da ke ƙunshe cikin labarin, yayin da kuma ta kwashe kusan dukkan littafi na biyu ta hanyar fayyace matsalolin da ta kawo a littafi na ɗaya tare da kawo wasu kuma ta fayyace su. Hakan zai sa mai karatu ya dinga fahimtar batun da ake kai ko wanda za a shiga ba tare da ya sha wahala ba.

Bugu da ƙari marubuciyar ta yi amfani da sassuƙar Hausa wajen rubuta labarin ta yadda kowa, zai fahimta. Sai dai an samu kalmomi da jumlolin turanci masu ɗan dama cikin labarin waɗanda da yawansu tana kawo fassarar su a cikin baka biyu (), sai dai duk da haka yawan amfani da su na  iya jawo naƙasu ga bunƙasar Adabin Hausa a tsakanin makaranta. Sannan ta ɗan yi amfani da Hausar Zamfara/Sokoto a wasu wuraren da basu canza komai ko kawo tangarɗa a cikin labarin ba sai ma ƙara mishi armashi da ta yi.

• Sarrafa Harshe: Har’ila yau an yi amfani da kalmomi masu tsima jiki, sa tausayi, kwantar da hankali da kuma gyaran tunani duk a cikin wannan littafi. Wani lokaci ma sai mai karatu ya ji kamar zaunar da shi aka yi ana mishi nasiha game da yadda lamarin ke faruwa. Ko da yake an samu ƙarancin karin magana, an samu kalamai na hikima masu yawa a cikin littafin.

Misali:

‘ƙauna bata cika sai da ganin kuskuren juna. (Littafi na 2, babi na 32)

‘Da gaske ne ba’a komawa baya a goge kuskure…” (Littafi na 2, babi na 33)

‘Ba ihu ba, ko gaba ɗaya Abuja da maƙotanta za su taru baya jin za su iya fitar da shi daga ɗakin Rafiq, duk abinda zai yi sai dai yayi. Ba zai yi kuskure kuma ya ce ba za’a faɗa mishi gaskiya ba. Shi ya koya musu ganin kuskuren junansu, kuma shi ya koya musu gyarama juna kuskure ba tare da tunanin banbancin shekaru ba indai za su yi hakan da babu raini a ciki. Babu abinda zai canza don koyarwarshi ta biyo ta kanshi yau. (Littafi na 2, babi na 34)

Zubi da Tsari

Labarin Alƙalamin cukurkuɗaɗɗen labari ne da ke cike da tarin sarƙaƙiya, ba don salo ko tsaurinsa ba. Sai don yadda yake cike da ƙwarewa da ɓatar da bakin duk wani zare da sauƙaƙawa mai karatu hasashe ko kintatar inda aka dosa. Ma’ana dai, duk yadda mutum yake tunanin labarin zai kasance, sai ya ga ba haka ba ne.

Marubuciyar ta gabatar da zubi da tsarin Alƙalamin Ƙaddara daidai yadda ya dace da yanayin halayyar taurarin littafin da kuma yadda ƙarshen labarin ya kasance, ta yadda mai karatu zai ƙagara ya ga yadda za ta kaya, tare da jefo ba-zata a wasu lokutan. Ta kuma yi amfani da nau’o’in mutuwa wajen kawar da wasu taurarin waɗanda ci gaba da kasancewarsu, za ta haramta warware sarƙaƙiya cikin littafin. Misali, an kashe baban su Tasneem, kuma an kashe iyayen su Ashfaq da biyu daga cikin ‘yan uwansu.

Marubuciyar ta  zayyana labarin Alƙalamin Ƙaddara ne a cikin litattafai biyu. Ta kasafta littafi na ɗaya ne zuwa shi babi-babi har goma sha ɗaya, littafi na biyu kuma ta raba shi zuwa babi-babi har arba’in da ɗaya.

Gaba ɗaya labarin ya faru ne a tsakanin garin Kano, Kaduna da kuma Abuja. Sai kuma wani ɓangare muhimmi da ya faru a ƙasar Indiya.

• Baɗoki Na gaske: “Allah ya ɗauke maka farin ciki kamar yadda kai min, Allah ya tsayar maka da dukkan al’amuranka kamar yadda ka tsayar mana da namu, Allah ya tarwatsa maka rayuwarka ta fannin da baka taɓa zato ba, A-Tafida ko? In shaa Allah sunan ka kanshi sai ya zamar maka tashin hankali kamar yadda ya zamar mumin, ka ji ni? Wallahi ba zaka taɓa samun wadataccen farin ciki ba.” (Littafi na 2, babi na 19) Kuma duk waɗannan abubuwan sun faru da Altaaf a cikin littafin.

• Baɗoki Na Giri: “Da baku zo ba… Da sai dai ya mutu? Nuri me yasa ba zaku faɗa min abin da yake damuna ba? Me yasa bana iya tuƙi?” (Littafi na 1, babi na 2)

• Ɗarsau Na Mamaki: Akwai wani abu tattare da ita da ya kasa fahimta, musamman yadda suna haɗa ido duk wata fara’a da ke fuskarta ta ɗauke, mamaki, shakku, da wani abu da Rafiq ya kasa fahimta yana maye gurbin fara’ar, sosai take kallon shi. Zuciyarshi ta ci gaba da dokawa, ji yake tamkar ya santa a wani waje, kusancin da yake ji a tsakanin su ya mishi wani iri. (Littafi na 1, babi na 1)

• Ɗarsau Na Tausayi: “Muneeb karka tafi… Don Allah ka tsaya tukunna… Wallahi bansan ya zan yi ba. Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…. Karka barni tukunna ka tsaya in sake ganin ka….” (Littafi na 1, babi na 11)

‘Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo ma Aroob, gaba ɗaya cikin kwana biyu rayuwar su ta hargitse, bata taɓa zaton zata kai ranar da Rafiq zai buɗe musu ƙofa yana nuna musu hanya da hannun shi ba, sosai abin ya mata wani iri, yadda ya nuna gaba ɗaya sun takura mishi. (Littafi na 2, babi na 34)

• Ɗarsau Na Tsoro: “Yaya… Innalillahi wa inna ilaihir raji’un, Yaya me kayi? Me kai mata? Na shiga uku Yaya… Ka kasheta ko?” (Littafi na 1, babi na 7)

• Ɗarsau Na Murna: “Oh! Wato Addu’a kika zauna kina min ko? Dame-dame kike roƙa? Faɗa min, hancina ya shige ciki kamar naki ko?” (Littafi na 1, babi na 2)

• Hoton zuci: marubuciyar ta yi  amfani da dabarar saka hoton zuci sosai a cikin wannan littafi ta yadda mai karatu zai ji kamar yana wurin abin ke faruwa.

 Misali:

 ‘Inda idanuwan Haj. A’i suke Tasneem ta kai nata, kwance akan kujera wani matashin saurayi ne da Tasneem bata iya ganin fuskarshi ba, saboda kanshi a juye yake, ƙafarshi ɗaya a ƙasa, kusan rabin jikinshi ma ba a kan kujerar yake ba. Juyi ɗaya zai yi ya faɗo ƙasa. (Littafi na 1, babi na 6)

‘Runtsa idanuwan shi Altaaf yayi yana buɗe su, yayi hakan yafi a ƙirga, kalaman uku na amsawa a ko ina na jikin shi ‘Ka aure ta’. Dube-dube yake cikin motar, daga gaba har ya juya baya yana hango robar ruwa, jikin shi na ɓari ya ƙarasa ya ɗauka, bai damu da zafin da ruwan ya ɗauka ba, buɗewa yayi yana ɗaga robar ya sha, amma baiji ya dawo dai-dai ba, iska bata kai mishi inda ya kamata, da sauri ya buɗe murfin motar yana ɗaga robar ya sheƙa ruwan daga kanshi zuwa fuskar shi yana wankawa, bakin shi ya buɗe yana jan iska ta ciki saboda tashin hankali.  (Littafi na 2, babi na 35)

Taurarin Labari

Alƙalamin Ƙaddara littafi ne da ke ɗauke da taurari masu tarin yawa, wasu manya, wasu kuma masu take musu baya. Akwai taurari guda biyu da suka fi fice, waɗanda ana iya cewa ma gaba ɗaya su suka ɗauki nauyin labarin a kafaɗun su. Waɗannan taurari kuwa su ne Altaaf Tafida da Kuma Rafiq Mustafa Shettima. Sai dai duk da wannan, Rafiq ya fi Altaaf shiga gwagwarmaya da rikici mai yawa. Kuma ƙalubalen da ya fuskanta ya fi na kowa a cikin labarin.

Halayen Taurarin Labari

Ga kaɗan daga cikin halayen wasu taurari da suka fito a cikin labarin.

Rafiq Mustafa Shettima: Rafiq mutum ne mai riƙo da addini sosai tare da sanin ya kamata. Yana son iyayen shi da ‘yan uwanshi sosai kuma yana ƙoƙarin kamanta adalci a dukkan al’amuran shi. A ko ina Rafiq ya samu kanshi zai iya cewa baisan menene rashi ba, kalmar bata taɓa ƙarasowa taku hamsin kusa da inda yake tsaye ba ma. Idan akwai abinda gaba ɗaya rayuwar shi da ta ƙannenshi ta ta’allaƙa akai bai wuce ƙin yin kuskure ba, a cikin rayuwarsu ta makaranta, da ta yau da kullum. Ko da yaushe cikin yin abinda Alhaji Mustafa zai yaba suke yi.

Banda ‘yan uwanshi da suke ciki ɗaya, mutane shida ne suke da kusanci da shi. Abdallah, Faruk, Zaid, Muneeb, Arfan sannan Samira. Ita kaɗai ce macen da take cikin rayuwarshi take kuma da kusanci da shi wanda babu alaƙa ta jini. Ita ma dalilin babanta, Alhaji Habibu da ya kasance babban aminin Alhaji Mustafa ne, kuma abokinshi a kasuwanci da siyasa.

Altaaf Tafida: shagwaɓaɓɓe ne kuma sangartacce na nunawa a kasuwa. Kamar wannan bai isa ba kuma yana shaye-shaye tare da bin mata. Bashi da kunya kuma baya tsoron ja da kowa saboda mahaifiyar shi ta ɗaure mishi gindi.

Tasneem Muftahu: Tana da tausayi tare da sanin ya kamata, amma ƙoƙarin ganin ta kare ƙannenta daga faɗawa halaka yasa ita ta zaɓi ta faɗa duk da ta san cewa hakan kuskure ne.

Bara’atu/Ummi:  Mace masifaffiya mai yawan surutu da rashin godiyar Allah. Ko sallah bata cika yi akan lokaci ba amma ta fiye yawan ƙorafi.

Aslam: Mutumin kirki ne mai sanyin hali da kamala.

Alhaji Mustafa Shettima:  A zuciyar Alhaji Mustafa Shettima bayan zama cikakken Alƙali yana da sha’awar siyasa, don haka duk wani taku nashi da hangen abinda gobe zata haifar mishi a cikar burinshi yake yin shi. Bayan ƙalubale da dama da ya fuskanta a lokacin da ya faɗa harkar siyasa za’a iya cewa ya shiga da ƙafar dama, inda ya yi kwamishinan ilimi a lokacin mulkin Fashola. Daga nan ne ya tsaya takarar gwamna inda tun a zaɓen primary aka kayar da shi, da yake shugaban ƙasar lokacin nasu ne aka sake bashi kujerar kwamishina ya riƙe. Yanzun kuma yana kan neman tsayawa kujerar mataimakin shugaban ƙasa.

Ta ko ina ana damawa da Alh. Mustafa, ta fannin kasuwanci inda yake da hannun jari da manyan ‘yan kasuwa, yake kuma da gidajen mai sama da guda goma. Da wahala ka shiga gari a cikin Najeriya ka kira Mustafa Shettima ba’a samu wanda yasan shi ba. Yanayin shi kawai yana cika idanuwan mutane tun kafin su san kowanene shi.

Kurakurai

Mutum tara yake bai cika goma ba. Akwai ‘yan kura-kure kaɗan a cikin littafin, waɗanda ba za su tauye kyawun aikin da marubuciyar ta yi ba.

Ga su kamar haka:

•  An ƙaranta littafi na farko an faɗaɗa na biyu. Domin littafi na farko babi goma sha ɗaya ne, shi kuwa littafi na biyu babi arba’in da ɗaya ne.

 • A cikin littafi na biyu, babi na 20 an nuna cewa marin da wadata ya yi wa Altaaf shi ne farkon lokacin da aka taɓa marin shi. Alhalin kuma a baya an nuna malamar makarantarsu ta taɓa marin shi.

• An nuna cewa Tariq yana ce wa Yasir abokin yaya a littafi na 1, babi na 40, alhalin kuma a baya an nuna cewa haushin shi yake ji saboda yana ganin kamar yasan abubuwa da yawa akan Ashfaq wanda shi ɗin bai sani ba.

‘Tariq dama tun kafin ya ji yadda Yasir ɗin da taimakon Allah ya kare rayuwar Ashfaq ɗin a lokuta da dama da suka shiga hatsari kala daban-daban Yaya yake kiran shi, yanzun kalmar tun daga zuciyar shi yake jin tana fitowa, ba su hada jini ba, amman zumuncin su abune da yake da yaƙinin har ƙarshen rayuwar su ne. (Littafi na 1, babi na 40)

“Duk sanda kuka fita tare sai an samu matsala… Ya akai harbin akanshi kawai ya tsaya? Maganin bindiga ka sha da bai same ka ba?”

“Babu sirri a tsakanin mu har sai da ka zo.” (Littafi na 1, babi na 1)

• Kuskuren cusawa mai karatu fahimta ko ankararwa ta ƙarfi da yaji ta shigo cikin littafin. Domin a  rubutu musamman kalar wanda ake lura ko kiyaye ƙa’idojin rubutu, babu wani dalili ko dokar da ta yarda marubuci ya zaɓi rubuta wata kalma da manyan baƙi ba bisa ƙa’ida ba. Kuma duk muhimmancin kalmar kuwa. Ba daidai ba ne, sannan yana lalata ganɗokin labarin, domin yana sa mai karatu ya tsinkayi inda ake son zuwa. Ya zo a wannan littafin a wurare da dama kamar haka:

‘Wai shi ne yake tunanin ganin ƙarshe yake wa Zafira a yau. Inda yasan ALKALAMIN KADDARA ya yi musu wannan rubutun da ya so ta daga nesa, da bai bari ya ɗanɗani yadda soyayyarta a kurkusa take ba tunda yasan zai rasa ta. (Littafi na 1, babi na 11)

• Marubuciyar ta shigo cikin labarin A littafi na 1, babi na 2 da cewa: “Ɗaga mata gira ya yi duka biyun kafin ya matsar da kanshi saitin kunnenta yana faɗa mata maganar da sirri ce kawai a tsakanin su.”

• An yi kuskure wajen bayyana Altaaf a matsayin mai son karatu da naci wajen yin tambaya a littafi na 1, babi na 2 da cewa: In akwai abinda ya tsana bai wuce ya kasa fahimtar wani abu ba, ko a makaranta Allah ya mishi nacin tambaya. In bai gane komai ba sam hankalin shi ba ya kwanciya, Majida ta fara sashi ciwon kai.’ Alhali kuma a littafi na biyu an nuna rashin maida hankalin shi akan karatu har sai da ya je jami’a tukunna, can ma abokai ne suka takura mishi.

• Labarin su Jawwad da Jawda sam bashi da hurumi a cikin littafin, domin ba a fara maganar su ba sai a littafi na 1, babi na 9 kuma daga nan har zuwa ƙarshen littafi na biyu ba a ci gaba da shi ba kuma ba a fayyace dalilin wanzuwar su a cikin labarin ba ko kuma yadda rayuwarsu ta ƙare.

• A littafi na 2, babi na 2, an tsarmo gabatarwa babu gaira ba sabab. Alhali ita gabatarwar  ana saka ta ne a farkon littafi in da buƙatar hakan. Kuma wani abin dubawa shi ne, saka shi a daidai wurin babu abinda ya yi face ƙara rikita mai karatu tare da sa tunanin shi ya tafi wani wuri can daban ya bar ainahin abinda ke gaban shi.

Abin Yabawa

Alƙalamin Ƙaddara littafi ne da za a iya gabatarwa ga kowanne irin makaranci saboda akwai darussa masu yawa a cikinsa. Babban darasin shi ne, mutum ya yi takatsantsan da irin zaɓukan da yake yi. Saboda duk zaɓin da ya yi watarana zai dawo ya same shi.

Littafin ya dace da matasa, ’yan jami’a, samari da ’yammata, har ma da masu burin zuwa jami’a. Sannan kuma ya dace da iyaye da matan aure da sauran rukununan mutane. Saboda su babban jigon labarin ya shafi kusan kowa da kowa ne.

Bisa wannan dalili, lallai wajibi ne a yaba wa marubuciyar bisa irin namijin ƙoƙarin da ta yi wajen ƙirƙiro tare da tsara wannan labari cikin tsari da zubi mai tsafta ta yadda kowa zai iya amfana da shi idan ya karanta. Dubi dai yadda ta ajiye wata magana mai muhimmanci da cewa,

‘Fadila ta tsammaci gori daga wajen Maimunatu, ko da wasa maganar bata taɓa haɗa su ba, asalima ba shiga harkarta take ba, sukan gaisa, in wani abu ya faru na farin ciki ko jaje a dangin ɗayan su sukan je ma juna, yaran su kuma babu wani abu wai shi ‘yan Ubanci a zamantakewar su, Hajiya Maimunatu ta tabbatar da hakan bata faru ba. Mace ce mai karamci a nata yanayin. Har abada kuma Fadila ba zata manta abinda sukai mata ba, tana da tabbacin cikin mata dubu kamarta ba za su wuce su biyar da suka taki irin sa’ar rayuwar data taka ba.  (Littafi na 2, babi na 37) Wannan ɗan yanki kawai na cikin labarin yana nuna yadda ya kamata a ɗauki ƙaddara ne, kuma ko shi aka bar mutum da shi ya isa abin a gani kuma a yaba.

Shawarwari

Zan so marubuciyar ta ci gaba da yin rubuce-rubuce irin wannan domin al’ummar mu su amfana daga tarin ilimi da kuma fasahar da take da ita.

Sannan ina mai bata shawarar da ta kauce wa saka sunaye masu kama da juna a cikin labarin ta na gaba domin hakan na iya ruɗar da mai karatu. Sunayen da suka yi kama da juna a cikin wannan littafin sun haɗa da:

Rafiq

Tawfiq

Ashfaq

Tariq

Kammalawa

Haƙiƙa duk wanda ya karanta Alƙalamin Ƙaddara tabbas zai ƙaru ta hanyar da bai taɓa tsammani ba, kuma saƙonnin da ke cikin littafin na da ƙarfin da za su iya canza wa mutum tunanin sa nan take.

Daga ƙarshe, yana da kyau mai karatu ya fahimci cewa ilimi da alfanun da ke tattare da wannan littafin sun zarta adadi da kuma rinjayar kuskuren da na gano a littafin. Ko ba komai, mun fahimci yadda ƙaddara take a tsakanin mutane iri daban daban. Ina jinjina ga marubuciyar wannan littafi tare da fatan Allah ya ƙara basira da ilmi mai amfani.

Kuna iya karanta littafin Alkalamin Kaddara na daya da na biyun dukka anan Bakandamiya Hikaya.

Manazarta

Ɗangambo, A. (1984) Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph

Junaidu, I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002). Harshen da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Ibadan: Spectrum Books Limited

Sani, M.A.Z., Muhammad A., da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. Ibadan: University Press Plc

Yahaya, I. Y. da Ɗangambo, A. (1986) Jagoran Nazarin Hausa. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company Limited.

Yahaya, I. Y., Zaria M. S., Gusau M.S., da ‘Yar Aduwa T.M. (1992) Darussan Hausa don Manyan Makarantun Sakandire 1. Ibadan: University Press Plc

Zarruƙ, R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. Ibadan: University Press Plc

2 thoughts on “Sharhin littafin ‘Alkalamin Kaddara’ 1 & 2 na Lubna Sufyan”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page