Skip to content

Sharhin littafin ‘Hoton Mijina’ na Nana Aicha Hamissou

Sunan littafi: Hoton Mijina

Marubuciya: Nana Aicha Hamissou Abdoulaye

Inda aka buga littafi: Hikaya

Shekarar bugawa: 2022

Mai sharhi: Hasssana Labaran Ɗanlarabawa

An gabatar da wannan sharhi ne da farko a zauren Bakandamiya Reading Club na Facebook a ranar 31 ga watan Junairu na 2024.

Tarihin marubuciya

An haife Nana Aicha Hamissou Abdoulaye a ranar Laraba ashirin da bakwai ( 27) ga watan Yuli na shekarar dubu ɗaya da ɗari tara da casi’in da huɗu (27/07/1994) a unguwar sabon gari ta jihar Maraɗi jamhuriyar Nijar.

Ta fara karatu a ɓangaren addini a madarassatul Hizibur Rahim da ke unguwar Zaria ta 2 a nan garin Maraɗi. A lokacin da ta cika shekara shida a duniya aka saka ta a makaratar boko a shekarar 2000 a wata primary mai suna Ecole sabon gari a nan garin Maraɗi. Ta gama primary a shekarar 2006 inda kai tsaye ta ɗora karatunta a wata ƙaramar Sakandire mai sunan CEG Rauda. Bayan ta gama wannan ne ta wuce babbar sakandare mai suna Lycée Ɗan Baskore. A lokacin ne kuma Allah Ya albarce ta da saukar Alkur’ani a shekarar 2013.

Bayan ta gama Sakandire ta samu gurbin karatu a jami’ar Gwamanti mai suna Université DanDicko DanKoulodo de Maradi (UDDM) a shekarar 2015. Sakamakon yajin aiki ba ta gama ba sai a watan Yulin 2020 inda ta samu kwalin digiri a fannin Etude d’Impact Environnemental (Nazarin Tasirin Muhalli). A ƙarshen watan Disambar shekarar ta ɗora master a jami’ar Abubakar Ibrahim International University a ɓangaren Gestion de L’environnement (Yadda za a kula da Muhalli). Wani uzuri mai girma ya ɗan tsayar da ita, da tun a bara za ta gama Master ɗinta. A taƙaice dai da izinin Ubangiji ta kusa gama digiri ta biyu in Sha Allahu.

A ɓangaren addini ma har yanzu tana neman ilmi, inda a halin yanzu tana karatu a madarassatul Imamul kisa’i, Al’islamiyatul Tahfizul Qur’an da take nan garin Maraɗi.

Ta fara rubutu a yanar gizo a shekarar 2019. Ta yi rubuce-rubuce da dama a kafafen sadarwa, a halin yanzu tana da labarai fiye ashirin daga dogwayen labarai zuwa gajerun labarai.

Game da labari

‘Hoton Mijina’ Labarin wata mace ce mai kishin tsiya da ɗaukar wa kai Dala babu gammo, wadda duk kusancin ta da ƙawaye bai sa ko sau ɗaya an taɓa ganin mijin da za ta aura ba saboda kishin masoyin nata da take yi. Daɗin daɗawa da ma ba garinsu ɗaya ba, sai abin ya zo mata a daidai wai mai ido ɗaya ya leƙa shantu.

Tauraruwar mai suna Rashida, ba ta tsaya a nan ba, ta yi ta girba wa ƙawayenta da aminiyarta Aisha ƙaryar mijin da za ta aura Kabir ustazu ne, shi ya sa bai yarda ta nuna hotonsa ba. A haka aka binne zancen, aka kuma ci biki aka suɗe ba tare da ɗaya daga cikin ƙawayenta ta yi arba da mijin ba.

A ɓangaren aminiyar amarya Aisha kuwa, ta fi son sai ta yi karatu mai zurfi kafin ta yi aure. Wannan ne ya zamo shamaki tsakanin ta da Rashida, bayan ta cale ƙasar Moroko karatu.

Kwatsam, babu zato babu tsammani bayan wasu shekaru, Rashida ta yi karo da fuskar Aisha a matsayin matar da Kabir ya auro mata. Sanadin hakan ta gigice har da suma, a ƙarshe bayan ta dawo hayyacinta ta warware musu zare da abawa, kan yadda ta yi ta kaffa-kaffa da hoton mijinta, sai ga shi a rashin sani aminiyarta ta aure shi. Dole babu yadda ta iya, ta naɗa gammon haƙuri, ta rungumi mijinta da kishiyarta, duk da aminiyar tata ta so rabuwa da mijin gudun a ce ta ci amana. Amma Rashida ta ƙi hakan ta nuna komai ya wuce za su ci gaba da zama a tare a matsayin kishiyarta cikin aminci.

Taken labari

A haƙiƙanin gaskiya take/sunan da aka ba wa labarin ya ja hankali ƙwarai da gaske. Aka kuma daɗa yin katari ya zamo asin-da-asin da abin da labarin ya ƙunsa. Dole a jinjina wa marubuciyar labarin, domin tun daga kan taken ta ɗarsa wa mai karatu tunane-tunanen abin da zai riska dangane da taken labarin ‘Hoton Mijina’, haka nan, wata ƙwarewa ce ga marubuci a ce sunan labarinsa yana da alaƙabda labarin.

Jigo

Babban jigon wannan labarin shi ne kishi, sai kuma ƙananan jiguna kamar nuna ƙarfin ƙaddara. Wadda duk yadda bawa ya kai ga dabara da kauce-kauce, bai hana abin da Allah Ya hukunta tabbatuwa. Kuma jigo ne mai ƙarfi kasancewar abin da ya fi damun mata kenan wato lamarin kishi, wanda yake warware karin maganar malam Bahaushe ta ciwon ‘ya mace na ‘yw mace ne.

Warwarar Jigo

Marubuciyar ta yi ƙoƙari wurin isar da saƙon da jigonta ya ƙunsa. Daga farkon labarin har zuwa ƙarshensa inda ta samar da mafita a ƙarshen labarin, hakan kuma ƙwarewa ce sosai ga marubuci.

Zubi da tsari

Haƙiƙa marubuciyar ta tsara labarin da zubi mai kyau da jan hankali. Ta tsara labarin daga tsakiya, farko sai kuma ƙarshe.

Abubuwan birgewa

Labari ne da farkonsa yake da jan hankali matuƙa, ta yadda marubuciyar ta bayyana mafarkin da tauraruwar labarin ta yi da ƙawarta, wadda aljanu suka zo a siffar ƙawar tata har suke tsorata ta da abin da ta fi tsana wato kishiya.

Duk da dai marubuciyar ba ta fito kai tsaye a farkon labarin ta bayyana cewa matsalar a kan kishi ba ne, sai dai ta yi ƙoƙari wajen ɗarsa wa mai karatu batun da zai ta kai-kawo a zuciyarsa a farkon labarin, a inda ta ce.

“Babban abin tashin hankalin shi ne yadda aljanu suka yi siffar ƙawata a mafarki har suke tsorata ni a mafi munin abin da na fi tsana a rayuwata.” (Abin da ta fi tsana a rayuwarta kishiya)

Iya wannan saɗarar ta isa haska wa makaranci/manazarci cewa abin da ta tsana a rayuwarta shi ne jigon labarin da aka gina labarin a kai; wato kishi ko kishiya.

Kura-kuran da ke ciki

Duk ɗan’adam ajizi ne tara yake bai cika goma ba, don haka ba zai yiwu a ce komai da yake cikin labarin nan daidai ba ne, akwai wasu kura-kurai da suke cikin labarin wanda ya kamata a ce an fito da su domin marubuciyar labarin ta nazarce su ta yadda a gaba za ta kaucewa faruwar hakan a yayin da za ta rubuta wani labarin ko wasu labaran. Don haka ga kura-kuran nan kamar haka:

Cushe

Rubuta kalmomin da suka zamo taken labarin da manyan baƙaƙe, cushe ne kai tsaye ake yi wa mai karatu na lallai ana so a ankarar da shi cewa ga sunan labarin fa, kuma hakan ragon salo ne tun da dai tun farko mai karatu ya san sunan labarin to babu buƙatar a yi ta rubuta shi cikin labarin kuma da manyan baƙi. Haka nan, an ta rubuta su a mabambantan wurare ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba. Misali.

“Ina tunanin hanyar da zan bi ki ga HOTON MIJINA…”

Da ire-iren waɗannan wurare, wanda kai tsaye hakan ke nuna cushe ga mai karatu, a wata mahangar ma ana ganin yin irin hakan kamar raina basirar mai karatu ne.

Kufcewar salo

Labarin tauraro fagen ciki ne, amma akwai wurin da aka samu kufcewar salo ya zama tauraro fagen waje. A maimakon a rubuta hana ni sai aka rubuta hana ki.

Haɗewa da rabewa

A ɓangaren nahawu cikin rubutun Hausa mun sani akwai ɓangaren haɗe kalmomi da rabawa, a cikin wannan labari duk da marubuciyar ta yi ƙoƙari sosai wurin kiyaye haɗe kalmomi da rabawa, sai dai akwai wuraren da marubuciyar ta haɗe alhali rabewa ne, fito da su zai sa marubuciyar ta nazarce su domin gujewa faruwar hakan a rubutunta na gaba. Don haka ga su kamar haka.

  • sarawa kaina ya yi – sara wa kaina  ya yi (Jakada wa)
  • akan – a kan
  • bana – ba na

Harufa masu ƙugiya

  • Watakila – Wataƙila
  • Karaji – Ƙaraji
  • Kasarsu – Ƙasarsu
  • roko – roƙo

Zamiyar alƙalami

Duk da cewa marubuciyar ta yi namijin ƙoƙari wajen rubuta kowace kalma yadda take bisa ƙa’ida, sai dai akwai wasu ‘yan wurare da na ci karo da su da ke tabbatar mini da zamiyar alƙalami ne. Fito da su zai sa marubuciyar ta ankara a rubutu na gaba domin kiyayewa, tare da sake bin rubutun ta duba kafin ta fitar da shi. Akwai wuraren da marubuciyar ta rubuta suffa, wasu wuraren kuma ta rubuta siffa, Shin wanne ne daidai?

Mumunnar – Mummunan

Marako – Maroko

Rashin azanci da karin magana 

Haƙiƙa rashin azanci ya tauye darajar wannan labarin sosai, domin kamar miya ce da ba ta ji kayan ɗanɗano sosai ba, kenan dai ba za ta yi daɗin ɗanɗano a kan harshe kamar wadda ta ji kayan ɗanɗano sosai ba. To kamar haka ne a rubutun labari, da labarin da ya ji azanci da karin magana da labarin da bai samu wannan tagomashi ba babu haɗi. Don haka wannan labari ya samu naƙasu ta fuskar karin magana da azancin da zai ƙara masa garɗi har mai karatu ya ji yana shauƙi da mararin karatu.

Ƙa’idojin rubutu

Dole a jinjina wa marubuciyar kasancewar ta kiyaye ƙa’idojin rubutu sosai a rubutunta, ba kamar sauran rubutu ba ne da za a gan shi ta-ci-barkatai babu saka alamomin rubutu a ciki, wannan kam an ƙawata shi sosai da ƙa’idoji sai ɗan abin da ba za a rasa ba na ajizanci ko mantuwa. Na ci karo da wuraren da marubuciyar ta saka alamar motsin rai a wuraren da ba muhallin ta ba, misali wurin da Rashida take tambayar mijinta shin shi ma ya yi mafarki ne? Sai ya ce, “Mafarki!”

A nan alamar tambaya ce za ta zo tun da tambayar ta ya yi, bai kamata alamar motsin rai ta zo a wurin ba.

  • Mafarki! – Mafarki?
  • Me ya sa na ce! – Me ya sa na ce?
  • Ba yanzu ba! – Ba yanzu ba (Aya za ta iya zuwa, ko waƙafi)
  • Ko ɗaya kam! – Ko ɗaya kam,
  • Raba mu da ustazunki da ya hana mu ganin shi! – Raba mu da ustazunki da ya hana mu ganin shi (Aya za ta iya zuwa ko waƙafi)

Sakin layi

A ƙa’idar gajeren labari ba a amfani da sakin layi mai nuna alama, misali:

*****

Amma marubuciyar ta yi amfani da shi a lokacin ta tauraruwar za ta yi tunanin rayuwar baya, wanda hakan ragon salo ne, an fi so gajeren labari ya kasance a numfashi ɗaya ba sai an tsittsinka shi ba, ya fi birge mai karatu ko mai nazari.

Tsinkaye

Anya kuwa mace mai kishi irin Rashida wadda ko hoton mijinta ba ta bari a gani za ta yi saurin zubar da makamanta ba tare da taratsi da kai ruwa rana ba? Duk da ƙawarta da mijin nata ba su da laifi, amma abin da kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa, a ce a lokaci guda kishin ya kau har ta karɓi kishiyar da hannu bibiyu, a yadda mata suke da ɗan karen kishi zai fi a ce an ɗan turza kafin ta gane shayi ruwa ne ta dawo kan hanya.

Jinjina

Dole ne a jinjina wa wannan marubuciya, domin ta yi namijin ƙoƙari wajen girka labarin da ya ji ɗanɗano mai daɗi, ga faɗakarwa da wa’azantarwa. Sannan ta ƙware a wurin gina gajeren labari wanda ba kowace marubuciya ce za ta iya ba. Haka nan, yadda ta bi matakai da kiyaye ƙa’idoji abin a jinjina mata ne, domin ba don karatun nazari na yi wa labarin ba da ba lallai ma na hango kura-kuran ciki ba saboda daɗin labarin. Don haka ina yi mata jinjinar ban-girma da addu’a da fatan Allah Ya ƙara hazaƙa da basira da kuma fikra. Allah Ya sa a daɗe ana yi.

Ku karanta littafin Hoton Mijina a Hikaya.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page