Skip to content

Sharhin littafin ‘Akan So’ na Lubna Sufyan

Sunan Littafi: Akan So

Marubuciya: Lubna Sufyan

Inda aka Buga Littafi: Bakandamiya Hikaya (Online)

Shekarar Bugu: 2022

Mai Sharhi: Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)

Manufar Sharhi: Bunƙasa harshen Hausa da ciyar da adabi gaba

Taƙaitaccen tarihin marubuciyar

Lubna Sufyan ‘yar asalin ƙaramar hukumar Ingawa ce da ke birnin Katsina. Fitacciyar marubuciyar ta fara karatun addini tun tana ƙarama kuma ta yi karatunta na Firamare ne a garin Katsina, daga baya ta koma garin Kano inda ta yi karatun Sakandire har ta gama. Bayan ta gama ne sai ta koma Katsina inda ta yi karatun Diploma a ɓangaren zanen taswirar gidaje. Daga baya kuma ta ci gaba da karatu a mataki na gaba, wato babbar Diploma, Higher National Diploma (HND) a garin Kaduna.

Marubuciyar ta fara rubuce-rubuce ne tun tana makaranta, kuma ta kasance ɗaya daga cikin fitattun sunayen da ke fara zuwa zukatan masu karatun online da zarar an yi maganar marubutan online a wannan zamani. Zuwa yanzu ta rubuta litattafai sama da guda goma sha ɗaya. Wasu daga cikin litattafan da ta rubuta sun haɗa da; Akan so, Rayuwarmu, Abdulƙadir, Rai Da Ƙaddara, Mijin Nobel, Martabarmu, Alƙalamin Ƙaddara da sauransu.

Marubuciyar kuma na ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar marubuta na Fikra Writers Association.

Labarin a taƙaice

Fu’ad Arabi shi ne ɗa na huɗu cikin ‘ya’ya bakwai da Alhaji Salman Arabi da Hajiya Aisha suka mallaka. Fu’ad ya fita daban da sauran ‘yan gidansu. Domin ya kasance mai son kai, taƙama da kuma nuna isa. Bugu da ƙari baya kallon kowa da gashi bayan iyayensa da ‘yan uwansa sai kuma babban abokinsa wato Lukman. Tun tasowarshi ba shi da aiki sai buga wasan ƙwallon ƙafa. Ya sha ƙin zuwa makaranta akan wasan ƙwallon na ƙafa. Tun suna duka da faɗa har suka gaji suka soma ba shi goyon baya. Lokacin da ya shiga aji shida a sakandire ne ya samu ɗaukaka zuwa ƙasar Europe.

Dole su Alhaji Salman suka ƙyale Fu’ad ya tafi. Da ƙyar ya dawo ya zana jarabawar WAEC kaɗai.

Can ya nemi gurbin karatu saboda aikinsa na wasan ƙwallon ƙafar ya sa zaman shi ya koma can.

Fu’ad da Safiyya sun yi aure ne ba tare da amincewar iyayensu ba, domin ana gab da ɗaurawa Safiyya aure ta bi Fu’ad suka je wani wurin aka ɗaura musu aure. Sai dai rashin samun albarka daga iyayen nasu ya sa auren bai yi ƙarko ba. cikin ‘yaya uku kacal da Malam Audu da Zainabu suka mallaka a duniya. Safiyya na da ‘ya guda ɗaya tal, wata yarinya me ɗankaren wayo tare da saurin shiga rai da ake kira da suna Nana wacce ke fama da cutar daji. Likitoci sun bayyana cewa, domin Nana ta rayu sai an yi mata dashe (transplant). Idan ba a samu wanda ya yi daidai da ita ba, za ta iya rasa ranta cikin watanni shida ko ƙasa da haka. Mutun na farko da ake sa ran ko nashi zai zo daidai da nata shi ne mahaifinta, wato Fu’ad Arabi wanda aka fi sani da ‘Moh’ wanda bai ma san da ita ba.

Shi kuwa Fu’ad tun asali baya son haihuwa, domin har zuwa ya yi aka yi masa aikin da ya kashe masa ƙwayoyin haihuwarsa gaba ɗaya don kada ya haihu, wato vasectomy. Fu’ad ya sake Safiyya ne yayin da ta nuna tsananin bacin ranta a sabili da ya gaya mata ya yi vasectomy. A tunanin shi ya sake ta ne domin shi ba zai iya bata abinda ta ke so ba, wato ‘ya’ya. Saboda haka bayan ya saketa ya sa kafanshi ya bar gida da ma kasan baki daya. Bai san da cikin Nana ba sam, itama Safiyya ta sani ne bayan tafiyan shi.

Ya san Nana ne ranar da ya dawo bayan shekara sha daya da ya je gidansa da Safiyya. A nan yayi arba da ita a karo na farko.

Nana na son ganin mahaifinta kafin ta rasu, a gefe kuma masoyanta na fata babanta ya zama dai dai da abinda likitoci ke so domin ta tsira da rayuwarta. To amma ita Safiyya tana ganin wannan abu ba mai yiwuwa bane, domin ta san halin Fu’ad da yadda yake da son rai. Kuma maganar da ya yi mata na ƙarshe kafin ya bar ƙasar ita ce; “I don’t do happily ever after. Daga ranar da kika yarda da soyayyata ya kamata ki san ban yi kalar wanda zai dinga zarya da yara da pampers ba. Ban yi kama da wanda zai yi asarar lokaci da soyayyar shi akan yara ba. Ina da su Haneef, ina da su Fa’iza. A duk lokacin da na ji marmarin ganin yara zan je gidansu in ga nasu.”

Dr. Jana ita ce likitar da ke kula da Nana. Auren soyayya suka yi da mijinta Jabir. Suna matuƙar son junansu, kuma sun aminta da juna sosai. Sannan Allah ya azurta su da zuri’a. To sai dai kuma, aikin da Jana ke yi na neman zama matsala a tsakaninsu, wanda hakan ya sa Jabir ya fara tunanin ƙara aure. Aina abokiyar aikin Jabir ce, domin waje guda suke aiki. Tana burge Jabir sosai saboda kamun kai, hankali da kuma nutsuwarta, wanda akarshe ya aureta.

Nuriyya matashiya ce mai kamun kai da riƙon addini, sai dai ta yi rashin samun nagartacciyar uwa. Domin kuwa, ita kullum ƙoƙari take yi ta sa ta a hanyar baɗala. Ta kamu da son wani bawan Allah mai suna Farhan wanda ya taimaka mata a rayuwa sakamakon mummunan halin da ta tsinci kanta a ciki. A dai dai lokacin da ya yi yunƙurin aurenta, a dai dai wannan lokaci ne kuma mahaifinsa ya turje akan shi ɗansa ba zai auri mace irin Nuriyya ba, ya kuma ba shi zaɓi ko su ahalinsa ko Nuriyyar. Wannan dalili ne yasa Farhan bin mahaifinsa suka bar ƙasar. Bayan tafiyar su ne Nuriyya ta haɗu da Nawaf, wanda ya maye mata gurbin Farhan ta fannoni da dama har suka yi aure. Allah ya jarabci Nawaf da shaye-shaye da kuma baƙin kishi na nunawa a kasuwa. Ita kuma Nuriyya duk da irin son da take yi wa Nawaf, ta kasa cire Farhan daga zuciyarta.

Yadda ta kasance a tsakani da kuma yadda labaran suka haɗe waje guda shi ne yadda labarin ya tafi a cikin wannan littafi.

Jigo

Wato ko da jin sunan wannan littafi ‘Akan So’ na san masu karatu za su iya fahimtar babban jigon wannan labari shi ne soyayya da kuma abin da so ka iya sa mai yin sa ya aikata. Kuma duk tirka-tirkar da ke cikin labarin za ka iske ta samo asali ne daga son da wani ke yi wa wani ko wata ke yi wa wani a cikin wannan labari. Domin an nuna irin yadda sabon shiga a so kan ji idan so ya kama shi kamar yadda a babi na goma sha uku marubuciyar ta ce “Wannan wane irin abu ne. Sati ɗaya kenan. Da duk numfashin da za ta ja ta fitar da tunanin shi a ciki. Ta ma rasa me take ji game da shi. Saboda wani irin yanayi ne take ji kala-kala. Ko lomar abinci za ta kai baki yana nan cikin kanta. Da shi take komai a manne. Bata da ikon bacci mai lafiya ba tare da shi a cikin mafarkinta ba. Gashi wani irin mafarki take yi da duk in ta farka sai ta ji shi kamar gaske. Kalaman da suke wa juna a mafarkin ya fi komai ɗaga mata hankali….”

Sannan a shafi na goma sha huɗu kuma an sake nuna mana yadda shi ma Fu’ad ya ke ji dangane da Safiyya a inda marubuciyar ta ce “A ‘yan kwanakin nan mafarkan da yake sun yawaita. Har idanuwanshi sun faɗa saboda ba shi da wata wadatacciyar nutsuwa… Ta ina ma zai fara ce masa shi Fu’ad yau tunanin mace ya saka shi a gaba. Tunanin macen ma kucaka ‘yar ƙauye. Abin da ɗan nauyin faɗa. Tunda shi bai san me ya sa ma yake jin abinda yake ji ɗin ba…”

Anan za mu iya fahimtar yadda asalin soyayya ta fara shiga tsakanin taurarin labarin guda biyu da kuma irin ƙalubalen da soyayyar tasu za ta fuskanta duba da irin yanayin halayyarsu da kuma yadda alaƙa ta haɗa su tun da fari. A ƙarƙashin wannan jigon kuma in aka yi duba da kyau za a ga wasu ƙananan jigogi waɗanda suka taru suka bada darussa masu dama a cikin labarin kamar:

• A babi na shida, sakin layi na farko an nuna mana muhimmancin tarbiyya da ilimi da kuma yadda iyaye ke ƙoƙarin ganin sun ba ‘ya’yansu tarbiyya. Kamar yadda marubuciyar ta ce “Dai-dai gwargwado daga Alhaji har Hajiya sun yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen ganin sun ba yaransu tarbiyya da ilimi na boko da addini…”

• Haka kuma an nuna mana irin matsalar da yin aure ba tare da amincewar iyaye ba ka iya haifarwa a cikin wannan labari. Dubi yadda a babi na ashirin ɗaya daga cikin taurarin labarin ya ce, “Abin da ka yi ba ƙarami bane ba. Ban ce ba zai yafu ba. Auren da aka gina ta hanyar da ya dace ma yana zuwa da matsala Fu’ad. Ballantana naku da babu amincewar iyaye ballantana albarkarsu…” da kuma inda a can gaba a babi na talatin da biyar yayin da al’amura suka fara kwaɓe musu inda Fu’ad ya fara zargin Safiyya akan rashin lafiyar ‘yarsa inda yake riyawa a zuciyarsa “‘Yar shi da ko damar saninta bai samu ba. Kuma wannan ba laifin kowa bane sai na Safiyya. Sofi ta ɓoye mishi ita gashi yanzun mutuwa za ta yi…”

Da abu ya yi tsamari kuma sai maganar ta fito fili inda yake cewa, “Saboda ke ba zan san abubuwa da yawa ba akan Nana.

Saboda ke na rasa shekaru goma sha ɗaya na rayuwa tare da ita.

Ba ke ya kamata ki yi kuka ba Sofi. Saboda ko da ace yau babu Nana kina da shekaru goma sha ɗaya a cikin kanki da za ki dinga dubawa kina samun sauƙi.

Ba ni da komai!!!

Ba ni da abinda zan duba nata banda watanni!!!

Wallahi ban san yadda akai zuciyata ta yi kuskuren sonki ba…”

Ita kuma ta ba shi amsa da cewa, “Kai ka tafi. Ban kama ka na turaka waje ba!  Kai ka zaɓi ka bar ni. Saboda me za ka ga laifina? Ya kake so in yi? Meye ban yi Akan sonka ba? Saboda me za ka ɗauka kai kaɗai ne za ka rasa Nana? Ko ka ɗauka ka fini sonta ne?”

Wannan hali da suka tsinci kansu a ciki ya sa shi yin nadamar abin da suka aikata wanda har ya sa shi yake cewa “Za mu gyara komai. Babu wanda zai iya saving Nana. Allah da ya ɗora mata ne kawai zai iya. Sofi za mu gyara komai. Zamu ba kowa haƙuri. Inna da Baba. Su Abba. Zamu fara ganin dai dai in suka yafe mana…” ita ma nadamar ta kamata sosai inda har take cewa “… “Komai zai gyaru in suka yafe mana. Mun yi kuskure na ɗaukar za mu iya tsara rayuwarmu da kanmu…”

• An nuna mana matsalar shaye-shaye da inda wani lokaci abokai ne kan ja ra’ayin wasu matasan har su shiga harkar. Kamar yadda a babi na talatin da huɗu marubuciyar take bayyana mana yadda Nawaf ke ji a ranshi da cewa “Yana tsoron karɓar ƙwayoyin da ke hannun Auwal, don bai san kalar ƙarfinsu ba. Codeine ɗin ma don ya zamana kowa a ajinsu yana sha ne. Kullum kallon ƙaramin yaro suke mishi. Shi ne abin da ya fara jan hankalinshi. Shekara ɗaya kenan ya kasa dainawa. Sam ba ya jin daɗi in har bai sha ba…” kuma a dalilin hakan ya sa ya ci gaba da shan ƙwayoyin har bayan fitarsa daga makarantar. Kuma shaye-shayen ya sa ya zamana yana ƙuntatawa ‘yan uwansa ba don yana so ba, dubi abinda yake ce musu a lokacin da yake kwance a gadon asibiti “…Ku yafe min. Na saka ku ɓacin rai da yawa a rayuwata. Ku taya ni roƙon Allah ya yafe min…”

• An nuna mana yadda tsanstar soyayyar iyaye take ga ‘ya’yansu, da kuma irin yadda suke da muhimmanci a wajen ‘ya’yan nasu. Dubi dai yadda Fu’ad ya shiga taitayinsa bayan gane kuskurensa kamar yadda marubuciyar ta bayyana “Gaba ɗaya jikin shi rawa yake. Ko ina na jikin shi ɓari yake. So yake ya ce Abba ya yafe mishi kalma ko ɗaya ta ƙi fitowa daga bakinshi.

So yake ya faɗa wa Abba yau ya ga wautar da ya aikata. So ya ke ya faɗa mishi yau ya gane amfanin neman shawara. Ya gane irin ƙaunar da suke mishi. Ya gane ba takura mishi suke yi ba.

Ya gane irin wannan ranar suke guje mishi…” Sannan an nuna mana yadda ya yi nadama har yake cewa “Abba na gane soyayyarku mai girma ce a gareni. Wallahi na gane duk wata soyayya ƙasa take da ta iyaye. Abba ka yafe min. Ka yafe min ko zan samu in ga dai dai a rayuwata….”

Bayan waɗannan akwai ƙananan jigogi da dama da marubuciyar ta taɓo kamar su soyayyar ahali, muhimmancin abota, adalci a tsakanin ma’aurata da sauransu

Salo da sarrafa harshe

Marubuciyar ta yi ƙoƙari sosai wajen ba da labarin. Domin ta yi amfani da salo mai burgewa wajen isar da saƙon labarin. Misali:

• Salon Tafiyar Kura: Marubuciyar ta yi amfani da salon tafiyar kura ne a cikin wannan littafi, inda ta datsi labarin daga tsakiya sannan ta ci gaba da warware shi ta hanyar komawa baya ta kwance wani batu sannan ta dawo ta ci gaba daga baya kuma ta sake komawa ta kwance wani a baya kafin ta kuma dawowa ta ci gaba.

• Salon Koyarwa: An yi amfani da wannan salo sosai a cikin wannan littafi wajen koyar da darussa da dama da suka shafi zaman duniya, zaman ma’aurata da yadda za a zauna da ahali cikin harshe mai sauƙi yadda mai karatu zai fahimta ba tare da wata wahala ba.

• Salo mai Armashi: Marubuciyar ta yi amfani da salo mai armashi sosai da sanya nishaɗi ga mai karatu ta hanyar kawo misalai masu motsa zuciya da kuma sa mai karatu dariya a wasu lokutan.

• Sarrafa Harshe: Har ila yau an yi amfani da kalmomi da za su sa mai karatu ya ji kamar da shi labarin ke faruwa. Ko da yake an samu ƙarancin kwarzanta harshe ta hanyar yin amfani da karin magana, zambo da sauransu, marubuciyar ta maye gurbin su da misalai masu jan hankali waɗanda suka ƙara wa labarin armashi.

Bugu da ƙari marubuciyar ta yi amfani da sassuƙar Hausa wajen rubuta labarin ta yadda kowa, zai fahimta. Sai dai ta yi amfani da kalmomin turanci masu yawa a cikin labarin waɗanda yawan da suka yi ka iya sa wasu makarantar su ji daɗi wasu kuma su ji akasain haka.

 Zubi da tsari

An tsara ko kasa wannan labari ne a zubin babi-babi, daga na ɗaya zuwa na arba’in da takwas. Littafin ya samu tsari mai kyau, domin tun daga babi na farko aka fara nuna mana irin soyayyar da ke tsakanin Safiyya da kuma ‘yarta Nana. Haka kuma an nuna mana irin halin wasu daga cikin taurarin labarin tun a babi na farko. Wani abin ƙarin armashi shi ne, tun daga nan, kowace jumla da ta biyo baya a labarin tana ƙarfafa ta bayanta ne. Sannan an samu zagi a tsakanin jumloli da babin labarin ta yadda na gaba ke ƙara fayyace na baya. Domin an fara ne da bayyana mana halin da Nana take ciki na rashin lafiya da kuma irin bauɗaɗɗen halin mahaifinta na rashin son yara wanda shi kaɗai ne ake tunanin zai iya taimaka mata ta rayu. Sannan a gefe an hasko mana irin yadda mu’amala ta fara tsami a tsakanin Dr. Jana da mijinta Jabir sakamakon aikin da take yi. To duk sauran babin da suka biyo baya suna ƙara fayyace waɗannan abubuwan ne.

Sannan an yi amfani da

Baɗoki na Gaske: “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un take furtawa a cikin zuciyarta. Ba mafarkin komai take ba da gaske ya faru. Da gaske ne ta bar komai ta zo ta auri Fu’ad. Ta baro Inna da Baba.

Ta watsar da duk wata tarbiya da suka gina mata shekaru goma sha takwas. (Babi na 18 sakin layi na ƙarshe). Da kuma cewar mahaifin Safiyya. “Na bar muku ita kyauta. Wallahi na yafe muku ita. Kamar yadda mahaifiyarta ta faɗa. Ba za mu yi mata baki ba. Sai dai zan tsine mata duk ranar da ta zo min gida.” (Babi na sha tara)

Wannan ya sa tun daga nan mai karatu zai iya fahimtar cewa tun da har ta watsar da iyayen ta ta auri wani akan so, to tabbas fushin su sai ya taɓa ta ko yaya ne. Wani ƙarin abin dubawa game da wannan labarin shi ne, ba wannan ne kaɗai baɗokin da aka yi amfani da shi ba, amma duk baɗokin na gaskiya ne, ma’ana duk sun faru daga ƙarshe, har ma da ƙari.

Ɗarsau na Tsoro:  An yi amfani da wannan dabara a wurare masu yawa a cikin wannan littafi, wasu sun faru da gaske wasu kuma ba su faru ba. Misali, “Option ɗaya ne kawai Ansar. Shi ne transplant idan an samu match…” Shiru Dr. Jana ta yi. Cikin aikinta babu abinda ta fi tsana sama da wannan ɓangaren. Kallon mutane a kullum lokacin da za ka faɗa musu mutuwar wani nasu. Ko lokacin da za ka tarwatsa musu burinsu da magana ɗaya… Muryar Jana can ƙasa ta ce; ‘Rayuwa a hannun Allah take Safiyya. Zan iya cewa ƙasa da wata shida. Idan Allah ya yi ƙarfin ikon shi, shekara ɗaya.” (Babi na uku)

Ɗarsau na Al’ajabi: “Safiyya kallon Fu’ad take zuciyarta na wani irin dokawa. Shi ma kallonta yake lokaci ɗaya maganganun Doctor ɗin da ya jagoranci yi mishi surgery na vasectomy suka dawo mishi. Cikin harshen turanci yake faɗa wa Fu’ad ɗin cewar, ‘Ko da bayan shekaru ko watanni matarka ta samu ciki karka zargeta. Ka ɗauka jikinka ya warkar da kanshi. Yana faruwa ga wasu mutanen.’ (Babi na 47)

Fu’ad ya ga abin al’ajabin da bai yi tsammani ba, domin ya sa an kashe mishi ƙwayoyinsa na haihuwa a asibiti, amma sai ga shi bayan shekaru goma sha ɗaya maganar da likitansa ya faɗa masa wasu ko an yi musu hakan suna iya ƙara samun haihuwa ta tabbata.

Ɗarsau na Tausayi: “Ji ya yi an dafa shi. Hakan ya sa ya ɗago da kanshi daga cikin hannayenshi sannan ya juyo, Safiyya ce fuskarta a kumbure. Wasu hawaye suka zubo mata. Kama hannayenta ya yi yana gogasu kan fuskar shi. “Sofi, ta rasu. Nana ta bar mu har abada.” (Babi na 45)

Ɗarsau na Mamaki: “Ba riƙo muka baku ba Fu’ad. Aisha Fu’ad Arabi. Mu muka haifeta. Amma ‘yarka ce Fu’ad. Allah ne shaidar mu akan wannan zamu amsa sunan masu haihuwarta ne kawai.” (Babi na 46)

Tabbas ko waye sai ya yi mamaki, ace mutane sun haifi yarinya nan take kuma su mallaka wa wani ita halak malak.

Ɗarsau na Murna: “Oh Allah. Ina bayin da suka sake ka suka kama waninka? Haƙiƙa suna cikin ɓata mai muni.” (Babi na47 sakin layi na kusa da ƙarshe)

• Hoton Zuci: An yi amfani da hoton zuci sosai a cikin wannan littafi ta yadda mai karatu zai ji kamar yana wurin abin ke faruwa. Misali, “Yadda ya yi da fuska ya ba Haneef tausayi. Don ya san bai saba ba sam. Kama hannunshi ya yi kamar yaro. Ya ja shi zuwa cikin shagon. Ko’ina a share yake tsaf. Da leda a shimfiɗe sai katifa an lailayeta da zanin gado. Kusurwar ɗakin jakunkuna ne da wasu kaya a rataye jikin ƙusa. Sai takalmansu can gefen wani bango akan siminti, wajen da alamu ledar ɗakin ba ta kai ba. Haneef ya ƙarasa ya cire takalminshi ya ajiye inda ya ga masu shagon na ajiye nasu. (Babi na 7 sakin layi na kusa da ƙarshe.

Tauraron labari

Ko shakka babu Fu’ad Arabi shi ne babban tauraron wannan labari. Shi ne ƙashin bayan labarin, kuma kaso 90% na matsalolin labarin shi ke ɗauke da su a ka. Kuma ya shafa wa duk wanda ke kusa da shi waɗannan matsaloli. A iya cewa shi ne silar samuwar matsala tsakanin Safiyya da iyayen ta, saboda da bai shiga rayuwar ta ba da bata fuskanci irin damuwar da ta tsinci kanta a ciki ba.

Halayen taurarin labari

• Bari mu fara da babban tauraron labarin wato Fu’ad. Matashi ne ɗan kimanin shekaru 22. Siriri ne, yana barin gashi akai sosai tare da son ƙananan kaya. Gwani ne a fagen ƙwallon ƙafa, yana da raina na ƙasa da shi musamman talaka. Yana da son kai, taƙama da kuma nuna isa. Kuma duk abin da ya ce zai aikata to sai ya aikata shi.

• Safiyya ita ce wacce ke take masa baya a cikin taurarin labarin. Ba baƙa bace, sai dai bata cika haske ba sosai. Gajeruwa ce ba kuma wata kyakkyawa bace a fuska, sai dai Allah ya bata idanu tubarkalla. Ba za ka kirata mummuna kai tsaye ba. Saboda jikinta na da kyau sosai. Tana da ƙira da dirin da mata da yawa za su yi hassada da ita saboda shi. Tana da haƙuri sosai kuma bata fiye yawan surutu ba.

• Haneef ɗan uwan Fu’ad ne na jini, domin ya girme shi. Shi ne mutum na farko da Fu’ad ke saurare kafin Lukman. Yana da haƙuri da juriya tare da son ‘yan uwansa. Musamman ƙanin nashi wato Fu’ad.

• Lukman shi ne babban abokin fu’ad tun suna yara. Abotarsu ta yi girman da har sun zama tamkar ‘yan uwa na jini. Mutum ne mai haƙuri da sanin ya kamata, kuma shi ne wanda ya zamo wa Fu’ad ɗin tamkar wani bango da yake jingina a jikin sa a duk lokacin da wani abu ya faru.

• Nana Yarinya ce ‘yar kimanin shekaru 12, tana da fara’a sosai tare da saurin shiga ran duk wanda ya ganta. Tana da wayon da har ya girmi shekarunta, domin wani lokaci in ta yi magana sai dai kawai a riƙe baki.

• Dr. Jana mace ce ɗaya tamkar dubu. Tana matuƙar son mijinta kuma tana da tsaron Allah sosai. Tana da ɗabi’u masu kyau, ciki kuwa har da danne kishinta na mace ta yarda da mijinta ya ƙara aure har ma da raka shi siyo kayan lefe.

• Nawaf matashi ne da Allah ya jarabta da Shaye-shaye. In ka cire wannan ba shi da wani mummunan hali face mugun kishin matarsa wanda shi ne ya zama silar ajalinsa.

• Nuriyya tsintacciya ce wadda mariƙiyarta da ta yi tunanin ita ce mahaifiyarta ta yi ta ƙoƙarin ganin ta sa ta a hanyar baɗala amma Allah ya tsare ta. Tana da haƙuri da juriya da halin rayuwa.

• Jabir kuma magidanci ne kuma ma’aikacin wani kamfani. Yana son matarsa sosai tare da ahalinsa. Duk da yana so ya ƙara aure, amma saboda soyayyar da yake yi wa matarsa da kuma irin matsyin da take da shi yasa sai da ya fara sanar mata kafin ma ya faɗa wa wacce yake so ɗin. Mutum ne mai ƙoƙarin kamanta adalci a koda yaushe.

Kammalawa

A dunƙule labarin yana isar da saƙonni ne masu tarin yawa a wuri guda. Daga cikinsu akwai gargaɗi ga masoya waɗanda wani lokaci idanuwansu kan rufe akan so har su je su yi abin da za su yi da na sani. Sannan an nuna muhimmancin iyaye da kuma yadda albarkar su ko fushinsu ke tasiri akan ‘ya’yansu. Sannan kuma an nuna muhimmancin ahali, da dangi da kuma abota mai tsafta. Haka kuma an nuna mana muhimmancin kyautatawa a tsakanin ma’aurata tare da ribar da za su samu yayin da suka yi wa juna adalci a zamantakewarsu, da sauransu.

Labarin zai sa ka shauƙi tare da duban rayuwa ta wani ɓangare sabo wanda ba ka taɓa tunanin akwai shi ba.

In da marubuciyar kawai ta samu kubcewar salo shi ne yawaita amfani da kalmomin turanci da ta yi a cikin labarin. Domin ta yi amfani da kalmomin turanci sama

da sau hamsin a cikin labarin. Ko da yake akwai wuraren da za a iya bata uzuri duba da irin sigar da labarin ya zo, akwai wuraren da za a iya amfani da kalmomin Hausa su zauna a wurin daram, amma sai aka yi amfani da na turanci. Misali, a cikin labarin akwai inda marubuciyar ta ce “Wani abu Fu’ad ya ji ya tokare masa wuya. Already baya jin daɗin komai….” (Babi na 10, sakin layi na uku)

Wanda wannan ‘yar gajeruwar jumla ana iya sauya kalmar ‘already’ da ‘tuni’ ko ‘da ma’ da makamantansu su ba da ma’anar da ake buƙata a wurin. Sannan kuma marubuciyar ta yi amfani da kalmar turanci ta ‘fuck’ kusan sau goma a cikin labarin wanda wannan na daga cikin irin abubuwan da ya kamata a dinga kaucewa.

In ka cire waɗannan abubuwan guda biyu, to babu abin da za a ce wa wannan littafi sai sam-barka, domin ya nishaɗantar, ya ƙayatar, kuma ya ilmantar.

Don karanta cikakken wannan littafi na ‘Akan So’ sai a latsa nan.

Kana ana iya duba sharhin ‘Abdulkadir’ wani daga cikin littattafan Lubna Sufyan.

Manazarta

Ɗangambo, A. (1984) Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph

Yahaya, I. Y. da Ɗangambo, A. (1986) Jagoran Nazarin Hausa. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company Limited.

Yahaya, I. Y., Zaria M. S., Gusau M.S., da ‘Yar Aduwa T.M. (1992) Darussan Hausa don Manyan Makarantun Sakandire 1. Ibadan: University Press Plc

6 thoughts on “Sharhin littafin ‘Akan So’ na Lubna Sufyan”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page