Skip to content

Sharhin littafin ‘Rayuwarmu’ na Lubna Sufyan

Sunan Littafi: Rayuwarmu

Marubuciya: Lubna Sufyan

Inda Aka Buga Littafi: Bakandamiya Hikaya

Shekarar Bugu: 2022/23

Yawan Babi: 51

Mai Sharhi: Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)

Manufar Sharhi: Bunƙasa Harshen Hausa da ciyar da adabi gaba.

Gabatarwa

Rayuwar duniyar nan cike take da ƙalubale iri-iri. Yadda duk mu ke tunanin mun gama ganin kowane shafi na rayuwa, matuƙar ba mutuwa muka yi ba, to akwai wani shafin a gaba. Wannan littafi na ‘Rayuwarmu’ ɗauke yake da madubin dubawa zuwa ga yadda rayuwarmu ta kasance a baya, yadda take a yanzu da kuma izna zuwa ga yadda za ta kasance a nan gaba.

Tarihin marubuciyar a taƙaice

Marubuciya Lubna Sufyan an haife ta ne a ƙaramar hukumar Ingawa da ke birnin Katsina. Fitacciyar marubuciyar ta fara karatun addini tun tana ƙarama kuma ta yi karatunta na Firamare ne a garin Katsina, daga baya ta koma garin Kano inda ta yi karatun Sakandire har ta gama. Bayan ta gama ne sai ta koma Katsina in da ta yi karatun Diploma a ɓangaren zanen taswirar gidaje. Daga baya kuma ta ci gaba da karatu a mataki na gaba, wato babbar Diploma wadda da turanci ake ce wa Higher National Diploma (HND) a Kaduna.

Kamar mafi yawancin marubuta, marubuciyar ita fara rubuce-rubuce ne tun tana makaranta, kuma ta kasance ɗaya daga cikin fitattun marubutan online na wannan zamani, domin abu ne mai wuya ka faɗi sunanta a duniyar marubuta da makarantan wannan zamani ba a samu wanda ya santa ba. Zuwa yanzu marubuciyar ta rubuta litattafai sama da guda goma sha ɗaya. Wasu daga cikin litattafan da ta rubuta sun haɗa da;

Rai Da Ƙaddara
Wata Bakwai
Akan So
Tsakaninmu
Abdulƙadir
Mijin Nobel
Martabar Mu
Alƙalamin Ƙaddara
da dai sauransu.

Har’ilayau kuma, marubuciyar ta kasance mai son girke-girke ce sosai. Kuma baya ga rubutu, marubuciyar tana yin fassara daga harshen Turanci zuwa Hausa, wannan aiki na fassara ne ma ya zama sanadin yin aikinta da kamfanoni da ƙungiyoyin gwagwarmaya masu zaman kansu a lokuta daban-daban a kuma kan batutuwa iri daban-daban kamar su GiveNorthEducation, WomenInArewa, WomenInFinance da dai sauransu. Sannan kuma, marubuciyar ta sha yin aiki da makarantun Islamiyya da bloggers wajen fassara musu aiyukansu. Haka kuma ƙwararra ce wajen haɗa ɗuwatsun ƙawa na adon mata. Sannan kuma tana aikin juyar da bayanan murya zuwa rubutu (transcription). A taƙaice dai, duk in da aikin rubutu yake, to a nan marubuciyar ta fi ƙarfi.

Marubuciyar kuma na ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar marubuta na Fikra Writers Association. Lubna Sufyan ta yi aure a shekarar 2022, kuma tana zaune ne a garin Kaduna yanzu haka tare da mijinta.

Labarin a Taƙaice

Rayuwarmu labari ne akan wani babban ahali da ya ƙunshi mutane da dama a cikinsa. Ko da yake kusan kowa da ke cikin ahalin mutumin kirki ne, hakan ba ya nufin babu saniyar ware a cikinsu, kuma hakan ba ya nufin ba za su fuskanci ƙalubale ba a rayuwarsu.

A daidai lokacin da rayuwa ke yi wa su Dawud daɗi duk da ƙarancin wadatar arziƙi da ta same su, kwatsam sai gashi wata mata ta yi wa rayuwarsu dirar mikiya ta hanyar ƙwallafa ranta akan mahaifinsu wato Auwal. A dalilin wannan mata ne suka tsinci kansu a cikin tashin hankalin da ko a mafarki basu taɓa tsammanin shiga cikin irinsa ba. Hakan ya sa Dawud ɗaukar nauyin da bai shirya ba a kafaɗar shi wadda ita ma neman wanda za ta jingina da shi take yi.

Labeeb jarumin fim ne wanda ya yi shura. Baya ga wannan, ya fito daga gidan kuɗi ta yadda ba za ka taɓa tunanin yana da damuwa ba a rayuwarsa. Sai dai kash, ya faɗa cikin rayuwar shaye-shaye da neman mata. Kwatsam kuma sai ƙaddarar rayuwa haɗa shi da Mamdud wanda ya ɗauka a matsayin aboki kuma ɗan uwanshi. Abinda bai sani ba shi ne, zuciyar Mamdud a koda yaushe ƙuna take yi bisa ganin yadda komai ke zuwa mishi da sauƙi sakamakon kuɗi da kuma baiwar shura da Allah ya yi mishi. Abin da Mamdud bai fahimta ba shi ne, duk iya farincikin da Labeeb ke bayyanawa a fili, damuwar da ke cikin rayuwarshi ta fi wannan. Rikici da turka-turkar da ke tsakaninsu ba ta fito fili ba sai da ƙaddara ta haɗa su son mace ɗaya.

Labeeb shi ne wanda ya zamo bangon da su Dawud suka jingina da shi a lokacin da suka shiga halin matsi na rayuwa. Wannan dalili ne ya sa suke ganin girman shi sosai. Kwatsam kuma sai ga wani mummunan al’amari ya ratso ta cikin wannan kyakykyawar mu’amala tasu. Yadda al’amarin ya fara, yadda ya ci gaba da faruwa da kuma yadda ya ƙare wata tafiya ce wadda za ta taɓa zuciyar duk wanda ya karanta wannan labari.

Jigo

Duk da cewa soyayya ta yi tasiri babba wajen ginuwar labarin, kai tsaye ba zai yiwu a ce soyayya ce jigon wannan labari ba. Babu ko tantama, babban jigon wannan labari shi ne ‘Ƙalubalen Rayuwa.’ Mai karatu zai yarda da ni akan wannan batu da zarar ya karanta babin farko na wannan labari kawai ba tare da ya yi nisa ba. Kuma tun daga nan har zuwa ƙarshen labarin taurarin cikinsa ba su daina fuskantar ƙalubale ba. Na daɗe ban karanta wani labari wanda taurarinsa ke fuskantar ƙalubale da yawa irin na wannan littafi na Rayuwarmu ba . Kuma ta wannan hanya ce marubuciyar ta yi ta ƙoƙarin fayyace jigon tare da ƙarfafa shi a kowane babi na littafin.

Warwarar Jigo

Ga wasu daga cikin hanyoyin da marubuciyar ta bi wajen warware wannan jigo:

• A babi na farko ta fara hasko wa mai karatu irin ƙalubalen da ke biyayyar manya da ƙananan taurarin labarin irin su Labeeb, Dawud, Zulfa, Mardiyya ds. Haka ta tafi da wannan salo har zuwa babi na biyu inda daga na uku kuma ta fara komawa baya domin ta bayyana wa mai karatu asalin yadda al’amuran suka fara afkuwa.

• Mahaifin Dawuda, wato Auwal ya samu ƙalubalen kora daga aiki wanda hakan ya kawo canji babba a zamantakewar shi da iyalinsa. Matsi na rayuwa ya sa shi shiga neman aiki fafur, yayin da matarsa Aisha (Ummi) ita ma hakan ya sa dole ta kakkaɓe kwalinta na NCE ta nemi aikin koyarwa. (Babi na 30)

• Hajiya Beeba ta samo wa Auwal aiki, sai dai kuma a ƙasan zuciyarta son shi take kamar ta yi hauka, yayin da shi kuma ba ta ita yake ba. Hakan ya sa ita ma ta zagara wajen ganin ta shawo kanshi. Saboda matsin lamba da Hajiya Beeba ke mishi ya sa dole Auwal ya ajiye aikin shi. Ita kuma Ummi hakanan ta siyar da filinta na gado ta bashi kuɗin domin su biya kuɗin makarantar yara sauran kuma ya ja jari da su. A ƙarshe dai sai ga Hajiya Beeba a wurin boka ta je neman asirin da za ta mallake zuciyar Auwal ɗin. (Babi Na 4-5)

• Asirin da Hajiya Beeba ta sa aka yi wa Auwal ya fara aiki. Hakan ya kawo mummunan sauyi a tare da shi. Daga ƙarshe dai sai da aka ɗaura musu aure da ita wanda hakan ya jefa rayuwar Ummi da ‘ya’yanta a cikin matsanancin hali, ciki har da yi wa ‘yarta (Sajda) asiri ta shiga wani yanayi mai kama da hauka. Kamar fa hakan bai isa ba kuma sai da ya sake ta, ya koreta da ciki tare da cewa ba nashi ba ne cikin, kuma sauran yaran ma ba shi da tabbaci akansu. (Babi na 6-9)

• Bayan Labeeb ya basu wurin zama, ba a jima ba kuma sai Ummi ta mutu a yayin haihuwar Khateeb. A sanadiyar hakan ne rayuwa ta sake jagule musu. Haka suka yi ta tafiyar da rayuwar har tsawon shekaru bakwai. A daidai wannan lokacin shi kuma Labeeb Mummy ta zaɓa mishi wadda zai aura ba tare na da yasan ko wacece ba balle a yi maganar soyayya. Shi ma Dawuda a cikin wannan hali ne ya haɗu da Yumna a wani yanayi mai ban mamaki har soyayya ta ƙullu a tsakaninsu, sai dai kuma ita ma tana da nata ƙalubalen da take fuskanta. Kwatsam kuma sai ga Auwal ya dawo cikin rayuwarsu da nufin su dawo wajen shi da zama. Ana cikin haka ne kuma Sajda ita ma ta mutu a sanadiyar gobarar da iskar gas ta haifar yayin da take girki. (Babi na 10-16)

• Rikicin ya sake ɓallewa ne lokacin da Labeeb ya gano cewa Zulfa na ɗauke da cikin Mamdud. Maimakon ya bayyana gaskiyar magana kawai sai ya tara danginsu gaba ɗaya ya ce cikin nashi ne domin ya kare ta daga fuskantar ƙalubalen da za ta shiga. Ana cikin haka kuma sai ga wani yaro an zo da shi wai na Labeeb ɗin ne alhali bai san da shi ba. Wannan lamari fa shi he ya jawo ɓallewar sabon rikici a tsakanin shi da matarshi wadda ke da tsohon ciki a daidai wannan lokacin da kuma rashin fahimta a tsakanin shi da sauran ‘yan uwanshi. Waɗannan da ma wasu misalai masu yawa irinsu su ne suka taru suka tabbatar da ƙalubalen rayuwa a matsayin jigon wannan labari

Bayan wannan babban jigo da na yi bayani, marubuciyar ta yi amfani da wasu ƙananun jigogi masu yawan gaske waɗanda su ne suka haɗu suka goya wa labarin baya ta hanyar koyar da darussa da dama a cikin wannan labari. Ga wasu kaɗan daga cikinsu kamar haka:

• An nuna illar biye-biyen mata ba aiki ba ne nagari. Kuma marubuciyar ta nuna mana haka a wurare da dama a cikin labarin, musamman akan rayuwar Labeeb da Mamdud.

• Wani ma bai taɓa sanin ana iya yi wa namiji fyaɗe ba, amma a wani yanayi irin wanda ba a saba gani ba, sai ga shi an nuna wa mai karatu irin yadda fyaɗe ke taɓa rayuwar maza idan aka yi musu. Kamar yadda Labeeb ke bayyana wa Mamdud, “Ba za ka gane ba….. Kullum da daddare sai ta shigo ɗakinaa….. She… She is so big….. She raped me…. Mummy ba ta damu ba, ba ta nan… Kullum kullum Mamdud, ba zai sake faruwa ba, ba mace bace za ta ɓata ni….. Ni ne zan ɓata ta…. Ba zai sake faruwa ba…..” Kuma wannan ya fito da illar barin yara a hannun ‘yan aikin gida. (Babi na 21)

• An yi nuni zuwa ga irin kaɗaicin da irin yaran da iyayensu ba sa samun lokacinsu kan shiga. Musamman irin yadda su ke kewar iyayen nasu. Misali, inda marubuciyar ta ce, ‘Su dukkan su magana suke yi a lokaci ɗaya. Babu mai bari wani ya gama, duka so suke ta basu hankalinta. So suke ta saurare su. Shi kanshi Labeeb da ke tsaye yana binsu da kallo hakan yake so.
Hira yake so su yi da Mummy ko na minti sha biyar ne, su zauna waje ɗaya, su yi labari, ya ji muryarta, dariyarta. Ba su Zainab kaɗai ke buƙatar kulawarta ba. (Babi na 22)

“Ba zai barmu ba? Ba zai dinga tafiya kamar Mummy ba?” (Babi na 21)

Na gaji da zama ni da TV, na gaji da kallo, ba wanda ya damu da ni, not Mum, not Dad and not you, ba za ka gane ba saboda kana da Yaya Anees………just…. Get out of my room.” (Babi na 21)

• An yi izna zuwa ga rashin dacewar shiga irin wadda ba ta dace ba. Misali, Mutane ne cike, maza da mata, Musulmai da kiristoci da ba za ka gane bambancin su ba, saboda kusan shigar tasu iri ɗaya ce, kuma sun cure waje ɗaya. (Babi na 22)

• An yi nuni bisa irin yadda makauniyar soyayya ke jawo matsala. Misali, ‘In don ta Mummy ne da wahala in basu gama maganar har da Dadyn su ba. Son da Dady yake mata ba ya barinshi ya ga kuskuren hukuncin da duk za ta yanke akansu ko da akwai shi. (Babi na 24)

• An koyar da mu darasi a likitance a wurare da dama na littafin. Misali, ‘Ni ba hatsari na yi ba…ina da lalurar PCOS (Polycystic ovary syndrome) ba lallai in haihu ba… Chances ɗin kaɗan ne. (Babi na 51)

• An koyar da muhimmancin sadaukarwa da alfanunta. Misali, dubi yadda labeeb ya ba wa Mamdud kyautar ɗansa da kuma inda yake cewa, “Na san ba daga jikinka ya fito ba… Na san babu jininka a jikinshi…sai dai zuciyarshi yanzun take girma… Soyayyar mahaifi a wajenshi yanzun za ta fara tasiri.
Ba zai gane banbancin jinin ba… Ƙaunar kawai zai fahimta…Allah ya sa zai iya rage maka raɗaɗin abinda ka rasa da wanda ba za ka samu ba…” (Babi na 50)

• An nuna tsantsar soyayyar da ke tsakanin ma’aurata ta hanyar nuna misali a zamantakewar Labeeb da Ateefa, Dawud Da Yumna, Abba da Ummi ds.

• An hasko mana irin yadda mutane masu halin Mummy suke tunani. Kamar yadda marubuciyar ta ce,
‘Ta gama tsara rayuwarta, ta gama hango lokacin da za ta ajiye kasuwancinta ta zauna da yaranta.
Lokacin da za ta ƙaunace su, ta ɗauka tana da dukkan lokacin da take buƙata a hannunta. Tun shekaranjiya ta gane ita ba komai bace ba. (Babi na 36)

• An nuna irin yadda hassada da rashin tawakkali ke tasiri wajen gurɓata wa mutum tunaninsa,
‘Gyara zamanshi ya yi yana kallon Labeeb na cashewa abinshi, sun cakuɗe waje ɗaya har da mata.
Hannuwan wata tsaf a ƙugun Labeeb ɗin , bai ko nuna hakan ya dame shi ba. Wasu lokutan har mamaki yakan ba Mamdud, komai yana yi kamar abin ya zo mishi natural ne ba tare da koyo ba. Abin na bashi takaici ba kaɗan ba. (Babi na 30)

• Sau da dama yanke hukunci cikin fushi kan sa mutum yin da na sani. Kamar yadda marubuciyar ta ce, ‘Mamdud ke tuna kalaman da ya yi wa Labeeb ɗin, furuci ne da ya yi cikin fushi, ba don yana nufin abinda ya ce ba. Sai dai ya riga da ya zo akan gaɓa.
Ya furta, Allah kuma ya ƙaddara faruwarshi, ya san ya taɓa abinda ya fi kusanci da Labeeb. (Babi na 34)

• An nuna irin yadda wasu matan ke jefa ‘ya’yansu cikin bala’i a gidan aure ta hanyar yi musu mummunar huɗuba.

“Maza irin El-labeeb Maska babu kalar matan da basu gani ba. Ba wani daraja za ki yi a idanuwanshi ba.
Ki tabbatar kin kwashi rabonki kafin ya gaji da ke. Kuɗi ne zai shigar da ke gidanshi, ba matsala ba ne su a wajen shi. Ki tabbatar kin cika account ɗinki kafin ki dawo min.” (Babi na 25)

“Ki tabbatar kin kwashi rabonki kafin ya gaji da ke. Kuɗi ne zai shigar dake gidanshi, ba matsala bane su a wajen shi. Ki tabbatar kin cika account ɗinki kafin ki dawo min.” (Babi na 25)

Da kuma inda ta ce,
What? Shi ɗin banza, aure zaman kurkuku ne da zai kafa miki sharuɗɗa haka. Waye El-Maska ɗin? Me ya tara? Ki tafi makaranta abinki. Kin ji ni, sai ka ce ba jinina ba za ki zauna kina ma namiji kuka.” (Babi na 26)

• Soyayya a tsakanin ‘yan uwa ta taka muhimmiyar rawa wajen ginin wannan labari. Misali, an nuna yadda ɗan uwa kan ji canjin yanayi a jikinshi yayin da wani abu ya faru da makusancin shi.
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.”
Ta faɗi da ya maida hankalin Ishaq kanta.
“Lafiya Zainab?”
Idanuwanta cike da hawaye ta ce,
“Nima ban sani ba… Wani abu ya faru… Don Allah ka kaini gida…” 36 nuni da girman kusancin ‘yan uwa.

• An nuna burin da iyaye kan ci wajen ganin ‘ya’yansu sun zama wani abu. Misali,
“Kasan yawan kuɗin da ke account ɗinka kuwa? Kasan garuruwan da fina-finanka suke zagayawa? Kana da fans all over Nigeria, wa ya sani ko harda wajenta ma.” (Babi na 21)

• An nuna muhimmancin aure da irin nutsuwar da ake samu a cikinsa. Dubi yadda marubuciyar ta bayyana wannan batu a cikin zance mai sauƙin fahimta, ‘Har mamakin kalar control ɗin da ya samu yake yi. Ya ɗauka aure ba zai taɓa zamar mishi mafita ba sai yanzun ya ga banbancin hakan. (Babi na 26)

• Wulaƙanci ba shi da kyau, kuma marubuciyar ta nuna irin yadda rayuwa kan juya ka koma neman wani abu a wurin wanda ka wulaƙantata. Kamar dai yadda marubuciyar ta ce, “Ba sai na faɗa maka ba, kasan yadda na raina ‘yan ƙauye. Ciki har da wasu daga dangin Mamana, kasan yadda nake wulaƙanta duk wani da ke ƙasa da ni. Nice yau zuciyata take dokawa ɗan Maigadi. ” (Babi na 33)

• Mutuwa da darasin da ke biyo bayanta sun taka muhimmiyar rawa a cikin wannan labari. Duniya yadda marubuciyar ta bayyana halin da Labeeb ya shiga bayan mutuwar Sajda, ‘tun bayan rasuwar Sajda sai da ya kusan kwana arba’in bai sha komai na maye ba. Inda duk yasan zai iya zuwa ya samu temptation baya zuwa. (Babi na 27)

Da kuma inda yake cewa, ‘Kamar wasa na rasa Arif… Ba zai dawo ba. Bazan sake asarar lokaci na ina faɗa da wani ba… Bamu da su da yawa… Babu… Babu lokaci mai yawa a rayuwarmu.” (Babi na 37)

Dubi kuma yadda Mummy ta shiga cikin tashin hankali bisa mutuwar Arif, ‘Ya za a yi ya ce mata Arif ya rasu. Ta yaya? Me ya same shi? Babu yadda za a yi ya rasu. Duka lokacin rayuwar shi nawa ta samu? Bata ma san abincin da ya fi so ba, ba za ta tuna sa’adda suka yi maganar awa ɗaya da Arif ba. Ba ta gama sanin ɗanta ba. Ba ta ko samu lokacin da za ta so shi yadda ya kamata ba. Ba yanzun ba, Arif ba zai barta yanzun ba ta nuna mishi kalar ƙaunar da take mishi ba. (Babi na 36)

Sai kuma inda marubuciyar ta ce, Arif yake kallo a kwance da idanuwanshi, a zuciyarshi yanayin shi yake kallo da rayuwar shi.
Shiru-shirun shi, murmushin shi, yanayin maganar shi. Cikin kunnuwan shi yake jin yadda yakan kira sunan shi, yanayin yadda yakan saka su dariya in har yai magana. (Babi na 36)

Salo da Sarrafa Harshe

Marubuciyar ta baje basira ƙwarai da gaske wajen ba da labarin wannan littafi. Saboda ta yi amfani da salo iri-iri kuma duk masu jan hankali ne da burgewa wajen isar da saƙon labarin a sauƙaƙe.

• Salon Koyarwa da Nuni: Marubuciyar ta yi amfani da wannan salo sosai a cikin wannan littafi domin isar da saƙonta. Ga kaɗan daga ciki,
‘Wajen bakinta ta kai kofin ruwan shi tana yin addu’a a ciki kafin ta ajiye a ƙasa, ta saka hannunta cikin kofin tare da yin Bismillah ta ɗibo. Murza shi ta yi tana shafa wa Sajda a saman kanta, sannan ta ƙara ɗibowa ta shafa mata a fuska, da hannu ɗaya ta riƙe kan Sajda, ta ɗibo ruwan ta buɗe bakinta ta ɗura mata shi.
Furzo shi waje Sajda tayi, saitin kanta ta tsugunna. Cikin kunne take mata addu’o’i har jikinta ya soma sanyi. A hankali ta bar ihun da take yi.
Sake ɗiban ruwan tayi ta shafa mata tun daga kanta har wuyanta, sannan ta karɓeta daga hannun Dawud ɗin. (Babi na 13)

Da kuma inda ta ce, ‘Dutsen da Anees ya samo wa Mamdud ya yi taimama da shi ya miƙa mishi, ya tsaya ya yi ya ja gadon yana juya shi yanda zai fuskanci gabas kamar yadda suka yi mishi ɗazu tunda babu dama ya motsa ƙafarshi. (Babi na 45)

Salon Barkwanci/ Nishaɗi: “Mami kinsan jiya da na biyo kasuwa sai da na ga wajen da kike cefane.”
“Halan ka biyo ta layin ‘yan doya.”
Dawud ya faɗi yana kallonshi. Sai da ya haɗiye abincin da ke bakinshi ya ƙara wani sannan ya juya ya ɗan kalli Dawud ɗin.
“Wallahi kamar ka sani, ta nan na biyo da zan dawo…..” (Babi na 14)

Da kuma inda marubuciyar ta ce,
“Kinsan Allah Aljanu fa, kin ga an wanke kayan wanke wanken dana ɓata, jiya kuma na ga wata yarinya a gidan da…”
Dariya Labeeb ya ji data sa shi juyawa, Asad ne a tsaye.
“Aljanun ne suka wanke kwanoni…” (Babi na 27)

Salon Tafiyar Kura: An yi amfani da salon tafiyar kura ne a cikin wannan littafi, inda marubuciyar ta fara ba da labarin daga tsakiya sannan ta ci gaba da warware shi a hankali a hankali ta hanyar komawa baya ta kawo wani batu sannan ta dawo ta ci gaba daga baya kuma ta sake komawa ta kwance wani a baya kafin ta kuma dawowa ta ci gaba. A iya cewa ma ta kwashe kusan rabin littafin ne wajen warware matsalolin da ke ƙunshe cikin labarin ta wannan hanya ko salo. Kuma hakan ya taimaka wajen fayyace wa mai karatu wasu abubuwan masu sarƙaƙiya ba tare da bayyana yadda ƙarshen littafin zai kasance ba.

• Sarrafa Harshe: Marubuciyar ta yi amfani da Karin Magana da kuma kalmomin azanci, hikima, tsima jiki, sa tausayi, kwantar da hankali da kuma gyaran tunani duk a cikin wannan littafi. Wani lokaci ma sai mai karatu ya ji kamar zaunar da shi aka yi ana mishi nasiha game da yadda ya kamata ya tunkari rayuwa da ƙalubalen da ke cikinta. Ga kaɗan daga ciki,

Sauka ba ya nufin ƙarshen karatunka na Islama, yana nufin ka dai samu ci gaba ne babba a hanyarka ta neman ilimi, don kogi ne, yana da faɗi, sai dai ka yi iya yinka. (Babi na 14)

Allah ba ya barin wani don wani. (Babi na 50)

“Me na faɗa maka? Tsintacciyar mage ba ta mage dama… Wanda ka tsamo daga rana zuwa inuwa gashi nan ya turaka tsakiyar rana har wuta ya kunna maka!” (Babi na 42)

Kowanne ɗan Adam a rayuwarshi ba zai rasa abu ɗaya mummuna ba. Ba zai rasa wani laifi ko aibu babba ba. Saboda me za ka danne naka ka nuna wa wani ɗan yatsa?
(Babi na 41)

Damuwa na ɗaya daga cikin abubuwan da rayuwa ta ƙunsa, babu wani farin ciki da yake dawwamamme kamar yadda babu damuwar da take dawwamammiya.
(Babi na 45)

“Ba muna zama da juna ba ne don mun manta laifukan da muka yi wa juna. Muna zama da juna ne don mun yafe… In babu yafiya duka za mu rasa kanmu ne.
Akwai laifukan da za mu aikata waɗanda da babu yafiya ba zamu iya kallon kawunanmu a mudubi ba. Akwai sauƙi mai girma a cikin yafiya…ka yafe duk sa’adda ka samu damar hakan.”
(Babi na 50)

“Idan har ba ka daina jin tsoron me mutane za su ce akan abin da ya wuce a bayanka ba, zai ci gaba da zama barazana a tare da kai . Abinda ya faru da kai naka ne… Akanka ya faru… Ka karɓe shi. Zai daina tsorata ka.”
(Babi na 51)

“Ba komai da ka ke so ba ne ka ke samu a rayuwarka Sajda. Lokuta da dama abubuwa suna faruwa da ba ka sanin dalilin su.
(Babi na 13)

A ƙarƙashin duk waɗannan kuma, marubuciyar ta yi amfani da sassauƙar Hausa wajen rubuta wannan labari. Sai dai kamar yadda mai karatu zai gani, ta yi amfani da kalmomin turanci sosai a cikin labarin waɗanda duba da yanayin Taurarin Labarin da irin rayuwarsu ba a ce kai tsaye suna da matsala ba sai dai akwai ƙofofin gyara.

Zubi da Tsari

Labarin Rayuwarmu cike yake da sarƙaƙiya da faɗi tashi. Ba wai kuma don rashin salo ko tsaurinsa ba. Sai don yadda yake cike da ƙwarewa ta yadda komai hasashen mai karatu ba zai iya hasaso abinda zai faru a gaba ba.

Marubuciyar ta gabatar da zubi da tsarin littafin ‘Rayuwarmu’ daidai yadda ya dace da yanayin halayyar taurarin littafin ta yadda mai karatu zai ƙagara ya ga yadda za ta kaya, tare da jefo ba-zata a wasu lokutan. Ta kuma yi amfani da nau’o’in mutuwa wajen kawar da wasu taurarin waɗanda ci gaba da kasancewarsu, za ta haramta warware sarƙaƙiya cikin littafin. Misali, an kashe taurari irin su Ummi, Sajda da kuma Arif.

Marubuciyar ta zayyana labarin Rayuwarmu ne a cikin littafi ɗaya duk da cewa ya ɗan yi tsayi. Sai dai irin yadda labarin ke da shiga zuciya da kama tunanin mai karatu, kana iya shafe tsawon lokaci ba tare da ka ankare ba. Sannan an nuno yadda rayuwar jaruman ta fara a lokacin da babu wayar hannu irin ta zamani har zuwa lokacin da akwai.

An kuma yi tsallaken lokaci a cikin labarin domin bayyana abin da ya faru a wasu lokuta na rayuwar taurarin labarin.

Misali

Bayan shekaru uku (Babi na 21)
Bayan Wata Ɗaya (Babi na 03)
Bayan Wata Biyu (Babi na 04)
BAYAN WATA BAKWAI (Babi na 08)
BAYAN SHEKARA BAKWAI (Babi na 13)

Gaba ɗaya labarin ya faru ne a cikin garin Kaduna. Sai kuma wani ɓangare da ba kasafai aka cika bayani akai ba, shi ne wuraren da Labeeb ke tafiya domin gudanar da ayyukan shi.

• Baɗoki Na gaske: “A gidanmu na karɓo, zam zam ne da addu’oi. Komai ya kusan zuwa ƙarshe In sha Allah.” (Babi na 35)
Kuma lallai bayan wani lokaci al’amuran duk sun faru.

• Baɗoki Na Giri: An nuna gabatowar tashin hankali bisa soyayyar Mardiyya da Danish amma ba a yi wani bayani gamsasshe ba. An kuma nuna matsalar da Yumna take ciki babba ce amma ba a faɗaɗa bayanin ba.

• Ɗarsau Na Mamaki: “I was so so stupid…ya aka yi ban gane ba?”(Babi na 48)

• Ɗarsau Na Tausayi: Zafin da yake ji yanzun ya girmi hassadar da ta baibaye zuciyarshi har ta kawo shi inda yake tsaye yanzun. Ya kasa ɗaga idanuwan shi ya kalli Labeeb. (Babi na 35)

Kallon su yake da wani yanayi a ƙirjinshi. Dukkansu suna jin ƙaunar junansu, suna jin yadda suka haɗa jini.
Ko sau ɗaya, ko sau ɗaya a rayuwarshi yake so ya ji ya kalar shaƙuwa irin wannan take. Ya za ka ji ka kalli mutum kasan jini iri ɗaya ne a jikinku. (Babi na 28)

Wasu hawaye ne masu ɗumi suka tarar wa Mamdud a idanuwa, da ka ga yanayin da Arif yake maganar kasan a wahalce yake yinta. Abinda yake ji bai hana shi roƙar mishi gafarar su Labeeb ba.
Bayan baisan me ya yi ba, wannan ƙaunar son zuciya ya ja mishi rasawa. Ƙaunar da yake da yaƙinin ko ‘yan uwan da suka haɗa jini da shi ba kowa zai so shi kamar Arif ba. (Babi na 35)

• Ɗarsau Na Tsoro: Yana zama ya ji ya zauna kan wani abu kamar mutum. Ƙara ya saki yana miƙewa. Ya tsorata ba kaɗan ba. Ba arziƙi ya lalubi switch ɗin ɗakin ya kunna. (Babi na 28)

• Ɗarsau Na Murna: “Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ke da Iko akan komai da kowa. Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da yake kyauta ga wanda Ya so. Tsarki ya tabbata ga Ubangiji…” (Babi na 51)

Hoton Zuci

Kusan kowane shafi ko babi na littafin ka buɗe kana karantawa sai ka dinga gani tare da jin kamar a gabanka abin ke faruwa saboda irin yadda marubuciyar ke bayani filla-filla.

Misali;

Ƙwanƙwasawa suka ji ana yi, tun kafin Dawud yai magana Zulfa ta tashi da gudu ta buɗe tana ƙanƙame shi. Ɗaga ta ya yi da faɗin,
“Zulfa ta ba ta kowa ba.”
Dariya ta kama yi tana ɓoye kanta a jikin wuyanshi. A dole kunya take ji.
“Yaya ka sauke ni.”
Sake riƙeta dam Labeeb yayi.
“Kin girma yanzun ko. Na ƙi in sauke ki ɗin.”
Harbe-harben ƙafa ta dinga yi. Jin tana neman kayar da su yasa Labeeb ya sauke ta yana ja mata kunnuwa.
“Shikenan yanzun Zulfan nan ba tawa bace ni kaɗai.”
Turo baki tayi.
“Taka ce mana.”
Ya girgiza mata kai yana haɗe fuska. Shirin kuka ta fara.
“Da wasa nake fa. Waye ma zai ce zulfan shi gani.” (Babi na 13)

Tana ficewa daga ɗakin ya ga ta ja ƙofar ya diro daga kan kujerar ya ɗauki kayanshi da ke watse a ƙasa, dogon wandon kawai ya saka da singlet, rigarshi a hannu ko takalmi bai saka wa ƙafarshi ba ya bita. (Babi na 23)

Taurarin Labari

Rayuwarmu littafi ne da ke ɗauke da taurari masu tarin yawa, wasu manya, wasu kuma masu take musu baya. Akwai taurari guda uku da suka fi fice, waɗanda ana iya cewa ma gaba ɗaya su suka ɗauki nauyin labarin a kafaɗun su. Waɗannan taurari kuwa su ne Labeeb Ibrahim Maska, Dawud Auwal da Kuma Mamdud. Sai dai duk da wannan, Labeeb ya fi Dawud taka rawar gani a cikin labarin, duk kuwa da cewa Dawud shiga gwagwarmaya da rikici mai yawa. Kuma ƙalubalen da Labeeb ya fuskanta ya fi na kowa a cikin labarin, domin shi ya ɗauki kusan nauyin kowa da laifin kowa a cikin labarin. Akwai taurari da yawa a cikin labarin bayan su da suka haɗa da Sajda, Mami, Yumna, Asad, Anees, Huzai da dai sauran su.

Halayen Taurarin Labari

• Dawud: Matashin likita ne wanda ke matuƙar son ‘yan uwanshi. Jarabawar rayuwa ta sa tun da sauran ƙuruciyar shi ya zama babba a hankali da zuciya. Yana da zafin rai sosai, kuma yana da tausayi da taimako. Kamar yadda marubuciyar ta bayyana shi da cewa, “Ban taɓa ganin mai ƙarfin zuciya irin shi ba.” in ji zainab a babi na 32. Da kuma in da ta ce, “Tun barin mu gida na fara haka. Sai rasuwar Ummi… Ga Khateeb….Ga Sajda. Ina jin tsoro… Ina ganin kamar da na rufe idanuwana wani abun zai same ni babu wanda zai kula da su. Kamar in na yi bacci wani abu zai same su su ma. (Babi na48)

• El Labeeb: Matashin jarumin fim ne. Yana shaye-shaye da bin mata, sai dai kuma yana da kyauta, tausayi da kuma ƙaunar ‘yan uwansa fiye da komai. A wurare da dama marubuciyar ta bayyana shi a matsayin mutumin da zai iya yin komai saboda ‘yan uwanshi. Kamar yadda marubuciyar ta bayyana irin halin shi. ‘Kallonta Labeeb ya yi yana daƙuna fuska. Da ka ga yanayinta kasan tana cikin halin rayuwa. In tana da iyali bai ga me dubu ashirin za ta yi mata ba.
“Nasan ba hurumina ba ne… Amma shin kina da yara?”
Kai ta ɗan ɗaga.
“Yarana shida…”
Sauke numfashi ya yi.
“In kin tashi dafa abinci kullum ki yi da yawa sosai, wanda zai isa har da su. Zan baki dubu hamsin duk wata… Ya miki?” (Babi na 41)

• Mamdud Maraya ne da ya taso a gidan marayu. Ƙaddarar rayuwa ta haɗa shi da Labeeb har ya samu ‘yan uwa a tattare da ahalin shi. Yana da buri sosai a rayuwa wanda hakan ya ba hassada damar shigar shi. “Karki yanke min hukunci baki ji nawa ba. Buɗe ido nayi na ganni a gidan marayu. Daga labarina da na sani yar da ni aka yi wani ya tsinta ya kai ni can.
Bansan asalina ba, bansan me yasa baibarni nan na mutu ba. Akwai lokuta da dama da na yi roƙon in mutu da kaina saboda rayuwa ta yi min wuya.
Kowa na gani a titi kallonshi nake, kallonshi nake ko zan ga kamanni, in ka cika kallona zuciyata zata fara roƙo da fatan za ka gane ni ka ce kasan ‘yan uwana.
Banda kowa a duniya da zan kalla in ce jinina ne Ateefa. Karki yanke hukunci kan abinda baki sani ba…” (Babi na 28)

• Zulfa: ‘Ya ce a wurin Auwal da Ummi, kuma ƙanwa ce ga Dawud. Ita da Labeeb ‘ya’yan yaya da ƙani ne, kuma tun tana ƙarama suka shaƙu da juna. Kowa ya ɗauka soyayya suke yi da Labeeb ɗin. Hatta matar Labeeb ɗin sai da ya zamana tana tantama, dubi yadda marubuciyar ta bayyana hakan da ce, “Na rasa gane tsakaninku da Zulfa. Kuma a haka ka ce min ba sonta kake ba. Komai a kanta daban ka ke yi, kullum da safe da ita kake fara waya. Ba ka kwanciya baka yi mata bankwana ba… Text sai ku yi wa juna sau nawa…” (Babi na 42)

• Hajiya Beeba: Tsohuwar ‘yar bariki ce wacce ta ga jiya ta ga yau a harkar bariki. Ba ta da kunya kuma ba ta da tsoron Allah. Za ta iya yin komai domin ta cimma abinda ta sa a gabanta.

• Auwal: Mutumin kirki ne mai son iyalanshi da kuma kyautata musu. Ƙaddara ta haɗa shi da Hajiya Beeba wadda ta asirce ce shi har sai da ta ga ta raba shi da iyalanshi.

• Ummi: Asalin sunanta Aisha, mace ce mai matuƙar kula da addini tare da biyayya ga mijinta. Tana da tausayi tare da sanin yakamata.

• Mummy: ita ce Mahaifiyar su Labeeb. Macece da ta fito daga gidan kuɗi kuma ta auri mai kuɗi sannan ta ci gaba da kasuwancin ta bayan ta yi aure, wannan ya sa ba ta da lokacin ‘ya’yanta. Ba ta damu da tarbiyyar su ba, ganin ɗanta na fari watau Labeeb ya zamo wani abu shi ne a gabanta.

• Ateefa – Mace ce kyakkyawa sosai. An haife ta ta hanyar fyaɗe ne da aka yi wa mahaifiyarta. Hakan ya sa ta taso cikin tsangwama a gidansu. Tana da kishi, kishin da ko sujjada ta yi sai ta roƙi Allah da ya sauƙaƙa mata shi, (Babi na 32)

Kurakurai

Kamar komai na rayuwa, labarin Rayuwarmu shi ma yana ɗauke da wasu ‘yan kurakurai waɗanda duk da fitowarsu, hakan bai hana labarin fita yadda ya kamata ba kuma bai yi wa saƙon tasgaro ba.

Ga su kamar haka:

• An yi amfani da kalmomin da basu dace ba irin su:

Crap
Shit
Damn it
“Kutuma….”

Da dai sauran su.

• Wasu wuraren ana sa sunan Aseem madadin Anees. (Babi na 21/22)

• Ba a faɗaɗa bayani akan Ateefa ba kamar yadda aka faɗaɗa akan sauran taurarin.

• An yi wani bayani wanda ka iya koyawa masu karatu mummunar ɗabi’a, ‘Ganin unguwar shiru yasa ta kama ta dira da niyyar zama ta huta, sai dai ba zata manta video ɗin da suka kalla da Yaya Musty gab da rasuwarshi ba.
Ɗankunnenta ta cire ta lanƙwasa da wani irin bugun zuciya ta zira shi cikin lock ɗin sai dai ga mamakinta buɗe gidan ta yi lafiya ƙalau. Har ta shiga gabanta na faɗuwa. (Babi na 29)

• Abin zai matuƙar ba ka mamaki ace mace mai kyau irin na Ateefa wacce take cikin irin rayuwa kamar yadda aka bayyana ace kuma tana zuwa gidaje irin na su Labeeb domin samun wajen kwana kuma ace babu wata matsala da ta taɓa fuskabta?

• A ƙarshen babi na 36 an nuna Mamdud ya yi hatsari har an kai shi asibiti, kuma bisa yanayin bayanin da likitan ya yi har an duba shi kafin wani nashi ya zo. Wannan ya saɓa da irin yadda ake gudanar da aiyuka irin wannan a asibitocin ƙasar nan. Sannan likitan ya ce sun ga lambar labeeb a cikin wayar Mamdud amma ta yi lalacewar da ba za ta yi kira ba. Alhali kuma a babi na 42 an nuna irin yadda da ƙyar masu asibitin suka amshi Hajiya Beeba a emergency duba da cewa ba ahalinta ba ne suka kawota.

• A ƙalla marubuciyar ta ambaci sunan littafin (Rayuwarmu) sau 35 a cikin labarin a wurare daban-daban wanda hakan kamar wani yunƙuri ne na tursasa wa mai karatu tare da ƙoƙarin cusa mishi wata ma’ana madadin a barshi ya fahimta da kanshi.

• Anya kuwa Nurse ɗin da ta san aikinta yadda ya kamata za ta daka wa mara lafiyar da ke jinya irin na Hajiya Beeba tsawa ko da ba ta da kuɗin biyan magani? Balle fa har da cewa za ta sa securities su jefa ta cikin incinerator. Bana tunanin akwai wata Nurse da za ta nuna irin wannan halin ko in kula da rayuwar ɗan Adam matuƙar dai ta san aikinta. (Babi na 42) Ko da yake Hajiya Beeba ba mutuniyar kirki bace, hakan ba ya nufin za a yi amfani da duk wata hanya wajen ganin an yi maganinta. Musamman in ya zamana hanyar ta ci karo da abinda hankali ya yarda da shi.

Abin Yabawa

Rayuwarmu littafi ne da abubuwan yabawa da ke cikinsa ba za su ƙirgu ba kuma za a iya gabatar da shi ga kowanne irin makaranci saboda akwai darussa masu yawa a cikinsa. Babban darasin da cikin wannan labari shi ne, babu wani abu da ke da tabbas a cikin wannan rayuwar, kuma kowa da irin ƙalubalen da yake fuskanta a cikin tashi rayuwar.

Haka kuma Littafin ya dace da matasa, magidanta, ma’aurata da ma sauran al’umma baki ɗaya. Dalili kuwa shi ne, jigon labarin zai iya shiga kowane lungu da saƙo na rayuwar kowa.

Ko ba a faɗa ba, kun san cewa marubuciyar ta cancanci a yaba mata bisa irin ƙoƙarin da ta yi wajen ƙirƙiro wannan labari da kuma tsara shi ta yadda ya dace. Wani abu muhimmi da zan so in yabi marubuciyar musamman game da shi shi ne, irin yadda ta bayyana Labeeb a matsayin mai bin mata ba tare da yin batsa ba kamar wasu marubutan wannan zamani waɗanda da zarar ka ɗauki littafinsu za ka fara ganin batsa ta ko’ina. Wannan ya nuna kenan za a iya gina labari akan jigo na rayuwar aure ko makamantansu ba tare da an wuce gona da iri ba kamar yadda wasu marubutan ke yi.

Dubi dai yadda marubuciyar ta koyar da wani muhimmin darasi cikin harshe mai sauƙin fahimta, Ita da Mami suka haɗo ruwa suka ɗauko, Mami ta auna Arif da farin zawwatin da ta yanka ta fita ta ba wa Dawud don a haƙa kabari, ta dawo ɗakin. (Babi na 36)

Da kuma yadda ta isar da wani saƙo shi ma mai muhimmanci da cewa,

ya saki hannunta ya zaro mukullan gidan, ya saka da bismillah yana buɗewa.
Hannunta ya kama yana faɗin,
“Bismillahi walajna wa bismillahi kharajna wa alallahi rabbina tawakkalna.” (Babi na 40)

Suna idarwa ya juya ya ɗora hannunshi na dama a saman kanta yana karanta,
“Allahumma inni as’aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha alaihi… Wa’auzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi.” (Babi na 40)

Wani ƙarin yabo da ya zama dole a yi wa wannan littafi shi ne irin yadda Labarin ya bankaɗo mummunan halin da marayu ke ciki a gidan rainonsu, babbar matsala daga ciki kuwa ita ce jahilcin ilimin addini. Kenan wannan ya zama izna ga masu ido a wannan fanni domin su tashi tsaye wajen ganin sun kawo canji akan hakan.

Abu na ƙarshe da zan ƙara jinjinawa marubuciyar akai shi ne, irin yadda ta bayyana matsalolin da rashin samun kular iyaye ke haifarwa ga ‘ya’yansu. Lallai wannan darasi ne da ke da matuƙar amfani, musamman in muka yi duba da yadda wannan ɗabi’a ke ƙara yawaita a cikin al’ummarmu.
Kuma irin waɗannan darussa da marubuciyar ke haskawa ta tsaftataccen harshe a cikin litattafanta ya sa ta zama ɗaya daga cikin shahararrun marubutan Hausa da ake alfahari da su a wannan zamani.

Shawarwari

A har kullum shi marubuci wani babban jigo ne a cikin al’umma wanda dubunnan mutane ke kallo su yi koyi da shi ko abinda ya rubuta. Ina ba wa marubuciyar shawara da ta ci gaba da yin rubuce-rubuce irin wannan domin al’ummar mu su amfana daga tarin ilimi da kuma fasahar da take da ita. Kuma ina na ta shawarar da ta ci gaba da zage damtse wajen yin bincike sosai domin gano matsalolin rayuwar mutanenmu na birni da ƙauye tana rubutu akansu domin wayar da kan al’umma.

Kammalawa

Bana tunanin akwai wani mahaluƙi da zai karanta littafin Rayuwarmu ya ce bai amfana da tarin darussan rayuwa da ke cikin labarin ba. Domin saƙonnin da ke cikin littafin sun fi ƙarfin a yasar da su gefe, kuma suna da ƙarfin tasirin da za su iya canza wa mutum tunaninsa game da wannan rayuwa da muke ciki ta duniya.

Baya ga haka, littafin ya ƙunshi duk abinda mai karatu zai iya tsammani da ma wanda bai taɓa tsammani ba. Za ka ci dariya, za ka shiga cikin shauƙi, zuciyarka za ta yi rawa kuma za ka wa’azantu matuƙa da wannan labari. Akwai wuraren da ni kaina sai da na ɗan dakata na yi wa marubuciyar tafi tukunna daga baya na ci gaba da karatun. A wasu wuraren kuma ba za ka san lokacin da za ka riƙe baki ba saboda tsananin mamakin abinda ke faruwa a cikin labarin Waɗannan da ma wasu abubuwa da dama waɗanda ban ambata ba su ne suka sa kai tsaye zan iya cewa ‘Kada ka sake ka wuce wannan labari ba tare da ka karanta shi ba.’

Kuna iya karanta littafin Rayuwarmu a Bakandamiya Hikaya.

Manazarta

Ɗangambo, A. (1990) “Gadon Feɗe Adabin Hausa (Ba a Buga ba).

Ɗangambo, A. (1984) Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph

Junaidu, I. da Yar’aduwa, T. M. (2007) Harshe da Adabin Hausa a Sauƙaƙe don Manyan Makarantun Sakandare, Ibadan: Spectrum Books Limited

Junaidu, I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002). Harshen da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Ibadan: Spectrum Books Limited

Sani, M.A.Z., Muhammad A., da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. Ibadan: University Press Plc

Umar, M.B. (1984) Dangantakar Adabin Baka da Al’adun Gargajiya na Hausa. Kano: Triumph Publishing Company

Yahaya, I. Y. (1981) “Adabin Gargajiya a Makarantun Sakandare. Lacca da ya gabatar a Makarantar ‘Yammata ta Dala

Yahaya, I. Y. da Ɗangambo, A. (1986) Jagoran Nazarin Hausa. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company Limited

Yahaya, I. Y., Zaria M. S., Gusau M.S., da ‘Yar Aduwa T.M. (1992) Darussan Hausa don Manyan Makarantun Sakandire 1. Ibadan: University Press Plc

Zarruƙ, R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. Ibadan: University Press Plc

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page