Skip to content

Sharhin littafin ‘Abdulkadir’ na Lubna Sufyan

Sharhin littafin Abdulkadir

Sunan Littafi: Abdulƙadir

Marubuciya: Lubna Sufyan

Inda aka Buga Littafi: Bakandamiya Hikaya (Online)

Shekarar Bugu: 2022

Mai Sharhi: Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)

Manufar Sharhi: Bunƙasa Harshen Hausa da ciyar da adabi gaba

Dangane da marubuciyar

An haifi Lubna Sufyan ne a ƙaramar hukumar Ingawa da ke birnin Katsina. Fitacciyar marubuciyar ta fara karatun addini tun tana ƙarama kuma ta yi karatunta na Firamare ne a garin Katsina, daga baya ta koma garin Kano inda ta yi karatun sakandire har ta gama. Bayan ta gama ne sai ta koma Katsina in da ta yi karatun diploma a ɓangaren zanen taswirar gidaje. Daga baya kuma ta ci gaba da karatu a mataki na gaba, wato Babbar Diploma, Higher National Diploma (HND) a garin Kaduna.

Marubuciyar ta fara rubuce-rubuce ne tun tana makaranta, kuma ta kasance ɗaya daga cikin fitattun marubutan online na wannan zamani. Zuwa yanzu ta rubuta litattafai sama da guda goma sha ɗaya. Wasu daga cikin litattafan da ta rubuta sun haɗa da; Rai Da Ƙaddara, Wata Bakwai, Akan So, Rayuwar Mu, Abdulƙadir, Mijin Nobel, Martabar Mu, Alƙalamin Ƙaddara da sauransu.

Har’ilayau, marubuciyar ta kasance mai son girke-girke ce sosai. Kuma baya ga rubutu, marubuciyar tana yin fassara daga harshen Turanci zuwa Hausa, wannan aiki na fassara ne ma ya zama sanadin yin aikinta da kamfanoni da ƙungiyoyin gwagwarmaya masu zaman kansu a lokuta daban-daban a kuma kan batutuwa iri daban-daban kamar su Give North Education, Women In Arewa, Women In Finance da dai sauransu. Sannan kuma, marubuciyar ta sha yin aiki da makarantun Islamiyya da bloggers wajen fassara musu aiyukansu. Haka kuma ƙwararra ce wajen haɗa ɗuwatsun ƙawa na adon mata. A taƙaice dai, duk in da aikin rubutu yake, to a nan marubuciyar ta fi ƙarfi.

Marubuciyar kuma na ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar marubuta na Fikra Writers Association, kuma tana garin Katsina ne da zama a yanzu haka.

Labarin a Taƙaice

Alhaji Ahmad Bugaje yana da matan aure har guda huɗu. Matar shi ta farko ita ce Hajiya Safiyya wadda ake kira da Hajja. Ta haifi yara takwas tare da shi, su ne Muhsin, Yazid, Khadija, Mubarak, Abdulƙadir, Zahra, Nazir da kuma Zainab. Matar shi ta biyu kuma ita ce Hajiya Saratu wadda ake kira da Mama. Tana da yara biyar da Alhaji Ahmad dukkan su maza. Ahmad (wanda ake kira da Babangida), Yasir da Yazid waɗanda suka kasance ‘yan biyu, sai kuma Salim da Khalid.

Hajiya Sakina ita ce matar shi ta uku da yaransu ke kira Mami, wadda kuma ita kaɗai ce ya aura a bazawara, don shekararta ɗaya da wata uku da yin aure Allah ya yi wa mijinta rasuwa bayan gajeruwar rashin lafiya da ya yi fama da ita. Ya kuma rasu a lokacin ya barta da cikin wata shida. Ta haifi yarinyarta mace, bayan ta yayeta ne suka haɗu da Alhaji Ahmad Bugaje. Bai aureta ba sai da ya yi mata alƙawarin riƙe mata yarinyar ta.  Bayan Waheedah, ta haifi yara uku da shi, su ne, Sa’adatu (wadda ake kira da Amatullah), Aminu da kuma Habib. Hajiya Halima kuwa da yaran duka ke kira Anty, ita ce mata ta huɗu kuma amarya a gidan Alhaji Ahmad, ‘yar tsohon Wazirin Kano ce da Allah ya yi wa rasuwa ya aura. A cikin matan shi ita kaɗai ce take aikin gwamnati, domin kuwa da aikinta ya aure ta. Allah ya azurta su da yara shida, saboda ta fi sauran matan shi haihuwa gab da gab, kusan abinda akan kira da kwanika ko gwarne. Yaran su ne, Nusaiba, Nabila, Kabiru, Adnan da Baraka.

Duk da wannan yawa nasu, hakan bai sa yaran kansu ya rabu ba, domin suna son junansu kuma suna girmama na gaba da su. Sannan suna da haɗin kai tare da zumunci da kuma damuwa da junansu. Domin ko ƙurjewa wani ya yi aka ce ga shi can kwance, to yanzu za ka gansu ɗuuu duk sun yo kanshi. Wannan dalili ne ya sa kusan ko’ina suka je nan da nan ake gane su. Hatta Waheedah da ba Alhaji Ahmad ya haifeta ba haka suke mata, saboda ba sa nuna mata wani bambanci, komai a tare suke yi.

Abdulƙadir tun yana da ƙarancin shekaru yake sha’awar aikin soja, kuma har ya girma yana da wannan ra’ayi. Yana da zafi sosai, kuma ba ya ɗaukar raini balle ɗaga ƙafa. Saboda takurawa ƙannensa da yake yi ne a gida ma har suka sa mishi suna ‘Commander’ a ɓoye. Yayan shi Yassar ne kaɗai yake ɗan saurarawa a duk cikin gidan saboda sun fi jituwa.

Waheedah tana da sanyin rai da sauƙin hali, ga haƙuri da ladabi da biyayya. Wannan yasa kowa ke sonta. Tana da wata ƙawa da ke maƙwabtaka da su mai suna Nuriyya. Duk da cewa gidan su Nuriyya talakawa ne, hakan bai sa Waheedah ta ƙyamace ta ba. Shaƙuwar da suka yi ne ma ya sa har ɗinki da sauran abubuwa na yau da kullum akan yi musu tare. Domin har ce musu ake yi ‘yan biyu. Babban abin da ya raba su shi ne, Nuriyya tana da son abin duniya.

Yau da gobe, duk da baƙin hali irin na Abdulƙadir da takura da dukan da yake yi wa yaran gidan da zarar sun yi laifi ko wani ɗan kuskure bai hana zuciyar Waheedah kamuwa da ƙaunarsa ba. Wannan kuwa ya faru ne tun tana da ƙarancin shekaru. Sai dai ta ɓoye soyayyar a zuciyarta domin da fari ita kanta bata san cewa abinda take ji a ranta sunan shi so ba saboda ƙarancin shekaru. Shi kuwa Abdulƙadir sam ba shi da burin auren mace irin Waheedah, wannan yasa ko sau ɗaya bai taɓa kawota a ranshi ba. Amma bayan ya zo bikin ƙannensa, a wannan lokaci sai ya ji zuciyarsa ta fara bugawa Nuriyya, domin tana da siffa irin ta macen da yake so, sai dai ya ƙi bayyana mata saboda a lokacin yana tsaka da karɓar horo a makarantar Sojoji ta NDA da ke Kaduna, kuma ya ƙudurce a ranshi cewa sai ya kammala tukunna ko da zai sa ranshi a wani al’amari da ya shafi aure.

A gefe kuma, Yazid ya kamu da son Waheedah sosai, sai dai shi ma bai faɗa mata ba saboda yana tunanin ta yi yarinya da yawa. Ita kuma Nuriyya, ta samu wani saurayi mai suna Anas wanda yake sonta tsakaninsa da Allah, sai dai ita kuma bata son shi, tana dai kula shi ne kawai saboda yana kashe mata kuɗi. A ƙarshe dai Mahaifinta ya aura mata shi duk da bata so ba. Hakan ya sa Abdulƙadir ya ji ba daɗi sosai.

Da Yassar ya gane cewa Yazid na son Waheedah, sai ya yi marmaza ya sanar mishi da cewa ai suna soyayya da Abdulƙadir. Shi kuma saboda ba zai iya haɗa soyayya da ƙaninsa ba sai ya ja baya, a ƙarshe ma ya yi nesa da garin. Abdulƙadir kuwa, da dai ya ji cewa ai Waheedah tana son shi, sai ya nemi ji daga bakin ta. Ko da ya samu tabbaci, sai nan take ya samu mahaifinsa da maganar aure.

Kowa na gidan sai da ya jinjina maganar auren, amma hakanan aka yi tunda sun nuna suna so. Bayan an yi auren da wasu ‘yan shekaru ne Nuriyya ta kaso nata auren ta fito, ta kuma zo ta aure wa babbar ƙawarta miji, wato Waheedah. 

Jigo

Na san ko daga ɗan wannan tsakure mai karatu zai iya fahimtar cewa babban jigon wannan labari shi ne soyayya. Domin an zuba gagarumar soyayya a cikin wannan littafi ta yadda mai karatu shi da kan shi zai ji ya faɗa soyayyar jaruman cikin wannan labari. Sannan duba da irin yadda soyayyar da kowa daga cikin jaruman ke yi wa juna ba tare da sanin juna ba zai nuna maka cewa ba ƙaramin ƙoƙari marubuciyar ta yi ba wajen tsara labarin. Kusan tun a farko-farkon labarin aka nuna mana yadda Waheedah ta kamu da son Abdulƙadir amma bata faɗa mishi ba. Kamar yadda a babi na biyar marubuciyar ta ce: “Jikinta gaba ɗaya a sanyaye take jin shi, banda yanayin fuskar Abdulƙadir ɗin lokacin da ya riƙo ta babu abinda take hasasowa, so take ta ji ta a kwance a ɗaki, ta janyo bargo ta rufe jikinta gaba ɗaya har kanta, ba za ta ƙi bacci ya ɗauke ta cike da tunanin shi ba, don a ɗaki ne kawai take da tabbacin babu wanda zai uzzura mata balle ya katse mata tunanin ta.

Shi kuma Abdulƙadir zuciyarsa ta fara bugawa Nuriyya wacce ƙawar Waheedah ce sai dai bai faɗa mata ba. Dubi yadda marubuciyar da bada misalin yadda yake ji game da Nuriyyar a babi na takwas: ” idanuwan shi ya fara saukewa kan fuskarta, kafin ya ƙanƙance su yana ƙare mata kallo, wani abu yake ji yana dokawa cikin kunnuwan shi daya rasa daga inda yake jin sautinshi, don ba shi da alaƙa ko kaɗan da kiɗan da yake tashi a wajen.”

A gefe guda kuma ita Nuriyya tana kishin son da Waheedah ke yi wa Abdulƙadir kuma tana fatan da ma ace ita za ta same shi, wannan ya sa ta yi ta bita da ƙullin ganin ta samu kusanci da shi ta hanyar yin shisshigi a cikin al’amuransa kamar yadda marubuciyar ta bayyana a babi na takwas da cewa: “Binshi take tana kallon hannun shi da yake riƙe da nata, zuciyarta kamar zata fito waje take jinta. Su duka biyun basu kula da Nuriyya da take bin bayansu tanajin kamar zuciyarta zata faɗo, ƙarshen abinda zai faru shi ne Waheedah ta samu abinda take so, fuskar Abdulƙadir ɗin take kallo ko zata ga alamun so, kamar yadda yake bayyane a fuskar Waheedah, amma bata ga komai ba, asalima kamar ranshi a ɓace yake. Ita dai komai zai faru kar Waheedah ta taɓa samun Abdulƙadir ɗin. Tana jin za ta yi komai don kar hakan ya faru.”

Shi kuma Yazid wanda yake Yaya ne a wajen Abdulƙadir ya kamu da son Waheedah ba tare da ya sanar mata ba. Domin shi ma dai har’ilayau marubuciyar ta bayyana yanayin da yake ji game da ita a babi na takwas inda take cewa:” tun ɗazun ya kula da yanayin fuskarta kafin su taho, bai san lokacin da abinda yake ji ya fara ba, kawai ta gitta ta gaban shi ya tsinci zuciyar shi da doka mata. Wannan yasa duk wanda ya karanta labarin zai so jin yadda wannan rikicin soyayya zai wakana, kuma waye zai yi nasara waye kuma zai faɗi.

To sai dai kuma, bayan wannan babban jigo da na yi bayani. An yi amfani da ƙananun jigogi masu tarin yawa waɗanda su ne suka haɗu suka ba wa labarin goyon baya ta hanyar koyar da darussa da dama a cikin wannan labari. Ga wasu daga cikin su kamar haka:

• A babi na 15 sakin layi na ƙarshe, marubuciyar ta koyar da mu darasin yin nazari mai zurfi kafin ƙaddamar da maganar aure ta hanyar kawo mana zance zucin da Abba yake yi dangane da maganar auren Waheedah da Abdulƙadir da cewa: “Sosai yake jinjina al’amarin auren Waheedah da Abdulƙadir, shi kam zai kira Waheedah ya tabbatar daga wajenta kafin ya yanke kowanne hukunci, don jikin shi na mishi wani iri akan auren, sanyin Waheedah ya yi yawa, zafin Abdulƙadir ko su da suka haife shi addu’a suke binshi da ita” wannan ke.

• Haka kuma a babin dai na 15 an nuna mana rashin dacewar yanke hukunci akan abin da mutum ke zato har sai ya tabbatar saboda gujewa abinda zai iya faruwa a sakamakon hakan. Kamar yadda marubuciyar ta bayyana da cewa “Yassar ya sake kira a karo na babu adadi, yana jinjina abinda yake gani a fuskar ƙanin nashi, har ranshi, duk tsawon shekarun nan ya ɗauka soyayya suke da Waheedah ɗin, yana kuma da tabbacin ba shi kaɗai bane yake zaton hakan. Wani zafi ya ji ƙirjinshi na yi, ya hana Yazid furta mata yana sonta saboda a tunanin shi Abdulƙadir ɗin na son ta, yana kuma da tabbacin idan shi baya sonta ita tana son shi, don yadda take tambayarshi akan Abdulƙadir ɗin kawai ya tabbatar mishi da haka daga nata ɓangaren.” Wannan kuwa ya faru ne bayan Yassar ya shiga nadamar faɗa wa Abdulƙadir cewa ya gano suna soyayya ne da Waheedah, alhalin kuwa shi a wannan lokacin ba sonta yake yi ba.

• Wani babban darasi kuma da aka koyar a cikin labarin shi ne ‘barin halas ko don kunya’, domin mun ga yadda Abba ya rufe Abdulƙadir da faɗa a lokacin da ya ce misi Nuriyya yake so ya aura a babi na 21, inda ya ce, “Ban taɓa yarda da baka da hankali ba sai yau Abdulƙadir, wallahi yau ka tabbatar min da cewar baka da hanlali. Nuriyya kake magana, ƙawar Waheedah, Nuriyya aminiyar matarka, ita ka zo kana faɗa min kana so ka aura.”

Haka kuma, Hajja, wato mahaifiyar Abdulƙadir ita ma ta ƙara ƙarfafa wannan darasi a babi na 22 inda ta ce, “Ita ma Nuriyyar don ubanta idan tana da kunya ai ko mutuwa Waheedah ta yi idan ka zo mata da wannan maganar zata dubi amintakar da ke tsakanin su ta ƙi amincewa. Amma na ga alama yadda ka sa ƙafa ka shure duk wata kunya da ake halittar ɗan Adam da ita haka ita ma ta yi fatali da tata.” da kuma Yassar inda shi ma ya ce, “”Mahaukaci ne kai wai? Don ubanka allurar sojojin kai ka miƙa musu suka caka maka ita? Addini bai haramta maka auren Nuriyya ba, amma al’ada ta haramta maka shi, kunya ta haramta maka, ko mutuwa Waheedah ta yi ka nuna kana son auren ta, akwai mutane da yawa da za su ga rashin kyautawar haka…” Duk a cikin babi na 22

• An kuma nusar da mu yadda ya kamata mu zauna da mutane, musamman a irin halin da muke ciki yau, kamar yadda marubuciyar ta ce, ‘Amma rayuwar haka take tafiya, wanda ya fi kusa da kai shi ya fi kowa samun damar cutar ka, yanzun mutanen kirki ba su ba ne wanda za su ɗauki abu su baka, mutanen kirki su ne wanda za ku yi tarayya tare da su ba su cutar da kai ba. Babi na 27

• “Babu inda haƙuri ya tashi a banza Waheedah, kar wani ya taɓa sa ki ji haƙurinki ya yi yawa. Karki bari halayen kowa ya canza naki masu kyau. Da yawan lokaci rashin kirkin mutane na gurɓata na masu kirki….karki bari hakan ya faru da ke kin ji?” babi na 30. Wannan shi ke koyar da mu muhimmancin haƙuri da kuma dagewa akan halaye nagartattu.

• ‘Bai san ko kaɗan cikin halayyarta ba lokacin da ya amince ma aurenta, halayenta sun fito mishi ne bayan ya aureta, a ƙasa da sati ɗaya bayan ya aureta ya fara kula da su, sun sake fito mishi bayan ta tare a cikin gidan shi, zama ya haɗa su, tana saka shi fahimtar dalilin da yasa mutane ke cewa zaka iya shafe shekaru da mutum ba ka san ko da kashi ashirin cikin halayen shi ba, saboda akwai ɓoyayyayun halayen da ba mutum bane yake ɓoye su don kar a sani, basa fitowa ne sai zama na a kwana a tashi ƙarƙashin inuwa ɗaya ya kama suke bayyana. (Babi na 33) Wannan ya koyar da mu muhimmancin yin bincike da ƙoƙarin fahimtar halin mutum tun kafin a yi aure.

•  Sannan kuma, an nusar da mu, musamman mata da kada su dubi kuɗi ko wadatar wanda za su aura, amma su kasance masu wadatar zuci, kamar yadda marubuciyar ta bayyana a babi na 33 da cewa, ‘a wasu lokutan kuma idan yarinya bata tashi cikin wadata ba, bata kuma da wadatar zuciya sai ta dora ginshiƙin aurenta da samun farin ciki akan auren mai kuɗi, wasu kuma hange-gange shi ne yake halakar da su, ki ga mace cikin rufin asiri, kin ganta daga sama da mijinta suna cin me kyau su sha me kyau, sai wannan ƙyallin ya haska miki shi, sai ki ga kamar ta samu duk wani abu da shi ne burinki a zaman aure.’

Bayan waɗannan akwai ƙananan jigogi da dama da marubuciyar ta taɓo a cikin wannan littafi irin su amintar da ke tsakanin ‘yan uwa, ƙawance, zaman mace da mijinta, muhimmancin iya girki da aikace-aikacen gida ga mace, biyayya ga iyaye da kuma illar son abin duniya, musamman ga mace. 

Salo da Sarrafa Harshe

Marubuciyar ta baje basira sosai wajen bada labarin wannan littafi. Domin ta yi amfani da salo iri daban-daban kuma duk masu burgewa wajen isar da saƙon labarin a sauƙaƙe.

Misali:

• Salon Tafiyar Kura: Marubuciyar ta yi amfani da salon tafiyar kura ne a cikin wannan littafi, inda ta fara bada labarin daga tsakiya sannan ta ci gaba da warware shi a hankali a hankali ta hanyar komawa baya ta kawo wani batu sannan ta dawo ta ci gaba daga baya kuma ta sake komawa ta kwance wani a baya kafin ta kuma dawowa ta ci gaba. Hakan zai sa mai karatu ya dinga fahimtar batun da ake kai ko wanda za a shiga ba tare da ya sha wahala ba.

• Salo Mai Armashi: An yi amfani da salo mai jan hankali da armashi sosai da sanya nishaɗi ga mai karatu ta hanyar kawo misalai masu jan hankali, motsa zuciya da kuma sa mai karatu dariya da nishaɗi a wasu lokutan.

• Salon Koyarwa: Babban salon da aka yi amfani da shi a cikin wannan littafi shi ne salon koyarwa, an yi amfani da wannan salo sosai ta yadda a kusan kowane shafi sai ka tarar da ana  koyar da darussa da dama da suka shafi zaman duniya, zaman ma’aurata da yadda za a zauna da ahali cikin harshe mai sauƙi yadda mai karatu zai fahimta ba tare da wata wahala ba.

• Sarrafa Harshe: Har ila yau an yi amfani da kalmomi masu tsima jiki, sa tausayi, kwantar da hankali da kuma gyaran tunani duk a cikin wannan littafi. Wani lokaci ma sai mai karatu ya ji kamar zaunar da shi aka yi ana mishi nasiha game yadda lamarin ke faruwa. Ko da yake an samu ƙarancin karin magana, an samu zambo da habaici da dai sauransu a cikin wannan littafi.

Bugu da ƙari marubuciyar ta yi amfani da sassuƙar Hausa wajen rubuta labarin ta yadda kowa, zai fahimta. Sai dai an samu kalmomin turanci masu ɗan dama cikin labarin waɗanda yawan da suka yi ka iya jawo naƙasu ga bunƙasar Adabin Hausa a tsakanin makaranta.

Zubi da Tsari

Marubuciyar ta yi wa wannan littafi shimfiɗa mai kyau tun daga farkonsa har zuwa ƙarshe. Da fari dai ta tsara wannan littafi ne a zubin babi-babi, daga babi na farko zuwa na 35. Sannan ya samu tsari mai kyau, domin tun daga farkon labarin aka nuna mana matsalar da ta afku a tsakanin ma’aurata kuma taurarin labarin, wato Abdulƙadir da Waheedah. Haka kuma an fara nuna mana halin wasu daga cikin taurarin labarin tun a babi na farko kamar su Waheedah, Abdulƙadir, Nuriyya, Yassar da sauransu.

Wani abin ƙarin armashi da burgewa shi ne, tun daga nan, duk bayanan da suka biyo baya ƙara fayyace labarin suke yi, kama daga wanda ake kan yi har zuwa wanda ake komawa baya a warware. Wato dai an samu zagi a tsakanin jumloli da babin labarin. Domin an fara ne da bayyana mana halin da Waheedah take ciki na rashin lafiya da kuma irin ƙeƙasashshen halin mijinta wanda shi ne sanadiyar kwanciyarta a asibiti da kuma irin roƙon da take mishi na ya ‘sauƙaƙe mata auren shi’ domin ta huta.  Sannan a gefe an hasko mana irin yadda ita kuma Nuriyya ko a jikinta bata damu da irin halin da Waheedah ke ciki ba duk kuwa da cewa ita ce babbar ƙawarta kuma gashi ta aure mata miji.

Sannan littafin ya ci sunan shi ‘ABDULƘADIR’, saboda tun daga farkon littafin babu inda ba za ka taras da sunan shi ba. Duba da cewa labarin kacokan akan wuyar shi ya rataya, lallai wannan ba zai zamo a fake ba. Sannan ita ke musu girki da wankin kayan su ko ba ranar girkinta ba ne, amma daga ranar da ta ƙi yin wanki sai ga shi Nuriyya ta je ta ɓata wa Abdulƙadir kaya wanda hakan ya fara hasaso mana yiwuwar rabuwar su, domin mun jiyo shi ya fara yi mata faɗa da cewa, “Aikin ki kenan, kullum baki san abu ba, ko yaushe uzurinki baki sani ba. Hankalin ki bai baki ba’a haɗe gaba ɗaya kaya wajen wanki ba? Idan kin haɗa wandon nan da sauran kaya, me yasa zaki haɗa farare da masu kala? Ke mahaukaciya ce?” (32)

Baɗoki na gaske: “… Aure ko? Auren cin amana, a yi lafiya Abdulƙadir, wallahi ba baki na yi maka ba, alhakin Waheedah ba zai barku ba.” Ai kuwa alhakin bai bar su ba, domin a ƙarshe da saki uku Nuriyya ta koma gida. (Babi na 22)

Baɗoki na Giri: “”Ban shigo da nufin yin faɗa da ke ba, har kuɗin hidimar gida na tura miki ɗazun… Kin ga Azumi ya kusa, saura kwanaki kaɗan, ana yafewa juna kafin azumi, ba ma kyau faɗa kafin azumi. Bazan iya sakin ki ba Waheedah… Ko meye nai miki me zafi haka haƙuri za ki yi ki dawo. In ke za ki iya barina ni bazan iya barinki ba wallahi… Bazan iya ba.” (Babi na 25)

Ɗarsau na Murna: ‘Kai Abba ya jinjina yana kallon yaran nashi, yanajin ƙaunar su fal cikin ranshi, yana kuma mamaki har lokacin yadda ƙaddarar rayuwa ta kawo su inda suke yanzun. Cikin ranshi yake wa Allah godiya yana ƙarawa da musu fatan zaman lafiya da rayuwar aure mai inganci.’ (Babi na 17)

Ɗarsau na Tsoro:  An yi amfani da wannan dabara sosai a cikin wannan littafi ta yadda a koyaushe mai karatu cikin fargaba da zumuɗin jin abinda zai faru yake. Misali: “Aurenka zaka sauƙaƙe min!” (Babi na 01) haka kuma an yi amfani da wannan dabara a kusan kowane babi da ke cikin wannan littafi.

Ɗarsau na Al’ajabi: ‘Yassar ya sake kira a karo na babu adadi, yana jinjina abinda yake gani a fuskar ƙanin nashi, har ranshi, duk tsawon shekarun nan ya ɗauka soyayya suke da Waheedah ɗin, yana kuma da tabbacin ba shi kaɗai bane yake zaton hakan. Wani zafi ya ji ƙirjinshi na yi, ya hana Yazid furta mata yana sonta saboda a tunanin shi Abdulƙadir ɗin na son ta, yana kuma da tabbacin idan shi baya sonta ita tana son shi, don yadda take tambayarshi akan Abdulƙadir ɗin kawai ya tabbatar mishi da haka daga nata ɓangaren. (Babi na 15)

Ɗarsau na Tausayi: “Ka sauƙaƙe min aurenka, don Allah ka sauƙaƙe min aurenka.”

Take faɗi tana kamo hannun shi, da sauri ya riƙe hannun nata yana dumtsewa, yana jin siraran yatsunta da suke barazanar ɓallewa a kowane lokaci cikin nashi, su suka sa shi sassauta riƙon da ya yi mata. “Anty ku ce ya sauƙaƙe min, don Allah ku ce Sadauki ya sake ni!” “Kun ji, ku ce kar ya fita daga ɗakin nan bai raba ni da auren shi ba…” (Babi na 02)

Ɗarsau na Mamaki: Akance sai halayya ta zo ɗaya ake zama wuri ɗaya ma har a ƙulla alaƙa, Abba na ganin ƙaryar zancen a abinda Abdulƙadir yake faɗa mishi, don ta kowacce fuska Abdulƙadir bai dace da Waheedah ba, halayyarsu da komai nasu ya banbanta, bai kuma hango ta yadda akai suka fara soyayyar ba. (Babi na 15)

Hoton Zuci: Sannan an yi amfani da dabarar saka hoton zuci sosai a cikin wannan littafi ta yadda mai karatu zai ji kamar yana wurin abin ke faruwa. Misali, “..

Nuriyya kettle ta ɗauka da nufin ɗora ruwan zafi su sha shayi, shaf ta manta da man da ya zube a kitchen ɗin, ga kuma ruwan da ta zubar don ta cika kettle ɗin, ta kuma taka shi tana nufar inda socket zai yi, ta taka man tana wata irin zamewa, sai da ta yi sama, kettle ɗin ma ta yi sama tukunna su duka suka sauka kusan a tare, kettle ɗin a gefe da ruwan ciki da ya mungule gaba ɗayan shi, ita kuma akan mazaunanta ta yi warwas a ƙasa. Ta ɗauki wasu daƙiƙai tana sauke numfashin wahala kafin ta ja ƙafafuwanta ta miƙe. (Babi na 31)

Tauraron Labari

Babu ko tantama na san cewa ko daga jin sunan wannan littafi mai karatu zai iya fahimtar cewa babban tauraron wannan labari shi ne Abdulƙadir A. Bugaje. Domin bayan sunan shi da aka yi amfani da shi a matsayin sunan littafin, gaba ɗaya matsalolin littafin in aka kasa su goma to tara da rabi shi suka yi wa zobe. Da fari dai kowa ya san irin halin shi na baƙar zuciya da tsaurin ido, amma a iya cewa matarsa Waheedah ta fi kowa ganin irin matsalolinsa, tun da har ya iya auran babbar ƙawarta ba tare da ya faɗa mata ba, kuma da ta zo gidan ta baje shaƙiyanci babi-babi yana kallo amma bai damu ba har sai lokacin da al’amari yayi tsami a tskananinsa da Waheedah.

Halayen Taurarin Labari

• Abdulƙadir baƙi ne dogo mai ƙananan idanuwa. ‘Yan gidan Bugaje suna da tsayi babu laifi daga mazan har matan, don gajerun cikin gidan ba su wuce su huɗu ba, amma tsayin da Abdulƙadir yake da shi har mamaki yake basu, duk manyan yayyen shi tsayinsu ɗaya da shi. Nabbe burinsa shi ne zama soja. Tun yana da ƙarancin shekaru yakan ce shi Soja zai zama, tun suna ɗaukar abin ƙuruciya har ya fara tasawa yana cigaba da jaddada musu ƙaunar shi da aikin Soja, ko a hanya yagan su sai ya je sun gaisa. Baya son raini ko kaɗan, kuma yana da saurin hannu

• Waheedah siririya ce fara mai ɗan matsakaicin tsayi. tana da kyau da in za ka tsaya ka kalleta sosai za ka ga bashi da alaƙa da hasken fatarta, sannan komai nata da sanyi take yin shi, gashi babu wanda zai ce ya taɓa ganin ɓacin ranta balle kuma faɗa. Tana da haƙuri sosai, wannan yasa kowa ke ganin cewa basu dace da Abdulƙadir ba.

• Nuriyya na da faɗa sosai, ba za ka ɗaga mata ɗan yatsa ka sauke ba tare da ta lanƙwasa shi ba, ba fara bace, za ka iya saka hasken fatarta a mutanen da ake ma laƙabi da masu kalar cakuleti. Kusan kyawun mahaifiyarta ta biyo, don kowane irin kaya Nuriyya ta sa sai ka ga sun amshi jikinta, tana da matsakaicin tsayin da mutane da yawa za su iya kiranta gajera, amma a dire take, tun da ‘yan shekarun tan nan za ka fahimci Allah ya halicci mace a wajen, cikar lokaci kawai take jira ta ƙarasa fitowa. Gashi fuskar nan tana ɗaukar kwalliyar da ke ƙara fito da ita, da wahala ka kalli Nuriyya ba ka sake kallonta ba.

• Yasaar shi ne wanda ya fi kowa kusanci da Abdulƙadir a duk cikin ‘yan uwansa. Yana da haƙuri sosai kuma yana son ɗan uwan nasa, sannan shi kaɗai ne yake iya faɗa wa Abdulƙadir magana ya saurare shi.

• Alhaji Ahmad Bugaje mutum ne tsayayye, ba zaka rasa rikici a gidanka ba ko da mata ɗaya ka ajiye, ballantana har huɗu, sai dai suna ƙoƙarin duk wani rikici da zai faru a tsakanin su ba ya ƙarasawa kunnuwan shi sai dole. Duk abinsu suna shakkar ɓacin ran shi, shi ya sa aka samu wadataccen haɗin kai a tsakanin yaran, don suna son junansu sosai.

• Hajiya Safiyya na da son girma tamkar ita ta yanke wa ƙasa cibiya, yawan faɗa, ɗaukar zuga da son yaranta da kuma matsananciyar rowa.

• Hajiya Halima jinin sarauta ce, hakan yasa tana da izza, ko kaɗan bata shiga harkar kowa, kuma ba ta ɗaukar raini ko ya yake, za ka iya cewa tana da faɗa in har ka shiga gonarta. Sannan tana da matuƙar kirki da kyauta irin ta saraki.

• Sakina macece mai yawan haƙuri da kau da kai, tana da sanyin hali da ko surutu bai dameta ba.

• Halayen Hajiya Saratu kuwa, tana da fuska biyu, a gabanka ba ka da mai ƙaunarka kamar ta, a bayan idonka kuwa ba ka da maƙiyi kamarta, tana da gulma da haɗin husuma, ga jarabtar cin bashi da Allah ya ɗora mata.

Kurakurai da Gyararraki

An samu kuskure babba guda ɗaya a cikin wannan littafi. Kuskuren kuwa shi ne, a farko-farkon littafin an bayyana irin yadda abin da ya faru a tsakanin Waheedah da Abdulƙadir  ya jawo rashin jituwa a tsakanin shi da sauran ‘yan uwansa kuma har littafin ya ƙare ba a nuna sun shirya ko ba su shirya ba. Abin da kawai aka nuna shi ne ya saki Nuriyya kuma sun koma kamar yadda suke da Waheedah da kuma hajja. Wannan shi ne babban kuskuren da aka yi, sai kuma kalmomin turanci da aka ɗan yi amfani da su. Duk da dai su ba wasu masu yawa aka yi amfani da su ba.

Abin Yabawa

Babban abin yabawa a cikin wannan littafi shi ne irin yadda marubuciyar ta bayyana yadda zamantakewar aure yake a wasu gidajen tare da kawo matsalolin da suke fuskanta ta hanyoyi masu sauƙi yadda kowa zai iya fahimta a sauƙaƙe. Sannan ta yi amfani da azancin maganganu na hikima da jan hankali wajen yin nuni da kuma kowayarwa ga mai karatu.

Kammalawa

A dunƙule, an koyar da manya-manyan darussa ga mata da ma’aurata da ma al’umma baki ɗaya a cikin wannan littafi. Don haka kai tsaye ina iya cewa wannan littafi ya kamata ace kowa ya same shi ya karanta, musamman ma’aurata da masu shirin yin aure, domin zai haskaka musu abubuwa da dama na zamantakewar aure.

Shawarwari

Ina ƙara jinjina ta musamman ga marubuciyar bisa wannan irin namijin ƙoƙari da ta yi. Kuma ina ƙara bata shawara akan ta ƙara jajircewa wajen ci gaba da kawo labarai masu koyar da darussa waɗanda suka shafi rayuwar al’ummar mu.

Kuna iya karanta cikakken littafin ‘Abdulkadir’ a nan.

Har ila yau, kuna iya karanta sharhin littafin ‘Akan So’ daya daga cikin shahararrun littattafan marubuciyar.

Manazarta

Yahaya, I. Y. da Ɗangambo, A. (1986) Jagoran Nazarin Hausa. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company Limited.

Yahaya, I. Y., Zaria M. S., Gusau M.S., da ‘Yar Aduwa T.M. (1992) Darussan Hausa don Manyan Makarantun Sakandire 1. Ibadan: University Press Plc Ɗangambo, A. (1984) Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph

10 thoughts on “Sharhin littafin ‘Abdulkadir’ na Lubna Sufyan”

  1. Avatar

    Hmm

    Jinjinata a gareka ne yah malam.
    Sannu da kokari wannan rubutu haka.
    Toh wllh ni nafi yabamaka mah fiyeda itamawallafiyar littafin domin kayi kaca kaca da gundarin lbrin ta yadda sokon littafin yafitowa mai maratu sarari.

  2. Avatar

    Masha Allah, gaskiya sharhin wannan yayi matukar daukar hankali da kuma burgewa. Fatan Alkhairi a gareka da marubuciyar baki daya

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page