Skip to content

Fasalin tonon silili a cikin littafin ‘Dambarwar Siyasa’ na gajerun labaran gasar Aminiya-Trust, 2020

1.0 Gabatarwa

Marubuta labarai na amfani da hanyoyi da yawa na bayar da labari ko gina labari a Hausa, sannan duk labarin da za a ba da ko a samar ko a rubuta ko a gina akwai hanyoyin da ake bi domin samun nasarar kai wa ga gaci. Abin lura a nan shi ne babban buri ko manufar duk masu bayar da labari ko rubutawa shi ne isar da saƙo da kuma nishaɗantarwa, hakan kuwa bai yiwuwa sai ta hanyar amfani da hanyoyi ko wasu matakai domin su jawo hankalin masu sauraro ko karatu zuwa gare su, ta amfani da dabara ko irin salo da kuma kalmomin da suka zaɓa domin samar ko gina labarin. Hakan ke nuna cewa matakai da ake bi domin samar ko gina labari har ya amsa sunansa su ne tubalai ko bulaluwan da suke sanya wa labari ya amsa sunansa. Daga cikin irin waɗannan matakai akwai:

  1. Bayyanawa
  2. Larabtawa
  3. Jan Ra’ayi
  4. Gardantawa
  5. Tonon Silili (Malumfashi, 2019:20-30)

Wannan maƙala za ta mayar da hankali ne a kan yin tsokaci, dangane da labaran da ake samu masu fasalin tonon silili a cikin littafin “Dambarwar Siyasa” wanda ke ɗauke da gajerun labarai guda 15 da suka samu ta dalilin gasar gajerun labaran Hausa da Jaridar Aminya – Trust tare da haɗin gwiwar Gandun Kalmomi da kuma Open Arts Foundation a shekarar 2020 wanda aka yi bikin ba da kyauta ga gwaraza a 5 ga wata yuni, 2021 a Hotel 17, Kaduna.

1.1 Ma’anar Fasali

Fasali na nufin tsari ko shiri. Sannan fasali na zama a matsayin kashi ko yana yi (CNHN,2006:136)

A taƙaice fasali shi ne yanayi ko hanya tsarin da ake ni ko amfani da shi domin fasalta ko shirya ko tsara abu.

2.0 Ma’anar Gasa

Gasa wata dabara ce ta gano ko fiddo da gwani daga cikin gwanaye. Haka kuma an ɗauke ta a matsayin siyasa ce wadda kan sanya al’amari ya bunƙasa, ya watsu tare da barbazuwa a tsakanin al’umma ko ana so ko ba a so. (Ɗan Amarya:433)

Sannan ana kallon gasa a matsayin wani al’amari da ake shiryawa kuma a gudanar da shi a tsakanin mutum biyu ko fiye kan wani abu ko al’amari.

A taƙaice gasa hanya ce ta yin hamayya ko yin kasayya ko yin takara tsakanin mutum biyu ko fiye a kan wani al’amari domin a fiddo da zaƙaƙuri daga cikin gwanaye, saboda haka ana iya gudanar da irin wannan al’amari na gasa ta fuskoki iri daban-daban da suka haɗa da karatu da sana’o’i da rubutu da aure da sarauta da sauran su (Ɗan Amarya, 2019:433)

2.1 Waiwaye Dangane Da Samuwar Gasa A Rubutattun Labaran Zuben Hausa

Haƙiƙa a iya cewa gasa a fagen rubutun labaran Hausa ta taka muhimmiyar rawa, idan ma ba ta zama ita silar samuwar rubutun zuben Hausa ba. Sannan hukumomi da cibiyoyi da ƙungiyoyi da gidauniyoyi sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da littattafan rubutattun labaran zuben Hausa Hausa ta sigar gasa tun daga da har zuwa yanzu. Tasirin hakan ya sanya har yanzu abun ke ƙara bunƙasa da samun tagomashi.

A tarihin gasar rubutun zuben Hausa an fara ta ne a shekarar 1927, sai dai babu sunan labari, kuma babu labarin da aka samar. Sai gasar shekarar 1929 wadda Hukumar Inganta Al’adu ta ƙasa da ƙasa ta samar wanda an samu sunayen labaran da aka shiga da su da marubutan labaran.

Amma daga gasar shekarar 1932/1933 aka fara samun labaran zube na ƙasa, wanda Hukumar Fassara ta sanya. Baya ga haka gasar shekarar 1978 wadda kamfanin NNPC da ke Zariya ya sanya ita ce gasa ta farko da ta fara samar da littattafan labaran zuben Hausa masu ɗauke da fasalin soyayya.

Gasar shekarar 1980 wadda Hukumar kula da Nazarin Al’adu ta Tarayya ta sanya ta samar da littattafan labaran zube guda 4 da littafin waƙa guda da wasan kwaikwayo 1 da littafin wasa kwakwalwa guda 1. Sai Gasar Rubutattun Labaran Zube ta shekarar 1988 wadda Hukumar kula da Kyautata Fasaha da Al’adu ta sanya ta samar da littattafan zube guda shidda da aka gina su kan rayuwa ta zahiri. Akwai Gasar Ƙungiyar Inuwar Marubuta Littattafan Hausa da ke Kano da aka yi a shekarar 2007 ta samar da littafi 3. Bugu da ƙari Ita kuwa gasar 2007-2009 wadda Gidauniyar Tunawa da Injiniya Bashir Ƙaraye ta sanya, ta samar da littattafan labaran zube guda 9 a shekaru biyu wato a shekarar 2007 da 2008 sai littattafan wasan kwaikwayo guda 5 a shekarar 2009.

Yayin da Gasar Mata Zalla Ta Gidan Rediyon BBC mai taken “Hikayata” ta samar da gajerun labaran zuben Hausa da suka zama zaƙaƙurai guda 18 a tsakanin shekarar 2016 (Shekarar da aka fara gasar) zuwa 2021. Sannan da ƙarin guda 54.

Wato 1 – 3 a kowace shekara sannan da ƙarin 54 a tsakanin shekarar 2016 -20121, wato daga na   4 – 12 a kowace shekara, waɗanda ake karantawa a shirin “Adikon Zamani” sai gasar PLBS da MMB ta shekarar 2018 ta samar da labaran zuben Hausa guda 15. Sai gasar Gusau Institute da aka fara daga shekara 2018 – 2021 ta samar da littattafai 12. Sai gasar Ɗangiwa ta 2020 ta samar da labarai 12, da gasar Aminiya Trust haɗin gwiwa da Open Arts da Gandun Kalmomi a 2020 ta samar da labaran zube guda 15. Gasar Sana’a da Ilimi Foundation a shekarar 2021 ta samar da littattafai guda 5. Yayin da gasar Dar Al-Andulus a shekarar 2021 ta samar da labaran zuben Hausa guda 24.

2.2 Gasa Mai Tsayayen Jigo

Duk gasar da aka yi a baya ana barin jigon gasar a sake ne wato zaɓin marubuta ne su yi rubutu kan abin da suke da sha’awa, wato ba a sanya jigo taƙamaimai da a kansa ake son a rubuta labarin ba. Amma daga shekarar 2013 aka fara samun gasa mai tsayayen jigo. Ga misalin abin.

Gasar Makarantar Malam Bambaɗiya, gasa ce da makarantar ta sanya a kan jigon Almajiranci a shekara ta 2013 ( Makarantar Malam Bambaɗiya makaranta ce da aka assasata a shafin sadarwa na Fesbuk ƙarkashin jagorancin Malam Ibrahim Malumfashi)

Baya ga haka a shekarar 2018 Pleasant Libarary And Book Club  Haɗin Gwiwa da Makarantar Malam Bambaɗiya sun yi gasa akan jigon Talauci wanda aka samar da labarai guda 15 da ba da awalaja daga na ɗaya har zuwa na sha biyar ɗin.

Sannan a shekarar 2020, Jaridar Aminiya-Trust Haɗin Gwiwa da Open Art Foundation da Gandun Kalmomi da ke Kaduna. sun gabatar da gasa akan jigon Siyasa, an bayar da kyaututtuka ga zaƙaƙuran gasar sannan an buga littafi mai suna “Dambarwar Siyasa”.

Sannan a shekarar 2020 akwai Gasar Dangiwa Literary da aka gabatar, akan jigon Muhalli da Matsalolinsa Da Ayyukan Bankin Bada Lamunin Gina Gidaje, an bayar da awalaja ga waɗanda suka samu nasara daga na 1-13, sannan aka samar da littafi mai suna “Muhalli Sutura”.

A shekarar 2021 Cibiyar  Dar Al-Andulus da ke Kano ta gabatar da gasa kan jigon “Kan Sha’anin Tsaro” wanda an bayar da kyauta daga 1-5 da takardar shaida (Certificate) da buga labarai 30 da aka shiga gasar da su a cikin littafin da aka sanya wa suna “Gane Mani Hanya

A shekarar 2021 Wata Ƙungiyar Marubuta da ke Kano ta saka gasa akan jigon “Dogaro da Kai da Hanyoyin samar da Tsaro da Illolin Shaye-shaye” gasar da aka kira da suna “Gasar Hikimata”

2.3 Gasar Gajerun Labarai

Gasa a kan gajerun labaran Hausa, wani sabon shafi ne aka buɗe a cikin adabin Hausa, kuma yunƙuri ne da zai sanya adabin Hausa ya yi gwajin kafaɗa da adabin Ingilishi da ma adabin kowane harshe a duniya, domin gajerun labarai sun jima da samuwa da kuma watayawa a cikin zube da adabin sauran harsuna a duniya (Malumfashi, 2019) sai dai a cikin zuben Hausa an fara samunsa a shekarar 2016 aka fara samun gasar gajerun labarai, Wato tun daga gasar Hikayata ta BBC da aka fara a shekarar 2016 har zuwa yau. Da gasar Pleasant Library and Book Club haɗin gwiwa da Makarantar Malam Bambadiya (PLBC/MMB) da aka yi a shekarar 2018. Da gasar Aminiya Trust tare da haɗin gwiwar Open Arts da Gandun Kalmomi da aka yi a shekarar 2020, haka gasar Ɗangiwa ta shekarar 2020, da gasar Dar Andulus da aka yi 2021 da gasar Tsibirin Gobir ta 2022, duk labaran gajerun labarai ne da suke farawa daga kalmomi 1000 suke kuma tsayawa a kalmomi 4000 zuwa 5000. (Sabe, 2020, Gidan Marubuta,2021)

3.0 Ma’anar Tonon Silili

Tonan Silili na nufin tonon asiri ko bankaɗen sirri (CNHN, 2006:396)

A wani ƙaulin tonon silili shi ne zaƙulo tare da bayyana duk wani abu da ke sakaye da ake so wasu su sani don mugunta ko fahimtarwa, yawancin irin waɗannan abubuwa mutane ba su san su ba ko kuma ana kaffa-kaffa da su domin ba a son a sani, idan kuma aka bayyana su ta kowane irin fuska zai iya cutar da wani ko wasu ko wani abu ko kuma ya ankarar da waɗansu game da illa ko kyawon tsarin abun, in marubuta suka yi haka a cikin labaransu, to a nan an yi tonon silili ke nan. (Malumfashi, 2019)

Ana iya kallonm tonon silili a matsayin kai wa matuƙa wajen tonon asiri da ake aiwatarwa cikin salo da azancin rubutu tare da goyon bayan jan ra’ayi.

3.1 Fasalin Tonon Silili A Cikin Littafin Dambarwar Siyasa

A Wannan Littafi Na Dambarwar Siyasa a iya cewa fasalin tonon silili ya wataya a cikin littafin sosai domin kusan duk labarai akwai tonon silili, sai dai wani labarin an yi tonon sililin da yawa, a wani labarin kuwa kaɗan aka taɓa. Misali:

“Ni ne kan gaba wajen kawo wa mutanen unguwa kayan masarufi domin jan hankalinsu. Ina cikin masu bin malamai da ‘yan tsibbu domin neman sa’a. Kuma ni ne lambawan wajen jagorantar matasa wajen ƙaddamar wa ‘yan adawar da ke hamayya da mu”.

Dimokuraɗiyyar Talaka:2020:4

(Rufaida Umar Ibrahim)

A wannan gaɓa marubuciyar tayi tonon silili ta hanyar bayyana yadda ‘yan siyasa ke raba kayan masarufi ga masu ƙaramin ƙarfi don su yaudare su su kaɗa masu ƙuri’a a lokacin zaɓe, wanda da an zaɓe su ba a sake jin ko ɗuriyarsu. Sannan ta bayyana yadda suke bin ‘yan tsibbu domin samun biyan buƙatarsu ba tare da fawwala lamarinsu ga Allah ba, sannan da yadda suke amfani da ‘yan daba don farmakar masu yin adawa da su. A wannan gaɓa an yi tonon silili dangane da mugun halin ‘yan siyasa tun daga tushe, tun daga masu ci (Waɗanda suke kan madaɓun iko) har masu neman takara, yadda suke da halin rowa da rashin taimakon talakawa da gajiyayyu da duk masu son taimako, musamman da abincin da za su kai bakin salati. Amma da zarar an kaɗa ƙugen siyasa sai a ga suna rige-rigen raba abin masarufi irin su kayan abinci ga al’umma domin jan hankalinsu su zabe su. Kuma da sun ci ba a ƙara ganinsu sai wani zaɓen ya zo wannan yaudara da sauran dangoginta haka  marubuciyar ta tona sililinta, sannan a zahiri ma haka ‘yan siyasa ke yaudarar mutane, sannan an tona sililin ‘yan siyasa yadda suka yi imani da matsafa da bokaye da aka fi kira da ‘yan tsibbu, wurin neman buƙatarsu wato ba su yi imani da cewa Allah ke ba da mulki ba, sai dai ‘yan tsibbu. A rayuwa ta zahiri `ma abin da ke faruwa ke nan har ta kai fagen da lokacin siyasa ya zo tun daga fitar da ‘yan takara zuwa yaƙin neman zaɓe, har zuwa lokacin zaɓe akan ci gaba da cin karo da ayyuka irin su sacewa da yanke mahaukata ko kashe mutane da cire masu al’aura ko wani sashe na jiki ko ɗauke gawarwaki daga cikin ƙaburbura ko yanke wani sashe na gawan, ko abin da ya shafi lalata da yara ƙanana ko mahaukata mata ko luwaɗi ko rufe dabbobi da ran su da sauran su, waɗannan abubuwa galibi ana aiwatar da su ne domin cika umurni ko wasu sharuɗɗa da ‘yan tsibbu suka bayar ga ‘yan siyasa domin samun mulki.

Sannan an tona sililin yadda ‘yan siyasa ke amfani da matasa a matsayin gugar yasa ko karnukan farautarsu masu yi musu bangar siyasa. Domin duk wanda yake adawa da su za su sanya matasa da aka lalata tunaninsu ta hanyar ba su kayan maye masu gusar da hankali da tunani da muggan makamai su ƙaddamar wa abokan adawar iyayen gidansu. A siyasa ta zahiri ma haka abin ke faruwa, yawancin lokuttan ma ana alaƙanta wasu ayyukan ta’addanci na zubar da jini babu cas, babu as da matasa marasa tunani ke yi, tushensa daga bangar siyasa ne, bayan ‘yan siyasa sun ci moriyar ganga sun kuma yada kwaurenta, sai matasan sun ɗauki makamai tun da an riga an nuna masu hanya.

“A je, a gabatar da zaɓen, kuma a bayyana Nuhu Agaji a matsayin wanda ya lashe zaɓen zan fita yanzu na yi hira da ‘yan jarida tare da bayyana wa duniya ina goyon bayan mataimakina, ina so jibi ka fito ka yi hira da ‘yan jarida ka shaida wa duniya cewa ka fita daga jam’iyyas BSC saboda rashin adalci da aka yi muku, aka tursasa ku wajen tabbatar da Nuhu Agaji a matsayin ɗan takara bayan shi ya zo na uku, sannan ka sanar da komawarkajam’iyyar PHD, a kan kai ma za ka je neman kujerar Gwamna”

Tubka Da Warwara, 2020:12-13

(Mubarak Idris Abubakar)

A nan marubucin ya yi tonon silili dangane da yadda ‘yan siyasa suke zama marasa alƙibla ko masu fuska biyu har su aiwatar da ba yadda za a yi a zarge su, saboda yaddab suke wasa da ƙwaƙwalwa ko tunanin mutane kamar yadda aka nuna gwamna Audu Maikaji ya nuna goyon bayansa ga mataimakinsa Nuhu Agaji, sannan a sirrance ya zuga tare da tsara wa shugaban jam’iyya Babangida Soja gadar zaren da za su shirya wa Nuhu Agaji ba tare da an gane ba. Wanda hakan ne ke faruwa a duniyar siyasa ta zahiri domin idan mutane sun kai dubu masu takarar kowanensu shugaba a keɓance tsakanin shi da kowa zai nuna shi yake so, sannan ana turo ɗan takara a ƙurarren lokaci wanda ake kira (Late comer)kuma a mara masa baya ya samu kujerar.

Sannan a zahiri duk ɗan siyasar da ya bar wata jam’iyya yakan ce, adalci ke ba a yi masa a jam’iyyar da ya baro ba. wanda galibi ƙarya suke yi duk wanda ya nemi takara bai samu ba zai bar jam’iyyar ko idan ya ga alamun jam’iyyar za ta durƙushe.

“A haƙiƙanin gaskiya kuwa korona farin ciki muka yi da zuwanta. Dalili shi ne ta samar mana da hanyar ƙafar ungulu da kuɗaɗe cikin ruwan sanyi”

Ranar Ƙin Dillanci, 2020:2(Ubaida Sani)

A wannan ɓangare marubuciyar ta yi tonon silili irin yadda shuwagabannin siyasar ƙasar nan suka ci karen su babu babbaka da dukiyar al’umma a ƙarƙashin ofisoshinsu da ikonsu da sunan Korona  wato Cutar Sarƙewar Numfashi da ake fama da ita (Covid 19/ Corona Virus).

Wato duk lokacin da wata cuta ko annoba ko wani yanayi marar daɗi da ya faru,  sai a yi amfani da shi ya zama hanyar takura wa al’umma da cutar da su ta hanyar ƙaƙaba masu wasu sharuɗɗa ko dokoki da sunan ana kare rayuwarsu ko ana matuƙar kula da su  ba a so wani abu ya cutar da su ko halaka su. Amma a baɗini da wannan cuta ko annoba ake amfani a samu kuɗi na tashin hankali musamman gwamnati da duk wani jam’i da abin da ya shafa kai tsaye ko kaikaice. A duniyar siyasa ta zahiri ma haka abin yake ba ta canza zani ba. Domin an ga yadda gwamnati da muƙarrabanta da sauran jami’anta suka fantama sakamakon cutar sharƙewar numfashi (Covid 19) musamman lokacin da aka garƙame jihohi (Lockdown) duk da cewa al’umma sun shiga wani irin hali na tasku. A zahiri abubuwa da ke faruwa na annoba ko cuttuka sukan zama azaba ga al’umma amma hatimin sa’a ko rahama ga gwamnati da kuma duk wanda abin ya shafa. Misali watanda a faruwar abubuwa irin Allurar shan inna (Polio) da murar tsuntsaye (Bird flu) da cutar Ebola da Zazzaɓin Ɓera (Lassa Fever). Duk a faruwar waɗannnan abubuwa an takura al’umma da cutar da ita da wai ana sunan ana sonta, yayin da gwamnati da jami’anta ke darawa da sam barka da faruwar yanayin sakamakon romon da ake sha daga masu kawo tallafi na ƙasashen ƙetare da kuɗaɗen da ke fita lalitar gwamnati da sunan daƙile yanayin.

“……………..Don haka kowane manomi ya gaggauta zuwa bankin manoma domin bude buɗe asusu. Gwamnati ta ware miliyan ɗari biyu domin wannan tallafin. Kuma manoma dubu biyu ne za su ci moriyarsa”. Cikin murmushi Malam Nasiru ya dube shi “Honarabul bana za a bayar da tallafin da gaske kenan?”

Dariya sakatare ya yi. “Ashe har yanzu Nasiru ba ka gama sanin siyasa ba.

Komai Nisan Dare, 2020:30

(Yaseer Kallah)

A nan marubucin ya tona sililin ‘yan siyasa yadda suke fitowa a kafafen yaɗa labarai su yi bayanan karya da yaudara da nufin za a taimaki manoma, su yi ta wahakar da bayin Allah sunan sanya masu rai alhaki ƙarya da yaudara ce suke yi.

Duk da cewa a gwamnatance ana fitar da kuɗin da sunan an ba da tallafin noma, amma kashe mu raba ake yi ko sisin kobo ba a ba asalin manoman da aka fitar da kuɗin da sunansu, ko kuma a ɗaya ko ɓalli cikin kaso ɗari.

Haka abin ke faruwa a duniyar siyasa ta fili, domin akan fito da tsarin tallafawa manoma a sanya su buɗe asusun ajiya a bankuna da samar da ƙungiyoyi, irin ƙungiyar manoman alkama da masara da shinkafa ko ƙungiyar manoman noman rani da sauran, wanda idan an fitar da kuɗin daga aljihun gwamnati, sai wasu jami’an gwamnati su karkatar da kuɗin, ko kuma a yi kashe mu raba da galibin shuwagabannin manyan ƙungiyoyin manoman, sai a bar ƙananan manoma da hamma da tsammani ko jiran gawon shanu.

“Ganin tafiyar Farfesa ta samu karɓuwa a birane da ƙauyuka, baƙin ciki hassada suka ƙara turnukezukatan su Alhaji Isiya a karshe dai suka yanke shawarar kawar da shi daga doron ƙasa”.

Hassada Ga Mai Rabo, 2020:40

(Mustapha Sufyanu Jikan Malam)

Marubucin ya bayyana yadda ‘yan siyasa ke yi wa mutumin kirki idan ya fito takara ya samu karɓuwa wato ko dai su yi kisan mummuƙe ko su yi wa mutum sharri ko su tsara yadda za su kashe shi ba tare da kowa ya sani ba domin samun biyan buƙatarsu, kamar yadda aka yi wa Farfesa duka.

A duniyar siyasa akan yi wa ɗan siyasa sharri ne daga abokan hamayyarsa da suke ba a jam’iyya ɗaya, amma sharrin cikin gida shi ake kira “yarfe” ko “yarfen siyasa” wanda maƙiya na cikin jam’iyya ke yi wa wanda ba su so ko wanda ya fi su karɓuwa ko samun goyon baya daga jama’a kamar yadda ake tuggun da su Alhaji Sambo da Alhaji Isiya suka yi wa Farfesa, haka abin ke faruwa a zahiri a duniyar siyasa, domin kuwa masu azancin magana na cewa “da ɗan gari a kan ci gari”’ kuma munafukinka na gindinka”.

“Lokacin zaɓe ya zo muka yi masa maguɗi ya ci zaɓe domin ya saki kuɗi sosai. Shekara biyu bayan ya ci zaɓe babu aiki guda ɗaya da zai nuna. Matasa ba aikin yi, mu da ya yi wa alƙawarin aiki ko ganinsa ba ma yi”.

Baki Guba Ne, 2020:51

(Basira Sabo Nadabo)

Marubuciyar a nan ta yi tonon silili dangane da yadda ‘yan siyasa ke amfani da matasa  a matsayin gugar yasa domin cimma muradunsu na siyasa daga baya su watsar da su bayan romon baka da suka yi masu, kamar dai yadda abun yake a cikin wannan labari. Kuma ko a zahirance haka ‘yan siyasa ke aiwatar da tsarin tsakaninsu da waɗanda suka yi masu hidima, sukan yi wa al’umma musamman matasa masu goyon bayansu ƙaryar za su ba su jari ko samar masu aikin yi, ko hidimta masu a cikin harkokin rayuwa. Amma bayan sun tura motar ta tashi, sakamakonsu shi ne a buce su da ƙura ko a fesa masu hayaƙi a bar su da ƙauri da wato dai haka za a bar su, babu aikin yi, babu jari, babu tallafi, babu magana mai daɗi, wasu ma daga ranar sun gama ganin ɗan siaysar gaba da gaba, kuma ko wayarsa suka buga idan sun yi sa’a ta shiga ma ba zai ɗauka ba. Wasu kuwa ko lambar wayar ɗan siyasar mai yi ba za su samu ba.

“Tana cikin zaman jiran nan ne sai ta fara bibiyar takardun, ta ga ashe bajat ne wanda aka fitar wa ƙaramar hukuma. Ba ta san lokacin da ta doka salati ba, saboda yadda aka reɗe kuɗaɗe masu yawa a cikin bajat ɗin, aka karkatar da su ta wata hanyar yaudara”.

Tsaka Mai Wuya, 2020:56

(Salim Yunusa)

Tonon sililin a nan ya shafi yadda ‘yan siyasa ke wandaƙa da kuɗaɗen al’ummar da suke mulka ta hanyar ƙarya da yaudarar tsara kasafin kuɗi a takarda, amma a zahiri a yi kwana da kuɗin. Wannan yaudara ta zama ruwan dare ga ‘yan siyasa yadda ake haɗa baki da masu ruwa da tsaki a yi kashe mu raba.

Irin wannan kitimirmira haka take faruwa a duniyar siyasa ta zahiri, ko a sake maimaita kasafin kuɗin da ya gabata, domin a cire kuɗi fiye da sau ɗaya, abin da ake kira “Cushen Kasafin Kuɗi” da “Kasafin kuɗin boge”.

“Ki yi shiru ki saurare mu, munafuka. Mun san ki, mun kuma san inda gidanku yake. Ko ki janye takararki, ko kuma duk abin da ya same ki, to ke kika sayo wa kanki da hannunki”.

Kawalwalniya, 2020:61

(Mujaheed Ameen Lilo)

A wannan fasali tonon sililin ya jiɓnci yadda ‘yan soyasa ke yin amfani da ‘yan ta’adda suna yin barazana da nufin salwantar da rayukan abokan hamayyarsu ko cutarwa ga ahalinsu, kamar yadda aka yi wa Badariyya. Wanda hakan ke sanyawa wani lokaci sai dai kawai a ji ɗan takara mai farin jini ko wanda al’umma ke so ya shelanta janyewarsa daga takara, a rasa me ya sanya faruwar hakan, ba a san a sirrance aka yi masa barazanar kisa ko cutarwa ga ahali ba.

Wanda a zahiri hakan ta sha faruwa dangane da siyasa ta zahiri, hasali hakan ma abu ne wanda ya zama ruwan dare a duniyar siyasa ta zahiri.

“Ummi! Kin tuna irin cin kashin da Alhaji Bukar ya sa akka yi miki a kafafen sada zumunta lokacin da kike jam’iyyar ANC?” Hajir ya faɗa bayan ya riƙo hannayenta. Sannan ya ci gaba da cewa “Haka ya sa aka yi wa Daddy. Yanxu ke ce abin son su tun da kin bar ANC kin dawo FAN”.

Kazar Kwanci,2020:71

(Maryam Umar Sakkwato)

Marubuciyar ta yi tonon silili dangane da halin rashin kunya da rashin dattako na ‘yan siyasa irin yadda suke cin mutuncin juna idan akwai bambancin Fati a tsakanisu, amma idan sun haɗe a Fati ɗaya sai su nuna wa duniya su masoyan juna ne. Har ana rungumar juna a gaban jama’a don nuna ƙauna da soyayya. Wannan kuwa haka abin yake a zahiri domin haɗuwar jam’iyya ɗaya ga ‘yan siyasa ita ce dangantaka mafi ƙarfi.sannan duk soyayya ko ƙiyyar ‘yan siyasa tana cikin jam’iyyar idan ana a jam’iyya ɗaya an zama masoya, idan an raba jam’iyya an zama maƙiya

“A jiya da hantsi, kamar yadda kuka ji labarin taho-mu-gama da ‘yan bangar siyasa mabambanta ra’ayoyi suka yi, lokacin na ziyarci gidan Almustapha inda yake ba ni labarin yadda ya ɗora burinsa a kana Zulaihat wadda ke ƙoƙarin a makaranta, da kuma son a daina muzgunawa ‘yan uwanta mata. Kwatsam! Sai ga shi an kawo gawar Zulaihat wai ‘yan bangar siyasa sun sassare ta a hanyarta ta dawowa daga Islamiyya”

Ci Ga Rashi, 2020:84

(Isma’il Gambo)

A nana tonon sililin ya shafi yadda ‘yan siyasa ke amfani da ‘yan bangarsu, suna zubar da jinin al’umma domin biyan buƙatarsu ta neman mulki da hawa mulkin ko ta halin ƙaƙa tare da maida ‘ya’yan talakawa karnukan farautarsu. Amma kuma saboda son kai ba su sanya ‘ya’yansu a cikin irin waɗannan miyagun ayyukan. Sannan ko siyasa ta zahiri haka abin ke faruwa, ba wai ayyukan zubda jini ba, a siyasa ta zahiri ‘yan siyasa ko yaƙin neman zaɓensu ba su zuwa da ‘ya’yansu da matansu, ba a liƙa fastar ɗan takara a ƙofar gidan ko ƙofar gidan ‘ya’yansa, wasu ko a motocin su na hawa ba a sanya fastar takararsu sai dai motocin yaƙin neman zaɓe da motocin yaku-bayi.

“Siyasa kasuwa ce, duk abubuwan da na ƙirgo ba wanda zan yi, ba ni da hankali ne, sau uku fa ina nema, ina faɗuwa. Daga hawa kawai sai in ɓuge da ayyuka, tun ban fanshe kuɗin da na kashe a kamfen ba”.

Kotun Allah Ya Isa!,2020:104 (Rufa’i Abubakar Adam)

A wannan gaɓa marubucin ya tona sililin ‘yan siyasa dangane da manufarsu da halinsu na yaudarar al’ummar da suka zaɓe su, wato abin da suka furta za su yi daban, abin da kuma suke yi a zahiri daban. Haka abin yake a siyasa ta zahiri. Galibin ‘yan siyasa sun ɗauketa a matsayin kasuwa da suke aiwatar da kasuwancinsu, saboda haka hannun jari ne suka zuba, duk abin da suka kashe a lissafe suke da shi,  idan sun ci kujerar, sai sun maida kuɗaɗensu sun lissafa riba kafin su iya yi wa al’umma wani abin kirki. Wasu ‘yan siyasar ma kai tsaye suke faɗa su ce “sayen kujerar ko takarar suka yi, saboda haka dole ne su maida kuɗin da suka kashe”.

“Ka gaggauta ficewa daga gida domin an turo ‘yan ta’adda su kashe ka”. Nabila ta sanar da Abubkar Mai-Allah, ɗan takarar jam’iyyar NCC ta wayar salula”.

Zaɓin Allah, 2020:107

(Faridat Husain Mshelia)

Kamar yadda aka ambata a baya, a nan madai tonon sililin ya shafi yadda ‘yan siyasa ke amfani da ‘yan ta’adda suna kashe abokan adawarsu. Wannan na nuna cewa kisa shi ne abu mafi sauƙin aiwatarwa ga ‘yan siyasa tsakanin su da abokan hamayyarsu. Ko a rayuwar siyasa ta zahiri yana daga cikin babban kudirin ‘yan siyasa barazanar kisa ko aiwatar da kisa ga abokan hamayyarsu wanda ya fi su cancanta ko wanda ake ganin mutumin kirki ne, kuma zaɓin mutane. Kuma haka ya zama ruwan dare.

“Kusan duk garin da muka je, idansuka faɗi matsalarsu sai na fashe da kuka na munafunci. Tabbas kuksan nawa ba ƙaramin karya musu zuciya yake yi ba tare da ɗarsa soyayyata a zuciyarsu”.

Tsalle Ɗaya,2020:120

(Nasiru Kainuwa Haɗejia)

A wannan gaɓa fasalin tonon sililin ya shafi amfani da yaudara da ‘yan siyasa ke yi a lokacin yaƙin neman zaɓe ta sigar jan ra’ayi.

Yadda suke ribatar mutane dangane da wasu halayensu na kirki da aka sani, ko wasu ayyuka ko sadaukarwa da suke yi wa al’umma kamar aikin gayya ko kula da tarbiyyar ‘ya’yansu ko koyarwa a Islamiyya, domin su samu tausayawar mutane da amincewarsu, wanda sai bayan sun amince, sai munanan halaye su bayyana, ashe daman “kowane gauta ja ne” rashin rana ce ta sanya ba a gane.

Haka abin yake a rayuwar siyasa ta zahiri akwai masu addini da malaman islamiyya da dama da suka samu tausayawar mutane aka zaɓe su da tsammanin za su yi wa al’umma mulkina adalci a ƙarshe suka yaudare su suka ci amanarsu kamar yadda ta kasance a wannan labarin.

“Allah ya gafarta Malam, idan muka ci zaɓe akwai tanadin kujerun Hajji da Umara kai da almajiranka, duk shekara. Sannan akwai muƙami na musammana da za a ba yar”.

Yanayi,2020:125

(Habib Sani Yahaya)

A wannan ɓangare , marubucin ya bayyana wani salon yaudara da ‘yan siyasa ke amfani da shi wajen jawo malamai na addini da shafa masu mai a baki ta hanyar yi masu alkawarin ƙarya, domin su je su yi masu kamfen da addu’o’i.

A rayuwar siyasa ta zahiri wannan abin shi ake ya yi, wato yadda ‘yan siyasa ke amfani da malaman addini na musulunci da kiristanci da jawo su a jika da yi masu alƙawuran ƙarya da yaudara, domin su amfana da matsayinsu wurin yi masu yaƙin neman zaɓe da yi masu zabarin ƙuri’u ga magoya bayansu a coci/majami’u da masallatai domin cikar burinsu na ɗarewa a kan kujerunsu, daga ƙarshe su bar rikici tsakanin malaman addinan da ɗalibansu ko magoya bayansu.

4.0 Kammalawa

A ƙarshe a iya cewa fasalin tonn silili ko salon amfani da tonon silili a cikin hanyoyi ko matakan ba da labari ya mamaye littafin “Dambarwar Siyasa” tun daga farko har karshe. Sannan saƙon ya isa ta wannan fasali kuma hakan ya nishaɗantar.

Manazarta

CNHN, (2006).Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero Kano. Zaria:Ahmadu Bello University Press

Dambarwar Siyasa (2021) Aminiya-Trust, Gandun Kalmomi, Open Arts Foundation. Kaduna:Tast And Print Ventures

Malumfashi, I. (2019), (ed). Labarin Hausa A Rubuce. Zaria: Ahmadu Bello University Press

Malumfashi, I. (2019) Laccar Kwas Ɗin Hau 817 (Modern Hausa Fiction) .Kaduna:Jami’ar Jihar Kaduna

Malumfashi, I. (2019) Laccar Kwas Ɗin Hau 818 (Narratology) .Kaduna: Jami’ar Jihar Kaduna

Mujallar Inuwar Marubuta, (2008). Kano:Anka-Graphic Fagge

Mujallar Malami, (2018) Shafi Adabi.Katsina:Pleasant Libarary And Book Club

Sabe, B. A.(2020) (ed) Muhalli, Sutura. Katsina:Darma Digital Prints

6 thoughts on “Fasalin tonon silili a cikin littafin ‘Dambarwar Siyasa’ na gajerun labaran gasar Aminiya-Trust, 2020”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page