Skip to content

Salon bayar da labari da salon ginin labari 1

A yau za mu yi bayani ne a akan salon bayar da labari da kuma salon ginin labari. Idan ba ku manta ba, a maƙalar da ta gabata, mun yi bayani game da fa’idar yin bincike a wajen ginin labari, inda muka ce mutunci, ƙima da kuma darajar rubutun marubuci tana zubewa a ƙasa wanwar a duk lokacin da ya tafka wani gingimemen kuskure yake kuma da’awar daidai ya yi a cikin labarinsa. Muka ce ta hanyar bincike ne marubuci zai zama shakundum, ya zama komai da ruwansa ta yadda zai iya yin rubutu a kowanne fanni kuma rubutun ya ƙayatar da duk wanda ya karanta. Muka kawo hanyoyin yin bincike, da cikakken bayanin kowanne.

Salon bayar da labari

Kafin mu tattauna a kan wannan salo mu fara sanin ma’anar salo mana. Salo wata dabara ce ko hanya da marubuci yake bi wajen isar da sakonsa ga makaranta cikin hikima da gwanintar harshe ta hanyar tsara kalamai da ayyuka. Ana son salo ya zama ƙaƙƙarfa ko nagartacce, wato ya zamana ana karanta rubutu yanayin salon da aka yi amfani da shi ya riƙa tafiya da hankalin mai karatu. Ba wai salo ya zama rarrauna ko miƙaƙƙe ba irin wanda babu wani abu na armashi a cikinsa.

Misalin yadda za a fahimci muhimmancin salo a cikin labari shi ne, irin misalin mutane biyu da suka sayi atamfa ko shadda iri ɗaya masu tsada ɗaya. Ɗaya a cikin su ya kai wa tela wanda ya iya ɗinki sosai, ɗayan kuma ya kai wa tela wanda bai iya ɗinki ba. Duk tsadar shaddar ko atamfar da telan da bai iya ɗinki ba ya ɗinka, ba za ta burge mutane ba har ta ja hankalinsu idan an saka a jiki kamar ta telan da ya iya ɗinki. Za ku yarda da ni cewa atamfa ko shadda mafi araha za ta iya fin ita mai tsadar jan hankali idan ta samu tela mai kyau. To haka shi ma rubutun labari yake. Shi ya sa wani lokacin sai ka ga wani wanda labarinsa bai kai naka samun jigo mai kyau ba, idan ya samu salo mai kyau sai ya fi naka ƙayatarwa, har ma ya yi nasara a gasa naka bai yi ba.

Marubucin da ya iya salo da ƙirƙira tamkar telan da ya iya ɗinki ne, hakanan marubucin da bai iya fitar da salo da alƙalaminsa ba tamkar tela ne da bai iya ɗinki ba. Shi ya sa mabanbantan marubuta za su iya ɗaukan jigon labari ɗaya amma ka tarar banbancin daɗin labaransu tamkar banbancin garɗin koko da madara ne.

Domin samun ƙarin fahimta, za mu nazarci waɗannan misalan na Rarraunan Salo da kuma Nagartaccen Salo:

Rarraunan salo;

i- Na je wajenta jin hirarta mai daɗi ta bar ni a tsaye ta ƙi fitowa.

ii- Har na fara gyangyaɗi na gaji na tafi.

Nagartaccen salo;

i- Na je ba wa ruhina abincin da yake muradi na daɗaɗan kalamanta masu yi mini daɗi kamar ana sosa mini kunne, ta bar ni a tsaye kamar kwatar raken da aka dasa.

ii- Har idanuwana suka fara nauyi, na fara gani dishi-dishi na yi gaba kafin bacci ya yi gaba da ni.

Abin lura, duk waɗannan misalan abu ɗaya ake so a ce a cikin su, abin tambaya a nan shi ne waɗanne daga cikin huɗun ne za su fi jan hankalin mai karatu? Ga wasu misalan:

Rarraunan salo;

i- Motar mai kyau ta shige cikin asibitin da mai gadi ya buɗe ƙofar.

ii- Kallon ƙofar asibitin kaɗai ya isa ka fahimci asibitin masu kuɗi ne.

 Nagartaccen salo;

i- Rantsattsiyar motar ta sulala cikin asibitin da mai gadi ya buɗe wawakeken ƙyaurensa irin yadda maciji yake sulalawa raminsa.

ii- Kallon ƙofar asibitin kaɗai ya wadatar ka fahimci asibitin na masu yatsu dayawa ne.

Wannan abin da ya shafi salon sarrafa harshe kenan, idan mun fahimta to mu koma kan asalin batunmu na farko, wato Salon bayar da labari, wanda shi ma ya kasu zuwa kashi biyu:

Salon tauraro cikin fage

Salon tauraro wajen fage

Za mu ɗauki kowannensu ɗaya bayan ɗaya mu tattauna muhimman abubuwa da suka shafe shi na ƙa’idoji da dabaru insha Allahu.

•Tauraro cikin fage: Wannan shi ne salon bayar da labari wanda tauraro da kansa yake bayar da labarin ga manazarci. Misali;

“Da yake dare ya tsala, wajen misalin shaɗaya da rabi, ban kula da yaron da yake gabana ba kawai sai maganarsa na ji, wacce ta haifar mini da faɗuwar gaba. “Wai ga shi!” Ya ce da ni yana miƙo mini wani abu.

‘Na yi amfani da hasken gilashin wayar hannuna na haska askakken ranƙwalelen kansa da ya yi mini kama da na fatalwu, wani irin kallo da na ga yana yi mini da daƙwa-daƙwan idonsa ya sa na fara ji a jikina tabbas ba mutum ba ne…’

Ta hanyar nazartar wannan misali za mu ji cewa tauraron, ko tauraruwar da kanta ce take bayar da labarin. Dayawan mutane sun tafi a kan cewa wannan salon ya fi tasiri wajen isar wa da manazarta saƙon da ake so a isar musu cikin sauƙi a zukatansu. Ana cewa waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi, to haka ma labari a bakin mai shi ya fi armashi, idan labarin tausayi ne an fi jin tausayinka sosai da wannan salo, idan ma labarin barkwanci ne an fi darawa sosai da wannan salo.

Sai dai kuma salo ne mai matuƙar sarƙaƙiya da wuyar sha’ani idan marubuci bai sanya kula ba, amma idan za a sanya kulawa salon yana da sauƙi sosai. Za mu nazarci wasu daga cikin dokoki, ko ƙa’idojin wannan salo yanzu insha Allah.

•Amfani da shuɗaɗɗen lokaci na farko: A cikin wannan salon, kuskure ne amfani da kowanne lokaci indai ba shuɗaɗɗen lokaci ba. Irin wannan salon ana bayar da labarin abin da ya riga ya faru ya wuce ne, don haka dole ne labarin ya ƙunshi shuɗaɗɗen lokaci na farko a yayin labarta shi.

Abin da nake nufi shi ne, wataƙila tauraron yana bayar da labarin tsohuwar soyayyarsa ne, ko kuma labarin wani ƙalubale da ya taɓa fuskanta, ko labarin wata tafiya da ya yi da sauransu. Don haka wajen bayar da labarin dole marubuci ya riƙa saƙa labarin a kan shuɗaɗɗen lokaci. Misali;

Ranar da al’amarin zai faru, gabaɗaya sai na tashi duk jikina babu ƙwari, ashe alhinin mutuwarta ne ya fara taɓa ni tun daga lokacin ban sani ba.’

A nan “Ranar da al’amarin zai faru” da mai ba da labarin ya yi amfani da ita, shi yake nuna mana cewa al’amarin ya riga ya faru har ya wuce, wato dai labari kawai yake ba mu. Sannan muna da masaniyar ya san labarin tun daga farkonsa har ƙarshen shi a ransa, don haka yana ba mu labarin irin alhinin da ya tsinci kansa tun kafin ya samu labarin mutuwarta ne. Amma kuskure ne marubucin da yake tsaka da amfani da wannan salo sai kuma a ji ya ce;

Yau na tashi gabaɗaya jikina babu ƙwari, ashe alhinin mutuwarta ne ya fara taɓani tun daga lokacin ban sani ba.’

Kalmar yau da ya saka ita take nuna mana cewa ba labarin abin da ya shuɗe yake ba mu ba, yana ba mu labarin abin da yake faruwa ne, wato Lokaci Na Yanzu Na farko kenan. Shi kuma labarin da yake faruwa a lokacin ba a sanin me zai faru a gaba, idan haka ne yaushe har ya san cewa za ta mutu bayan tashin shi kenan?

Amfani da abin da aka ji aka gani kaɗai: A cikin irin wannan salon, iya abin da mai bayar da labarin ya ji ko yake ji, ya gani ko yake gani yake da ikon bayar da labarinsa. Misali;

Da na je ƙofar gidansu na tarar tuni jama’a sun taru, wasu sun yi alwala wasu suna kan yi, da alamu jira ake yi a gama shirya ta a yi mata salla.

Wannan duk abin da yake iya gani ne, idan ya ba da labarin shi babu matsala. Matsalar ita ce a ji shi a ƙofar gida amma yana suffanta irin yawan mutanen da suke cikin gidan. Misali kamar ya ce:

Amma duk da yawan waɗannan mutanen ba su kai na cikin gidansu yawa ba, acikin gidansu fa babu masaka tsinke, duk inda ka hanga mata ne sai koke-koke suke yi. Ita kuwa mahaifiyarta tana can a sume ana watsa mata ruwa ko za ta farfaɗo.

Ta yaya ya san yawan mutanen gidan shi da yake ƙofar gida? Ta yaya ya san cewa mahaifiyarta ta suma ana ta watsa mata ruwa? A irin wannan salo kuskure ne babba faɗar abin da ba ka gani ko ka ji ba. To amma akwai wata dabara da ake yi idan ana so a bayyana me yake faruwa a cikin gidan, don haka bari mu ɗauki misalin da muka yi amfani da shi mu ɗan yi masa kwaskwarima.

Sai daga baya ake faɗa mini cewa ashe wai duk da yawan waɗannan mutanen na ƙofar gida ba su kai na cikin gidansu yawa ba, acikin gidansu wai babu masaka tsinke, duk inda ka hanga mata ne sai koke-koke suke yi. Ita kuwa mahaifiyarta ma aka ce suma ta yi ake ta watsa mata ruwa sannan ta farfaɗo.

Idan mun duba duk saƙo ɗaya aka isar, kuma babu wanda zai tuhume ka da cewa ya aka yi ka sani.

Shiga zuciyar wani: A salon tauraro cikin fage haramun ne ga marubuci ya riƙa shiga zuciyar wani ya faɗi me ta ƙunsa, ko da kuwa a kujera ɗaya suke zaune. Misali:

Kamar kullum, da zan fita na ɗakko kuɗi Naira ɗari biyar ta cefane na ba wa Rabi, muka haɗa ido da ita a ranta tana cewa ‘Ko ka fita babu wani abinci da zan girka, na samu kuɗin zubin adashe ne kawai.

Ta yaya ya san abin da yake zuciyarta? Yin hakan kuskure ne, sai dai shi ma a yi amfani da ‘yan dabaru irin wancan. Bari mu sake ɗaukar misalin.

Kamar kullum, da zan fita na ɗakko kuɗi Naira ɗari biyar ta cefane na ba wa Rabi, muka haɗa ido da ita ina nazarin ta, duk da dai ban san abin da yake ranta ba amma ina zargin tunani take yi na fita ta je ta biya kuɗin adashe ta ƙi yi mana girki kamar yadda ta saba.

A nan ma idan marubuci ya yi amfani da wannan dabarar zai isar da saƙonsa ga manazarci, sannan babu wanda zai tuhume shi da saɓa ƙa’ida.

Za mu dakata a nan, amma za ku iya ci gaba a maƙala ta gaba inda muka kawo karshen bayanin a wannan maudu’i.

2 thoughts on “Salon bayar da labari da salon ginin labari 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page