Skip to content

Salon bayar da labari da salon ginin labari 2

A maƙalarmu da ta gabata, mun tsaya da bayani ne a kan salon bayar da labari, inda muka ce salon bayar da labari ya kasu zuwa gida biyu. Akwai salon tauraro cikin fage, da kuma salon tauraro wajen fage.

Mun bayyana yadda salon bayar da labari na tauraro cikin fage, wato labarin da ake bayarwa ta bakin shi tauraron yake. Sannan mun fara jero wasu ƙa’idoji da muka ce ana kula da su a cikin irin salon, waɗanda da su ne yanzu za mu ɗora a wannan sabuwar maƙalar da amincewar Allah.

Iyakar da ta shafi shekaru: A wannan salon kuskure ne tauraro ya bayar da labarin abin da ya girme wa shekarunsa, da abin da bai girme wa shekarun nasa ba amma dai lokacin da abin ya faru yana jariri, ko yaro daga shekara ɗaya har zuwa shekara bakwai. Saboda yaro ba zai yiwu ya san me yake faruwa ba balle har ya iya riƙewa ya ba da labari, idan ma ya sani zai manta indai bai wuce shekaru bakwai ba.

Lokacin ina jariri na yi farinjini, don kuwa duk wanda ya gan ni sai ya ɗauke ni yana mini wasa, ga shi kuma dama kullum cikin tsafta nake.”   Irin wannan misalin kuskure ne kamar duk sauran misalan, sai dai shi ma a yi masa dabara, a nuna cewa labari aka ba wa tauraron, misali:

An ce fa da ina yaro na yi farinjini, wai duk wanda ya gan ni sai ya ɗauke ni, saboda kullum tsatsaf nake.” Hakan ba kuskure ba ne tunda labari aka ba ka.

•Iyaka dangane da mutuwa: Kuskure mafi girma da za a samu a wannan salon bayar da labarin shi ne a ji shi mai bayarwar ya mutu. Babu yadda za a yi a irin wannan salon daga karshe a nuna tauraron labarin ya fadi ya mutu. Idan haka ta faru to wanene zai karasa labarin kenan? Idan kuma labarin ya je har ƙarshe ta yaya aka yi matacce ya ba da labarin?

Sai dai kamar dukkannin misalan baya, ana iya yin wata dabarar a kashe tauraron. Misali ana iya cewa shi tauraron ya gama rubuta labarin nasa ne gabaɗaya a wani littafi, don haka littafin nasa wani ya karanta ya samu labarinsa tun kafin ya mutu, wataƙila ma labarin dalilin mutuwarsa ko kashe kansa labarin ya ƙunsa.

Haka nan idan ma ba a gama labarin ba to marubuci yana iya yin dabara ya ɗora alhakin ƙarasa labarin a kan shi wanda ya karanta labarin, ta yadda zai yi ta bibiyar ‘yan’uwa da abokai da kuma waɗanda labarin ya shafa don haɗa kan ƙarshen labarin.

Da wannan kuma muka kawo ƙarshen dokokin da za mu tattauna game da salon bayar da labari a ƙarƙashin salon tauraro cikin fage. Yanzu kuma za mu matsa zuwa gaba insha Allahu.

Salon ginin labari

Wannan salon ya ƙunshi tubalan gini har guda shida kamar haka:

• Miƙaƙƙen salo

• Salo tafiyar kura

• Sassauƙan salo

• Salo ɗanmagori

• Ragon salo

• Salo mai karsashi

Za mu ɗauki kowanne ɗaya bayan ɗaya mu tattauna insha Allah.

• Miƙaƙƙen salo: Tun daga yanayin sunan wannan salo muna iya hasaso alƙiblarsa, saboda duk abin da aka ce miƙaƙƙe to a miƙe yake samɓal kamar rula babu wani bauɗiya ko kwana-kwana. Labari ya kan amsa wannan suna ne idan ya zamana babu kwan gaba kwan baya, haka nan babu cukurkudewar zarurruka a cikinsa, kenan dai an ɗakko shi daga farkon samuwarsa zuwa ƙarshen tiƙewarsa. Kamar daga haihuwar tauraron zuwa mutuwarsa ko kuma wani wuri da aka ƙarƙare labarin.

Mafi yawan labaran da aka gina su da miƙaƙƙen salo ana ɗora labarin ne kai-tsaye a kan tauraron labarin, wato shi yake kwashe kaso casa’in da doriya na labarin.

• Salo tafiyar kura: Shi kuma wannan salon kishiyar salon farko ne, a miƙaƙƙen salo mun ce ana farawa ne daga farkon labari, shi kuma wannan salon ana fara labari ne daga tsakiya ko karshe sannan a koma farko sai a sake komawa karshe. Wato labarin zai tafi ne kamar yadda kura take tafiya.

An ce kura ba ta tafiya kaitsaye, sai ta yi ta kwana-kwana. Idan za ta je gabas sai ta fara yin kudu sannan ta dawo yamma sannan ta koma arewa, daga nan sai ta yi gabas. To shi ma rubutu mai irin wannan salon na tafiyar kura haka ake saƙa zararrukansa ta hanyar yin wasa da hankalin mai karatu, sai an yi gaba da tunaninsa kamar za a kai shi gabas, sai a dawo da shi yamma a ba shi wani labarin da ya faru kafin wanda ake kan ba shi. Wannan salon ya fi kowanne salo tasiri wajen rike mai karatu musamman idan salon ya haɗu da gwani.

• Sassauƙan salo: Shi ma wannan salon daga sunansa ana iya fahimtar hanyar da ya bi, irin wannan salon shi ne salon da aka yi amfani da sassauƙar Hausa da zubi da tsari, maganganun taurari da ayyukansu, ta yadda makaranci ba zai sha wata wahala ba wajen fahimtar yadda ginin labarin yake. Yawancin irin wannan salon labarin, manazarci mai hikima yana iya hasaso abin da ya ƙunsa, wanda hakan yana daga cikin raunin labari a iya hasaso abin da ya ƙunsa.

• Salo ɗanmagori: Kamar yadda muka sani idan an ce ‘Ɗanmagori’ shi ne mai wasa kansa da kansa, to shi ma wannan salo kwatankwacin hakan ne domin dai marubuci ne da kansa yake fitowa a matsayin ɗaya daga cikin jaruman labarin ya yi ta ba ka labarin abubuwan da suka faru a kansa, wanda kuma da cikakken sunansa yake amfani. Misalin irin labari mai wannan salo akwai labarin Ganɗoki   na Bello Kagara, Ruwan Bagaja   na Abubakar Imam ko labarin Kukan Jini   nawa da sauransu.

• Ragon salo: Shi wannan salon shi ne salo mai gundura wanda idan aka yi amfani da shi da kyar makaranci yake iya karanta littafin yayin da wani makarancin ma da ya fara yake ajiyewa. Yawancin abubuwan da suke mayar da salo ya zama rago sun hada da; yadda marubuci zai yi ta ƙago masifu yana lafta wa jaruminsa ba tare da jarumin ya yi wani kuskure ba, ƙaga abubuwan da ba za su taɓa iya faruwa ba da sauransu.

• Salo mai karsashi: Wannan wani salo ne da ake amfani da kalmomi na azanci da gwanintar harshe cike da barkwanci, ko wasu kalmomi na nishaɗi da kan saka karsashi da tsayawa a ran mai karatu ta yadda zai riƙa jin yana so ya maimaila labarin saboda yanayin yadda aka bayar da shi, musamman wajen kwatantawa, siffantawa da kamantawa. Karatun labari mai irin wannan salon yana sanya nutsuwa da son maimaita karanta littafin.

Abin lura: Ko ma dai wani irin salo marubuci ya yi amfani da shi ana so ya kula sosai ta yadda zai riƙa goce wa hasashe ko iya hakaito ƙarshen labarin daga manazarta. Daga cikin manyan rauni ko nakasu da yake hana labari armashi ko samun maki masu yawa a cikin gasa shi ne iya fahimtar akalar labarin na abin da zai faru a gaba.

Wannan matsalar ba ‘yar ƙarama ba ce, ‘kamar yadda idan uwargida ta yi laɓe a ɗakin amarya ta ji hirar da kuka yi idan ita ma ka je ɗakinta za ka yi mata irin wannan hirar ba za ka burge ta ba haka shi ma wanda yake iya hakaito ƙarshen labarinka ba za ka burge shi ba.’ Wani lokacin ma wasu na iya jefar da labarin su haƙura da karanta shi ba tare da sun wani damu ba, ba don komai ba sai don za su iya ƙarasawa kansu labarin a zuciyarsu.

Amma idan ya zamana labarinka yana zuwa da saɓanin hasashen mai karatu, zai zamana kamar wanda ya yi tunanin za ka ba shi naira ɗari ne kai kuma sai ka ba shi dubu ɗaya. Ko kuma ya tsammaci ka kai shi yawan shaƙatawa kai kuma ka kai shi Madina. Zaka tarar ɗokinsa da ƙaunar shi ga labarin ninkuwa suke yi a duk shafin da ya buɗa.

Don haka yana da kyau matuƙa mu sani cewa wannan gaɓar tana kankaro mutuncin labari yadda ya kamata, musamman labarin gasa. Mu riƙa yin ƙoƙari matuƙa wajen ba wa makarantanmu ƙafa, ta yadda za su kasa fahimtar alƙiblarmu. Mu riƙa yin rubutu kamar faɗan ɗandambe mai hikima, wanda zai yi kamar zai naushi abokin dambensa da hannun dama sai ya sauya ya naushe shi da hannun hagu. Ko kuma labarin namu ya zama kamar gidan kurege, ta yadda sai an tsaya a bakin ƙofar shi ana yi masa hayaƙi da tunanin ya fito ta ƙofar za a ga ya faso wata ƙofar ta inda ba a zata ba ya gudu.

A nan za mu dakata, amma kuna iya karanta makala ta gaba akan hadakar salo sama da daya wajen samar da labari. Kamar kullum, ƙofar gyara, sharhi, ƙarin bayani ko tambaya a buɗe take.

1 thought on “Salon bayar da labari da salon ginin labari 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page