Skip to content

Hadakar salo sama da daya wajen samar da labari

Hadakar salo shi zamu tattauna a yau. A maƙalar da ta gabata ta dabarun rubutun labari, mun tsaya da bayani ne a kan salon bayar da labari, da kuma yadda marubuci zai riƙa yin rubutu cikin hikima ta yadda zai riƙa goce wa hasashen manazarcinsa wanda ka iya hakaito ƙarshen labarin ya rage masa armashi.

Mun bayyana yadda salon bayar da labari na tauraro cikin fage, wato labarin da ake bayarwa ta bakin shi tauraron yake, sannan mun bayyana dokoki da ƙa’idoji da muka ce ana kula da su a cikin shi irin wannan salon a yayin rubutu. Haka nan mun tattauna a kan salon bayar da labari na tauraro wajen fage, wanda shi ma mun bayyana irin dokoki da ƙa’idoji da ake so marubuci ya kula da su a yayin yin amfani da salon. Duba salon bayar da labari don tunawa sai ka ɗora.

A wannan maƙalar za mu tattauna ne a kan haɗakar salo sama da ɗaya wajen samar da labari. Ita ma wannan gaɓar tattaunawa ce mai muhimmanci, amma bari na yi mana wani kwatance ko bayanin da zai fito mana da muhimmancin da nake faɗa.

Na san za ku yarda da ni cewa idan aka samu ƙwararriyar mace a fagen girki, aka ba ta tsurar shinkafa aka ce ta dafa, za ta iya dafawa har shinkafar ta yi daɗi a ci cikin armashi. To amma yaya kuke tunanin abin zai zama idan ba a ba ta tsurar shinkafa ba aka haɗa mata da wani abin haɗin, kamar wake, ko doya, ko dankali, da su kifi da nama, da tumatir da kayan ganyaye da mai da sauransu aka ce ta haɗa da wannan shinkafar ta tashi girki? Na tabbata indai har ƙwararriyar ce girkin da za ta yi da kayan haɗin da yawa sai ya fi daɗi da burgewa a kan girkin tsurar shinkafa da za ta dafa.

To kamar haka ne labarin da aka saƙa shi da salo ɗaya tamkar shinkafar da aka dafa ta tsura ce, haka nan labarin da aka ƙayata shi da salo mabanbanta wajen gina shi tamkar shinkafar da aka haɗa ta da wake ko wani abin haɗin da nau’in su kifi ko nama da kayan ganye wajen girka ta ne. Idan mun iya hakaito fifikon a zukatanmu, to bari mu tafi kai tsaye zuwa gaɓar yadda ake haɗa mabanbanta salon ya ba da irin wannan armashin a labari.

Zan ɗakko mana wani labari mai suna Sawun Ɓarawo, wanda a cikin farkonsa nake so mu yi darasin namu na yau, don haka ga yadda labarin ya fara kamar haka:

SAWUN ƁARAWO

     ‘Na rubuta da manyan baƙi a saman littafin nawa daidai lokacin da na sake gyara zama irin na ɗalibin da ya gurfana a gaban malami don ɗaukar darasi, bambancinmu ɗaya da shi kawai ni ba a gaban kowa na gurfana ba, amma kuma ni ma zama nake yi na jiran tsammani. Lokaci-lokaci ina kai dubana zuwa bakin ƙofa don ganin shigowar Abbanmu da har zuwa lokacin bai dawo daga masallaci ba.

    A daidai lokacin ne kuma ita ma Fatima ta shigo ɗakin, na ɗaga kai muka haɗa ido sanadin da ya sa take yi mini dariya.

    “Kaiii… Young Barrister! Don zumuɗi har ka zo ka wani zauna kamar wanda zai ɗauki darasi?” Ta jefe ni da kalaman zolaya daidai lokacin da take ƙoƙarin samun wuri ta zauna. Ni ma murmushin na yi sannan na amsa ina kallon ta.

    “Ai darasin da ma na zo ɗauka tunda na san dole na ƙaru da wata hikimar ta tsofaffin hannu, kuma ke ma kin san ba zumuɗi ba ne ya kawo ni kawai dai so nake na ji wanda zai taka wannan sawun ɓarawon, don kuwa da alama kamar labarin zai yi daɗi shi ma…”

    “Ai zumuɗin kenan” Ita ma ta amsa bayan ta zauna.

    “Amma kuma ban ga laifinka ba fa, don kuwa ni ma kaina jikina yana ba ni kamar labarin zai yi daɗi sosai.”

    “Ato dai!” Na faɗi kana muka yi dariya gabaɗaya lokaci guda kuma muka mayar da kallonmu bakin ƙofar ɗakin tare da amsa sallamar Mahaifinmu da ya shigo a daidai lokacin shi da su Usman da suka dawo daga makaranta su ma. Ya kalle mu ya yi dariya ganin yadda gabaɗaya muke farin ciki da dawowarsa.

    “Ashe ku har kun zo kun zazzauna kuna jira na kenan?” Ya tambaye mu.

    “Ai ina sani na ƙi dawowa sai da na bari na yi sallar la’asar saboda labarin gaba mai ɗan tsaho ne, tazara tsakanin Azahar da La’asar ta yi mana kaɗan mu gama, kuma ba na so mu fara ba mu gama ba a kira salla mu tashi, shi ya sa ma na yi hakan.” Ya ƙare daidai lokacin da yake cire malum-malum ya samu wuri ya zauna.

    “Sai ku jira ni na ci abinci kenan!” ya faɗi daidai lokacin da ya ga Ummanmu ta shigo ɗauke da kayan abincinsa. Muka amsa da “To” kana muka ci gaba da hirarmu har zuwa lokacin da ya gama komai ya samu nutsuwa sannan ya nisa ya fara da cewa….

Kafin ya fara ɗin mu yi wani nazari. Idan kuka kalli wannan labari ya fara ne da salon Tauraro Cikin Fage, tunda labarin kaina nake bayarwa ni da ‘yan’uwana da mahaifina. A ɓangaren Salon Ginin Labari kuma za mu iya cewa Miƙaƙƙen Salo na ɗauka. To bari mu ƙara matsawa gaɓa ta gaba cikin labarin kuma ku ga sauyin da za a samu.

“Zare na farko da zan fara saƙa muku labarin da shi cikin tarin zararrukan labarin namu shi ne zaren wata hira tsakanin wasu marasa gaskiya biyu da suke waya kowannan su a sirrancen gudun kada wani ya gan su ko kuma ya ji abin da suke tattaunawa.

“Da wa nake magana?” Alhajin ya tambaya cikin wata irin murya da ta yi kama da irin muryar wanda aka tilasta wa yin magana.

“Ai ba za ka gane da wa kake magana ba yanzu tunda ka ci moriyar ganga ka watsar da korenta. Kuma ni ma da ma ba wai na kira ka ba ne don ka gane da wa kake magana, kawai dai na kira ka ne saboda in faɗa maka cewa na gane dukkan mugunnufinka na gaba a kan kisan Alhaji da kake shiryawa, kuma ko tantama kar ka yi sai na tarwatsa shi, ba zan ba ka damar cika ƙudirinka ba, ba zan bari ka kashe Alhaji ba. Don haka ka…”

“Kai dalla dakata malam! Sha-sha-sha kawai!” Alhajin ya katse masa zancen nasa ba wai don ya ƙarasa ba, lokaci guda kuma ya ɗora da cewa.

“Kai har kana da ƙwarin guiwar da za ka iya tsorata ni? Ko kuwa kana tunanin har ka yi ƙarfin da za ka iya karawa da ni? Kodayake ba zan hana ka yin abin da kake son yi ba, don kuwa wataƙila ajalinka ne ya matso kusa tunda na san ka fi kowa sanin wane ne ni idan aka shigo gonata. Don haka kawai ina ganin sai mu zuba tunda ga fili ga kuma dawakai!”

Mu sake dakatawa mu yi nazari, a wannan gaɓar kuma za ku ga labarin ya sauya zuwa salon Tauraro Wajen Fage, yanzu ba ni ne nake ba da labarin da lamirina ba, mahaifina ne yake ba da labarin wasu da lamirinsu. To ku sake biyo ni zuwa gaɓa ta gaba cikin labarin ku ga wata dabarar.

“…Abbanmu ya yi shiru a iyaka nan yana kallon mu, bayan ya yi murmushi ne kuma ya ce.

“Kodayake ba ta nan ya kamata na fara da labarin nan ba idan har ina son ya tafi a daidai, don haka ina ganin za mu jingine wannan gaɓar a nan ne, amma kuma kada ku damu za mu dawo mu biyo ta kanta a gaba nan ba da daɗewa ba.”

FARKO:

“Labarin sawun ɓarawo ya fara saƙuwa ne da safe wajen misalin ƙarfe goma na wata ranar Asabar cikin wani irin yanayi na sanyi da hazo da garin ya tashi da shi, kasancewar a lokacin ana cikin tsakiyar sanyi irin mai ratsa ƙashin nan, wanda hakan shi ne ya sa duk da ranar da ta fara yi amma dayawa cikin jama’a ba su fito ba suna cikin gida kwance cikin bargo a duƙunƙune.

To a daidai wannan lokacin ne kuma shi ɓarawon mai hikima ya cire sawunsa ya yi musanye da sawun wani ya laɓaɓa ya bi cikin hazo da sanyin da ya sauyawa gari yanayi ba tare da wani ya gan shi ba ya ɓace ɓat!

Idan kun kula da wannan gaɓar kuma abubuwa biyu ta ƙunsa. Na farko dai cikin hikima an yi wa mai karatu Tsakure, ko Somin Taɓi na abin da zai faru a gaba cikin labarin (wayar da alhaji da wani ke yi.) Na biyu kuma mun sauya daga miƙaƙƙen salon da muka faro labarin mun koma Salo Tafiyar Kura da kuma Salo Mai Karsashi. Kusan gabaɗaya da irin wannan salon na gina labarin Sawun Ɓarawo, wanda kuma yana ɗaya daga cikin labaraina da suka fi tara masoya saboda yadda salonsa yake da jan hankali.

Mu ɗan ƙara gaba kaɗan cikin labarin ku ji.

A wani katafaren asibiti ne na wani likita mai zaman kansa da ke wata unguwa ta masu yatsu da yawa mai gadin da yake aiki a wannan lokacin ya janye ƙaton kyauren (Gate) ɗin asibitin wata tsaleliyar mota mai numfashi ta sulala cikin asibitin kamar yadda maciji yake sulalawa cikin raminsa, sannu a hankali kamar ba za ta tafi ba har zuwa cikin harabar asibitin, wani fili da aka tanada don ajiye motoci.

A nan wurin farar motar Jeep ɗin ta samu matsuguni tare da daidaita sawunta kamar yadda sauran motocin wurin suka daidaita nasu, bayan kamar mintina uku zuwa huɗu kuma mamallakinta wanda ya yi anko da kalarta cikin wata lallausar farar shadda ɗinkin malum-malum da ta sha wani aiki irin na sarauta mai launin toka, kan shi sanye da wata farar hula damanga ya fito yana mai saka wani farin tabarau a idonsa, hannunsa na dama kuma yana riƙe da wata baƙar leda wacce take cike da kaya, a ɓangare guda kuma kamar wanda yake nazarin cikin harabar asibitin.

Ya saka hannu ya mayar da murfin ƙofar motar ya rufe tare da danna linzamin da ke hannunsa (wato remote), motar ta ɗan yi wani ƙara, lokaci guda kuma ya juya ya nufi hanyar da za ta sada shi da ainahin cikin asibitin wurin da ake kwantar da mutane, farin takalmi saucikin da ke ƙafarsa yana haɗuwa da daɓen kwalbar tiles ɗin asibitin yana ba da wata ƙara ‘ Ƙwas! Ƙwas! Ƙwas!”

“Kun san me ya zo yi asibitin kuwa?” Cewar Abbanmu bayan ya ɗan yi shiru yana nazarin fuskokinmu, yayin da mu kuma muka gyaɗa kai alamar a’a damar da ya samu kenan ya ci gaba da cewa.

“Ya je duba wani amininsa ne da aka kwantar a asibitin…”

Irin wannan salon yana da wasu fa’idoji da ya kamata mu tattauna su. Amma kafin sannan ƙofar gyara, sharhi, tambaya ko ƙarin bayani a buɗe take.

1 thought on “Hadakar salo sama da daya wajen samar da labari”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page