Skip to content

Sharhin littafin ‘Dama Sun Fada Mini’ na Jibrin Adamu Jibrin

Sunan Littafi: Dama Sun Fada Mini

Marubici: Jibrin Adamu Jibrin

Kamfanin Ɗab’i: A. A. Bature Publishers

Yawan Shafuka: 200

Shekarar Bugu: 2020 an sake bugawa 2021

Mai Sharhi: Muttaka A. Hassan (Abu Ahmad)

Manufar Sharhi: Bunƙasa harshen Hausa da ciyar da adabi gaba.

Dangane da marubucin

An haife shi a Jos, cikin Nassarawa, unguwar ‘yan shanu, a shekara ta dubu ɗaya da ɗari tara da casa’in (1990) miladiyya. Ya fara karatun firamare a Saint Michael Primary School, Jos. Daga bisani ya dawo jihar Kano garin Rano inda ya ci gaba da karatu a Special Primary Rano, ya kammala a shekarar 2004. Daga nan kuma ya wuce babbar Sakandire G.S.S Rano inda ya yi karatu a ɓangaren kimiyya (Science), ya kammala a 2010. Daga nan ya shiga Kwalejin Ilimi Da Shari’a ta Malam Aminu Kano (Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies) in da ya samu kwalin diploma a bangaren Shari’a (Law). Daga kuma nan bai ci gaba da karatu ba. Yana zaune a garin Rano tare da matarsa da ɗiyarsu ɗaya.

Ya fara rubutu a shekarar 2007, in da ya fara da labarun yaƙi. Daga bisani ya ajiye ya dawo rubutun soyayya, zamantakewa, da gwagwarmayar rayuwa musamman ɓangaren Shari’a. Ya rubuta littafai da dama kamar: Shari’a Saɓanin Hankali, Kukan Jini, Tufkar Makaho, Dama Sun Faɗa Mini da sauransu. Ya samu nasarar lashe gasanni da dama.

Labari

Zainab da Aliyu ma’aurata ne da suke matuƙar ƙaunar juna, soyayyar da suke yi wa juna abar sha’awa ce ga kowa, musamman yadda suke sadaukarwa da juna lamuransu. Lokacin da Zainab ta samu ciki, Aliyu ya sake ninka kulawar da yake ba ta. Koda yake bayan cikin ya tsufa ne tauraruwar matsalar rayuwarsu ta haska, in da Zainab take yawan munanan mafarkai da wasu halittu masu muni suna mata barazanar ta haihu ta ba su jaririnta su sha jininsa.

Watarana tana kwance a jikin mijinta sai ta yi mummunan mafarki, wai tana naƙuda dodanni sun zagayeta suna tanɗar baki. A lokacin da jaririn ya diro duniya suka daka masa wawa, sai ta farka a razane. A nan ne mijinta ya tambaye ta abin da ya tashi hankalinta, ta sanar da shi. Aikuwa sai mijin ya yi ɓarin zance ya furta “DAMA SUN FAƊA MINI.” Haka ya sa ta tsare shi da tambayoyin waɗanda suka faɗa masa, da abin da suka faɗa masa; sai dai ba ta samu amsa ba.

Bayan wasu ‘yan kwanaki aka kuma, wai mace ta haifi mace, domin kuwa mafarki ta sake yi mai ban tsoro, da ta sanar da Aliyu ya sake furta DAMA SUN FADA MINI. Daga nan ne mijinta ya fara zama abin gudunta, domin kuwa gani take yi shi ma ɗan ƙungiyar shan jini ne. Musamman da yake ya ƙi ba ta amsar tambayoyinta, bugu da ƙari a cikin munanan mafarkan nata tana ganin rubutu a bayan rigar dodonni, sai kuma ta ji mijin nata ya faɗi wannan rubutun na rigar. Daga kuma nan ne ta yi ta tuno irin tarin dukiyar da yake da ita, da yadda ya kulle wani ɗaki ba ya bari a buɗe, da yadda ta tsinci saƙon kar ta kwana a wayarsa ana sanar da shi “Iya buhun mutane biyar aka samu.”

Hakan ya sa ta gudu ta koma gidan iyayenta, su kuma suka ce ko dai ya amsa tambayoyinsu ko ya sake ta. Ganin ya gaza aiwatar da ko ɗaya suka maka shi a kotu.

Jigo

Ko iya ɗan abin da muka tsakuro a labarin aka karanta za a fahimci babban jigon labarin shi ne zargi, ko kuma a ce zato, ko dai tuhuma. Domin dai tun daga haihuwar labarin (Mabuɗi) zuwa girmansa za mu iske an fara ne da zargi, sannan sarƙaƙiyar ko sa-toka-sa-katsin da aka yi ta yi duka dai a kan zargi ne. Mu fara da inda aka buɗe labarin a shafi na huɗu, tun a sakin layi na farko marubucin ya ce “….Zainab wacce take ZARGIN mijinta Aliyu da zama ɗan ƙungiyar asiri….Aliyu wanda shi kuma ya fitittike cewa shi ba ɗan ƙungiyar asiri ba ne….iyayen Zainab da suka maka Aliyu a kotu cewa ‘yarsu ba za ta zauna ɗan shan jini ba….” A nan za mu gane Zainab na zargin mijinta, shi ya kasa kare kansa, zuwa kotu da iyayenta suka yi kuwa tuhumarsa ce ta kai su. Idan an warware jigon za a iske yana ɗauke da wasu ƙananan jigogi waɗanda suka taru suka samar da darrusa da dama kamar:

  • Shafi na 167, sakin layi na 3 marubucin ya kawo mana faɗar Annabi (S.a.w) cewa:  “Al-zanna zanbun, walau kana haƙƙun” Watau dai ‘zato zunubi ne, ko da kuwa ya kasance gaskiya.”
  • Haka nan a shafi na 120, sakin layi na 2, nadamar Zainab ta fara in da take zance a zuciyarta cewa: ‘Shi ne ni kuma na ɗauka huhu na mutane ake nufi na ƙara fusata Aliyuna?’ A nan za mu fahimci matar da take zargin mijinta da tara buhun mutane har biyar, ta kuma gano huhun goro ake nufi, har ta yi wannan zancen a zuci, lallai nadamar zargin da ta yi ta riske ta.
  • Shafi na 167 sakin layi na huɗu an nuna alkali na jawabi da cewa: “…mu guji yanke hukunci kai tsaye ba tare da bincike ba…” A nan littafin yana koyar da mu yana da kyau kafin yanke wa mutum hukunci, mu yi bincike.
  • “….duk in da muka haɗu da wani aljani ko boka ko mai sihiri, to kuwa mu yi takatsantsan da shi kada mu kuskura mu yarda da su….” Shafi na 168 sakin layi na 2. Wannan darasi ne muhimmi, domin dai malamai ma suna ta bayani makamancin wannan. Wato sau tari aljani kan shigo rayuwar mutum ta siga mai kyau (ya nuna zai taimaka maka da magani ko wani abin duniya) sai tafiya ta yi nisa sai su yi ta ɓatar da mutum a hankali.
  • Wani darasi kuma da littafin ya zo da shi shi ne kuskuren da mata suke yi na binciken wayar mazajensu. In da matsalar take, matsawar mutum ya ɗarsa zargi a zuciyarsa, to yana da wahalar gaske shaiɗan bai kawo masa ɗauki ya jefo wani abu da zai ɗarsa masa wasu-wasi tare da ƙarfafa masa gwiwa a kan lallai abin da yake zargi gaskiya ne ba. Kamar dai yadda ya faru a shafi na 52-53, Zainab ta ɗauki wayar Aliyu saboda zargin wata tana turo masa saƙon soyayya, sai kuma ta ci karo da batun da ya rikitata har ma ya kusa zama sanadiyyar rugujewar aurensu.
  • Har wa yau, an nusar da mu sakacin ƙin riƙe addu’a, kamar dai yadda ya faru ga mahaifan Aliyu. Da kuma muhimmancin addu’a kamar yadda ya faru a ƙarshe, an haifi jaririn, ‘yan ƙungiyar asirin sun zo amma addu’a ta zama katanga tsakaninsu.
  • Sannan kuma, an nusar da mu ko da mun yi addu’a sai mun zamto masu haƙuri. Domin dai ba nan take da an yi addu’a za a karɓa ba, saboda ta yiwu an jinkirta tabbatuwar addu’ar ne saboda jarabtar imaninmu. Kamar dai yadda ta faru ga Aliyu, tare da cewa ya kasance mai yawan ibada, sadaka, kyauta da kyawawan halaye, amma matsalolinsa ba su yanke lokaci ɗaya ba.

Salo da sarrafa harshe

Idan har akwai abin da ya mayar da littafin zakaran gwajin dafi, to babu kamar salo da sarrafa harshe. Domin an yi amfani da salalai iri-iri kaɗan daga ciki a iya cewa akwai tsoho da kuma sabon salo. Misali:

• Salon Koyarwa: An yi amfani da wannan salo wurin koyar da darasin da ya shafi kimiyya da fasaha, duba shafi na 5-6, 21-22, 31-33, 57-60 da sauransu. Duka idan mutum ya bibiyi shafukan zai ga yadda aka koyar da kimiyya da fasaha a sassauƙan harshe.

• Salo Mai Armashi: An yi amfani da salo mai matuƙar jan hankali, ta hanyar amfani da wasu gwala-gwalan kalmomi da suka yi wa rubutun ado tare da samar da armashi, ta yadda mutum yana karantawa yana ƙara jin daɗin labarin. Har’ilayau an yi amfani da salon magana mai kama tunani matuƙa.

• Sarrafa Harshe: A nan ma marubucin ya kwarzanta harshe matuƙa, ta yadda ya riƙa amfani da azanci, da hikima, da kuma tarin karin magana da suka doshi hamsin. Su kansu karin maganar da aka yi amfani da su sun kasu aji-aji, idan an taƙaice dai a iya cewa an yi amfani da sababbi da kuma tsofaffi, ta yadda marubucin ya riƙa yi wa wasu karin maganar gyaran fuska suna komawa sababbi. Misali: “Mara gaskiya ko a kan doki yake, sai ya yi ɗingishi.” (Shafi na 14) sakin layi na 3, da sauransu.

Zubi da tsari

An tsara labarin tare da kasa shi zuwa babi-babi, daga na ɗaya zuwa na goma shabiyar, sannan kowane babi yana ɗauke da kannun labari. A taƙaice dai, ya samu kyakkyawan zubi da tsari, don idan muka koma muka duba jigon labarin (zargi) za mu iske tun daga mabuɗi an yi wa jigon shimfiɗa a kan tabarma mai kyau. Ta yadda za mu ga tun daga farko har ƙarshe kowace jumla na ƙarfafar ‘yar’uwarta ne, watau an samu cikakkiyar yarjejeniyar kalmomi wurin gina labarin. Misali: Babi na 1, Aliyu ya yi furucin “Dama Sun Faɗa Mini” (kuma sunan babin ne) furucin Aliyu ya jawo zargin Zainab. Da aka shiga babi na biyu mai suna AN KUMA, IN JI ƊAN SHAYI DA AKA YANKE SHI A GABA. A nan ma dai zargin ne ya tsananta, domin Aliyu ne ya kuma furta dama an faɗa masa! Haka ma yake a babi na 4 mai suna GARIN TONE-TONEN KAZA….a nan an bayyana yadda garin binciken wayar miji Zainab ta binciko abin da ya tsananta zarginta har ta yi yaji. Abin burgewa, da ta yi yaji kamar marubucin ya san mai karatu zai ce me ya faru a gaba sai ya ba wa abin da ke biye da shi suna DUK GIRMAN GONA TANA DA KUNYAR ƘARSHE, watau dai ta tabbata ma’auratan sun rabu. To haka ya yi ta faruwa daga farko har ƙarshe, watau kowane babi, na ƙarfafar na baya (ko a ce kowace jumla na yi wa wata zagi) har dai zuwa lokacin da matsalar ta kai kololuwa, da kuma yadda aka sauko.

• Hange: An yi amfani da dabarar hange, an hasko wa mai karatu wani abu da zai faru a labarin tun kafin a zo kansa, watau dai an lasa masa zuma a baki. Misali: “Zainab wacce take zargin mijinta Aliyu da zama ɗan ƙungiyar asirin da ya bayar da abin da zata haifa ga ƙungiyar tasu, Aliyu wanda shi kuma ya fitittike cewa shi ba ɗan ƙungiyar asiri ba ne, sai iyayen Zainab da suka maka Aliyu a kotu cewa ‘yarsu ba za ta zauna da ɗan shan jini ba, da kuma Alƙali da muƙarrabansa da mu kanmu ‘yan kallo wanda da mu aka kawo ƙarshen tirka-tirkar.” (Shafi na 4)

• Waiwaye: Harwayau, ana cikin tafiya sai aka dawo baya aka tuna wa mai karatu wani abu da ya faru a littafin, sannan aka yi gaba. Misali: “Huhu ɗaurin goro yake nufi kenan?” Ta tambayi kanta cikin girgiza kai, lokaci guda kuma wata ƙwaƙwalwarta mai adana shuɗaɗɗun abubuwa ta danna mata tariyar baya ta mayar da ita  zuwa kan saƙon kartakwanan da ta karanta a cikin wayar Aliyu, wanda yana ɗaya daga cikin dalilan da suka sa ta ƙara tsananta zarginta gare shi.

‘Mai gida ba a samu wannan huhun duka ba. Na mutum biyar kawai aka samu.” Ta tuno yadda sakon yake a rubuce cikin wayar salular ta Aliyu. (Shafi na 119) sakin layi na 3 da na 4.

• Baɗoki Na Gaske: “Na je kallon rikicin tun wancan satin ina jira na koma wani satin na ga yadda za ta kaya kamar yadda Alƙalin ya ce zai ci gaba da sauraron ƙarar. Sai da ka yi magana ka ankarar da ni ashe fa kusan matsala ɗaya ce ta haifar da shi, ga shi aure yana shirin mutuwa a sanadinsa….” (Shafi na 7) sakin layin na farko. Tabbas aure ya kusa mutuwa, domin dai sai da ta yi yaji, kuma iyayenta suka goyi bayanta.

• Baɗoki Na Giri: “Shi ke nan Iman ki je gida ki tona min asiri kamar yadda kike so, ki je gida ki faɗa wa Umma da Baba cewa ni ɗan mafiya ne kamar yadda kike zargi. Sai dai ina so ki sani cewa kamar yadda nake roƙon ki akan kar ki tafi gidan ku yanzu, haka ke ma watarana za ki zo ki roƙe ni akan ki dawo ɗakin ki bayan kin ƙaryata kanki cewa ni ba ɗan mafiya ba ne, daidai lokacin da ni kuma ba ni da buƙatarki, wataƙila ma na nemo wacce za ta yarda da ni za ta iya rufa min asiri a cikin kowane hali.” (Shafi na 68).

Tare da cewa ta tafi gidan nasu, bayan matsalar ta warware kuma ba ta roƙe shi ba (kamar yadda aka faɗa a shafin na 68) sannan bai nuna ba ya buƙatarta ba, hasalima ya dawo da ita ne saboda yana ƙaunarta.

• Ɗarsau Na Tsoro: A wurare da dama an yi amfani da wannan dabara, inda aka riƙa dasa wa mai karatu tsoro. Misali: “Zainaaaaaab.! Zainaaaaaaab.!! Zainaaaaaaab.!!!… Sai kin ba mu ɗan da ke cikinkiiii…” Maganar su ta fizgi hankalinta gami da sake dugunzuma tunaninta, sai a lokacin ta ga ashe gaf suke da ƙarasowa inda take suna masu ɗaga hannayensu masu ɗauke da farata cakar-cakar kamar takobi. (Shafi na 10) da saura a wasu shafukan.

• Ɗarsau Na Al’ajabi: “Murad.! Me ya faru?” Zainab ta tambaye shi tana mai ƙara yin nazarin shi ganin yadda a cikin ƙanƙanin lokaci yanayin shi ya sauya. “Dama sun faɗa min” ya ambata hakan daidai lokacin da ya goya hannayen shi a baya da alamar ƙololuwar damuwa a tare da shi. (Shafi na 13). A nan an ɗarsa wa mai karatu al’ajabi, a ce mata ta yi mafarki wasu dodonni na binta suna so ta haifi jariri su shanye jininsa, ta farka a razane ta labarta wa mijin, shi kuma ya ce dama sun faɗa masa!

• Darsau Na Mamaki: “Ban ga riba ba wajen faɗa miki su waye IZAGA kamar yadda ban ga abin da yin hakan zai amfana mana ba sai dai ma ya jawo mana matsala….” (Shafi na 65)

• Ɗarsau Na Murna: “Nan fa kowa ya shiga jandal cikin gode wa Ubangiji tare da ƙara gasgata ƙarfin addu’a da ƙarfin Allah wanda ya fi na kowa….” (Shafi na 190) sakin layi na farko.

• Hoton Zuci: An yi ƙoƙari an samar da hoton zuci a wurare da dama, ta yadda mai karatu zai riƙa ji tamkar yana kallon abin a zahiri. Misali “…kamar yadda ƙudaje ke bin mushen da ke fitar da tiririn wari haka suke binta, hangamemen bakinsu mai haƙora cako-cako da za su yi saurin tuna maka da bakin manjagara ko tarko. Wani irin baƙin jini yana falala daga bakin nasu babu kyan gani, duk ya ɓata ilahirin jikinsu tun daga kan wuya har ƙirjinsu irin yadda yaro mai tumbudi ko yoyon baki kan yi da gaban rigarsa.” (Shafi na 9 da sauransu)

Tauraro

Babban tauraron labarin shi ne Aliyu, mijin Zainab. Shi ne wanda duk inda aka je aka dawo matsalolin shi suke yi wa zobe. A iya cewa matarsa Zainab ita ganin matsalolin take muraran, amma bisa al’ada inda duk matsalar mata ta kai ta kawo mijinta shi zai ɗauke matsalar. Musamman ma shi Aliyu da ya kasance a wani yanayi mai kama da gaba zaki, baya ɓauna, hagu da dama kuma sayaki da kura, babu wurin da zai jefa kansa. E mana, matarsa ita ce za ta iya zama yayyafin da zai sanyaya damuwarsa, amma kuma sai ya kasance ita ce sawun farko a cikin masu zarginsa.

Halayen taurarin labarin

  • Farawa da babban tauraro Aliyu. Matashi ne mai shekaru 32-33, kyakkyawa ne gwanin ƙawa. Mai arziki ne, yana da yawan kyauta da ibada. Bugu da ƙari mutum ne mai matuƙar farin jini. Shi ya sa kowa (maza da mata) ke son mu’amala da shi.
  • Zainab, kyakkyawa ce, mai kyawawan ɗabi’u, hasalima da kyawawan halayenta ta saye zuciyar Aliyu har ya zaɓe ta a matsayin matar aure, suka yi aure. Babbar matsalarta tana da kishi mai tsanani, wanda sai da ya haifar mata da nadama.
  • Khadija, buduruwar da dashen son Aliyu ke dawainiya da ita. Makaranta ɗaya suke karatu, don haka koda yaushe take ƙoƙarin raɓarsa.
  • Ibrahim (mahaifin Aliyu) dattijon da aka laƙabawa maita shi da matarsa, kasancewar sun taso da wani irin baƙin jini da suka rasa dalilinsa. Inda duk suka raba babu sa’a tamkar beguwa. Don haka ya kasance babu abin da suke buri tamkar rabuwa da baƙin jinin da ke bibiyarsu.

Nagartar littafin

Babu buƙatar sai an yi dogon tsokaci a kan nagartar wannan littafi. Domin dai nagartarsa ce ta sa ya zamto zakara a mataki na farko a gasar Aliyu Muhammad Research Library Kaduna 2020, da kuma: Gasar Abubakar Imam Hausa Fiction Kano 2021.

A taƙaice dai, ko me aka faɗa na nagarta ko yabawa a kan wannan littafi, a iya cewa an dora ƙwarya ne bisa gurbinta. Domin idan marubucin ya durfafi bangaren kimiyya da fasaha sai ka rantse digirin digirgir ne da shi a wannan fannin. Haka ma da ya dawo bangaren Shari’a. Babu ko shakka wannan littafi zai taimaka wa ɗaliban da ke karatu a ɓangaren kimiyya, kamar dai yadda zai taimaki duk marubucin da ya karanta shi musamman shafi na 7, zai samu hujjojin riƙewa a hannu ya tunkari wanda duk ya ce da shi marubuci maƙaryaci ne!

Manazarta

Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph

Yahaya I.Y., da `Dangambo A. (1986). Jagoran Nazarin Hausa. Zaria: Madaba’ar Northern Nigeria Publishing Company Limited

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. Ibadan: University Press Plc

3 thoughts on “Sharhin littafin ‘Dama Sun Fada Mini’ na Jibrin Adamu Jibrin”

  1. Avatar

    Gsky nakaranta step by step
    Yayi Matuqar kayartar da ni Kuma harna himmatu da IN samu full enshi dannaji yarda xata kaya
    Allah yaqara basis👍

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page