Skip to content

Matsalar rubutun online shi ne babu amana – Sumayyah Abdulkadir (Takori)

A ci gaba da gudanar da shirin tattaunawa da Hikaya ke yi da shahararrun marubuta, a wannan karon ta tattauna da marubuciya Sumayyah Abdulƙadir Takori game da abubuwan da suka shafi rubutu da kuma rayuwar marubuciyar. Ga yadda hirar ta kasance:

Tambaya: Da farko dai za mu so jin cikakken sunanki da kuma taƙaitaccen tarihin rayuwarki in ba za ki damu ba.

Amsa: An haife ni a jihar Kano Unguwar Kabara, a ƙaramar hukumar Municipal, a shekara ta 1988.  Na halarci Fedwa Nursery School ta cikin FCE Kano, da kuma makarantun firamare guda biyu; Masallaci Special Primary school, da Gidan Galadima Primary School, wanda na kammala a shekara ta 1998. Daga nan na wuce ƙaramar Sakandire a ‘Izazuddeen Foundation Sani Mainagge, 1999-2001. Na halarci Special Education School, Kano 2001-2002; sai babbar sakandire a (WTC Kano) a shekarar 2002-2005.

A shekarar 2006 na wuce jami’ar Bayero na karanci Diploma a (Social Policy and Administration) 2006-2008. A 2012 na wuce karatun Digiri na farko a jami’ar Bayero inda na karanci ilmin zamantakewar ɗan’adam (Sociology), wanda na gama a shekarar 2015. Daga nan kuma na wuce digiri na biyu duk a jami’ar Bayero, inda na nazarci fannin ilmi na musamman (MA Ed Special Education). A halin yanzu ni ma’aikaciya ce ta gwamnatin tarayya, ƙarƙashin Federal Ministry of Humanitarian Affairs and Poverty Alleviation, a hukumar kula da masu buƙata ta musamman (National Commission for Persons with Disabilities).

Tambaya: A wacce shekara ki ka fara rubutu? Kuma me ya ja hankalinki har ki ka fara rubutun?

Amsa: Na fara rubutu a 2002. A makarantar Sakandire da Islamiyyarmu Zubairiyyah Islamiyya kawai na tsinci kaina cikin yawan rubutu da biro a littafi, amma ban taɓa tunanin bugawa ba. Na tashi na gan ni cikin yawan rubuce-rubuce a makaranta, na boko da na addini.

Hira da Sumayyah Abdulkadir Takori
Sumayyah Abdulkadir ke karbar shedar karramawa daga Aliyu Tanko, shugaban sashen Hausa na BBC a wurin taron Gasar Hikayata ta 2023.

Tambaya: Zuwa yanzun littattafai nawa ki ka rubuta? Kuma za mu so mu ji sunayensu.

Amsa: Daga lokacin zuwa yanzu na wallafa littafai guda 30 har wanda nake kan yi yanzu. Sun haɗa da:

 1. Siraɗin Rayuwa
 2. Tuna Baya Shine Roƙo
 3. Alheri
 4. Girma Ya Faɗi
 5. A Bari Ya Huce
 6. Alƙawari Bayan Rai
 7. Zuciyar Mutum Birninsa
 8. Wasan Ƙanin Miji
 9. Zumuntar Kenan
 10. Rayuwar Rayhana
 11. Kwana Sittin
 12. Sanadin Kenan
 13. Auren Kwangila
 14. Aalimah
 15. Masarautarmu
 16. Amana Ta
 17. Yiwa Kai Hisabi
 18. Babban Goro
 19. Yakanah
 20. Aure Ko Boko
 21. Hasna’u ‘Yar Najeriya
 22. Kulsum
 23. Fahhimah
 24. Na Huce
 25. Sakacin Waye?
 26. Raunin Zuciya
 27. Amani
 28. Hauwa-Kulu

Tambaya: Wanne littafi ki ka fi so a duk cikin litattafan da ki ka rubuta, kuma me ya sa?

Amsa: Duk cikinsu na fi son Rayuwar Rayhana, saboda na ba wa character ɗin littafin wasu daga cikin halayena.

Tambaya: Shin kina da Maigida ko Uwargida a harkar rubutu?

Amsa: Da kaina na dogara da kuma taimakon Ubangiji wurin rubutuna, sai taimakon iyayena da abokan arziƙina na jiki da na kan nemi gyara da shawarwarinsu.

Tambaya: Wanne littafi ne ki ka taɓa karantawa da ya fi burge ki?

Amsa: Suna da yawa musamman littafan Zainab Alƙali, William Shakespeare, Abubakar Gimba, kafin na fara karanta su Jiki Magayi, Budurwar Zuciya na Haj. Balaraba Ramat Yakubu, da sauran iyayenmu a rubutu.

Tambaya: Shin kin taɓa shiga wata gasa, idan eh ne amsar, shin ko kin taɓa yin nasara? Sannan wasu irin nasarori ki ka samu a rayuwa game da harkar rubutu?

Amsa: Ban taɓa shiga kowacce gasar marubuta ba a tsawon shekaru 20 da na kwashe ina rubutu sai a bana. Na shiga gasar Hikayata ta BBC Hausa, na yi nasarar fitowa a sahun fitattu 12 da labarina mai suna Duniyar Mafarkina.

Nasarorina a harkar rubutu ita ce soyayyar al’ummah. Idan Allah ya ba ka mutane ya gama ba ka komai. Alhmdulillah.

Tambaya: Idan za ki yi rubutu, shin ki kan tsara komai da komai ne kafin ki fara ko kuwa kai tsaye ki ke farawa?

Amsa: Gaskiya ba na tsarawa, hasalima ɗora biro nake kawai akan takarda da niyyar fara rubuta labari, amma da jigonsa a raina, sai in nutsu in saurari kwakwalwa da zuciyata. Sai in ji kamar a cikin kaina ana ce min rubuta kaza rubuta kaza. A idanuna kuma sai in ga majigin labarin na gilmawa daki-daki kamar a idona yake faruwa.

Tambaya: Ya ki ke yi idan wani tunani sabo ya zo miki game da wani rubutu na daban alhalin kina tsakiyar rubuta wani. Ki kan saki wancan ne ki yi wannan sabon ko kuma sai kin gama da wanda ki ka fara?

Amsa: Bana sakin wanda na fara sai dai na samu takarda na adana ita sabuwar basirar da ta kutso min a taƙaice, na ajiye a gefe. Sai na cigaba da wanda nake kan yi har sai na kai shi ƙarshe.

Tambaya: Ki kan ɗauki kamar tsawon wane lokaci kina bincike kafin ki fara rubutu, kuma daga nan yakan ɗauke ki tsawon wani lokaci kafin ki kammala rubutun littafin?

Amsa: Ina rubutun nake haɗawa da binciken ba rabasu nake yi ba. Misali, sai na zo kan abinda nake son sani a labari sai in dakata in bincika ko in tuntuɓi masana ilmin abin.

Yana ɗaukata a ƙalla watanni shida kafin na kammala labari ɗaya.

Tambaya: Wacce hanya ki ke bi wajen samun jigon labarinki?

Amsa: Ina samun jigon labaraina ne daga kintacen rayuwar da za ta iya faruwa a zahiri ta hanyar kallon rayuwar mutanen da nake tare da su.

Tambaya: Wacce hanya ki ke bi wajen fitar da halayen taurarinki tare da ba su sunan da ya dace da su?

Amsa: Ina ba wa taurarina halaye mabanbanta da ya dace da zubin labarin da na zaɓa, birni ko ƙauye, amma ban fiye basu halin ashararanci ba, ina dai basu halin masu zurfin ilmin boko wato halin ‘yan boko a yawancin lokuta.

Sunaye kuwa normal sunayenmu na Hausawa nake zaɓa in saka wa jarumai na, da laƙanin ƙauyukan da suka fito. Kamar Ibrahim Mansur Takai, Al’amin Bello Maƙarfi, Bello Waziri Ƙaraye, da sauran su. Mata kuma akwai irin su Rahane, Hauwa Kulu, Ruƙayyah, Mairo, Altine, Hadiza, Amina da sauransu.

Tambaya: Shin ko kin taɓa amfani da wani ɓangare na tarihin rayuwarki a cikin rubutunki?

Amsa: Sau-tari ana cewa haka a kaina. Amma amsar ita ce a’a. Ina dai amfani da iya abinda na san yana faruwa ko zai iya faruwa. Hasali ma ban taɓa rubuta (true life story) ba, duk labaraina na da can da na yanzu, ƙirƙirarrun labaru ne.

Amma a Rayuwar Rayhana kasancewar na ba wa jarumar littafin irin lalurar da nake ciki da halayena, shi ya sa waɗanda suka san ni a zahiri ke tunanin labarina ne.

Amma banida alaƙa da labarin sai lalurar matsalar dana suffanta Rayhana da ita a cikin labarin.

Tambaya: Wanne littafi ne ya fi ba ki wahala daga cikin dukkan litattafan da ki ka taɓa rubutawa?

Amsa: Kwana Sittin. Na sha wahalar bincike akan sa akan lalurar (schizophrenia) da cututtukan da ke da alaƙa da ita, da kuma Girma Ya Fadi, wanda shi kuma na hargitsa ƙwaƙwalwata sosai a kansa, na je har Maraɗi ta Nijar a kansa.

Hira da Sumayyah Abdulkadir Takori
Sumayyah Abdulkadir yayin da ta karbi shedar karramawa Gasar Hikayata ta BBC Hausa a shekarar 2023.

Tambaya: Wanne irin ƙalubale ki ka fuskanta a harkar rubutu, kuma ta wacce hanya ki ka bi har ki ka tsallake ƙalubalen?

Amsa: Babu irin ƙalubalen da ban haɗu da shi a rubutu ba. Akwai lokacin da publisher ɗina da muka jima tare ya haɗa jarin nawa gaba ɗaya ya gudu da shi kuma har gobe bai biyani ba.

Haka lokacin da aka yi gobarar Sabon Gari sai yafe kuɗaɗena masu yawa na yi gaba ɗaya ba don littafaina sun ƙone ba. Sai matsalar overprinting, da ƙin biyan kuɗaɗen bashi daga ‘yan kasuwa da gangan. A ƙarshe duka na yafe musu, ban taɓa kai kowa kotu ko hannun ‘Yansanda da sunan shari’a akan sana’ar mu ba, a tsawon shekaru 20 da na kwashe ina rubutu da tarin matsaloli. Na daɗe ban ci gajiyar rubutuna ba. A cinye jarin, mahaifiyata ta sabunta min, a haka dai na miƙe har na koyi karɓar rance kai tsaye daga (microfinance) duk don in cigaba, saboda sana’ar ta bi jiki na. ƙalubalen da na yi ta fuskanta kala-kala bai sa na sare na barta ba har lokacin da duk marubuta suka barta.

Tambaya: A duk cikin Taurarin labaran da ki ka rubuta wanne ki ka fi so, kuma me ya sa?

Amsa: Na fi son Ya Himu da Rahanensa, a littafaina na baya kenan. A na yanzu-yanzu kuma na fi son jarumin Sakacin Waye, ɗan ƙabilar Berom, Hamzah Mustapha Mawonmase.

Tambaya: Akan samu wani lokaci da kan marubuci ke cushewa har ya kasa rubuta komai. Shin kin taɓa shiga irin wannan yanayin? Kuma ta wace hanya ki ka bi wurin magance hakan?

Amsa: Gaskiya in dai lafiya ta kalau basirar sabon rubutu ba ta taɓa yanke min ba, sai dai in adanata zuwa wani lokaci don na huta.

Tambaya: Mene ne abin da ki ka fi so game da rubutu?

Amsa: Masoya na gaskiya da na samu sanadinsa, gida da waje, birni da ƙauye. Sannan yana ɗebe min kewa, yana tayani hira, yana mantar dani kowacce damuwa musamman ta lalurar da nake ciki.

Masoyan da na ke da su a sanadinsa kuma suna sanya ni alfahari da shi da godiyar Ubangiji a kodayaushe, musamman wadanda suke tsaye tare da ni tun daga tushe har kawo yau, suna ɗokin in fidda sabon littafi su karanta kullum. Zumunci da nake samu a duk garin da naje sanadin rubutu ya fi komai faranta min rai da rubutuna.

Tambaya: Me ki kan yi a duk lokacin da ki ke da sarari?

Amsa: Ina karanta Alqur’ani ina kuma rubutu, sannan ina saƙa zaren sabon labari.

Tambaya: Wace karin magana ki ka fi so? Kuma me ya sa?

Amsa: ‘Ba naƙasasshe sai kasashshe/Naƙasa ba kasawa bace.

Dalili? Na yarda cewa (there’s ability in every disability).

Tambaya: A naki ra’ayin, tsakanin rubutun online da bugun littafi na hannu wanne ya fi? Kuma me ya sa?

Amsa: Duka na yi su. Na san daɗin su da rashin daɗinsu. Kowanne na da irin nasa amfanin da rashin amfaninsa. Amfanin na online shi ne yanzu bana bin ‘yan kasuwa akan su ba ni kuɗina suna wahalar da ni.

Matsalar rubutun online shine babu amana. In daya ya saya zai iya turawa dubu babu yadda za ka yi. Amma na bugawa yaɗuwarsa da sauƙi tunda ka san adadin da ka buga. Matsalar na bugawa kawai kasuwancinsa ce wanda akan bashi muke yinsa amma ya fi security.

Tambaya: A naki ra’ayin, wanne tasiri marubuta suke da shi a cikin al’umma?

Amsa: Sosai marubuta ke da tasiri don ana sauraron su sosai kamar yadda ake sauraron malaman makaranta, don haka nake so mu tuna hakan koyaushe mu tsarkake alƙalaminmu daga rubuta abinda zai cutar da tarbiyyar yara da al’umma.

Tambaya: Shin ko akwai wani labarin da ki ke rubutawa a yanzu haka da masoyanki za su yi tsumayin fitowarsa?

Amsa: Eh akwai goron sabuwar shekara in Sha Allah mai suna… Da Kyar Na Sha (Labarin Aisha-Siddiqah).

Tambaya: Wane ne tauraronki a cikin marubuta?

Gaskiya suna da yawa na publishing da na online, duk ina da kyakkyawar alaƙa da su, muna zaman tare cikin aminci da mutunta juna da taimaka wa juna.

Tambaya: Tsakanin Fim da littafi wannene ya fi saurin isar da saƙo?

Amsa: A ganina kowannensu da irin yadda yake isar da saƙonsa. Koda yake dukkansu Ɗanjuma ne da Ɗanjummai.

Tambaya: Wacce irin shawara za ki iya ba wa sabbin marubuta masu tasowa?

Amsa: Ka yi rubutu da kyakkyawar manufa ta isar da saƙo mai kyau, ka yi rubutu don ra’ayin kanka ba don neman suna ba.

A duniyar rubutu ɗaukaka ta Allah ce da ƙoƙarin marubuci. Ka tsaya iya matsayin da Allah ya ajiyeka a rubutu sai ka zauna lafiya cikin wadatar zuci. Ban taɓa rubutu don neman na yi suna ba sai don ina jin daɗin yin sa akan karan-kaina.

Tambaya: Mene ne burinki a harkar rubutu?

Amsa: Burina faɗakarwa da nishaɗantar da al’umma. Ina alfahari da rubutu, kuma kowanne mataki na kai a nan gaba ba zan manta da cewa litattafan da na wallafa su ne sanadin da duniya ta sanni ba.

Tambaya: Me za ki iya cewa game da Bakandamiya Hikaya?

Amsa: Bakandamiya manhaja ce da ta zo da tsari mai ma’ana da ban sha’awa domin ta kawo maslaha daga kokenmu na yaɗa littafanmu ba bisa doka ba da sauran matsalolin online da muke kuka da su. Kuma suna biyan marubuta abinda suka yi yarjejeniya da su cikin aminci babu cutarwa ba saɓa alƙawari. Ina roƙon Ubangiji Allah ya taimaki Bakandamiya da ma’aikatanta.

Amin. Mun gode sosai.

An yi wannan hira da Sumayyah Abdulƙadir ne a ranar 01 ga watan Disamba 2023.

Tsara tambayoyi da gabatarwa: Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page