Skip to content
Part 1 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

LITTAFI NA DAYA

1 Ga Watan Junairu, 2023

HAKKIN MALLAKAR LITTAFIN DA DUK ABINDA YA KUNSA NA MARUBUCIYAR SHI NE SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI). A GUJI KARANTAWA A YOUTUBE KO SARRAFA SHI TA KOWACCE HANYA BA TARE DA RUBUTACCEN IZNI NA BA. 

                             “GEMBU”

(Garin mu da babu kamar sa a sanyi a fadin kasar Najeriya)

Garin Gembu, kamar yadda na samu cikakken labari daga bakin Ummati, da sauran bincike na na ilmi a kan tarihin yankin namu, kasancewa ta wata irin mutum mai son sanin Tarihi da bin ussin salsalar ilmin abu, yankin Gembu wani babban birni ne ko kuwa in ce alkarya da ke a yankin Duwatsun “MAMBILLA” a jihar Taraba a Najeriya, shine babbar Hedkwatar karamar hukumar Sardauna wato (Sardauna Local Government) da aka fi sani da “Tsohuwar Mambilla” a jihar Taraba.

Sunan Sardauna Local Government ya samo asali tun daga zuwan Alhaji (Sir) Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto yankin mu na Gembu a shekara ta (1956).

Mutanen Mambila ko Mambilla suna zaune ne a Tudun Mambila (Mambilla Plateau). Garin yana kusa da Boda wato iyakar da ta raba kasar Najeriya da kasar Cameroon. A wasu lokutan masana tsaunin Mambila kan kira tudun na Mambila da ‘Heaven on Earth’ wato (Aljannah a duniya), wannan ya samo asali da kasancewar garin Gembu gari mafi kyawun yanayi na sanyi mai ban mamaki a arewa maso gabashin Najeriya.

Masana ilmin labarin kasa (Geographers) sun tabbatar da cewa a kasar Najeriya bakidaya babu gari mai irin kyawun yanayi na sanyin Gembu. Sannan gari ne mai cike da albarkatun kasa wanda da gwamnati zata maida hankali wajen bunkasa shi da ta samu arzikin kudin shiga mai yawan gaske a kan sa, sakamakon yadda garin ya ja hankalin masu yawon bude ido na ciki da na waje. A Gembu akwai wasu manyan Dams guda biyu wato ‘Barup Dam’ da ‘Tunga Dam’ masu tsohon tarihi tun tana ancient town of (Bommi), garin Mambila na zaune a matsakaitan duwatsu tsayin kusan mita 1,348 (4,423 ft) sama da matakin Teku, yana daga cikin manyan biranen Najeriya.

Gembu na da habakar kiwon shanu, tumaki, awakai da Buffalo. Tuntsayen gida kuwa Allah ya yi albarkar su a Gembu, wanda ya sanyawa garin albarkar nama da abinci mai lafiya, duk da cewa sun fi kiwon dabbobin su fiye da cin su.

Abincin da ya fi yawa a Gembu shine kayan marmari (fruits) wanda ke taimakawa kwarai wajen kasancewar mutanen garin cikin koshin lafiya, yawan shan ‘Piya’ ya maida fatar mutanen Mambila wata irin danyar fata mai taushi da sulbi kamar larabawa.

Gembu gari ne da Allah ya halicci kyawawan mata, in na ce kyau, to ina nufin tsurar kyau na halitta fiye da na sauran duka kabilun fulanin Najeriya. Akasarin ‘yan Gembu (musulman cikin mu) zaka gan mu dogaye haka sirara masu cikar zati da kamala, sirantakar dake kara mana kyau, matan Gembu masu asalin dogon hanci da doguwar fuska ne, masu sassanyan kyau da babu fulanin da suka mallaki irin sa a fadin kasar Najeriya.

Wadannan din dana ambata ba dukkan su ne ‘yan kabilar Manbila ba, mutanen Gembu sun fito ne daga rukunin kabilu daban – daban wadanda suka hada da; Mambilla, Kaka, Kambu da Panso.

Yaren garin Gembu shine fulatanci ziryan din sa, Hausa bata da tasiri sosai. Yaran da aka haifa a Gembu ko “zo in ka she ka” da Hausa basu sani ba sai wadanda suke fita ko suke ta’ammali da bakin haure.

Matan Gembu wasu irin kyawawan mata ne na bugawa a jarida kamar sun hada iri da larabawa, sabida tsananin sanyin garin basa ta’ammali da fanka ko A/C. Mutanen da aka haifa a Gembu basu taba ganin fanka ko A/C a zahiri ba sai a talbijin ko a littafi.

Sabida karfin harshen fulatancin su hatta a Choci da fulatanci a ke sermon kasancewar kiristocin su kusan sun fi musulmai yawa.

A wancan lokacin dana ke magana a kai mazan Gembu na fita cikin jihar Taraba don yin karatun boko amma matan Gembu basa karatun boko sai daidaiku, wadanda a wannan karnin da ake ciki ne ma suka dan fara karatun boko, shi yassa ake fadin cewa matan Gembu ‘yan kabilar Mambila basu da wayewar kai kamar na sauran fulanin Jalingo. Amma kuma suna bada karfin su a kan neman ilmin muhammadiyya wanda yasa bazaka taba kiran su jahilai ba.

Sana’ar matan Gembu sakar kayan sanyi da zannuwan gado na rufuwa masu kauri, wadanda suke sakawa don amfanin kan su sabida yanayin garin su. Sai ko kiwo da noma.

Sunan yaren garin ne “Mambila” sunan grain kuma shine “Gembu”. Kamar yadda na fada a sama Gembu shine birnin Mambilla wanda ke karkashin karamar hukumar Sardauna.

Gabadayan garin da sauran kauyukan da ke makwabtaka da shi a kan Duwatsu suke tsugunne, wato (Mambilla Plateau).

“Mambillah, the coolest wheather in Nigeria – (Wikipedia-Britannica)”

Mambilla ya zama tourist attraction na jihar Taraba sakamakon ni’imar sanyi da Allah ya yi wa garin da sauran albarkatun kasa da bazasu lissafu ba.

Geographers da yawa sunyi rubutu a shafin wikipidia a kan tsaunin Mambila, haka masu binciken albarkatun kasa (soil scientists) sun tabbatar da cewa akwai Zinare da Shudin Yaqutu (Gold and Blue Sapphire) kwance a cikin kasar Mambilla Plateau, wasu marubutan ilmi kuma sun yi ittifaki a kan garin Mambila wanda sam gwamnati bata maida hankali akan albarkatun sa ba, da cewa; da gwamnatin Najeriya zata maida hankali a kan sa da ya tabbata “Heaven on Earth” din da ake kiran sa da shi ko kuwa ya zama tamkar kasar Dubai a Najeriya.

Hanyar zuwa garin Mambilla kan shi a kan dutse yake, wanda ya taho daga garin Jalingo. Mambilawa wato ‘yan asalin Gembu basu cika ji ko yin yaren harshen Hausa ba musulmin su da kiristocin su. They have a very strong Fulfulde accent wanda ya bambanta dana dukkan fulanin Najeriya.

Kauyukan da ke yankin Gembu sun hada da; Tunga, Maisamari, Yelwa, Gurgu, Sabon gari da kuma Nguroje.

Kafin zuwa garin Gembu sai ka fara isa Numan ta jihar Adamawa, sannan ka dauki hanyar Taraba, tafiyar awanni biyu a tsakani kafin ka iso Jalingo, daga nan ne zaka dauki hanyar da zata kai ka Gembu, tafiyar awanni takwas a tsakani kafin ka samu isa Gembu.

Don haka tafiya daga Kano ko Kaduna zuwa Gembu tafiya ce mai nisa ta tsahon awanni 21-22, tafiyar kwana daya kenan cur, idan har ba mutum ya yi transit (matsaya) a garin Jalingo ba.

Kasashen turawan yamma sun maida Gembu ‘tourist destination’ na Taraba, ba ka raba Gembu da bakin jar fata lokaci-lokaci suna daukar hotuna a cikin motocin su masu budadden sama. Ba turawa kadai ba duk ma wanda ya san ni’imomi da albarkatun da ke tattare da Gembu kuma ya ke da halin zuwa to kuwa zai so ya kai kan sa yawon bude ido wannan gari namu mai dimbin albarka, don hutawa da karin fadadar ilmi, musamman in ka kasance mai son karin ilmi a kan geographical setting na kasar Najeriya.

Gembu na kusa da wata karamar hukuma mai suna Gashaka, inda a can ne ‘Gashaka Gumti National Park’ ya ke.

– GEMBU; Garin da ya tara tsala-tsalan ‘yammata mafiya kyawu a Najeriya – (Saliadeen Sicey)

Da zarar ka fara haurawa kan tsaunin Mambila daga wani tsauni da ake kira ‘Mayo Selbe’ da ke karamar hukumar Gashaka, zaka hangi Tsaunin Mambilla mai tudun gaske lullube da korran ciyayi da wasu irin dogayen bishiyoyi da yayyafin hazon kankara ya yi musu mayafi, don wasu lokutan kankara har zuba ta ke.

Dalilai da yawa zasu sa ka son ziyartar Gembu; na farko zaka so ziyartar garin Gembu ko don ka ga tsala-tsalan matan da Allah ya halitta a can, in kai mai son zane-zane ne har ka so ka zana su da alkalamin ka, ka sha fruits nunannu iyaka shan ka (musamman Piya), ka sha danyar madara da nono kindirmo iyaka yunwar ka, ka ji ni’imar sanyia jikin ka da zuciyar ka iya ka jin ka, ka ji kamar ba a kasar Najeriya ka ke rayuwa ba, ka kuma amfana da tarin albarkatun kasar da ke tattare da garin, ka kara girmama girma da buwayar karfin ilmin halittar ubangiji.

*****

Ummatin Mambillah

Ummati, sunan Kaka ta kenan wadda ta haifi mahaifi na. Sunan ta na asali Saudatu, ni na saka mata suna (Ummatin Mambila), kasancewar ita ta raine ni, daga madarar shanun ta mai dumi da gardi da ta zama makwafin nonon uwa a gare ni a wancan lokacin. Ban taba sanin dumin jikin mahaifiya ta ba sai na Ummati, na san fuskar ta dai a hoto kan wani tsohon farin hoto marar kala daukar zamanin da, da Ummati ta taba nuna min, sai naga ba maraba da tawa fuskar banda kuruciya dana fi ta, duk da cewa sanda aka yi hoton ma da tarin kuruciyar ta don bata cika shekaru ashirin ba.  Kuma Ummati ta sha gaya min da kuruciyar ta ta rasu.

Sunan Ummati da na lankaya mata tun ina koyon magana shi ya bi ta a bakin ‘ya’ya da jikokin ta, dama jama’ar garin Mambila baki daya, ita da kan ta ‘Ummati’ ta ke kiran kan ta da kanta, Saudatu ya dade da bacewa a bakin kowa.

Ita da mijin ta mai rasuwa Malam Dalhatu ‘yan asalin garin Gembu ne, iyayen su da kakannin su sune tushen kabilar Mambila, wato wadanda sune ‘yan asalin garin Mambillan tun daga iyaye da kakannin su, aka kuma haife su a nan, suka girma suka yi aure suka rayu tsayin rayuwar su a nan.

Malam Dalhatu Abdullahi Gembu, ya rasu ya bar matar sa Ummati da ‘ya’ya maza guda uku, Gidado da Mamman wadanda shekaru biyu ne kawai a tsakanin su sai suke tamkar tagwaye a idon mutane, sai kuma autan Ummati wato Baffa Adamu wanda suka baiwa ratar shekaru kusan bakwai.

Wadannan zaratan ‘ya’ya maza guda uku na Ummati duka sun tashi sun girma tare karkashin kulawar ta da jajircewar ta a kan kiwo da sana’ar saka da ta ke yi don ta tallafi maraicin su a bayan ran mahaifin su. Ban taba ganin jarumar uwa irin Ummati ba. Wadda ta tsaya tsayin daka wajen hada kan ‘ya’yan ta da daukar dawainiyar su ta yadda basu taba kukan basu tashi tare da mahaifi ba.

Lokacin da ta tashi yi wa Gidado da Mamman aure sai ta yi takakkiya ta tafi har makwabtan su garin da ake kira kauyen Gashaka, ta nemo musu auren Yaya da kanwa ‘yan asalin Gashaka masu nasaba mai girma sabida tsoron ta na kada mace ta raba mata kan su.

Asshe da Hassu ‘ya’yan wani attajirin bafillace ne a Gashaka, in aka ce miki attajirin mutum a Mambila to fa ba tsabar kudi ko tarin dukiya ya bashi wannan sunan ba, a’ah; yawan dabbobin ka da gonakin ka na gado sune arzikin ka a Mambila.

Sakacin Waye? 2 >>

12 thoughts on “Sakacin Waye? 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×