Skip to content
Part 1 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

21 Muharram

Da Karfe Shidda Na Yamma Agogon Garin Miami

Dr. Al’ameen Bello Makarfi, ke kwance cikin sofa mai juyawa dama zuwa hagu, idanun shi a rufe suke tamkar mai barci, amma a zahiri ba barcin yake ba, shi kadai ya san hakikanin abin da ke damunsa. Alal hakika rigimar matar shi IHSAN ne ya ishe shi a yau. Shi kam tun barin sa kasar haihuwar shi bai sake waiwayar ta ba balle ya tuna ta da sunan zama na din-din-din ba.

America, ta bude wani shafin rayuwa mai dimbin tarihi da nasarori a tare da shi, ta maida shi wane, ta zamo silar dukkanin nasarorinsa a rayuwa ta warkar da bakin cikin kuruciyar da ya zo Miami da shi ta kuma shafe rayuwar shi ta baya, ta wanke tsanar kan shi da yake a da can, shin a kan me zai bar ta?

Sai dai wani bangaren na zuciyarshi sam, ya ki amince mai da hakan. Idan ya yi hakan ya tabbata hakkin yarinyar kadai na iya wargaza masa farin cikin da yake takamar ya samu a Miami; Shekaru goma kenan cif da rabuwarta da iyayenta, shi kuma goma sha biyar cif in har lissafin da yake daidai ne bai rage ba, sun turo ta karatu sun sarke da soyayyar da har ta kai su ga aure ba tare da sanin iyayen ko dayan su ba.

Ta jure rashin soyayyar nan ta iyaye a tare da ita tsayin shekarun nan wadda ta fi komai dadi da muhimmanci ga dan adam, idan shi namiji ya iya ya jure, ita Ihsan mace ce, ya kuma tabbatar ta yi hakuri kan hakuri ba don komai ba sai don masifaffen son da take masa. To shi don me ba zai nemo mata wannan soyayyar ba, ko don albarkacin wadda take masa? Shi kansa ya san a yanzun zuciyarsa ta yi sanyi da takaicin kuruciyarsa ta gida.

Tunanin Daddy din shi ya addabe shi, ko an harbe shi? Ko har yanzu yana kulle a kurkuku (Prison)? Zuciyarsa ke bijiro masa da cewa, yanzu ne ya dace ya je ya tallafi mahaifiyarsa da ‘yan uwansa duk da ya san a kowanne hali mahaifiyarsu za ta iya kula da su, kasancewarta mace mai dumbin arziki. Yana ganin yanzu ne ya dace Hajiyarsu ta huta da guminsa, shi a yanzu ya san Allah ya yi masa ludufi da nasibi ta kowanne fanni a rayuwa;

Bar ta kasancewarsa mamallakin shahararren asibitin kwakwalwa wato “MERITIME” da ke cikin birnin Miami, hakan nan shi ne babban likita a sashen kwakwalwa (consultant) a babban asibitin garin Miami (Jackson Memorial) da ke Florida. Har ila yau, Dr. M.A.B (Senior lecturer) ne da ke daukar daliban “Medical Psychology” a jami’ar da ya yi karatu (University of Miami), kuma masani a kan duk wata larura da ta shafi kwakwalwa. Don haka kasar America ke ji da shi, suna lailayar shi da ruwan arziki kasar su na amfana da dumbin baiwa da fasaharshi. Baya ko tuna kasar shi ta haihuwa (Nigeria) balle iyayen shi da ya tafi da niyyar barin su har bada, don yana ganin ba abin da zai masu, ‘ya’ya irinsa ba abin bukata ba ne, don haka bashi da amfani a gare su. Ga ingantacciyar kauna da kulawa daga matarshi abin kaunar shi Ihsan, yalwataccen gida a Miami, motocin hawan da ko a U.S. sai wane da wane.

Kenan duk wani buri da dan adam zai iya ciwa rayuwar duniya, ya samu. To amma zai so ya mutu ba tare da sanin halin da iyayen shi ke ciki ba? Ba tare da ya kara sa wani jinin shi a idanun shi ba? Bai sake sanin halin da kanwarsa SARATU-INTISAR ke ciki ba, shakikiyarsa kuma kanwarsa da ya NAKASTA?

Mafarke-mafarken da yake na Daddy a dan tsukin kadai na tayar masa da hankali, ya kasa nutsuwa kwata-kwata wanda hakan ya janyo masa yi wa wani mara lafiya (Patient) rubutun magungunan da ba su dace da lalurarsa ba, ba don Ihsan ta lura ba da an yi mamakin shi M.A.B ne da wannan danyen aikin. To haka ko rubutu yake yana daburcewa ya rasa me zai rubuta?

Gaba daya hankalinsa ya yi gida ya kuma tabbatar kwanciyar hankalinsa kadai ya bude ido ya gan shi a gida.

Baya jin zai sake samun nutsuwa bai baro Turai haka nan ba. Anya ma kuwa babu hakkin Dady din shi a kan shi? Mutumin da ya wanzar da ran shi da lafiyar shi cikin wahala, domin nema masu farin ciki, anya ya cancanci hukuncin da ya yanke masa?

Bar ta so da gatan da yake nuna masa throughout sauran kannensa to haka Hajiyarsa, ya tuno yadda a kullum take gaya masa ba ta son ya yi nisa da ita, ya fiye mata duk sauran ‘ya’ya taran da ta haifa a duniya! Sai ya ji kansa ya yi wani irin gingiringim, idanuwansa sun yi mai nauyi, baya ko iya bude su. Ya lumshe ido cikin wani sabon yanayi a tare da shi. Allah kadai ya san halin da zuciyarsa ke ciki.

Ihsan ta karaso rike da tambulan mai garai-garai cike da danyar madarar shanu mai sanyi (fresh) wadda shan ta ya zamewa likita Ameenu lazim a duk yammaci, a gida ne ko ofis. Sanye take cikin fararen kayan wanka (bikini), gashin kanta ke digar da ruwa tabbacin daga wanka ta fito. Ganin yanayin da Al’ameen ke ciki sai ta ja dan karamin tebur da ke gabansa ta ajiye kofin.

Sannu a hankali ta kwanta jikin Al’amin sannan ta marairaice kamar za ta yi kuka ta ce, “Ameenu isn’t this enough? America is not our motherland…. Don Allah mu koma gida…” Sai kuka.

Shiru ya yi cikin tunani, shi kam bai san ma abin da zai ce mata ba ma. Zuwa gida? Ai shi ne mai cewa a je ba ita ba yanzun. Bai ce komai ba, baya ga dora hannu cikin gashin kanta, don in ta soma yi mai wannan rigimar ta “a dawo gida…” da kyar yake iya samun kanta. Hakika tana ba shi tausayi, dole su baro MIAMI a wannan watan.

*****

1 GA WATAN SAFAR (HIJRIYYAH)

Jirgin American Airways ya sauke su a birnin Ikko da karfe tara daidai na safe. Sai da kowa ya fita amma Al’ameen da Ihsan ba su ko motsa daga “seat” dinsu ba. Gaba dayansu jikkunan su sun yi sanyi, domin a take zazzafan zazzabi ya rufe Ihsan, ba su san da fuskokin da za su aro su dubi iyayensu ba.

Sai da wata ma’aikaciyar jirgin ta yi masu magana cewa za a rufe jirgin, sannan ne Al’ameen ya tuna cewa shi fa namiji ne, ya rungume matarsa da hannunshi na dama a yayin da na hagun ke rike da ‘yar kyakkyawar jakarta ‘Japanese” a haka suka soma tako matattakalar jirgin cikin nutsuwa har suka taka kasarmu mai dimbin albarka.

Dole idan ka kalle su sai ka maimaita su kuma yi bala’in ba ka sha’awa. Kwarjini da cikar zati irin na Al’ameen da ke sanye cikin edpensive Italian suit, kalar baki da ratsin fari sol sun taimaka ainun wurin kara fiddo ilhama da cikar zatin shi, ya saya kwayar idon shi cikin bakin dark-spaces da ganinsa dai ka ga bakon Ba’amurke. To haka itama Ihsan din tamkar aljana take don kyau, baby face gareta mai dauke da kayatattun idanu tare da kyakkyawan dogon karan hanci da gassun gira mai tsari. Yarinya ce ‘yar gajeriya mai jiki kuvul-kuvul, kamar na tarwada saboda tsabar hutu tamkar ba bakar fata ba, domin tun fil’azal ita brown ce, sai kuma zaman kasar sanyi da jin dadin samun gwarzon miji irin Al’ameen Bello, da suka kara wanke ta tas.

Dr. M.A.B zai yi wuya ka fassara daga kabilar da ya fito a lokaci daya, kamannin shi na da ruda tunani da sanya shakku, bi-ma’ana (by appearance) ba za ka kira shi Bahaushe ba sam-sam duk da cewa ya fi son yin magana da harshen Hausa a kodayaushe fiye da duk wani harshe da ake magana da shi a duniya. Hakan nan ba za ka ce shi din Balarabe ba ne, domin baya da tarin nannadaddiyar suma irin tasu kullum kansa cikin saisaye yake, amma ya bar siririn saje a gefen fuskarshi abin nan da ake kira Man’s pride. Mutum ne dogo siriri, don tsayi har ya rankwafa, wanda mutane da dama ke (kuskuren tsammanin) cewa yanayi ne don kwalisa, amma Al’ameen Bello komai nashi natural ne babu artificial. Idanun shi abin so ne, ba ga mata kadai ba har maza ‘yan uwansa will not keep wishing they were like him (Ba za su bar fatan ina ma a ce sune shi ba).

Idanuwa ne manya kuma lumsassu, tamkar kuma an diga masu zaiba har wani maiko-maiko suke. Bai kama da Turawan ma sam-sam shi dai kawai Al’Ameen ne, haka Allah ya yi sa.

Da wuya ka karanci zuciyar Al’ameen Bello, ko matar shi ba ta iya gane wasu al’amuran shi. Mutum ne murdadde mai yin komai straight forward (kansa tsaye) ba tare da tunanin illar da abin zai haifar ba, mai tsayawa a kan mgana daya, ba kankanin abu ke sa shi canza ra’ayi ba. Kuma mutum mai tausayi da masifaffar kyauta. Ya sha sauka daga mota in ya ga wani a gefen titi yana jiran bus a Miami, ya kira shi ya danka mai mukullin ya ce, “Tafi.” Shi kuma ya sayi wata.

Tun Ihsan na masifa har ta gaji ta kyale shi don ta lura abin a cikin jinin shi ne. Ita kanta ba karamar barna yake wa kayan ta ba wurin baiwa masu karamin karfi dake tareda su. Sau tari, tana kwance a mike ya kan dafa mata abinci, ya dauko ya kawo mata yana sanya mata a baki, yana mai lallashinta ta ci sosai.

Cewa yake wannan hakkinshi ne ya ciyar da matarshi, tunda a Alkur’ani mai tsarki babu inda aka ce mace ta ciyar da mijinta hakan nan bai son mata suke wahala, domin su ne uwayen al’umma duk wata wahala a wuyan su take. Idan suna nakuda ji yake kamar ya taya su.

In yana fada mata irin wannan kallon shi kawai take ta yi dariyarta mai isar ta ta ce wata rana zai daina ne, don yana ganin ba su da kowa ne a nan inda suke sai junansu. Shi wani irin mutum ne da bai bambancewa cikin mu’amalarshi da kowa, abin nufi, mai kudi da mara kudi, mace ko namiji. Dr. Al’ameen Bello kowa nasa ne.

Don haka ya sha fama da mata iri-iri a zamanin karatunsa, daga Turawan zuwa ‘yan sauran kasashen duniya da karatu ya hada su. Ihsan A.A kadai Allah ya bai wa sa’ar koda yake zan iya cewa, Al’ameen ya auri Ihsan ne domin ceton ta daga masifar son shi da ta sanya kanta, amma ba wai don wani mashahurin so na Allah ko na Annabi ba.

Ihsan Abubakar Argungu, ‘ya daya tal ga mataimakin Governor na (Central Bank of Nigeria), Dr. Abubakar Argungu. Iyayenta mazaunan Abuja ne na din-din-din duk da cewa dukkansu aiki ne ya kawo su a garin, daman an ce wai birnin Tarayyah ne. Kasancewar Ihsan ‘ya daya jal ga iyayenta ya sanya duk wani buri na Dr. Argungu da mahaifiyarta Ann Hathaway wadda ta kasance Kirista ‘yar uslin Birnin Gwari, akan Ihsan yake.

Mahaifiyarta Ann ce mamallakiyar bankunan Savannah da ECOBANK da ake damawa dasu a halin yanzu a kowacce jiha ta Najeriya, don haka gaba da baya Ihsan ‘yar gata ce ta karshe gun iyayenta baya ga watsi da ta yi da su kan son Al’Ameen Bello.

Iyayenta sun turo ta karatun medicine ne a University of Miami, inda ta hadu da Al’ameen, wanda a lokacin ke ba da lacca cikin makarantar bangaren masu karantar lafiyar kwakwalwar dan-adam.

Tun daga wannan lokacin Ihsan ba ta kara nutsuwa ba sai da ta zamo friend din Aminu. A hankali a hankali ta yi amfani da hilarta wajen jan ra’ayinsa gare ta tana bayyana masa yadda take son shi wani zubin har tana kuka take rokon shi ya aure ta gudun kar ta sanya kanta cikin gurbatacciyar rayuwa.

Ga Al’ameen mutum mai tsananin tausayin mace, tun ba in tana fidda mai hawaye ba, sai dai sam a lokacin bai da ra’ayin aure, tunda kuwa zai sada shi ne da gidan da ya baro baya ko son tunawa. Yaya ma za ai ya yi aure, ba tare da sani da yardar mahaifansa ba da baya da kamar su? Don haka ya rungumi Ihsan suka tsunduma watsewarsu ba tare da tunanin illar da hakan zai haifar ba.

Wannan ya fi komai dadi ga Ihsan domin dama ita ba auren ne a gabanta ba, illa tana tsoron idan ta bijiro mai da irin soyayyar da ta zaba musun ba zai amince ba, kasancewarsa mutum mai tsananin kamewa daga barin jin dadin rayuwar Turai a ko’ina kuma a cikin kowanne hali ya sami kansa, duk zalamar yarinya kuwa haka za ta ga Aminu Bello ta kyale domin abin da ya kai shi kadai yasa a gaba.

To itama Ihsan din kowa da ke tare da su ya yi mamakin yadda ta samu Ameenun haka a hannu, ba mamaki, domin an ce kowacce ‘ya mace da kissarta ake haifarta, hakan nan Ihsan tun tana mitsitsiyarta take koyan kissa gun uwarta har girmanta iri-iri ba wadda ba ta iya ba, don haka duk saurayin da ta kimsawa kanta sha’awarsa ta same shi ta gama kuma da kyar ne yake kubuta daga tarkonta.

To haka shi ma Al’ameen, ta tabbatar sha’awarshi ya fi son shi yawa a tare da ita kamin su yi aure, sai dai a dan zaman da ta yi da shi ta koyi kaunarsa saboda wasu kualities nasa da ke burge ta da ba duk maza Allah ya mallakawa ba.

Don haka ne ma duk wulakancin da yake mata in ya bushi iska ko ya yi sabuwar girlfriend take hakuri tana shanyewa, don ta tabbatarwa kanta tana samu nutsuwa 100% and beyond  a tare da Al’ameen fiye da duk wasu maza da ta taba mu’amala da su gida da wajen. Hakan nan tana ganin Al’ameen ko a cikin maza daban ne wurin nuna kauna. Samun maza irin su a matsayin MIJI sai mai sa’ar gaske. Ba ta taba haduwa da namijin da ke gamsar da ita ba har ya kure ta kamar Al’ameen ba. Ba ta taba haduwa da namijin da ya san darajar diya mace kamar Al’ameen ba.

Don haka ta kara manne masa ta like masa tare da kara zage damtse wurin nuna masa ingantacciyar kauna da kulawar da ta sa shi dole ya so ta, ta kuma shiga yakar macen duk da ta gani tare da shi ba tare da shi din ya sani ba ma. Ta kuma alkawartawa ranta, ruwa ko iska baya raba su.

Daga baya ne Al’ameen ya tuna cewa shi fa Musulmi ne, da kuma irin horon da Daddy dinsu ya yi masu, wanda da a ce yana tare da shi, hakan ba zai taba faruwa da shi ba.

Ya roki Allah ya yafe masa ya kuma nemi Ihsan da ta yi Istibra’i su yi aure, ita kuma ganin lokacin Aminun na sonta kamar me ta ce ba ta san wannan ba, jin hakan shi kuma ya fita harkarta kwata-kwata, ko a tunaninta kuma ko a mafarkinta a lokacin ba ta kawo Al’ameen zai iya rayuwa ba tare da ita ba.

Ta kuma tabbatar gab yake da ya shafe ta kwata-kwata a babin rayuwarsa in har bata amince su yi auren ba, ta amince ta saduda cewa shi din mai ra’ayin kansa ne, don haka ba ta isa ta sashi ko ta hana shi ba.

Suka yi auren su mai tsafta ba tare da sanin iyayen ko dayansu ba.

Daga baya ne ita Ihsan ta aikawa Ann cewa ta yi aure da wani likita Al’ameen. A lokacin hanyoyin sadarwa basu yi kamarin da suka yi yanzu ba. Ann din ta aiko mata da zagin cin mutunci ta waya da e-mail kan don me ta auri Musulmi ba ta auri dan Addininta ba, bayan ta yi mata alkawarin muddin ta tashi aure Kirista za ta aura, don wai sun fi rikon aure. Shi kuma mahaifinta ya ce kwata-kwata ba ta kyauta musu ba ta dauke su ba a bakin komai ba tunda kuwa har za ta iya ta yi aure ba tare da sani da amincewarsu ba, don haka ta je Al’ameen din ya maye mata gurbinsu.

To Ihsan ranta ya baci sosai da iyayenta a ganinta gata ta yi wa rayuwarta ai, domin shi kansa auren ai mutunci ne ko bature yana daraja aure, da dai ta ci gaba da gurbatacciyar rayuwar turai da babu komai cikinta sai lalacewa, kuma ba su yi mata uzuri da soyayyar da ta rinjaye ta ba sun manta an ce luv is overall, wato soyayya tana gaba da komai.

Wannan ya faru shekaru uku da suka gabata, tun daga lokacin Ihsan ba ta kara waiwayarsu ba, duk da cewa daga baya su din sun neme ta amma ta share su, don tana ganin son Ameenu ya fiye mata komai, ko in ta sauraresun me za su yi mata? Za su hana ta aurensa ne? To gara ita, shi din ko sanar da su bai yi ba, tunda kuwa a lokacin ya riga ya shafe gida kwata-kwata daga kundin tarihinsa illa sabuwar rayuwar da ya gina a gaba. Sai suka hade abinsu suka dunkule junansu wuri guda suka bude sabon shafin rayuwa cike da soyayya mai ban sha’awa.

Daga Al’ameen har Ihsan kowa na son Da, musamman ita Ihsan da take ganin haihuwa da Ameenu ne kadai zai dorar da dangantakarsu. Tana ganin in ta haihu da shi zai mallaka mata dukkan so da kaunarsa da har yanzu kwakwalwarta take gaya mata bata mallaki komai a ciki ba duk da cewa da wuya a karance shi, amma hakika ta san bata da dukkan so da kauna a zuciyarsa. Hana rantsuwa za ta iya cewa ‘yana son ta’ kadai.

Wannan ita ce matsala ta farko da suka fara cin karo da ita a rayuwar auren su, kuma in har suna da matsala a auran to wannan ce. Lokacin da Al’ameen ya soma complain (korafi) wai abortion (zubar da ciki) da ta-yi ta-yi ya shafi lafiyar mahaifarta, cikin kwafa kuma sai ya ce ko ciki har nawa ta barar oho. Da haka suka fara fada, ta ce ya san tana bare-baren cikin ai ya neme ta da watsewa, don ita tun farko ai aure ta ce su yi. Yadda ta lurra Al’ameen mutum ne mai masifar son yara, ko tafiya suke bisa hanya ya ga yaro sai ya tsaya ya dauke shi ya yi kissing ya ba shi choculate da baya rabo da saye cikin kantuna.

Ranar da Ihsan ta yi nadamar aurenta da M.A.B shi ne ranar da ya ce da ita wai shi dama tun ranar da ya soma saninta ya yi mamakin maza nawa ta sani? Shi ba irin matar da ya so aure ba kenan a rayuwarsa, amma ya zai yi da kaddara? A wannan ranar ne Ihsan ta yi kuka wanda rabonta da shi tun na sallamar ta da iyayenta shekaru goma a baya.

Kewar iyayenta ya zo mata. Ta tuna masifaffen gatan da take da shi a wurin iyayenta da yadda suke sonta, suke kula da ita, suke gudun duk wani bacin ranta. Yau ga namiji kwaya daya na yi mata yawo da hankali. Sai take tambayar kanta ko me Al’ameen ke takama da shi da yake gara ta haka?

Ba ya takama da komai illa jarababben son da take masa. Ta tabbatar duk wani cin mutunci ma in da a gaban iyayenta take zai zo da sauki fiye da nan din da yake ganin ba ta da kowa sai shi. Sai dai ta kudurce a ranta koma me zai mata ko duka ne ba za ta taba rabuwa da shi ba.

Daga baya Al’ameen da Ihsan duk sun amince ba hayaniyarsu ko tashin hankulansu ne za ya ba su haihuwa ba, illa ma ya rugurguza masu kyakkyawar rayuwar da suke ciki, ta so da fahimtar juna, sai suka dangana. Shi Al’ameen yana addu’a ita ko Ihsan Addinin nata ma gashi nan ne, sallah sai in ya takura mata za ta yi in baya nan ko a hadu a gaba.

Tun daga wannan rigimar da suka yi Ihsan ta soma yi wa Ameenu korafi da koken su koma gida ta ga iyayenta ta kuma roki gafararsu, tunda shi ba ya son nasa. Shekaru bakwai ta yi tana karatu, shekarun su uku da aure kuma a cikin shekarun tana aiki a asibitin (Baptis Health) da ke South Florida, cikin birnin Miami matsayin karamar likitar zuciya (cardiologist) kuma kwararriya a fannin heart-transplantation

Da fari hankalin Al’ameen ya tashi da wanann sabon abu ko ko ya ce rigima da Ihsan ta kinkimo mishi har ya dinga ganin bekenta, to amma shi ma da ya yi tunani mai kyau sai ya ji shi din ma ba abin da yake so irin dawowar, ya kuma bude ido ya gan shi a gaban Daddy din shi ya ga SARATU-INTISSAR din da ta sa shi barin gida, ko a wanne hali take yanzun? Yaya take gudanar da rayuwarta a hakan? Uwa-uba tausayin Ihsan, yau shekaru goma kenan ba ta kara sa iyayenta a idanunta ba, shi kuma shekaru goma sha biyar kenan sai ko yau da jirgin da suka shigo ya sauke su a birnin Ikko.

Ihsan Abubakar matashiya ce da jin dadi ke boye mata shekaru a kullum, amma a zahiri shekarunta ashirin da tara cif, don dai gajera ce kawai ba a fiya kimanta shekarunta ba, a yayin da Dr. Al’ameen Bello ke da talatin da biyar da wasu ‘yan watanni. Daga Ihsan har Ameenu kowa na ji da kyau, sai dai nesa ba kusa ba Al’ameen ya darawa Ihsan tsari. Kusan kyawun Ihsan ya fi yawa a fuska, amma ba ta da wannan fasalin na ‘ya mace sai ko ‘yar lafiyayyar fuskarta da Ameenu ke matukar so.

Sanye take cikin English wears ruwan hanta riga da wando masu kauri, amma da yake ta baro Miami a yau ta dora bakar after dress kirar Oman a kai, bata da sumar kai mai yawa don haka sau da dama gashin kanta cikin tarin attachement yake.

To yau ma hakan, sai dai ta yane kanta da gyalen abayar yayin da kyawawan tafin kafarta ke sanye cikin wani rantsatstsen ‘high hill shoe’ bakin takalmi (mai tsayin dunduniya) mahadin jakarta kirar Japan. In ka dauke zobban diamond kwaya uku da ta yi wa kyawawan yatsunta ado babu komai a hannunta don ‘yar jakarta na hannun Al’ameen ne har suka shiga jirgin da zai kai su Abuja.

A Abuja Al’ameen ya riga Ihsan sauka don ta tsaya make-up dinta da baya karewa. Hannuwan shi duka biyu zube cikin aljihu ya doshi reception wato wajen karbar baki duk da dama shi bai yi tsammanin zuwan wani nashi ba.

Nan ya hango wata mata sanye da malfa mai tsananin kama da matarsa, ko ba a gaya mai ba ya tabbatar Ann ce mahaifiyar Ihsan.

Kallo daya ya yi mata ya dauke kai a ransa ya yi mamakin yadda mahaifiyar Ihsan ta kasance Kirista amma ba ta taba gaya mai ba, domin ya hango cross a sarkar da ke wuyanta.

Har ya yi gaba sai kuma ya yi tunanin bai kyauta ba, ya juyo ya komo inda suke daidai lokacin da Ann ta rungume diyarta suna ta kukan dadi tamkar ba wani sabani da ya faru tsakanin su, sai ya yi fatan hakan ta kasance a gare shi shima.

Ihsan ta saki mahaifiyarta ta yi mata nuni da Al’ameen da ya harde hannuwa bisa kirji yana kallon su kawai ta ce shi ne mijinta Al’ameen.

Duk kin da Ann ke wa auren Ihsan da Al’ameen, amma kwarjini da kamala irin na Al’ameen Bello, ba ta san yaushe ne ta sami kanta a mai mika masa hannu ba, ya mika mata nasa a ransa ko cewa yake wai kakar ‘ya’yana ne wannan Inyamurar kuma suruka ta ke mika min hannu mu gaisa kamar a turai? DA YA SANI… Wai me yasa har kullum yake gamuwa da DA NA SANI MARA AMFANI NE a rayuwarsa? To haka suka gaggaisa da sauran ‘yan uwanta ma gaisuwar hand shake fuskar shi ba annuri sam-sam sun nemi da ya bi su gidan su a Garki, domin ya gana da mahaifinta inda shi kuma ya nuna uzrinsa  yana cike da dokin ganin nasa iyayen shima. Sai dai in ya huta ita ma Ihsan din ta huta zai zo su gaisa da shi din, ya kuma dauki Ihsan din zuwa gidan iyayen shi.

Siradin Rayuwa 2 >>

39 thoughts on “Siradin Rayuwa 1”

  1. Sadiya Kabir Alhassan

    Allah ya kara basira ya kara lafiyar rubutu da fadakarwar da akeyiwa Al,umma.
    Wannan littafin ya kayatar dani kwarai da gaske Dan bangajiya da karantashi akwai darasi mai tarin yawa a cikin sa.

      1. mashaAllah daughter Ubangiji Allah ya kara basira, da fasaha,hakika Siradin rayuwa littafi ne dake cike da darussa da ke ilmantarwa,Al’amin na Ihsan gaa kuma zabin iyayen shi Intisar,bari mu bi muji wake nasara.

    1. Ramatu Mustapha Abubakar

      Allah ya qara basira da zaqin hannun rubuta,haqiqa dukkan rubuce-rubucen ki babu na yarwa,suna fadakarwa, ilimantarwa tare da nishadantarwa.
      Muna godiya qwarai, Allah ya qara lafiya.

  2. Kai masha Allah, wannan book din ya kayatar yakuma fadakar ,zamu dauki darasi acikinshi kalakala. Allah y kara basira our takori

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×