Skip to content

Tsarin murhun girka jigo a labari

A maƙalar da ta gabata, mun yi bayani sosai tare da misalai na yadda ake girka jigo ya koma labari. A yau kuma insha Allahu maƙalarmu za ta yi duba ne a kan irin tsarin murhun da ya kamata a girka jigon a kai. Shin ta wacce mahangar za mu kalli irin wannan hikimar mu samar da labari mai armashi?

Irin yadda ake tanadar duwatsu uku domin haɗa murhu, haka ake samar da ɓangarori uku wajen gina labari. Ɓangarori ukun su ne:

  • Tsini (farkon labari)
  • Doro (tsakiyar labari)
  • Tushe (ƙarshen labari)

Kamar yadda murhun ɗora tukunyar girki ba ya yiwuwa sai da duwatsu uku, haka ma babu wani labari da zai girku ya yi ɗanɗano ga masu karatu idan ba a ɗora shi a kan salon waɗannan murahun ba. Kowanne labari dole ne marubucinsa ya tanadar masa farko, ya tanadar matsa tsakiya, sannan ya tanadar masa ƙarshe. Saɓanin haka kuwa wata matsalar za ta iya biyo baya, irin matsalar da wanda ya ɗora tukunya a kan duwatsu biyu zai samu don yana taƙamar ya riƙe tukunyar da hannunsa. Don kuwa da zarar tukunyar ta ɗauki zafi ta yadda ba za ta ruƙu ba wataƙila sai dai ya saketa ya yi asarar girkin tunda duwatsu biyun ba za su iya riƙe tukunyar ta zauna ba.

Marubuta da yawa, musamman sababbin marubuta suna yi mini ƙorafin cewa sai sun fara rubuta labari sun yi nisa, wataƙila ma har sun je tsakiyarsa kawai kuma sai su kasa yin gaba ko su yi baya. To a inda matsalar take shi ne rashin ɗora labarin a wannan mizanin tun asalin lokacin da za a fara girka shi. Dayawa kawai fara yin rubutun suke yi ba tare da tsara masa doro da kuma tushe ba.

Kamar sikeleto ko ƙwarangwal na mutum, haka ake samar da sikeloto na labari mai ɗauke da farkon labarin, tsakiyar labarin, da kuma ƙarshen labarin. Wanda da zarar ka tashi za ka gina ainahin labarin shi sikeleto ɗin kawai za ka kalla ka ɗora masa tsoka da fata ya dawo halitta.

Yadda ake samar da sikeleto ɗin shi ne, a cikin ‘yan taƙaitattun kalmomi ka samar da yadda kake so farko da tsakiya da ƙarshen labarin ya kasance, ta yadda idan ka zo za ka rubuta ainahin labarin sai dai ka yi ta faɗaɗa gaɓoɓin kana ƙara musu armashi.

Misalin sikeleton labari: Mu nazarci wannan

Ɓaddabami

Labari ne a kan wani gari, duk girman garin otal ɗin saukar baƙi guda ɗaya ne, wannan dalilin ya sa mai otal ɗin yana yin cikini sosai. Kwatsam kuma sai ga wani shi ma ya zo ya gina sabon otal a garin. Sabontakar sabon otal ɗin da aka gina, da kuma irin abubuwa na zamani da aka zuba a cikinsa sai ya kashe wa mai wancan tsohon otal ɗin kasuwa mutane suka dena zuwa nasa, wanda wannan abin ne kuma ya fusata shi  mai tsohon otal ɗin ya ji lallai ya kamata ya ɗauki matakin durƙusar da sabon otal ɗin.

Bayan dogon nazari, sai ya gane cewa idan ya shirya wani kisan kai a ɓoye cikin sabon otal ɗin, zai kashe wa otal ɗin farinjinin mutane su ce babu tsaro a cikinsa tunda har za a iya bin wani a kashe shi a ciki. Wannan dalilin ne ya sa shi mai tsohon otal ɗin ya biya wasu ‘yan ta’adda suka tsara masa wani kisan kai mai sarƙaƙiya, ta yadda har sai da aka rufe sabon otal ɗin da sunan bincike, kuma aka kama mai otal ɗin.

A ƙarshe da ƙyar wutar rikicin ta mutu bayan asiri ya tonu cewa kisan shirya shi mai tsohon otal ɗin ya yi da gangan don ya ɓata wa mai sabon otal ɗin suna. Bayan ‘yan jaridu sun baza labaran yadda abin ya faru sai sabon otal ɗin ya sake dawowa da martabarsa irin ta farko.

Abin lura shi ne, gaɓa ta farko na rubutun ta ƙunshi ainayin yadda za a tsara farkon labarin. Gaɓa ta biyu kuma sai ta nuna yadda matsalar, ko kuma ainahin rikicin da aka yi bayaninsa a gaɓa ta farko zai je ƙololuwa. Yayin da gaɓa ta ƙarshe kuma nake bayyana irin yadda nake so ƙarshen labarin  ya kasance.

Indai har marubuci zai riƙa samar da sikeloto na labari irin wannan kafin ya fara, to zai yi wuya ace zai samu matsalar kakarewa a tsakiyar labari idan ya fara. Da zarar ya rubuta sikeleto irin wannan duk lokacin da ya zo zai faɗaɗa labarin ba zai samu matsalar rashin makama ba.

Bayan tsara sikeleton labari, abu na gaba da ya rage wa marubuci ya naƙalta shi ne ya san yadda zai faɗaɗa gaɓoɓin labarin nasa, wanda kuma yanzu abin da za mu yi bayani kenan.

Ya ake so farkon labari ya kasance?

Wannan gaɓar tattaunawa ce mai matuƙar muhimmanci, domin kuwa gaɓa ce wacce da ita ne makarancin labari yake yi wa labarin da ya ɗauka hisabi, daga nan ne zai fahimci shin zai karanta ko ba zai karanta ba. Bincike ya nuna cikin kaso ɗari na manazarta, kaso saba’in zuwa tamanin suna iya jefar da muhimmin labari kuma mai daɗi idan aka samu akasi shi marubucin labarin bai iya tsara farkon labari irin yadda ya kamata a tsara shi ba. Sau tari wasu manazartan suna karanta irin wannan labarin ne bayan an samu yaɗuwar cewa labarin ya yi daɗi, ko ya yi ma’ana daga bakin ƙalilan ɗin mutanen da suka yi juriyar bibiyar labarin da karanta shi duk da rashin tsaruwar farkonsa.

Shin ba ka kula ba cewa ko wajen masu sayar da littafi ka je za ka ga mutane suna ɗaukan labari suna duba farkonsa ko za su karanto abin da zai iya jan hankalinsu a cikin littafin kafin su saya? Akwai maganar da na ɗakko ta wasu shahararrun marubuta a waccan muƙalar da ta gabata wadda maganar tana ƙarfafar wannan zancen, inda nake ce wa:

Jodie Archer da Matthew L. Jockers sun ce jumlolin da fitattu kuma shahararrun marubuta irin su Sylvia Day, da Toni Morrison, da Jeffrey Eugenides da Virginia Woolf kan yi amafani da su wurin buɗe labaransu wato a farkon labarinsu, sukan dunkule rikicin da ke cikin littafi mai shafuka 300 a cikin jumla guda mai kalmomi 20 ko ma ƙasa da haka. Kenan dai suna amfani da hikima su bayyana jigon su a ciki taƙaitattun kalmomi don kama zuciyar mai karatu, ya ji yana so ya karanta labarin. Shi ya sa za ka ga ko a bayan bangon littafi akan yi wani ɗan taƙaitaccen bayani game da labari, ta yadda koda farkon labari bai yi maka yadda kake so ba za a iya jan hankalinka da wannan ɗan bayanin don ka sayi littafin.

A taƙaice dai ana so marubucin ya yi amfani da salon da zai yi matuƙar jan hankali ya burge mai karatu a farkon labari ta yadda zai ji lallai ya kwaɗaitu da karanta labarin don ya ji me ya ƙunsa. Jeffrey Archer ya ce a irin wannan gaɓar marubuci ya tabbatar mai karatu ya juya shafi na gaba cike da shauki da son gano mai zai faru a cikin shafin da ya buɗa ɗin.

Dabarun gina farkon labari

Ana gina farkon labari ta yadda zai ja hankalin duk wanda ya ɗauka ta sigogi da dama waɗanda za mu ɗauki wasu daga muhimman ciki ɗaya bayan ɗaya mu tattauna tare da misali.

i – Dunƙule abin da labari ya ƙunsa a taƙaitattun kalmomi

Wannan dabarar ita za mu fara dubawa, dabara ce wacce ake yin ta ta fuska biyu ita ma,  ya danganta da irin salo da yanayin da marubucin yake so ya ɗauka. Ko dai ya bayyana abin da labarin ya kunsa ta sigar bayani, ko kuma ya bayyana cikin hikima a labari.

Bari mu fara da bayar da misalin yadda marubuci zai bayyana abin da labari ya ƙunsa ta sigar bayani a cikin taƙaitattun kalmomi. Mu ɗauki labarina DA MA SUN FAƊA MINI, ga masu littafin a hannu su duba shafin farko na littafin, ga bayanin da shafin ya ƙunsa kamar haka:

MABUƊI

Kalmar sila  wata kalma ce da Bahaushe yake amfani da ita don nuna sanadi ko dalilin samuwar wani abu. A wasu ararrun kalmomin na shi, yana iya cewa maƙasudi ko musabbabi, wanda duk suna nufin abu ɗaya ne da sila. Sila takan zamo ta fuska-fuska, kamar yadda silar samuwar labarin ‘Dama sun faɗa min’ ta zamana dalilin zaman majalisa irin na al’ada ta matasa, wanda kuma taurarin cikinsa ba wasu  ba ne face ƙungiyar asirin da suke yi wa amaryar wata takwas Zainab barazanar hallaka duk abin da zata haifa, Zainab wacce take zargin mijinta Aliyu da zama ɗan ƙungiyar asirin da ya bayar da abin da zata haifa ga ƙungiyar tasu, Aliyu wanda shi kuma ya fitittike cewa shi ba ɗan ƙungiyar asiri ba ne, sai iyayen Zainab da suka maka Aliyu a kotu cewa ‘yarsu ba zata zauna da ɗan shan jini ba, da kuma Alƙali da muƙarrabansa da mu kanmu ‘yan kallo wanda da mu aka kawo ƙarshen tirka-tirkar…”

Idan muka kalli wannan misali, shi ne abin da marubuci Jodie Archer yake nufi da ‘ a dunkule rikicin da ke cikin littafi mai shafuka 300 a cikin jumla guda mai kalmomi 20 ko ma ƙasa da haka.’ Da iya ɗan wannan bayani ka haska wa makaranci duk abin da labarin ya ƙunsa, duk da dai kuma ba zai iya gane komai yadda ya kamata ba har sai ya karanta labarin. Amma dai ko babu komai za ka lasa masa zumar son jin yadda aka haihu a ragaya.

Akwai misalai iri-iri daga labarai kala-kala, sai dai za mu dakata a nan. Ku kanta maƙala ta gaba inda na ɗora da misalin yadda ake bayyana labari ta hikima ba tare da mai karatu ya fahimci bayyana masa aka yi ba.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page