Skip to content

Yadda ake sanya tsakure, taba ka lashe da somin tabi a labari

A maƙalar da ta gabatai, mun yi bayani ne game da tsarin murhun girka jigo a labari, inda muka bayyana madogara uku da suka zama kamar duwatsu uku na murhu da idan babu su babu labari. A cikin bayaninmu mun tsaya ne a kan misali na farko a ƙarƙashin dabarun gina farkon labari, inda muka ce ta sigar bayani   ana dunƙule abin da labari ya ƙunsa a taƙaitattunkalmomi don tafiya da hankalin manazarci da dasa masa ƙaunar karanta labarin a zuci.

A wannan maƙalar insha Allahu za mu yi bayanin yadda ake bayyana abin da labari ya ƙunsa ta hikima ba tare da an bayyana wa mai karatu ya fahimci cewa bayyana masa abin da labarin ya ƙunsa ake yi ba.

Kafin faɗaɗa bayanin, mu fara nazartar wannan misalin mai zuwa tukuna:

KAƊAICI

Cikin yanayin ƙara da razana matashin saurayin ya furta “Wayyo Allahna!” Lokaci guda kuma ya yi zumbur ya miƙe tsaye yana dube-duben wurin da ya zauna, a ɓangare guda kuma ya dafe mazauninsa da hannu.

“Me ya faru?”

“Ya aka yi?” Abokanan hirarsa biyu kowa da tambayar da yake yi masa suna kallon shi kamar waɗanda ya tsorata su.

“Kunama ce ta harbe ni wallahi.” Ya ba su amsa yana sosa mazaunin nasa, yayin da su kuma suka yi haɗin bakin tambayar shi.

Kunama kuma?”

Eh wallahi!” Ya ba su amsa.

Kun gan ta kuwa da girmanta.” Ya sake yin maganar yana mai nuna musu ƙatuwar kunamar da ta sake ɗana ƙarinta sama tana jiran kotakwana ta mayar da martani. Lokaci guda kuma ya ɗan matsa daga inda take tare da nemo wani tsinke da zai tsire ta da shi.

Sai dai kuma har ya kai hannu zai soketa da tsinken, kamar wanda aka yi wa wahayi, kamar wanda ya tuna wani abu sai ya fasa, tare da sauke wata ajiyar zuciya. Kawai kuma sai ya ɗan saka tsinken ya taɓa ta da shi, sanadin da ya sa ta yi wani gare tana neman maɓoya cikin tarin yayin da yake wurin ƙarinta a ɗage.

“Meye hakan? Ka kasheta mana kana ganin za ta gudu!” Guda cikin abokanan nasa mai amsa suna Buba ya hau yi masa ihu, yayin da shi kuma kawai ya ɗaga kai ya kallesu ganin sun zubo masa ido ya ce.

Ƙyale ta kawai, ai ba ta harbe ni sosai ba.” Gabaɗayan su sai suka bi shi da kallo kamar waɗanda suka rasa abin da zasu ce masa na irin wautar da yake shirin yi, lokaci guda kuma ɗaya matashin saurayin Ilu ya cire takalminsa farɗo zai zafga mata amma caraf Zaidu , wato shi matashin saurayin da ta harba ɗin ya riƙe masa hannu.

“Don Allah kada ka kasheta Ilu.”  Zaidu ya yi maganar tare da ƙwace takalmin hannunsa.

“Mece ce ribarmu ta kasheta?” Ya sake tambaya yana kallon matasan biyu da suke yi masa kallo na ƙololuwar mamaki da rashin fahimta.

“Kai mece ce ribarka na barinta ta tafi bayan cutar da kai ta yi?” Shi ma Buba ya zaburo da tambayar shi tare da nufar cikin yayin zai mutsittsiketa da ƙafarsa, amma bai kai ga wurinta ba Zaidu ya yi zunbur ya sha gabansa.

“Kada ka kasheta don Allah Buba!” Zaidu ya yi maganar yana marairaicewa da muryarsa mai sanyi.

“Ni ma da kasheta zan yi sai na yi wani tunani.” Ya yi shiru kamar wanda zai biya musu darasi.

“Idan har kunamarnan mace ce, yanzu haka na san tana da masoyi wanda yake son ta kamar yadda nake son Sufi, yanzu haka idan na kasheta shikenan na raba su da ita har abada kamar yadda ni ma aka raba ni da Sufina. Zafin rabuwa da masoyi na musamman ne, na ɗanɗane shi ban ji daɗi ba, don haka ba na fata ko maƙiyina ya sake ɗanɗanar raɗaɗinsa. Shi ya sa ba zan kashe ta ba kamar yadda ba zan bari a kashe ta ba. Ina so yadda ta baro gida lafiya ta koma ta tarar da masoyinta lafiya.”

Ba wai maganar da yake yi ba ce kawai ta ba wa abokanan nasa mamaki, sai dai yanayin yadda yake maganar ne da kuma hawayen da yake zuba a idanuwansa ya sa duk jikinsu ya yi sanyi. Ba don komai ba sai don sanin irin walagigi da guguwar soyayya ta yi da matasan biyu da kowa ya kwana da sanin labarin soyayyarsu a cikin ɗan ƙauyen…

Idan muka kalli wannan misalin, za mu ga a cikin shafi biyu na farkon littafin an bayyana gabaɗaya alƙiblar labarin.

•Su waye taurarin?

•Mene ne jigon labarin?

Duk mai nazari zai iya fahimtar hakan da iyaka wannan rubutun da ya karanta, sauran abubuwan da ya kamata ya sani kuma sai ya shiga cikin labarin sosai. Al-muhim dai dole za a dasa masa son jin ta yadda aka haihu a ragaya game da matasan.

Bayan wannan kuma akwai ragowar gaɓoɓin da ake gina farkon labari da su, wato irin su:

ii- Tsakure

iii- Taɓa ka lashe

iv- Somin taɓi

Asalin kalmar tsakure daga tsakurowa aka samo ta, wato dai a nan marubuci yana so ya nuna wa mai karatu cewa ya tsakuro masa wata gaɓa ne a can cikin tsakiyar labarinsa, wataƙila don yana tunanin gaɓar za ta yi wa shi mai karatun amfani, ko kuma yana so ya nuna masa muhimmin darasin da yake cikin labarin nasa da idan ya yi jimirin karatu zai tarar a gaba.

Ku duba makalarmu ta farko da ta yi cikakken bayani game da jigo.

Taɓa ka lashe da somin taɓi ma duk kusan abu ɗaya suke nufi. Akwai wata al’ada ta mahauta masu sayar da balangu, idan mai saya ya je kafin ma ya faɗi na nawa za a ba shi sukan ɗan yanko masa tsokar somin taɓi ya ci, ta yadda idan ya ci zai ji daɗin suyar ya saya da yawa. To shi ma wannan hikimar kenan, ana tsakuro wa manazarci wata daddaɗar gaɓa ce da za ta tsaya masa a rai ta yadda hankalinsa ba zai kwanta ba sai ya karanta labarin.

Akwai misalai na kowannen su, sai dai kuma idan aka tsawaita zance a wuri ɗaya yana kawo gundira ga mai karatu. Don haka ba sai mun kawo nasu misalan ba za mu ƙara zuwa gaɓa ta gaba, kuma ta ƙarshe a cikin gaɓoɓin dabarun rubuta farkon labari.

V- Sanya rintsi ko zaƙuwa a farkon labari: Idan har marubuci ba zai yi amfani da duk salo biyar ɗin da muka kawo bayanansu a baya ba, wato dai yana so kawai ya buɗe farkon labarinsa da asalin masomar labarin. To yana da kyau matuƙa ya kula da wasu muhimman abubuwa biyu wajen samar da farko mai armashin da zai iya jan hankalin mai karatu. Abubuwan su ne:

  • Ganɗoki
  • Baɗoki

Su ɗin me suke nufi?

Ganɗoki

Ganɗoki a labari shi ne idan mutum ya fara karatu ya riƙa jin labarin yana fusgar hankalinsa, ya riƙa jin har ya matsu ya ji abin da zai faru a gaba cikin labarin. Wato dai a yi ta marubuci Jeffrey Archer da ya ce ‘marubuci ya tabbatar mai karatu ya juya shafi na gaba cike da shauki da son gano mai zai faru a cikin shafin da ya buɗa ɗin’, mai karatu ya riƙa jin ba ya son ya ajiye littafin ma kwata-kwata.

Kodayake ba a iyaka farkon labari ba, a gabaɗaya cikin labari ma saƙa ganɗoki yana da matuƙar muhimmanci ga labari. Duk labarin da ya samu ganɗoki mai kyau yana iya hana shagalalle yin salla a kan lokacinta, yana iya mantar da mai karatu cewa ƙirƙirarren labari yake karantawa ba labarin gaskiya ba.

Yana da kyau mu mayar da hankalinmu sosai a kan wannan gaɓar, saboda hatta alƙalan gasa idan suka samu labari mai ganɗoki yana yi musu tasiri, ta yadda suna iya sha’afa da duba kura-kuran marubucin, su yi ta tafiya daɗin labarin yana fusgar su. Wani lokacin sai sun yi nisa za su tuna cewa ashe fa har da duba kura-kurai suke yi ba nishaɗi kawai ba.

Ba sai an faɗa ba, duk labarin da ya ja hankalin alƙali zai yi wuya shi alƙalin ya ba wa wannan labarin makin da bai kamata ba, irin haka ne ke jawo sai ka ga labarinka ya fi na wanda ya zo na ɗaya jigo mai kyau, amma shi an ba shi na ɗaya kai ba a ba ka ba. To abin tambaya shi ne ta yaya za a yi mu samar da ganɗoki a labaranmu? Wannan yanzu ya kamata mu tattauna kafin mu je gaɓa ta gaba.

Ana samar da ganɗoki ne da dabarar da mai jan kunne yake kira ‘what happens next’ ma’ana me zai faru a gaba?Dabarar ita ce a riƙa yanyanka labari yadda kafin a gama warware matsala guda an sake saƙa wata, ana warware wacce aka sake saƙawa kuma sai wata mai girma da ta fi ta baya ta sake rikitowa. A haka za a yi ta tafiya har a zo ƙarshen labarin. Wannan salon yana sanya mai karanta labari ya ɓata lokacinsa yana karatu cike da zaƙuwa da son jin me zai faru a ƙarshen labarin ba tare da ya gajiya ba kamar yadda na faɗa.

Ku ci gaba da karanta misalin da muka kawo a wannan maƙala ta gaba, wanda zai ƙara mana fahimtar ganɗoki sosai insha Allahu.

Kamar kullum, ƙofar gyara, sharhi, ƙarin haske ko tambaya a buɗe take.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page