Skip to content

Ma’anar jigo da yadda ake samar da shi a labari

Bisa sunna ta rayuwa komai yana da mafari ko tushe, kafin ka fara gini kana buƙatar haƙa fandisho, kafin ka yi shuka kana buƙatar huɗa ko saran shuka, amma shi yin rubutu na zube JIGO shi ne abin buƙata na farko kafin komai. Wannan shi ne dalilin da ya sa tunda dabarun rubutu muke so mu koya daga tushe, ba za mu tsallake jigo ba don gudun kada mu yi tuya mu manta da albasa. Sai dai duk da haka za mu yi ƙoƙarin taƙaita bayani sosai, mu fito da iyaka muhimman abubuwa da suka shafi jigo.

1. Ma’anar jigo

Kalmar jigo tana da ma’anoni guda biyu wato ma’ana ta lugga (literal meaning) da kuma wadda aka ba wani fannin ilimi isdilahi (technical meaning).

Jigo a luggance na nufin abin da ake amfani da shi wajen banruwa a lambu. Muhimmancin jigo a lambu shi ne ya samar da su kansu tsirran ta hanyar amfani da shi wajen banruwa. Idan babu jigo babu ruwa, idan babu ruwa babu tsirrai, idan babu tsirrai su kuma babu lambu. Ganin muhimmancin jigo ga lambu, irin muhimmancin saƙo a labari ya sa manazarta suka yi  amfani da kalmar a matsayin manufa ko kuma saƙo na labari, wanda shi ma a labari idan babu saƙo babu manufa, idan babbu manufa kuma babu labari. (East da Wasu, 1948:47)

Ɗangambo, (1981:6) cewa ya yi “Jigo shi ne saƙo ko manufa ko abin da labari ya ƙunsa, wato abin da yake magana a kai.”

A sauƙaƙaƙƙiyar jumla, jigo shi ne sakon da ake so labarin ya isar ga manazarci (mai karatu). Marubuci zai zaɓi wani maudu’i ko kuma matsala ko gaɓa da ya yi rubutunsa a kai da niyyar haskakawa ko kuma isar da wani saƙo akan wannan jigon ko maudu’i ga mai karatu.

2. Ta yaya ake samar da jigo?

Hanyoyin samar da jigon labari suna da yawa, ya danganta da yanayin kowanne marubuci.

  • Wata rana ina zaune ina danna waya, sai na ci karo da hoton wani zobe na zinare da ya yi matuƙar ƙayatar da ni a wayar, kawai sai na ji a raina ya kamata na yi wani rubutu da zai motsa tunani a kan wannan zoben. Daga haka kawai na samar da jigon labarin ZOBENA.
  • Wata rana labarin wani yaro da ya mari mahaifiyarsa ya riske ni. Abin ya ɗaure mini kai, gani nake ta yaya za a yi duk soyayyar da ke tsakanin uwa da ɗa amma har ya iya marinta. Da na bincika sai aka ce mini ai a shege ta haife shi babu aure, wai gori wani abokinsa ya yi masa ya koma gida a fusace yana mata ƙorafi har ta kai shi ga mari. Tun daga lokacin da na fahimci cewa ba kowanne shege ba ne idan yana tuna ciwon abin da uwarsa ta yi masa yake iya girmama ta, sai na ɗauki jigon na rubuta labarin ZANEN DUTSE don ankarar da mata illar kusantar namiji da haihuwa kafin aure.
  • Wata rana ina zaune na yi tunanin tunda nake ban taɓa yin rubutu a kan siyasa ba, sai kawai na ji ina so na yi hakan. Da tunanin hakan na samar da jigon labarin TUFKAR MAKAHO.
  • Shi kuwa labarin RIKITACCE ina bacci na yi mafarkin jigonsa, da na farka na ji ban manta ba kawai sai na hau yin rubutu.

Abin lura, hanyoyin samun jigo suna da yawa. Akwai masu cewa samun jigon labari ne yake yi musu wahala, su yi ƙoƙari su riƙa faɗaɗa tunaninsu suna zurfafa shi a kan duk matsalar da suke so su yi rubutu a kanta, insha Allahu al’amarin jigo zai riƙa zuwa musu da sauƙi.

3. Raunin labari game da jigo

Raunin labari game da jigo shi ne rashin haskakken jigo a rubutun. Me kuka fahimta da hakan?

Shin ba ku taɓa karanta labari kun gama kun yi nadamar karantawa ba? Akan yi nadamar karanta labari, ko kallon fim ɗin da bai samu haskakken jigo ba, saboda wayargari ake yi labarin ba shi da wata ma’ana ta a zo a gani, ko kuma wani darasi da mutum zai ɗauka a cikinsa. Hakan sai ya jawo makaranci ya yi ta tsaki yana nadamar ɓata lokacinsa wajen karanta abin da ba zai amfane shi ba.

Idan har mutum zai yi tsaki silar karanta labari, to ina kuma ga alƙalan gasa waɗanda ba labarin shi kaɗai suka karanta ba? Ɗaruruwan labarai ne suke shiga manyan gasa, shin ta yaya labari zai zama abin a kalla idan ba a tace an tsefe ba?

4. Ta yaya zan haskaka jigon rubutuna?

Hasken jigo ya dogara ne da irin yadda aka zaro shi a cikin al’umma, shi ya sa zaɓar jigon da ya dace a rubutu yana da matuƙar muhimmanci. A bisa yadda tsarin ɗan’adam yake, ya fi yarda da abin da ya ji ko ya gani ya faru da shi ko waninsa, ashe kenan idan kana so ka kama tunanin manazarcinka, zana masa rubutunka a cikin irin tarin matsaloli ko abin farincikin da ke kewaye da shi.

Abin da nake so na ce, son samu marubuci wajen ɗakko jigon labari ya ɗakko irin jigon da ya shafi al’umma walau kai tsaye ko a kaikaice.

Mun san cewa girgizar ƙasa gaskiya ce kuma ana yin ta, to amma fa duk wanda ya ɗakko jigon girgizar ƙasa a wannan ƙasar tamu ta Najeriya ba lallai ne rubutun na shi ya kama ranmu yadda ya kamata har ya isar mana da saƙo ba, akan wanda zai ɗakko jigon abin da muka sani kuma yake damun mu irin su rashin tsaro, rashin ruwa, rashin wuta, rashin tituna da sauran su. Abin da nake so na ce a taƙaice shi ne ‘hirar shanu a bar wa ɗan fulani da mahauci, hirar kifi kuma sai masunci’.

Shi ya sa duk lokacin da za ka zaɓi jigo na rubutu, musamman rubutu irin na gasa, yana da kyau ka duba wasu abubuwa….

5. Me zan duba wajen zaɓar jigon gasa?

Indai har gasa ce mai buɗaɗɗan jigo ba keɓaɓɓe ba, marubuci yana da buƙatar ya duba abubuwa uku da za su zamo kamar duwatsu uku na ɗora tukunyar jigon sa.

a. Lokaci

Lokacin da mutum zai yi rubutu yana da matuƙar muhimmanci, da lokacin rubutunka za ka auna irin jigon da kake buƙatar ka girka wa al’ummarka har su ci suna santi. Za a fahimci wannan gaɓar sosai idan muka je gaɓa ta gaba.

b. Abin da lokacin ya zo da shi

Bayan duba lokaci, sai a duba abin da lokacin ya zo da shi. A shekaru biyar zuwa shida baya, an samu yawaitar yawan fyaɗe ga ƙananan yara, matsalar ta saka mutane da yawa kuka, yayin da wasu suke Allah wadai! Shin ko za ku iya tuna irin yadda aka riƙa rububin duk rubutun da aka yi shi a kan fyaɗe a wannan lokacin? Idan ban manta ba hatta gasar mata zalla ta Hikayata BBC da jigon fyaɗe kazar shekarar ta yi nasarar ƙyanƙyashe ƙwanta.

A shekaru uku zuwa huɗu kuma sai lokacin ya zo da yawaitar yadda mata suka riƙa yanka mazajensu, a lokacin shi ma idan kana so ka ga ruwan sharhi da jinjina to ka ɗora alƙalamin rubutunka a kan wannan gaɓar.

Shekaru biyu zuwa uku baya kuma aka yi ebola, shekara ɗaya zuwa biyu kuma aka yi corona, wanda babban misali shi ma kazar shekara ta gasar mata zalla ta Hikayata BBC ita ma da coronan ta yi nasarar ƙyanƙyashe nata ƙwan ɗaukakar.

A kula da wani abu, ba wai ina cewa dole ne sai ka yi rubutu a kan abin da lokaci ya zo da shi ba za ka iya yin nasarar girka labarin da manazarta za su yi santinsa, amma dai kula da hakan yana da matuƙar muhimmanci. Idan kuma ba ka kula da zaɓar abin da lokaci ya zo da shi ba, to ka tabbata ka kula da gaɓa ta gaba yadda ya kamata…

C. Su wa za ka yi wa rubutun?

Wannan gaɓa ce mai muhimmanci ita ma, koda ka muhimmantar da gaɓoɓi biyu da suka gabata, to yana da kyau sosai ita ma wannan gaɓar ka ƙara musu da ita.

A lokacin da za ka yi rubutu da ya shafi shari’a, yi tunanin cewa kamar wani alƙali kake rubuta wa labarin. Yin hakan zai ba ka damar ka yi iyaka yinka wajen ɗora rubutun a kan irin layin da ya kamata.

Idan kana rubuta labarin gasa a matsayinka na marubuci ɗalibin Adabi, yi tunanin cewa alƙalan gasar da za su duba labarinka su ma marubuta ne malaman Adabi ba ɗalibai ba, ashe kenan wasu waɗanda suka fi ka gogewa, daɗewa da ilimin rubutun za ka tura wa rubutunka. Kai kanka ka san cewa dole ne ka zo musu da wani salo kafin har ka iya jawo hankalinsu ta ƙarfi ta yaji.

Za mu dakata a nan. amma a rubutu na gaba mun ci gaba da bayani akan yadda ake girka jigo ya koma labari.

Ga duk wanda yake da gyara, sharhi, ƙarin haske ko tambaya ƙofa a buɗe take.

5 thoughts on “Ma’anar jigo da yadda ake samar da shi a labari”

  1. Avatar

    Tambaya na anan shine, shin mutum zai iya fara qirqiran labari ba tare da sanin jigon labarin nasa ba?
    Manene makoman wannan labari?
    Bayan ka fara labari zaka iya samar da jigon labarin ko dole sai kamun ka fara zaka samar?

    1. Jibrin Adamu Rano

      Malama Harira, akwai wasu maganganu da na yi guda biyu:
      a- Jigo shi ne wani muhimmin saƙo da ake so a isar wa mai karatu da wannan labarin…
      b- Shin kin taɓa karanta labari a ƙarshe kin kasa gane alƙiblarsa?

      Fahimtar wannan gaɓoɓin zai iya amsa mana tambayarki. Duk labarin da ba shi da jigo ba ma za ki fahimce shi ba gaba ɗaya. Idan kuma ba a fahimci labari ba ai babu amfanin yin shi.

      Jigo kala biyu ne, babban jigo da ƙananu. Dole ne marubuci ya fara samar da babban jigon labarinsa kafin ya fara rubutu, amma ƙananun jigo ana iya shigo da su ko da an fara labarin ne.

  2. Avatar
    Halimatu Ibrahim Khalil

    Shin idan za’a rubutawa labari suna wanne hanyoyi ake bi sunan ya hau da labarin da kakeson rubutawa?

  3. Jibrin Adamu Rano

    Malama Halima tambayarki har muƙala guda aka yi mata. Ki duba ALAƘAR SUNA DA LABARI, za ki ga akwai suna iri biyu, da yadda kowanne yake, amfanin da kuma tasirin kowanne.
    Na gode.

  4. Jibrin Adamu Rano

    Malama Halima, ki duba maƙala mai lamba 11, in sha Allahu za ki tarar da amsarki har ma da wasu amsoshin.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page