A maƙalar da ta gabata, mun fara yin bayani game da fa’idar samar da ganɗoki a cikin labari, muka ce matsayin ganɗoki da baɗoki a cikin labari, da yadda suke armasa labari, tamkar matsayin dabbobi ne a cikin gidan zoo da irin yadda samuwarsu a ciki yake ƙara wa gidan kwarjini da armashi ga masu ziyara. Irin yadda wanda ya je kallon dabbobi a gidan zoo zai ji idan ya je ya tarar babu dabbobin kirki a ciki, sai tarin karnuka da akuyoyi ko kaji, haka karatun labari zai ƙi yi wa manazarci armashi idan a cikin labarin babu ganɗoki da baɗoki.
Wannan shi ya sa muka ce za mu faɗaɗa bayaninmu game da yadda ake samar da ganɗoki a waccan maƙalar, to cikin amincewar Allah za mu yi bayani yanzu daidai gwargwadon yadda za’a fahimta.
Da farko mun ce ana amfani da dabarar mai jan kunne ta ‘what happens next? ‘ , to hikimar ita ce: Kana cikin nuna tauraronka yana matuƙar buƙatar kuɗin gaggawa da zai yi wani muhimmin al’amari da shi a cikin labarin ya rasa, kwatsam kuma sai ka nuna cewa ga shi ya tsinci wasu maƙudan kuɗaɗe a jaka da za su ishe shi ya yi wannan gagarumin al’amarin har ma ya samu canji. A daidai wannan gaɓar da tauraron yake murna ya samu kuɗin biyan buƙatarsa, to shi ma fa mai karatu murna yake yi cewa tauraronsa ya samu kuɗin wannan muhimmin al’amarin. Ashe kuma a baya ka nuna cewa tauraron mutum ne mai gaskiya da amana, don haka kafin ya yi amfani da kuɗin kawai sai ka nuna cewa ga wasu marayu sun zo wurin shi suna cigiyar kuɗin kayan gadonsu da aka sayar za a raba musu ya ɓata.
Kun ga kenan dolen tauraron ya ɗauki kuɗinsu ya ba su tunda shi mai amana ne kamar yadda ka labarta a baya, don haka sai kawai a ji tauraron ya ɗakko musu kuɗinsu ya ba su suna ta yi masa godiya suna murna da amanarsa sun tafi. To daga nan ne bayan ya ba su kuɗin shi kuma mai karatu zai fara tunanin ‘what happens next?’ ma’ana a ina kenan kuma tauraron zai sake samo wasu kuɗaɗen da zai yi wannan muhimmin al’amarin nasa? Yana cikin wannan tunanin kuma sai ka samar wa da tauraron mafita ta hanyar da bai taɓa zato ba.
Irin wannan tunanin shi zai riƙa riƙe makarancin labarinka ba tare da ya sani ba har ya je ƙarshensa. Ba sai lallai da matsala irin wacce muka yi misali ba, ana iya saƙa ganɗoki a labari ta mabanbanta fuskoki iri-iri. Ana iya saƙa ganɗoki da soyayya, abota, rashin jituwa da duk sauran al’amuranmu na yau da kullum. A don haka za mu bayar da wani ɗan taƙaitaccen misali da wani labarina mai taken Nisan Kwana.
Nisan Kwana…
(Sai da gwaji)
A cikin tsakar rana mai tafasa ruwan kai, a cikin tsakiyar kwaltar mai cike da cunkoso, yana tsaka da tafiya, sai ga shi tsidik a tsakiyar jama’a kamar an jefo shi, a kan tsakiyar siddin babur ɗinsa roba-roba.
Yana zuwa ya riƙa danna amsakuwwar babur ɗin da niyyar cincirindon mutanen da suke wurin su ba shi hanya ya wuce. Amma kuma abin da ya ba shi mamaki shi ne ganin wata mota mai ƙirar ‘Jeep’ da take a gindaye a tsakiyar titin, ta tare hanya ta yadda babu wurin wucewa wadatacce, sai dai motoci su riƙa ratsewa a hankali ta bayanta.
Cikin takaici ya kafe babur ɗin a gefen hanya ya nufi wajen motar, bisa ji da ya yi jama’ar da suka kewayeta suna ta hayaniya. Sai da ya ƙarasa wajen ya fahimci kamar da gayya direban motar ya ajiyeta a tsakiyar hanyar. A tare da shi wata kyakkyawar matashiyar budurwa ce mutane suka kewayeta suna ta ba ta haƙuri, yayin da ita kuma ta yi burus kamar bata ji ba, kamar ita ce ma ta sa direban ya ajiye motar a haka.
“Me yake faruwa ne?” Matashin ya yi tambayar da ya jawo hankulan dayawan jama’ar wurin kan shi, duk da dai babu wanda ya tamka masa in bacin nazarin shi da ya ga kamar suna yi. Gabaɗaya jikin shi a rufe yake da kayan tsere ta yadda babu abin da za a iya gani a jikinsa sai farin sandan wuyansa, kan shi sanye da irin hular nan ta kwano.
“Me yake faruwa a nan ne?” Ya sake maimaita tambayar ta shi jin an rasa mai amsa masa. Wani dattijon mutum ne da ya fara manyanta ya shiga yi masa bayanin abin da ya faru cewa.
“Wallahi bawan Allah ka ga muna zaune a nan wasu yara sun zo wucewa da keke wannan baiwar Allahn..” Ya nuna matashiyar budurwar.
“Mai tuƙata ya buge yaran, shi ne ya fito yana duba su ta sakko tana yi masa masifa wai ya wuce su tafi ya rabu da ‘yan talakawan nan, wa ya ce basu iya keke ba su hawo kan hanya. Shi ne fa mun zo muna yi mata magana kawai sai ta ɗaga hannu ta mare ni ko duba girmana bata yi ba duk da na san ko mahaifinta ba zai girme ni ba, bayan tarin shekaru da na kwashe ba a mare ni ba.” Ƙwalla ta kawo idanuwansa, ya saka hannun riga yana gogewa a raunane ya ci gaba da cewa.
“To shi ne fa wai a hakan ma ta tare hanya wai sai ta ga uban da ya tsaya mana da har za mu tare ta da maganar banza, bayan ta saka waya ta kira mahaifinta ta faɗa masa ƙarya da gaskiya ya ce yana zuwa.” Tsohon bai gama sauke numfashi ba matashiyar budurwar ta sake kwaɗa masa tafi.
“Ni ce nake yi maka ƙarya?” Ta tambaye shi da tsiwa abin da ya yi matuƙar ba wa matashin saurayin mamaki kenan sanadin da ya sa ya daka mata tsawa.
“Ke ba ki da kunya ko? Wannan babban mutumin da ya girmi ubanki za ki mara a gaban taron jama’ar yara da ƙannensa?” Ya tambayeta yana nuna mata yatsa.
“Na mare shi ko zaka rama masa ne?” Ta tambayi matashin saurayin.
“Ok! So kike na rama masa kenan?” Shi ma ya tambayeta tare da cire hular kan shi wacce ta bayyana tsananin kyan surarsa da kwarjininsa.
“Baba riƙe mini hular nan na rama maka marin ka.” Ya furta hakan tare da ba wa tsohon hular ƙarfen da ya cire ya nufi kan matashiyar budurwar gadan-gadan. Sosai saurayin kyakkyawa ne, kuma ya yi mata kwarjini. Amma saboda shegen jiji da kai irin nata, da taƙamar su suke da garin ta dake tana jiran shi ya ƙarasa wajen nata ta ga ƙarshen rashin kunyarsa kamar yadda zuciyarta take raya mata.
“Ke ‘yar gidan uban waye da za ki daki sa’an ubanki kuma ki tare wa mutane hanya?” Ya watsa mata tambayar cikin muryar shi da ta kaɗa hantar cikinta.
“Kana so ka sani ne?” Ta yi masa tambayar da bata bari ya amsa ba ta ce.
“To bari na nuna maka.” Kawai sai ta ɗaga hannu za ta mare shi, ya yi caraf ya riƙe hannunta tare da watsa mata wani murmushi na mugunta sannan ya ce.
“Ni za ki mara?” Bata amsa ba ya ce.
“Tunda ke kin kasa nuna mini ke ‘yar gidan uban waye bari ni na nuna miki ko ni waye.” Bai jira komai ba kawai ya yi amfani da ɗaya hannun nasa ya riƙe hannunta kamar almara, ai kuwa sai ya karya ta ɓaras kamar yadda ake karya guntun itace. Sanadin da ya sa ta ƙwala wata razananniyar ƙara ta azaba yayin da kowa a wurin kuma ya wage baki cikin tsananin mamakin ganganci da tarar aradu da ka irin na matashin saurayin, wasu ma tuni sun ɗora hannu a ka, don sun tabbata haƙiƙa ya kira wa kansa ruwa.
“Zan baki adireshina koda za ki neme ni.” Cewar matashin saurayin yana kallonta har yanzu kuma dariyar muguntar yake yi mata. Ya saka hannu ya zaro biron da ke saƙale a gaban rigarsa, ya juya tafin karyayyen hannun budurwar ya fara rubuta adireshinsa a jiki, yayin da ita kuma babu abin da take yi sai kuka tana bin shi da kallo kamar a mafarki. Yana gama rubutawa kuwa ya miƙe ya karɓi hular kwanon shi a hannun dattijon ya ce.
“Ga adireshina nan za ki ga har da lambar wayata koda za ki neme ni! Kai kuma malam ka janye wa mutane wannan motar idan har ba so kake yi kai ma na karya ka ba!” Ya ƙare yana kallon direban nata.
Ai kuwa babu shiri direban jiki na rawa ya shiga ya janye motar ya ba wa mutane hanya matashin saurayin ya sallami kowa ya ba wa dattijon haƙuri ya saka hular ƙarfen shi ya hau babur ɗin shi bayan ya ɗaga wa matashiyar budurwar hannu, gami da gwalo ya cilla a guje ya bar wurin….
Ta yaya aka samar da ganɗokin?
•Tun daga lokacin da mai karatu ya ji jarumar ta sa direbanta ya gindaya mota a kan titin da tarin jama’a ke wucewa ya tabbatar cewa ta taki wani abin, a ransa zai fara tunanin ‘wace ce ita haka?’ Da ya ji kuma ta mari dattijo sannan ta kira mahaifinta ya zo ya ɗaure mata gindi, mai karatu zai fara cewa ‘wataƙila ‘yar wani hamshaƙin ƙasar ne wanda ya sangarta ta da gata, ba ya son abin da zai ɓata ranta.’
•Sai kuma kawai aka sake jefo wa mai karatu jarumin, da wani salo na tarar aradu da faɗin goshi. Tunda mai karatu ya tabbata cewa jarumar ‘yar mai faɗa a ji ne, ya san tabbas jarumin ba zai iya karyata ya ci bulus ba sai idan ya taki wani abin shi ma. A ransa zai fara tunanin ‘To shi wannan jarumin me ya taka? Ko shi ma wani ƙusan ne a ƙasar?’ To idan ba ƙusa ba ta yaya za ka taɓa ‘yar manya kuma ka rubuta mata adireshin ka da gadara?
Da waɗannan tunane-tunanen za ka riƙe zuciyar mai karatu, ka saka masa zaƙuwa, zumuɗi, da ɗoki ya ji ya matsu ya buɗa wani sabon shafin don gani irin wainar da za a toya. To wannan shi ne taƙaitaccen misali na ganɗoki, wato dai a sanya wa mai karatu ɗokin labari a ransa.
Ku duba maƙala ta gaba inda muka tattauna game da baɗoki, wanda shi kuma kishiyar ganɗoki ne.
Kafin sannan kamar kullum, ƙofar gyara, sharhi, tambaya ko ƙarin bayani a buɗe take.