Bismillahir rahmanir rahim
Daji ne sosai da ya ke cike da dogaye da kuma gajerun bishiyoyi wanda ganyayyakinsu suka kasance koraye sharr.
A can wata kusurwa mai kama da lambu, wata matashiyar yarinya ke zaune kan wani dutse, ta zira ƙafafunta a cikin wani ƙaramin ruwa da ke gudana. Gefen ta kuwa wani matsakaicin kwando ne da ta cika shi da kayan marmari. Aƙalla shekarunta na haihuwa za su kai 16. Kyakkyawa ce fara sol, ga diri na jiki, irin su ake yiwa laƙabi da ƙasaitattun mata.
Sanye take da kaya irin na kabilar Yoruba, wanda kalarsu ya kasance shuɗi, hannayenta, kafafunta da kuma wuyanta cike suke da duwatsun ado masu matukar kyau. A sama kanta kuwa wata hula ce mai kyau da ta rufe mata saman kai, sai dai ana iya hango gashinta baƙi sidiƙ kuma dogo daga inda hular ba ta rufe bah.
Ajiyar zuciya ta sauke tare da share kwallar da ta zubo mata, ko me ya sa suke rayuwa a wannan jeji? Me ya sa mahaifiyarta ta kasa ba ta gamsasshiyar amsa game da rayuwarsu? Me ya sa za su bar cikin mutane su dawo tsakiyar dabbobi suna rayuwa?.
“Ya kamata na san abin da Maama ke ɓoyewa tsawon shekarun nan” ta fada a siririyar muryarta mai dadin amo. Lokaci guda ta miƙe tare da ɗaukar kwandon ta fice a lambun ta bi siririyar hanyar da za ta sadata da gida. Abu ta ji yana bi mata ƙafa, ba ta ko kula ba ta sunkuya ta janyo don ganin mene ne.
Murmushi ne ya suɓuce mata da ta ga wani ƙaramin maciji kore, babu ko firgici ta ƙora mai ido tana juya shi a hannunta. “Ban san ka a wannan yankin ba.” Ta faɗa a hankali. Kwantar da kai macijin ya yi a kan yatsunta yana lumshe ido, gabaɗaya rayuwarta tare da dabbobi tayi su, masu hatsari da akasin haka, shi ya sa ta kan gane duk wata alama da suke yi.
Tsugunnawa tayi tare da miƙar da hannunta a ƙasa, a hankali macijin ya sulale ya shige cikin ciyayin da ke wajen.
Kwandon ta ɗauka ta cigaba da tafiya cike da tunanin yadda tun tasowarta ba ta da wasu abokan hulɗa sai dabbobi, idan aka cire mahaifiyarta, tana jin daɗin rayuwa da su sosai amma duk da haka tana son ta kasance cikin jinsin mutane ƴan’uwanta, wannan wani buri ne da take addu’a da fatan ya kasance.
Kasancewar a daji bai hana ta samun ilimi ba daidai gwargwado, kama daga kan ilimin addini da na boko, ado da kwalliya, girke-girke, gyaran jiki da sauran abubuwa da ya kamata ta sani a matsayinta na ƴa mace. Ɗaki guda Maama ta ware a gidan don koya mata karatu da sauran abubuwa. Ba su rasa komai na jin daɗin rayuwa da mutum zai buƙata ba, amma duk da haka ba ta son wannan gidan, tun da tayi wayo ta fahimci a inda suke rayuwa. Tana sha’awar tayi rayuwa da ƴan’uwa da abokai kamar yadda take karantawa a littafan da Maama kan siyo mata a duk lokacin da ta shiga cikin gari.
Tun tana yiwa Maama tambayoyi tana amsa mata har aka kai gaɓar da Maama ta haramta mata yin kowace irin tambaya da ta shafi dangi ko rayuwarsu a nan ɗin.
A daidai nan ta iso wani ƙaramin muhalli mai ɗauke da wani ginin laka mai kyau sosai, ɗakuna ne guda uku ta gefen dama, sai wani madaidaicin kitchen, daga can gefe guda kuwa banɗaki ne. Duk da ginin laka ne hakan bai hana ƙayatuwarsa ba. Ta gefen hagu kuwa wata rumfa ce ta kara mai kyau wacce aka yi ginin laka a cikinta aka fitar da samfurin kujeru wanda za a iya zama a huta. Gabaɗaya wajen zagaye ya ke da shukoki masu kyau da tashin ƙamshi.
A tsaye take tana ƙarewa wajen kallo da kyau, wani sashi na zuciyarta na ƙoƙarin karyata tunaninta na cewa Maama ita kaɗai tayi gini haɗe da tsara wannan waje. Dole akwai wani ko wasu da suka saka hannu. Amma su waye? Tambayar da tayi wa kanta kenan, don tun tasowar ta ba wanda ta taɓa gani ya tako inda suke. “Ko dai hakan na nufin Maaman kaɗai tayi ginin?.” wani sashi na zuciyarta ya sake tambayaa, girgiza kai tayi a hankali tana mai faɗin, “Inaaa! Ba ita kaɗai tayi wannan aikin ba.”
Dafata da ta ji anyi ne ya katse mata tunanin, koda ba ta juya ba ta san mahaifiyarta ce. “Ayo mi (Farin cikina)!.”
Juyuwa tayi tana kallon Maama da murmushin yaƙe a fuskarta tace, “Iya mi (Maamana).”
“Tsayuwar me kike haka sarauniya?.” Ta faɗa tana jan hannunta suka nufi rumfar hutunsu. “Akwai abin da ke damun ki ne sarauniyata?” Ta sake yi mata tambaya bayan ta zaunar da ita.
Kallon Maamar tayi wacce ta ajiye mata ruwa tana ƙoƙarin zuba mata abinci dake ajiye a tukunya can gefe tace, ” Maama ki kira ni da Eraj ɗina kawai, ni ba na son wannan sarauniyar.” ta ƙarasa maganar tana shagwaɓe fuska.
Ba tare da ta waiwayo daga abin da take yi ba tace, “Me ya sa ba zan kira ki sarauniya ba bayan daga gidan sarauta kika fito? Ko ni ban kira ki da haka ba ai mutane za su kira ki.
A firgice Eraj ta tashi ta isa ga Maama ta riƙe ta gam tare da faɗin, “Gidan sarauta? Maama yau ke ce ke maganar dangina? Don Allah ki fada mini kar ki ce a’a Maama!.” Ta ƙarasa maganar da rauni sosai a muryarta.
Maama da ba ta san zancen zucinta ya fito fili ba ta kalle ta tare da miƙa mata plate ɗin abincin tace,” Ki ci abinci Eraj, ba ki ko karya ba.” ta ƙarasa faɗa tana miƙewa don ta fice a rumfar.
Riko mata kafa Eraj tayi hawaye na bin kuncinta tace, “Maama don Allah!”
Ɗago ta tayi tare da share mata hawayen fuskarta tace, “Ba wannan lokacin ba, ki ci abinci kawai.”
Har Maama za ta fice sai kuma ta dawo saboda sanin halin Eraj ɗin, in dai ba tambayar ta amsa mata ba, to ba abincin za ta ci ba sannan za ta ƙara wa kanta damuwa a kan wacce take ciki kullum, zama tayi tare da cewa, “Eh Eraj, gidanku gidan sarauta ne.”
“Maama!.” Iya abin da ta iya furtawa kenan saboda tsananin mamaki da farin ciki da ya lulluɓe ta lokaci guda.
Kallon ɗiyar tata tayi cike da tausayawa, lokaci guda ta hangi farin cikin da ba ta taɓa gani a fuskarta ba saboda da kawai ta ji wata magana da ta danganci danginta. Za ta so a ce yadda Eraj ke so da kaunar kasancewa da danginta su ma su yi nata, sai dai kash ta san wannan abu ne ba mai yiwuwa ba. Ba za ta taɓa dangana Eraj da danginta ba, har yanzu tana kallon lokacin da wannan ahalin ke azabtar da rayuwarta.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta sauke ta kalli Eraj wacce ta zuba mata idanu tana jiran amsarta, murmushi tayi gami da cewa, ” Eh Ife! Mahaifinki shi ne ɗa na farko ga sarkin da ke mulkar wata masarauta a ƙasar yarbawa, UMUAPALA ROYAL KINGDOM, shi ne magajin mahaifinsa da zarar ya kwanta dama. Ina fata yanzu kin gamsu da dalilin da ya sa nake kiran ki sarauniya?. ” Ba ta jira amsar Eraj ɗin ba ta sake miƙewa don tafiya.
“Maama!.” muryar Eraj ɗin ya doki kunnenta, juyawa tayi da nufin yi mata magana. Gabanta ne ya bada wani sauti rass, lokaci guda tashin hankali ya bayyana a fuskarta.