Sansanyar iskar damina ce ke kaɗawa, alamun za a yi ruwa, saboda yadda labulen ɗakin da na taga ke rawa. Na ƙara jan ɗan fallen zanin da nake lulluɓe da shi na rufe ƙafafuna. Naso a ce zanin ya rufe min jikina har zuwa kaina, amma saboda rashin girmansa bai kai ba. Babban abin takaicin ma shi ne zanin ba shi da kauri sosai, ballantana ya hana iskar daminar da ke busowa, sanya jikina karkarwa.
A daidai lokacin da rugugin hadari ya haɗu da tsawar da ake yi, a lokacin ne na ji kamar an turo ƙyauren kofar da aka rufe ɗakin, wanda dama ba sakata nake sawa ba tura ta kawai nake yi. Na yi tunanin ko Ummi ce ta shigo ɗaukar abu, saboda dama a cikin ɗakin take ajiyar kayan wanke-wanke da sauran shirginta. Ni kuma idan dare ya yi sai na shigo na yi shimfiɗata.
Motsin shigowar mutum da na ji ya sa na firgita, don na san idan Ummi ce za ta yi magana ko gyaran murya don in san ita ce. Kuma ma me Ummi za ta shigo ɗauka a cikin daren nan, kuma ga hadari. Alhalin duk kayan taren ruwa da ake ajiyewa a wajen indararo na saka su a wurin da aka saba ajiyewa. To, ko kuma dabba ce?
Na ɗauke numfashina ban yi motsi ba, sakamakon yadda na ji alamun motsin yana kusanto inda nake kwance. A raina ina cewa, ai in dabba ce ba za ta shigo cikin sanɗa ba, tunda ita ba wayo take da shi ba.
“Salma.”
A cikin raɗa na ji an kira sunana. Muryar namiji ce, kuma da alamun naso na gane muryar waye. Amma saboda rugugin hadari da tsawa da ake cigaba da yi, ban iya tantance muryar ba. Kuma bana jin ina da natsuwar da zan tsaya tunanin ko wane ne ya shigo min ɗaki a wannan baƙin daren.
Na ji alamun mutum yana matsowa kusa da ni. Na ji an taɓa ƙafafuna. Zumbur na miƙe zaune. “Wane ne?”
“Kar ki yi magana da ƙarfi. Ni ne, Salma. Ki yi shiru, na kawo miki nama ne!”
Gabana ya sake faɗuwa, musamman da na gane muryar Bala ne, ƙanin Umma.
A tsorace muryata na rawa na ce, “Kawu, don Allah ka fita. Ba na so. Me ya sa ka shigo min ɗaki?”
“Ki yi shiru. Abin daɗi na kawo miki. Ki bani haɗin kai kawai. Za ki samu alheri a wajena.”
Da sauri na yi yunƙurin tashi tsaye, sai na ji ya rarumo ni, na faɗi a jikinsa. Ya yi caraf ya matse ni a jikinsa. Muka shiga kokawa da shi, ina ƙoƙarin ture shi daga kaina. Duk da ƙarfinsa da nawa ba ɗaya ba ne, amma ban bari ya ribace ni ba. Da na ga abin nasa da gaske ne, sai na yi yunƙurin yin ihu.
“Wayyo Allah, Umma!”
Na ji ya yi sauri ya rufe min bakina da wani tafkeken tafin hannunsa wanda ya sha kanta, saboda riƙon garma. “Ki rufa min asiri mana, Salma. Soyayya ce ta kawo ni, ba cutar da ke zan yi ba.”
“Uhhmm… Uhhmm… Uhhmm..”
A zuciyata ina son in ce masa, ya fita min daga ɗaki ba na buƙatar soyayyar. Amma babu yadda zan furta saboda ya matse min baki da kafcecen hannunsa, yayin da yake ƙara danne jikina yana ƙoƙarin hawa kaina. Duk da dagewar da nake yi don kar ya ci galabata, amma da alamun ƙarfina ya gaza. Dama yaya ƙarfin gardin namiji mai kimanin shekaru ashirin da biyar zai yi daidai da na ƙaramar yarinya ƴar shekara goma sha biyar?
Wata dabara ta zo min. Na dage iya ƙarfina na gantsara masa cizo a tafin hannun, amma abin ka da hannun da ya saba da riƙon fatanya. Ko gezau bai yi ba! Duk da haka bai nuna alamun zai sake ni ba. Don haka na fara kai hannuna gefen inda nake kwance ko Allah zai sa in samu wani abu da zai taimake ni in kuɓutar da kaina. Caraf, cikin ikon Allah sai hannuna ya kama wani abu mai kama da muciya. A hankali na jawo shi, na taƙarƙare da duk ƙarfina, na buga masa a daidai kansa. Sannan na yunƙura na shure shi da ƙafata, yayin da ya sake bakina yana ƙoƙarin dafa kansa.
“Umma…! A zo a taimake ni!! Wayyo Allah!!!”
Na ƙara kwarma ihu da ƙarfi. Da alamun hakan da na yi ya tsorata shi, don na ji yadda ya ruga a guje ya fita, har ma na ji kamar ya buge da ƙyauren ƙofar ɗakin. Fitarsa ya sa na ƙara fashewa da wani kukan. A lokacin ne kuma na ji an sake turo da ƙyauren ɗakin, duk da yake akwai duhu amma na gane Umma ce.
“Kyauta!” Ta kirani da sunan da ita kaɗai take kirana da shi, kasancewar ba ta kiran ainihin sunana.
Walkiyar da aka yi ita ce ta haske ɗakin, yayin da na yi sauri na rungumeta ina kuka. Ita ma ta sa hannu ta rungume ni tana tambayata. “Me ya sa kike kuka, ‘yata? Wani abu ya faru da ke ne?”
“Mama, ni ba zan iya kwana ni kaɗai a ɗakin nan ba.” Na faɗa ina cigaba da kuka.
“Zo mu je ki kwanta a ɗakina.”
Na bi ta muka fita daga ɗakin, ina lulluɓe da zanin da nake rufe jikina, yayin da iskar ruwan sama ke ƙara kaɗawa. Umma ce ta jawo ƙyauren ɗakin ta rufe. Sannan muka wuce zuwa ɗakinta, inda muka kwanta tare a kan ƙaramin gadonta, na rungumeta a jikina ina shassheƙar kuka, tana shafa bayana cikin rarrashi da nuna damuwa. A wannan lokacin ne tunanina ya fara komawa baya ina ƙoƙarin hararo abubuwan da suka faru da rayuwata.
Ni dai na taso ne a cikin maraici da rashin gata. Rayuwata ta gamu da gwagwarmaya iri-iri, waɗanda a koyaushe na tuna da su sai na zubar da hawaye. Kafin mutuwar mahaifina, ni da ummata da ƙanina Musa, muna rayuwa ne ta rufin asiri. Kasancewar babana jarumi ne wajen neman na kansa da kula da sauke haƙƙoƙin iyalinsa. Duk da kasancewar bai yi ilimin boko ba, amma yana da burin ganin mu yaransa mun samu ilimi mai inganci da za mu taimakawa kanmu da al’ummarmu. Yana ce mana, “Ilimi shi ne fitilar da ke haskawa mutum hanya don ya fahimci rayuwarsa da abubuwan da ke kewaye da shi. Kuma ilimi haske ne mai yaye duhun jahilci.”
Sai dai Allah bai nufa mahaifinmu zai yi tsawon kwanan da zai cimma burinsa a kanmu ba, sakamakon kisan gillar da masu garkuwa da mutane suka yi masa, bayan sun sace shi a hanyarsa ta fitowa daga gona, sakamakon kuɗaɗen da suka nema don kuɗin fansa ba a samu ba. Kodayake a wata majiya na ji cewa, wai haɗin baki ne da wasu ƴan’uwansa da suke masa hassada da arziƙin da ubangiji Ya yi masa, saboda ƴan’ubanci. An ce ma su ne suka hana a sayar da gonakinsa don a biya kuɗin fansa, har masu garkuwar suka gaji da ɓata musu lokaci da ake yi, suka kashe shi. Wannan ya bai wa ƴan’uwan mahaifinmu damar mallake dukiyarsa, da wulaƙantar da rayuwar iyalinsa. Don na ji har Kawu Tanko yana iƙirarin shi yake so ya auri mahaifiyarmu. Kamar wata kayan gado!
A dalilin haka ne watarana cikin dare ba tare da kowa ya sani ba, ta tattara wasu daga cikin kayanmu, da asubar fari kuwa zakara ya bata sa’a, ta bar garin zuwa asalin mahaifarta, wato garin iyayenta a Sabon Birni. Da nufin ta tsira da mutuncinta da kuma samar wa rayuwarmu makoma mai kyau, domin ta san akasarin ƴan’uwan mahaifinmu ba imani ne da su ba!
Sai da gari ya waye ne, bayan mun idar da sallar asuba, sannan nake gaya wa Ummata abin da ya faru jiya da daddare tsakanina da ɗan’uwanta Kawu Bala. Na lura hankalinta ya yi matuƙar tashi, kuma ta damu sosai. Har ta rarrashe ni, sannan ta yi min alƙawarin ɗaukar mataki akan abin. Sai dai ta roƙeni da kada in bari kowa ya san wannan maganar, in ɓoyeta a raina.
Da hantsi ina wanke-wanke a tsakar gida, sai ga Kawu Bala ya shigo cikin gidan da ɗaurin bandeji a ƙafarsa da kuma alamun miki a goshinsa. Ina jin mutane ana tambayarsa ko me ya same shi, shi kuma yana musu ƙaryar sun faɗi a mashin ne cikin dare. Da yake gidan da muke gida ne na gandu, wato irin gidan gadon nan mai sashi-sashi. Duk inda ya shiga sai jaje ake yi masa. Ni dai kaina na sunkuye ina aikin da ke gabana, na yi kamar ban san me yake faruwa ba. Sai dai duk san da ya zo gilmawa muka haɗa ido da shi sai in ga yana hararata. Amma bayan kwana biyu, sai na lura yana kauce min, ba ya yarda mu haɗa ido, kuma duk yadda wani abu zai haɗa mu da shi a cikin gida ko a waje yana kiyayewa.
Ko da na tambayi Umma ko ta yi masa magana ne, sai ta tabbatar min da zatona gaskiya ne. Ta ce ta ja kunnensa da kada ya kuskura ko da wasa ya sake kusantar inda nake. A nan ta bar maganar ba ta sake cewa uffan ba, nima kuma ban sake tambayarta komai ba. Amma abin da ya faru ya ƙara sa min tsoro da rashin yarda da maza, don ko yaya na ga namiji yana sake min fuska, musamman wanda ya girme min ko babban mutum, na kan yi nesa da shi, kuma ba na yarda wani abu da za ta kai ga keɓewa ko wata magana ta soyayya ta haɗa mu da wani. Musamman ma da yanzu nake ƙara zama budurwa, surorin jikina na ƴa mace suke ƙara bayyana.
Hankalina bai ƙara tashi da al’amarin wasu mazan ba, sai rannan a makaranta, inda ƙawata Sailuba take kuka tana ba ni labarin fyaɗe da wani makwafcinsu ya yi mata, yayin da ta kai masa koko da ƙosai da suke sayarwa da safe.
Ta ce, “Na saba samunsa a ƙofar shagonsa da safe ya karɓa, ya bani kuɗina. Wannan karon da na kai masa, sai ban same shi ba, ina ta sallama ban ji motsinsa ba. Sai na ji muryarsa daga lungun da suke shiga wanka kusa da shagonsa, yana ce min in shiga in ajiye masa a ciki, akwai kuɗi a tsakar ɗakin in ɗauka. Ban ji komai a raina ba, na kutsa kai na shiga, saboda sanin ba ya ciki. Ai kuwa da shiga ta, na ajiye kwanon ina ƙoƙarin ɗaukar kuɗin, sai na ji motsi a bayana kafin in fahimci mai ke faruwa, sai na ji mutum ya ribace ni ya jefa ni kan katifar da ke shimfiɗe a ɗakin. Ashe ya laɓaɓo ne ya rufe ɗakin ban ji motsinsa ba, don ya samu damar cimma mugun nufinsa a kaina!”
Sailuba ta ƙarasa maganar cikin hawaye, yayin da nima na ji idanuna sun cika da ƙwalla, tausayinta ya kamani. A raina na ji takaicin irin halin da ‘ya’ya mata ke shiga a hannun azzaluman maza, marasa tausayi. Saboda yadda suke lalata musu rayuwa, da jefa su cikin mawuyacin hali.
“Kin gaya wa mamanku abin da ya faru?”
Ta ce, “Na gaya mata, amma ta ce in kame bakina kada kowa ya ji. Wai zan iya rasa mai aurena, za a ce ni ba cikakkiyar budurwa ba ce. Tunda wani namiji ya taɓa saduwa da ni.”
Wannan magana ta yi matuƙar girgiza ni, ta kuma sa ni cikin tsananin tunani da fargabar makomarmu, a matsayin mu na ‘ya’ya mata. Me ya sa iyaye ke ƙoƙarin rufe irin waɗannan abubuwa da suke faruwa da yaransu mata, da sunan kare mutuncinsu. Ba sa tunanin abin da zai iya faruwa da yaran nasu a gaba, yayin da su azzaluman da suka aikata musu fyaɗen suke can suna cigaba da rayuwarsu, babu abin da ya sha musu kai.
Bayan ‘yan watanni da faruwar wancan al’amari, sai Sailuba ta fara rashin lafiya, tun tana fashin zuwa makaranta, yau ta zo gobe ta ba za ta zo ba, har zuwan ma ya gagara. Ashe ciki ne ya bayyana mata, sakamakon fyaɗen da aka yi mata. Ba a jima ba, sai muka ji labarin rasuwarta. Ashe babarta ce ta yi ta bata magungunan zubar da ciki na gargajiya, har abin ya kai ta ga ƙarar kwana, bayan ta yi ta zubar da jini, ba tare da an kaita asibiti ba. A maƙwafta ana cewa wai ciwon daji ne, daga ni sai mahaifiyarta kaɗai muka san asalin me ya faru da ita.
Rasuwar ƙawata Sailuba ya canza min tunanina da rayuwata gabaɗaya, saboda tausayawa wahalar da ta sha ta jinya kafin ta rasu. Tun daga wannan lokacin na ƙudiri aniyar ganin na taimakawa rayuwar ƴaƴa mata a duk inda suke, ta hanyar wayar musu da kai da faɗakar da su hanyoyin da za su bi su kare mutuncinsu da ɗiyaucinsu. Ba tare da sun bari wani shashasha kuma azzalumin namiji ya cutar da rayuwarsu ba.
Duk da nasan nima ban fi ƙarfin hakan ta faru da ni ba, kuma ba wani ilimi ko wayewa nake da shi na tunkarar wannan ƙalubale ba. Amma na yi imani in har zan iya samun haɗin kan ƙawayena da ƴammatan gari, mu jajirce, da faɗakar da iyayenmu mata, za mu iya cimma nasara wajen shawo kan wannan matsala. Ko da ba mu kawar da ita gabaɗaya ba.
Bayan an koma makaranta bayan hutun canjin aji, mun zama ƴan aji uku na ƙaramar sakandire, har ma kuma an bani shugabar ɗalibai mata. Wannan ya taimaka min wajen samun damar da na riƙa faɗakar da ƴan’uwana ɗalibai, musamman a lokacin da ake yin jerin gwanon ɗalibai na safe. Kodayake wasu malamai sun yi ƙoƙarin dakatar da ni daga yin taƙaitacciyar faɗakarwar da nake yi, suna ganin iyayi ne kawai da karambani. Amma sai na samu goyon bayan wata malamarmu Malama Amina, wacce ta ce hakan yana da amfani sosai, don zai rage wasu abubuwa na kwamacala da jahilci da suke faruwa a ƙauyenmu.
Rannan bayan an fito daga darasi za a tafi hutun tara, sai Malama Amina ta kira mu ni da Yahanasu, Saude, da Khadija zuwa ofishin malamai. Bayan mun shiga muka tarar da Malam Haruna ne kaɗai zaune a ciki, sai kuma ita da ta shiga yanzu. Ta sa muka zauna akan wani dogon benci da ke cikin ofishin, duk mun yi zuru-zuru kamar marasa gaskiya. Domin Malama Amina na daga cikin malaman da kowanne ɗalibi ke tsoro, saboda ba ta da wasa. Kullum fuskarta a ɗaure take, kamar wacce aka yi wa mutuwa. Ba ta dariya sam, zan ma iya cewa ni dai tunda na shiga makarantar ban taɓa ganin ta yi ko murmushi ba. Kuma idan aka kai mata ƙarar ɗalibi ya yi laifi to, ranar fa kashinsa ya bushe!
Ta katse min tunanin da nake yi, yayin da ta ja kujerar da take zaune gaba, ta ƙara kusantar teburin da aka cika shi da takardu, wanda kuma yanzu shi ne ya raba tsakanin mu.
Ta ce, “Na kira ku ne domin in bayyana muku muna sane da duk abin da ku ke ƙullawa a makarantar nan. Kuma ina mai shaida muku cewa, ba za mu lamunci duk wani abu na rashin kunya ko rawar kai da karya doka a makarantar nan ba.”
Na ji gabana ya faɗi ras! Muka kalli juna da sauran ƙawayena. Ko me aka ce mun yi kuma? Oho.
Ta cigaba.”Ke, Salma! Na fuskanci kina so ki kawo mana wani sabon iyayi makarantar nan, kina hurewa sauran ɗalibai mata kunne ko? Ke har nawa ki ke? Tun baki tafasa ba za ki ƙone ko?”
Malam Haruna da ke zaune yana duba rijistar ɗalibai da ke gabansa, ya yi caraf ya sa baki a zancen cikin fushi. “Ai Malama sai kin yi musu da gaske. Abin nasu yana neman wuce gona da iri. Kuna ganin a makarantar nan akwai wani malami da zai nemi wata ɗaliba ne? Ƙwailaye da ku ƙazamai da ko iya gyara kanku ba ku iya ba.”
Malama Amina ta dakata daga maganar da take yi tana saurarensa, bayan ya gama ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Dalilin kiran da na yi musu kenan, Malam Haruna. Ka ɗan ba mu wuri in yi magana da su, don Allah.”
Ya yi jim kaɗan kamar bai ji daɗin maganar ba, sai kuma ya girgiza kai, ya ajiye biron da ke hannunsa akan rijistar, sannan ya tashi ya fita. Sai da ya fita daga ofishin sannan Malama ta cigaba da magana.
“Kar ku ji na fara muku magana da faɗa ku zaci ko laifi ku ka yi, a’a, sam ba haka ba ne. Amma dole ne mu fahimtar da ku cewa, muna hallare da ku kuma muna sa muku ido, don kar ku je ku yi abin da ba daidai ba, saboda ƙuruciya. Amma tabbas ina tare da ku, ɗari bisa ɗari, kuma ina goyon bayan abin da ku ke yi.”
Muka sake kallon juna muka ɗan yi murmushi a sace, amma ba mu saki jiki ba. Domin har yanzu da take nuna tana tare da mu, fuskarta ba ta sake ba, a ɗaure take kamar mahaukaci ya ci kashi.
“Naso a ce nima na samu ƙwarin gwiwa tun ina ƙarama na yi wani abu mai kama da wannan da kuke yi, don tun ina ƙarama, mijin babata ya min fyaɗe a gona lokacin mun kai masa abinci. Abin haushi da takaici babu abin da aka yi masa, ita babata ma sai musanta abin ta yi, don kar aurenta ya mutu. Ni kuma ta riƙa min barazana tana zare min idanu don kada na kuskura na gaya wa kowa.”
Ta yi jim kaɗan yayin da ta share ƙwallar da ta fara taruwa a idanunta. “Da wannan baƙincikin da takaicin abin da ya faru da ni na girma, yayin da hakan ya sa min tsananin tsoron maza da jin haushinsu. Sai bayan da na fara girma na shiga makarantar ƴammata ta kwana a can birni kusa da ƴan’uwan mahaifina, shi ne na koma can ƙarƙashin kulawarsu. Saboda haka duk wani da zai fito yana magana kan kare ɗiyaucin ƴa mace to, babu shakka zan bashi goyon baya.”
Ta yi shiru, mu ma muka yi gum, kamar mutuwa ta ratsa ta ofis ɗin. A raina ina jinjina halin da ta rayu a ciki, a ce mijin mahaifiyarka shi ne zai yi maka wannan ɗanyen aikin. Ban san lokacin da hawaye ya fara zuba daga idanuna ba.
Ta ce, “Ba kiranku na yi nan don in baku labari ku tausaya min ba, ina so ne ku sani wannan abin da ku ke yi ba naku ne ku kaɗai ba. Amma ina so ku dakatar da maganganun da ku ke yi a gaban sauran malamai, yayin da ake tsayuwar assembly.”
Caraf sai Saude ta ce, “Malama, yanzu ki ka gama cewa kina bayanmu kan abin da muke yi, amma kuma na ji kina cewa mu daina.”
Cikin ƙarin tausasa murya Malama Amina ta ce, “E. Na ce ku dakata ne saboda sauran malamai suna ƙorafi kan abin da ku ke yi. Kun ji dai abin da Malam Haruna ya fara faɗa. Don haka nake so ku daina, ni zan karɓe ku a wannan ɓangaren. Ku kuma sai ku cigaba da yi a tsakaninku ɗalibai da cikin gari. Ba tare kuma da kun ja hankalin jama’a a kanku ba.”
Na ce, “Malama, mun ji daɗin wannan bayani naki sosai. Kuma in sha Allahu za mu kiyaye, ba za a sake jin mun yi magana kan batun ba. Kuma da yardar Allah za mu share miki hawaye, sai mun fallasa duk wani mugun mutum mai cin zarafin ƙananan yara a garin nan.”
“Yawwa, abin da nake so da ku kenan. Allah Ya yi muku albarka. Ku tashi ku koma aji, na ji an buga ƙararrawa.”
Khadija da Yahanasu ne suka fara yi mata godiya. Muka tashi cikin ƙwarin gwiwa da farinciki, muka koma aji don cigaba da ɗaukar darasi.
Yahanasu, Saude da Khadija duk ƙawayena ne da muke karatu tare a wannan makarantar sakandiren ‘ƴammata ta GJSS Ɗandurumi da ke Sabon Birni. Dukkanmu kusan sa’o’in juna ne, ba mu wuce shekaru goma sha biyu zuwa sha huɗu ba. Kuma muna karatu ne a ajin ƙarshe. Labarinmu kusan duk iri ɗaya ne, daga wacce aka ketawa haddi, sai wacce aka ci zarafi a ƙoƙarin a yi mata fyaɗe. Shi ya sa muka haɗa kai don mu ɗauki fansa kuma mu kare ƙannenmu mata masu tasowa daga wannan ɗanyen aiki da wasu lalatattun maza ke aikatawa.
Cikin zaƙuwa da zumuɗi na zayyane wa mahaifiyata yadda muka yi da Malama Amina, ita ma ta tausaya mata ainun, duk da kasancewar yanzu ta zama babbar mace mai iyali, amma a cewar Ummi raɗaɗin da waɗanda aka yi wa fyaɗe suke ji a ransu ba ya taɓa fita daga zuciyoyinsu har abada.
“Kullum abin da nake gaya miki kenan, duk abin da za ki yi matuƙar kina so ya yi tasiri to, sai kin yi takatsantsan, domin waɗanda ki ke so ki yaƙa su ma ba barinki za su yi ba. Shi ya sa ake cewa yaƙi ɗan zamba ne. Kuma ki riƙe addu’a sosai. A matsayina na mahaifiyarki dama wannan wajibina ne, amma bai wadatar ba, sai ke ma kin yi da gaske. Allah Ya tsare mana ku bakiɗaya.”
Tun daga sannan salon faɗakarwar mu ta canza, muka koma bincike kan duk wata yarinya da muka samu labarin an yi mata fyaɗe, tare da ɗaukar sunan wanda ake zargi da yi mata. Sannan kuma muna gaya wa iyayen yara lallai su daina yin shiru, dole ne a riƙa fallasa irin waɗannan azzaluman, in ba haka ba ba za su daina abin da suke yi ba. A daina rufa musu asiri.
Da taimakon Malama Amina muka ziyarci ofishin Babban Jami’in ‘Ƴansanda na yankinmu, wanda ya ba mu cikakken haɗin kai da goyon baya, yayin da ya saurari uzurorinmu. Sannan ya ba da umurnin sanya wasu jami’ai biyu mace da namiji da za mu riƙa aiki tare da su, a duk lokacin da muka samu labarin an yi wa wata yarinya fyaɗe a cikin gari. Su kuma ya ja kunnensu lallai su tabbatar doka ta yi aikinta akan ko waye.
Mun kuma ziyarci gidan Hakimi, inda nan ma Malama Amina ta gabatar masa da buƙatunmu, da kuma haɗin kan da muke nema a wajensa. Ya nuna mana matuƙar jin daɗinsa da wannan yunƙuri namu, ganin ashe shi ma abin ya daɗe yana damunsa. Kuma jin cewa mun je wajen DPO ya sa ya ji daɗin abin. Ya yi wa Malama Amina godiya da taimakon da take bamu, don in ba haka ba da dama mutane ba za su ɗauki abin da muke yi da muhimmanci ba. Daga nan ya yi mana alƙawarin tattaunawa da malaman gari don a riƙa faɗakarwa a masallatai, sannan kuma ya sa Sanƙiransa da yaransa su riƙa bi unguwa-unguwa suna faɗakar da jama’a da jan hankalin iyaye, a daina shiru a riƙa kai ƙara wajen hukuma don ƙwatowa ‘ya haƙƙinta.
Waɗannan nasarori da muka samu sun ƙara ƙarfafa min gwiwa sosai, na kuma ƙara fahimtar lallai ilimi shi ne ginshiƙin rayuwa, kuma mata da sauran al’umma ba za su samu cimma burinsu na rayuwa ba sai sun haɗa kai sun nemi ilimi, kuma sun jajirce. Haɗuwar mu da Malama Amina ya taimaka mana sosai, don ita ce ta yi mana jagora muka fallasa duk masu yi wa yara fyaɗe a Sabon Birni.
Ta kuma tabbatar cewa iyayenmu ba su katse mana karatunmu ba mun je gaba zuwa babbar sakandire, har ma da na gaba. Duk da ƙalubalen da na fuskanta a rayuwata, yanzu kam Alhamdulillahi. A halin yanzu ni malamar jami’a ce inda nake koyarwa a Jami’ar Tarayya ta Ɗanbaiwa sashin nazarin ilimin Fasahar Sadarwa ta Zamani. Shekaru biyar kenan, ina matsayin malama, a lokaci guda kuma ina cigaba da karatuna na neman samun ƙwarewa a matakin Digiri na Uku. Nan ba da jimawa ba, in sha Allahu ina sa ran kammalawa, yayin da zan fara amsa sunan Dakta Salma. Matakin da na daɗe ina kwaɗayin samu.