Ya turo ƙofar ɗakin ya shigo. Na gaishe shi ya ce, "Ki haɗa kayan ki waɗanda kike ganin zaki buƙata zan yi tafiya ne zuwa course kasar Canada na kimanin shekara ɗaya, gobe zan wuce ke kuma daga Airport direba zai wuce da ke gidanku, maybe sai na dawo zan zo in taho dake. Kamar in buɗe baki in ce kawai ba ni takarda ta kayi tafiyar ka, amma kwarjinin shi ba zai iya barina in buɗe baki in yi wata doguwar magana a gaban shi ba, bare har in iya faɗa mishi mara. . .
Allah sarki.
Abokin gaskiya