Ummu da Yusuf da yaya Azima suka haɗa kudi suka sayi ragon suna, ranar da na kwana biyar na tashi da ciwon nono ga zazzabi ya rufe ni, za muje kauyen dawo karɓo magani ganin yadda nake rawar sanyi Innarmu ta ce in kwanta bari ta je ita kaɗai.
Ina nan kwance na tattake a kuryar gado, maganar mata na ji sun shigo falo, ban ko motsa ba illa kara kashe kunne da nayi ina jin hirar da suke ɗaya daga cikin su tana cewa; To kwaɗayi yasa aka ja ma yarinya wahala, ga shi. . .
Dakyau. Fatan alheri.
Na gode kwarai
Allah yasa mugama lafiya