Bismillahir Rahmanir Rahim
Da hannu ɗaya ya bude ɗakin, wanda Farhan ya taɓa gaya min na shi ne tun yana saurayi. Ga mamakina kan luntsumemiyar katifar da ke yashe kan carpet ya wurga ni, ya naɗe hannuwansa akan kirjinsa ya kafeni da ido, "Ke ba ki jin magana ko? Taurin kunne ne da ke ko?” Ya yi kwafa.
"Daga yau idan na ce bana son abu ba za ki yi marmarin ƙara aikata shi ba." Tuni jikina ya soma rawa har ban san sanda na soma fadar gaskiyar lamarinba. "Ka yi hakuri wallahi ga laffayata nan a jaka. . .