Kwalliya na yi sosai cikin wani dandasheshen less golden color na yafa mayafi na koma bisa gado nayi zugum har ga Allah bana son rabuwa da mutanen masu dinbin karamci duk kuwa da san da nake wa Ahmad. Kiran da momi take min ya dawo dani daga duniyar tunanin da na fada, na fito na zauna a kasa nesa kadan da ita.
Na ce, "Ga ni momi" saitin inda na zauna Ahmad yake zaune, kallo daya ya min ya kauda kanshi, nasiha tayi mana ta kuma gaya min akwai dattijuwar da ta samo min suna da dangantaka da mahaifin Ahmad. . .