Skip to content
Part 18 of 28 in the Series Canjin Bazata by Maryam Ibrahim Litee

Kwalliya na yi sosai cikin wani dandasheshen less golden color na yafa mayafi na koma bisa gado nayi zugum har ga Allah bana son rabuwa da mutanen masu dinbin karamci duk kuwa da san da nake wa Ahmad. Kiran da momi take min ya dawo dani daga duniyar tunanin da na fada, na fito na zauna a kasa nesa kadan da ita.

Na ce, “Ga ni momi” saitin inda na zauna Ahmad yake zaune, kallo daya ya min ya kauda kanshi, nasiha tayi mana ta kuma gaya min akwai dattijuwar da ta samo min suna da dangantaka da mahaifin Ahmad za ta zo daga Bauci za ta rika debe min kewa, ta dubi Ahmad “Kai kuma duk da haka ka ce a samo maku a nan, to na yi wa Haj Turai magana ta ce akwai me kawo masu masu aiki, tayi mata magana gobe za a zo da ita. Ya ce, “Allah ya kaimu.” ta umarci Abakar ya kwashe kayana zuwa mota, muka je na yi wa su Haj Babba sallama da Aunty Amarya, Abba baya kasar tun kusan sati biyu da suka wuce.

Mun fito ina kokarin maida hawayen da ke taho min, dan na hango Husna a gaban sashensu tana nata hawayen, a hankali ya tashi motar yana leka fuskata, kuka kike kina san bata kwalliyar?

Na yi mashi shiru shima daga haka bai sake magana ba, mun isa me gadi ya wangale get ya samu waje yayi parking, yana tafe ina biye da shi, Khausar ce cikin sashena ta taremu da sauri tana fadin oyoyo Amarya. Juyawa ya yi mu kuma muka wuce daki mun zauna bakin gado ta ce “Amarya kin sha kamshi.”

Na ce “Ke ni fa Amaryar nan kunya yake bani”. “Dole kuwa a kiraki Amarya dan shima me gidan na ji suna tsiya da Dear yana cewa shi fa ango ne shi kuma yana ‘ Ina? Akwai ma abubuwan da na zo maki dasu, ki dage wajen yin amfani dasu” Kallonta nayi “Hala so kike ya kasheni dan ko Momi ban san iya abinda ta bani ba.”

Ta murmusa “Ki ce Momi ta gyara wa danta wurin? Na ce na ” Na shiga uku” ina kai hannuna na toshe bakinta, ” Wai ke wace iri ce? cire hannun tayi “Daga zan fadi gaskiya”. Idona ya kai kan wani tsalelen show glass da ke aje gefe na ce ” Amma kamar rannan da muka zo ban ga wancan ba? Ta ce ” E yanzu na zo da shi turaruka ne na maiduguri a gida nayi sako sai aka kawo min” godiya sosai nayi mata.

Ya shigo ya shaida min zai fita, Khausar ta ce, “Ko zamu shiga kitchen? Na ce lallai ma wannan maman biyun ba ki jin nauyin jikinki. Sai da aka yi isha’i Ahmad ya dawo shi da Abdullahi, Abdullahi dai dariya kawai ya yi ya ce, ya fi kowa murnar hakan (daidaitawarmu).

Har mota muka rakasu na ce “Sai kin kiramu.” “Haba ke kin fara kin zuwa har in haihu?” Ahmad ya ce ” Amarya ta kan yi wata ko sama da haka kafin ta fara fita, ki dai yi hakuri har ki saukan. Ta ce “lallai au haka ne? Suka yi dariya. Ina hanyar komawa ciki Husna ta kirani ta ce “Ba ki ji part din namu ba ba dadi kin barmu cikin kewa.”

Na ce “Nima cikinta nake kar ki tona zuciyata ina farhan? Ta ce ya ce zai kiraki. ” Kiranta na katsewa na shi ya shigo. Karfe tara da kwata agogon dakina ya nuna zaune nake gaban dressing mirror ina tsala kwalliya na rika tunanin kayan da zan sa dan hudubar da zuciyata ke min duk da gargadin da yayar ke min zunubin da zan kwasa, matukar na aikata abinda nake nufin. Wata jar rigar barci da bata da maraba da babu nasa na saka jan pant na haye gado a buna ina taunar cingam ina jin dadin daddadan kamshin da ke fita jikina, tura kofar da akayi yasani daga kai, na amsa sallamar da ya yi cikin farar jallabiya ya ke.

Ya ce “Taso muje dakina ki dauko hijabinki” na ce ” To” Na daura zane saman rigar na zura hijab sai na bi bayanshi, muna tafe ina dariya a raina wannan shi ake cewa daga baya wai an yi sadaka da bazawara, ina shiga umurtata ya yi da in shiga toilet ya nuna min da hannu in yo alwala ban yi musu ba nayo na fito na same shi kan sallaya muka yi sallah da muka idar ya dade yana addu’o’i daga nan ya juyo ya kama kaina ya karanta addu’ar Allahumma inni as’aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha ilaih, sau uku sai ya saki kan, ya rika tanbayata game da addinina ina ba shi amsa har sai da ya ga na fara hamma, ya ce,

“Na fa manta gwana ce wurin barcin wuri, to hau gado” ba musu na haye kallona yake amma barci da zane hada hijabi ya hawo gadon ya zare min hijabin da zanen sai ya shiga sha’aninshi bayan ya zare jallabiyar jikin shi, ban motsa ba nannauyar ajiyar zuciya yake fiddawa, sai da na fahimci ya kamu ba abinda yake so sai ni din, sai na shiga gunjin cikina tilas ya saurara min cikin wata Irin murya yake tambayata abinda ke damunta, na ki magana kuma na ki barinshi ya ci gaba da abinda yake, ina ji ya sassauta rikon da ya yi min sai na mike a guje na bar dakin na shige nawa na rufe, barcina na shiga yi lakadan ban farka ba sai asuba nayi sallah sai na cire keyn na koma na kwanta, sai dai na ji ana shafa fuskata, a hankali na bude idona zaune yake gabana “Ta so muyi breakfast.”

“Ni fa banyi wanka ba” na fadi a hankali ya ce, ” Muje in taimaka maki” Na ce ” A’a” ya ce “To ina jiranki” na mike yana bi na da kallo, na gama na fito yana zaune inda na barshi, sai dai yanzu waya yake, a darare nayi shafar na zabi kayan da zan sa na koma bathroom na saka cikin less din da ya aiko mun ne kalarshi blue, na zauna daf da kafafuwanshi ina gaisheshi, ya amsa yana shafa gefen fuskata sai ya mike ina biye da shi har kan dinning, nayi mamakin wanda ya yi girkin kamar yasan tunanina ya ce “Albarkacinki momi ta aiko da shi ta ce har sai kin saba da zaman gidan, sai ki rika yi da kanki” Kura ma fuskata ido ya yi har saida na sunkuyar da kaina, yasa hannu ya dago min fuskar sai na rufe idanuna ya ce,

“Me yasa ki ka yi min abinda ki ka yi jiya? kin kuwa san a halin da kika barni ba ki ji tausayina ba? Shekara guda har da wasu watanni ina zaune haka sai jiya nasa rai za ki min haka. ni dai da nasan ban da abin cewa sai nayi shiru, da muka kammala danni sama sama na karya saboda ban taba cin abinci gabanshi ba,kama hannuna ya yi zuwa doguwar kujera ya kwanta sai ya kifani kanshi, yana gaya min kalamai masu dadi na yanda nake a ranshi, mun dauki wani lokaci a haka.

An kawo me aikin da Momi ta ce za a kawo yau, me suna ma’u na nuna mata inda za ta zauna,wadda ta kawo ta ta tafi ya tara masu hidimar gidan ya gabatar mini dasu, akwai me gadi sai me kula da shukoki wanda Tonny ne ya dawo sai me wanki da guga sai direba wanda zamana zai yi sai cefane, ma’u kuma zata rika masu abinci. Da rana Momi ta aiko da abinci me yawa muka ci har masu hidimar gidan. Da daddare ma haka aka kwata nayi kwalliya ta jan hankali ya kawo kanshi nayi mirsisi naki. Ranar laraba wadda na ci barcina na more sannan na tashi na ci abincin da momi ta aiko ganin ba a taba ba sai nayi tunanin bai dawo ba, na koma daki na watsa ruwa saboda ana fama da zafi, sai na dauko wata doguwar riga me taushi yadinta baki ne sai aka dan mata kwalliya da fari bata da nauyi kuma me kama jiki ce tsawonta ta gota gwiwa kuma me kama jiki ce hula nasa wa kaina, na zura silifas, baya na zagaya dan in sha iska, kan kujerar da ke girke ina zaune ina cin apple ina jin dadin daddadar iskar da ke kadawa kamar an ce in dubi wajen motsa jiki, Ahmad na hango kan mashin din motsa jiki, sai faman digar gumi yake, gani nayi ya sauna ya nufo inda nake daga shi sai gajeren wando kallo daya nayi mashi na sunkuyar da kaina.

A hankali na gaisheshi, bai amsa ba kallona kawai yake ya zauna kujerar da ke fuskantata, “Je ki kawo min ruwa” Na mike cikin jin kunyar rigar da ke jikina na wuce na hado mashi hada lemo da wani danbun naman da nayi na ajiye gabanshi, kiran sunana ya yi na amsa ya ce “Me yasa ne wai ni ba ki iya kallona? Sai ki yi ta faman sunkuye sunkuye, na ga kin ki bani dama ne da kin amince min da yanzu na zame maki mutumin da za ki fi jin dadin mu’amala da shi sama da kowa.”

Ya kai danbun naman bakinshi ya ce, “Amma ba karamin dadi ya yi ba, momi ta aiko maki da shi? Na girgiza kai “Ni nayi” Ya gama ci ya kara shan ruwa ya mike “Zo muje daki ki tayani fira” nasan irin firar da yake nufi dan dai ban iya mashi musu na bi bayanshi har dakinshi jagwalgwalani ya yi tayi ina mashi kuka, sai da ya gamsar da kanshi ya mike ya shiga wanka, saida ya gama shiryawa ya juyo inda nake kwance.” Zan leka hospital akwai wani patient dina da zan kara dubawa.”

Ya kamo hannuna muka fito har wajen motarshi, sai da ya bace wa idona sai na koma ciki raina cike da sanshi, sai dai ina jin ba zan iya sallama mashi kaina ba sai na ja ranshi ko na sati ne ya ji Irin takaicin dana dandana. Wasa wasa sai da week din ya kare bai samu kaina ba duk ya zama wani mara kuzari ni kaina nakan tausaya mashi dan kullun nake shigar da zan tsokanoshi.

Yamma likis ya shigo wanka kawai ya yi na nemi ya ci abinci ya ce in bar shi in dauko lillibina kawai. Cike da mamaki nayi yanda ya ce na same shi cikin mota, har muka bar unguwar bai yi magana ba duk da nasan a yan kwanakin nan ba shi da walwala amma yau kam ya fi kullun sai na ji nadamar abinda nake ta lullubeni dan nasan sarai zunubi nake kwasar ma kaina istigfari na shiga yi a hankali.

Unguwarsu ya shiga wanda sai na ji na samu kaina da jin faduwar gaba, jama’ar gidan muka fara gaisarwa sai muka dire sasan momi momi tayi murnar ganinmu amma ba kamar Husna na ce “Ba wani ai ba ki iya leko ni ba” Ta ce “Yi hakuri Auntyna dazu ma direba ya kawo min sakonki “ashe kina tafe na gode.” Murmushi na yi “Ina Farhan da Abakar?”

Ta ce, “Sun nufi Bauci dazu su da Abba” Momi ta fita tana amsa waya, muna nan zaune muna maganar komawar da Husna za tayi makaranta gobe Ahmad ya shigo ya zauna, kallon Husna kawai ya yi ta tashi ta bar falon, kujerar kusa da ni inda Husna ta tashi ya dawo ya zauna kiran sunana ya yi na kara shiga nutsuwata kafin na amsa ya ce “Ban so ta kaimu da haka ba Shuhaina to ba yanda zan yi, na rasa abinda ke damunki a matsayinki na yarinya me tarbiya wadda tayi karatun islama, tasan addininta dan nasan kinsan abinda kike abu ne daya sabawa addininmu na islama, kina ganin yanda kika maida ni wani sukurkutacce da da ba ki kusa da ni na hakura amma yanzu ina ganinki gabana ina kuma sane da cewa ke din mallakina ce, ga shi an cika maki surarki ta yanda ba wani namiji lafiyayye da zai kauda kai daga gareki na rasa me zan yi ki gane irin kaunarki da ta kamani, ki bar ni ma in ji da radadin da zuciyata ke yi na zargin kaina da wofintar da matar da aka duba girma da mutunci aka bani har kika yi wahalar ciki wanda ni ne me shi kika yi ta haihuwa har abinda kika haifa ya rayu tsawon wani lokaci a matsayina na mahaifinta ban mata komai ba na hakkin diya akan mahaifinta hasalima ban taba ganinta ba.”

A hankali na ce “Kama daina damun kanka dan hadisin manzon Allah ne abu uku an yafe wa al’ummata, na farko abinda akayi da kuskure, da abinda akayi da mantuwa da wanda aka tilasta mutum akanshi, ka ga kuskure kayi kuma ka gane ciki kuma ba ka san da shi ba. Ya ce, “To ke kuma barin da nayi maki fa alhalin kina matsayin matata?”

Na ce, “Tuni na yafe maka dama kuma ban taba neman sakayya akanka ba.” ya ce “Na gode amma hakan ba zai hana in gaya wa Momi abinda kike min na rowar kanki.”

Gabana ne ya yi mummunar bugawa jin zancenshi na fara mashi kuka, da wane idon zan dubi Momi matukar ya furta mata wannan zance me nauyi. Saurin sauka kasa nayi ina ba shi hakuri.

Ya ce, “To goge fuskarki.” Ya miko min hankachif din shi ” Tunda kin daina kar momi ta zo ta nemi jin ba’asin kukan.” Da sauri na amsa na goge fuskata. Sai da muka ci abincin dare. Sai muka nufi gida da kyar ya bar ni na isa dakina nayi wanka, mai kawai na murza ina mutsutstsuka wata humra ta musamman ya shigo dakin daga ni sai tawul din jikina ya daga ni ina fadin ka bari in sa rigar barcina, bai ma san ina yi ba bai direni ko ina ba sai kan ni’imtaccen gadonshi bai tsaya wata wata ba salon kaunarshi ya shiga nuna min, wadda ni da kaina saida na fahimci irin wuyar da na ba shi, to ya fanshe dan na dandani kudata. Ban samu wani isashshen barci ba sai asuba dan bamma san fitar shi ba, sai sha daya da rabi na farka yunwa ce ta addabeni text na gani daga gare shi jinjina yake min da yabo na irin farin cikin da na saka shi. Kunya na ji kamar yana wurin.

Ma’u ta leko muka gaisa na tambayeta sun karya ba matsala ko? Ta ce “Babu” Duk yadda naso in daure idan ya dawo in ce ya kaini muyi bankwana da Husna gajiya bata barni ba kara kwanciya nayi barci me nauyi ya yi awon gaba dani. Da ya dawo sama sama na ji yana tashina in ci abubuwan da ya shigo min dasu. Ranakun da suka biyo bayan nan morewarshi yake yayinda nake jin jiki, shakuwa me yawa ta shiga tsakanina da shi, kullun kara san shi nake kamar yanda na lura yana ji dani.

Ranar wata Alhamis na same shi da misalin karfe tara yana karyawa kujera na ja na zauna ina fuskantar shi, yana cin abinci yana bina da kallo har na rufe fuskata da hannuwana, na ce “Dama zuwa nayi dan Allah ka barni zuwa sallon a tsefe min kaina duk ya dameni, kullun na tanbayeka sai ka ce ba yau ba”. ya ce ” Idan kin shirya sai isa direba ya saukeki idan kin kare zan zo in taho da ke”. Godiya na yi mashi.

Ya ce “Nawa ne kudaden da za a yi amfani dasu wurin gyaran gashin? na fada mashi, ya ce “Zan bayar kafin in fita” na mike ya ce “Ina za ki? Na ce” Zan gyara maka dakinka ne sai in shirya” kai ya daga, Sai da na kare shirin sai na samu isa direba muka wuce. Sun tsefe min kan sannan aka wanke ana daf da kammala min kiranshi ya shigo wayata shaida min ya yi ya iso na ce “Zan fito ba dadewa, dan an kusa kammalawa. da aka gama na basu kudaden sai na fito a kofa muka yi kacibis da Rufaida ita da wata mun gaisa tana wani dauke kai.

Ta ce, ” Ke kadai? Na girgiza kai “Muje in gaishe shi. ” Na wuce suna biye dani, har inda ya ajiye motar ina jinta a bayana tana fadin samun waje har ya Ahmad ke kaita salon,”

Ni dai dariya na yi a raina ina mamakin irin wannan kyashina da take ji, mun isa wurin motar suka gaisheshi daga ciki ya bude min gaban na shiga muka wuce su kuma suka shiga ciki, muna tafiya ya dan dubeni da idanuwanshi da duk suka canza “Wallahi a gajiye nake nayi aiki yau har na ji ba dadi, muje gida in watsa ruwa sai ki matsa min jiki na daga mashi kai.

<< Canjin Bazata 17Canjin Bazata 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×