Uku da rabi muka shiga Malumfashi. Ya yi parking kofar gidan mu, wanda na rinƙa ganin kamar na ɗau wani dogon lokaci rabona da shi. Cikin sauri na shiga gidan, gidan ya dau hayaniyar gani na abin ka da gidan yawa. Innarmu ta yi matukar murnar ganina, Yusuf ya shigo muka yi hira.
Sai da muka yi sallar magrib muka nufi gidan Ummu ni da Yusuf da Salma. Mun samu yayarmu za ta wuce gida dan sun kammala aikin gobe suna. Sai tara da rabi muka baro gidan inda Ummu ta yi tayi in kwana na ki na ce ta bari sai gobe yau zan yi hira da Innarmu.
Da safe da wuri yayarmu ta biyo min zuwa gidan sunan, na cire gudummawar me jego, ina mikawa Innarmu nata da na sauran jama’a sai ta fara hawaye. Ba sai mun tambayeta kukan da take ba mun san Aunty Amina ta tuna. Muma sai kowa ya fara goge ido Yusuf ne me bamu baki. Sai da muka natsa sai muka wuce. Yarinya ta ci suna Fatima sunan uwar mijin ne sai aka yi daidai mu ma sunan Innarmu kenan, nan na kwana na taya ta kintsa gidan. Yayarmu ta dawo da safe dan suyar ragon suna. Sai yamma sosai muka bar gidan.
Da daddare muna hira a kofar dakinmu bayan kammala cin abincin dare, kiran Ahmad ya shigo wayata na mike na shige uwar dakanmu na haye gado. Na ce, “Da rana na kira na ji a rufe shi ne na yi zaton ko an fita rage rana ne kuma aka rufe wayar ka da irin mu mu dame ku.” Dan murmushi me sauti ya yi, “Kishin kuma can ya kaiki? To maida wukar a sannan ina fama da wata me haihuwa ne kwananta bakwai tana bleeding sai da abun ya yi worse aka nufi asibiti da ita sai da ta kwana suka ce ba za su iya ba, shi ne akayo hospital dinmu da ita ina ma barci aka yo min waya ga emagency an kawo, sai da zu da la’asar na samu nasarar janyo mata yarinyar ba tare da na fede ta ba.” Ajiyar zuciya na fidda.
Ya ce “To kin maida harsasan na ki ko? na ce, “Wane irin harsasai kuma? ya ce “Na yaka ta mana, na je wajen girlfriend ko ba haka ki ke nufi ba?” Dan murmushin kunya na yi jin ya gano ni, ya ce “Ni wanka ma nayi ina kwance kewarki na damuna, ina jin haushin kaina me yasa na barki har kwana uku?” Dan murmushin jin dadi na yi.
“Na yau ne kadai gobe iyanzu muna tare in sha Allah.” Ya ce “Ki yi kokari ku taho da wuri kar ya yi gudu da ke, ku taho a hankali kin ga ba ke kadai ba ce.” Gyada kai na yi kamar yana kallona. Mun jima kafin muka yi sallama sai na kwanta.
Da safe na yi ma babannina alheri da sauran mutanen gidan.
Mun fita da wuri kamar yanda ogan ya bada umarni, Innarmu tana ta sa min albarka ni da sauran yan’uwana sai da muka biya gidan Haj kanwar kakarmu da gidan yayarmu sannan muka dau hanya.
Mun kusa shiga Abuja Khausar ta kira, “Maman twince kun shigo ne?” Na ce. “Dan Allah bana son wani mmn twince mun kusa dai” Dariya ta yi. “To amaryar Dr, idan kun shigo ki biyo ta gidana an kawo humrad da muka yi sako Maiduguri.”
Na ce “To sai mun shigo.” Mun biya sai da nayi wa Al’amin wasa sai ta bani sakon. Masu hidimar gidana sun nuna murnar dawowata, sai da na ci abinci na yi sallah muka zauna fira da Baba Kulu har da Ma’u. Ahmad ya yo waya mun iso na ce “E” ya ce, “Good Allah ya shi maki albarka zan shiga operation yanzu ina bukatar addu’arki.” Na yi mashi fatan samun nasara, na kuma tura mashi text na kalamai masu dadi. Sai yamma muka shiga kitchen muka yi girki na sha kwalliya cikin wata tsaleliyar shadda amma shiru ba Ahmad. Na gaji na cire na sa wata doguwar rigar barci me kalar ruwan goro shara shara ce na daure gashin kaina na sa wata mitsitsiyar hula na koma na mike kan cushion. Abin ka da dama ina tare da gajiyar tafiya, sai barci ya dauke ni.
Sanyin da ya rika ratsa fuskata shi ya sa ni yin sheshsheka na dan bude idona tsugune yake gabana wanka ya yi sanyin ruwan hannunsa ne yake taba fuskata na yunkura na tashi zaune, “Sannu da zuwa ya aiki? “Ke ke da sannu babyna ya hanya? ya su mama da kowa da kowa?”
Na ce, “Lafiya lau.” Ya kewaye ni da nau’ikan abubuwan da ya shigo mini da su, na ce “Abincinka fa na kan dinning.” Ya ce “Ok na yi tunanin gajiya ba za ta bar ki yin girki ba.” Ya hau teburin ni kuma na soma cin abubuwan da ya shigo min da su sai da muka kammala sai muka kwanta.
Kwana biyu bayan nan wani yammaci na fito daga falona sai na isa na Ahmad har ga Allah ni ban san ba shi kadai bane, ashe bayan fitata su Farhan da Najib sun shigo riga da siket ne jikina rigar fara siket din na jeans ne kalar shi blue sai na yi sallama kuma har sun fara gaisheni zan zauna kan masangalin kujera Ahmad ya daka min tsawa abinda bai taba min ba ya ce kuma in fita.
Na isa dakina ko gani ba na yi idona cike da kwalla ina faduwa kan gado na soma zubda hawaye, ban san iya lokacin da na dauka a haka ba na dai ji motsin bude kofa ban tada kaina ba muryarshi na ji fada ya rufe ni da shi kan shigar da nayi Ina sane akwai maza a ciki ya kare sai ya fice. Ba abinda yake kara sani jin bakin ciki irin a gaban kannanshi ya wulakantani ya kore ni, da daga ni sai shi ne sai in ba shi hakuri dan dama zaman bauta nake daga aure ibada ne, muryar Baba Kulu na ji tana min magana daga kofar falo saurin tashi zaune na yi na fada bathroom na dauraye fuskata sai na fito na sameta. “Tsaye kike Baba ba ki zauna ba?” Na fadi ina kakaro murmushi.
“Na ji shiru ne ba ki fito ba uwar dakina.” Na ce. “Kaina ne na ji yana dan sarawa shi ne na dan kwanta.” Bayan firar wani dan lokaci na bi bayanta a wurinta na ci abincin da suka girka ita da Ma’u, ko da na ji dirin motarsa ban motsa ba, har ta ce “Ba ki ji dawowar mijinki ba maza ta shi.” Na ce “Bari Baba in dan ga karashen labarun nan.”
Ta ce “Can ma ai akwai talabijin din.” Muna cikin haka ya shigo gefen da yake ma ban kalla ba, suka gaisa da Baba ya fita, ta ce, “Kin ga har ya biyo ki maza ki bi mijinki, ku yaran yanzu rashin dabara ke damunku, ki ka ga mijinki na sanki kema ita kokarin jawoshi jikinki kina kyautata mashi b… ban ji karashen zancen nata ba nayi waje ko kallon sasanshi ban yi ba dakina na shige na datse kofar na yi kwanciyata. Da safe sai da na tabbatar da fitarshi sai na fito na samu abincin da su Ma’u suka yi na ci, da rana ma da na yi ajiye mashi kawai na yi. Sai yamma na zagaya baya dan in sha iska na zauna sanye da riga da wando na English wear masu kama jiki ruwan madara, tafiya na ji sai gabana ya dan fadi dan ban tunanin akwai me zuwa wajen ba, sai dai in ka biyo ta falona ko na Ahmad kuma na rufo falona, waiwayawa nayi Ahmad ne na maida kaina na sunkuyar ina kallon yan yatsuna ya karaso ya zauna gabana, “Ke kunnen kashi ne da ke ko?”
Ban daga kaina ba kuma ban yi magana ba. “Yanzu wannan kayan idan wani ya shigo fa? Dubi komai na ki a bayyane yake fa.” Ya kare maganar yana jan rigar kamar zai cireta na kwace rigata ta hanyar cire hannunsa. “Sai dai idan wulakancin ne bai ishe ka ba amma nan waye zai shigo am…. Sauran maganar ya makale saboda kukan da ya taho min da gudu na bar wajen.
Da daddare ina kwance a falo na yi rigingine ina kallon sama kayan ne jikina ban cire ba, ya shigo bai min magana ba wata katuwar leda ya ajiye sai ya juya ya fita, na tashi na rufe falon bayan kwanciyata ina ji yana buga kofata na yi banza da shi. Sai da muka yi kwana uku a haka.
Ranar na ukun ne da hantsi ranar ta kama asabar ina zaune ina kallo a tashar pox movies sallamar Momi na ji na mike ina mata sannu da zuwa duk da na raya a raina zuwan nata yana da dalili dan ba kasafai ta cika zuwa ba. Na shiga gaisheta cikin tsantsar ladabi kafin na shiga kitchen na kawo mata abin motsa baki, sai da na zauna ta ce,
“Wai ya akayi ne Shuhaina na zo in ji, mijinki ya ce kwana uku ba ki yi mashi magana daga ya yi maki fada haka ne?” Maimakon in yi magana sai na fara mata kuka daidai nan ya shigo ya zauna “Abin yana bata min rai Momi kowace irin shiga ta yi haka take fitowa ko ina da baki da da farko ba haka take ba bata zama sai da hijab jiya ma na shigo mata da hijabai kin ga ledar can ma ko tabawa bata yi ba.” Jin abinda ya ce sai na kara tsananta kukana ni wane bako ya yi na fito a haka? leda kuwa ni ban ma taba ba bare in san meke ciki. Momi ta yi fada da nasiha ta tashi za ta tafi na bita har gaban motar inda direba ke jiranta sai da suka tafi na dawo falona na zauna shigowa ya yi “To zo mana.”
Kamar in yi banza da shi sai na tuna girman Momi da na ke gani kuma ta ce ya wuce, sai na mike na bi bayansa. A bedroom dinshi na same shi jawo ni ya yi jikinsa har yana fitar da ajiyar zuciya, “Haba yammatana daga fada sai fushi ya ki karewa? har sai na dauko Momi, yi hakuri ban iya jurar ganin da wani zai maki ba ni ba kishi rufe min ido yake sai in ga kamar ke kadai ake kallo kar ma yanzu da ki ke da cikin nan. Rufe bakinsa na yi da hannuna yasa hannunsa ya cire hannun.
“Ban taba kishin wani abu a rayuwata yanda na ke kishinki dan haka na ke son ki kiyaye abin da zai tunzura ni.” Jin ya sake babi sai na fara kokarin kwace kaina kashi ya gwada min. Bai bar ni ba sai azahar inda muka yi wanka muka yi sallah.
Cikina yana girma dan ya shiga wata na bakwai, zaune nake gaban Dr na kafata ya ke matsawa dan ta dan yi kunburi, a bayan gidan mu muke zaune inda ya kan rakani in rika exercise idan na gaji mu zauna in huta, dan baya barina zuwa ko’ina hidimar cikin da kula da lafiyarsa duk shi ke yin kayansa, sai dai ya sa min dokar da na ji ina da matsala ko baya nan in je asibitinsu.
Wayarsa ta shiga kara ya daga, “Aunty Kubra ya gida?” Ina jin muryarta dan hands free, “Yasa ya su Zayyad da babansu?” “Kowa lafiya ya Shuhaina?” Ya dubeni “Ga ta nan tana zama da kyar tashi da kyar” Dariya ta yi “Ka ce in hado kayan baby zan yi ya ko ɗa? Dama muna London ne mun zo ganin kanwar babansu Zayyad da ke aure a nan, idan na gama sayayyar zan turo.” Ya ce “Zan turo maki kudi Aunty kubra sai ki yi wa madam dina nata sayayyar, amma masu kyau na ke so.” Ta ce “Kar ka damu kai ka sanni ai magana ce ta iya kudinka iya shagalinka.” Dan murmushi ya yi “Na sanki ne Aunty kubra akwai iya business.” Ta ce. “Haba dai Allah ya kyauta in maka, har ciko zan yi idan ta kama.” Ya ce “Na sani Anty kubra ke din ai babba ce.” Dariya ta kara yi “Sai na ji ka.” Ta katse wayar.
Sati biyu bayan nan kayan suka iso. Da na duba akwatunan da ta shako da kayan baby sai da na jinjina sai ka ce wadda za ta haifi yan hudu, nawa kuwa nasan tabbas bata sa san rai ba wurin zabar min kaya. Da safe Dr na ta shiri Katsina za shi wajen wani taronsu na likitoci, ina zaune bakin gado na tasa katon cikina ina kallonshi na ce,
“Ji nake kamar ka tafi da ni ka sauke ni Malumfashi idan ka dawo sai ka biyo ka daukoni.” Yar harara ya bani “Ba ki da hankali a haka yanda ki ka zaman nan ina za ki ko an barki.” Na ci gaba da kallonshi yana saka safa fara kullun sai in ga kamar kara mashi kyau ake shigar farar shadda ya yi ya soma daura agogonshi citizen ya yi kyau har ban san dauke ido a kanshi na kai hannu zan dauki breaf case dinshi da ke gefena ya ce “No” Ya dauka ya kuma miko min hannunsa na kama sai na mike muka isa wurin motarshi ya shiga ya zauna na sa hannuna kan murfin motar na ce “Allah ya kaika lafiya yasa ka dawo lafiya.”
Shima ya fada cikin kwaikwayon muryata “Nima Allah yasa in dawo in iske baby na kamar yadda na bar ta.” Ya leko da hannunshi ya shafi cikin ya yi dan murmushi na daga mashi hannu sannan na koma wurina na kwanta kamar yanda ya bani umarni. Uku na ranar washegarin tafiyarshi na ji shigowar mota kamar in yi gudu in taro shi dan sosai na yi kewar tarairayar da ya ke min, sai dai katon cikina bai bar ni hakan ba. Da nayi yunkurin mikewa sai kafar ta rike dole na zauna. Sai ga shi ya shigo, wa zan gani bayan shi Haj ce murna na kama yi na ce, “Ashe gaskiya na kasa tashi ke ce kika rike kafar” Yar dariya ta yi “Ragwanta dai yarinya shi yasa na biyo maigidan tun da kin tsufa.” Na ce, “Ai na ga alamar hakan ga shi daga isowarki na gaza tashi.” Na cicciba na tashi na umarci Ma’u ta kawo mata ruwa da abinci. Na ce “Ina zuwa Haj” Ta ce “Yi maza wurin mijinki.” Na daukar mishi ruwa na wuce.
Ina shiga janyo ni ya yi ya zaunar na tsiyaya ruwan na mika mashi, “Ba ki ji ko? ba za ki bar girkin nan ba ko? Exercise din da kike yi ma is ok” na ce “Yi hakuri na ga kamar ba ka san girkin Ma’u.” Ya ce “To ba lalura ba ce za ki tabbata ne a haka? wanka kawai ya yi ya ci abinci sai ya dauki key dan bata rai na yi “Haba dan Allah daga dawowa ba ka bari ka huta? Kallona kawai ya yi sai ya bar gidan.