Ku karanta littafi na na gaba; WA GARI YA WAYA? (Labarin zaman kishin mata hudu wanda ake ragargaza kishi a gwangwaje, abun sai wanda ya karanta)
“Ina za ki ne? Koma ki zauna.” Na koma na zauna ta cigaba tana fyace hanci, “Kamar ni kawai ya rasa wa zai auro min sai ƴar aikina, bai ko gaya min ba, sai dai ganin an kawo ta na yi.” Faɗuwar gaba na ji ta same ni jin abinda ta ce. “Wani wulaƙancin sashin shi aka ajiye ta, yanzu yasa gini kusa da sashena, wai idan ya kammala gini sai ta koma, na baro gidan na je gida Abba ya ƙi goya min baya, wai in koma gida zai hana mijina aure ne, na ce ni ba auren ya fi damuna ba ya rasa wa zai aura sai ƴar aikina.
Da na baro gidan gidan yaya Kabir na nufa Aunty Aisha bata nan, Sai amarya ina tunanin ita ta hana shi ya saurare ni, shima ban samu goyon bayan sa ba. Kwanana uku yau na taho nan.” Ahmad da ya yi tagumi tun soma maganar ta ya ce “To ke Rufaida ya za a yi mu hana mijinki aure, magana ta gaskiya ki koma ɗakinki ki yi haƙuri. Yanzu ma shin ina yaranki? Ta ce “Na baro ma shi abin shi.” Ya ce “In kin bar mata mijin kya haɗa har ƴaƴan ki? Ribar me ki ka ci to? ta ce “Ni da in zauna da ƴar aikina gara auren ya mutu.” Ya yi saurin cewa “Subhanallahi, ban san hauka. Kuje ciki Shuhaina, ta yi wanka, ki bata kaya ta sauya, sai ta samu ta ci abinci zan ga mijin nata.”
Na miƙe tana biye da ni har bed room ɗina, ta shiga wanka na ciro mata kaya, sai na fita. An ɗan jima na dawo na samu ta saka kaya tayi tagumi kawai na ce “Ba ki yi make-up ba? Ta ce “Barni da kwalliyar nan, har na manta rabon da in yi ta.” Nan dai na yi ta bata baki har ta ɗan yi sama sama, muka fito ina ta tausarta har na samu ta ci abinci, ta koma ta kwanta rigingine idan ta na kallon silin.
Da muka zo kwanciya a bed room ɗina na ce ta kwanta na bata sabuwar sleeping dress kwanciya tayi tana kallona ina kwalliyar tafiya turaka, na gama nayi mata sai da safe na ja mata ƙofar, na wuce wajen mijina. Wasa wasa sai da Rufaida ta shafe sati biyu a gidana, dan har sai da na je sunan Husna na dawo, sannan mijinta ya amince zai sake ma amaryar shi wani gidan cikin gidajen sa, ita kuma ta koma gidanta, ni yasa na rakata tana ta min godiya. Na dawo gida ina ta kakkaɓin al’amarin, wato gaskiyar hausawa da suke cewa abinda ya baka tsoro wata ran shi zai baka tausai, yau Rufaidar da ke ganin ni ɗin ban cancanci zama matar yayansu ba, saboda ni ba yar kowa ba ce, an wayi gari yau mijinta ya auro me aikin ta, sun zama daidai a wajen shi in ta ɗauro ma ta fi ta a zuciyarsa, tun daga nan muka ƙulle da ita.
Wani hantsi zaune nake a ƙayataccen falon Innarmu, wanda na ƙayata mata shi, bayan na gyara gidan gaba ɗaya. Dan ta ƙi komawa gidan da na gina mata. Nasa an buɗe ɗakunan nata,an kuma yi mata kicin da bayi, tunda gidan yana da wadataccen fili. Fira muke da Innarmu, ban daɗe da isowa ba daga Katsina, Maman Ihsan Rabi ta aurar da ƴar ta, ɗan da na haifa namiji Abdurrahman yana ta dabo a tsakar ɗakin, yayata Zinatu tayi sallama ta shigo sai da muka gaisa sai tayi min godiyar alherin da na aiko mata da shi na kayan abinci da kudaden cefane. na ce mata “Ba komai” shekaru biyu kenan da aka cafke mijinta bisa ga kamashi da akayi ya shigo da haramtattun ƙwayoyi, komai nasu an karɓe, Ƴar’uwarta da ya kamata ta temaka mata itama yanzun sai a hankali, a kullum na dubi matsayin da take a da da kuma yanzu sai tayi ta ban tausayi ga ƴaƴanta basu san wahala ba, na kan ƙara girmama girman Ubangiji dama a cikin sunayen sa ya faɗa, ya girmama wanda yake so, ya ɗaukaka wanda yaso, ya kuma ƙasƙantar da wanda yaso.
Salma ta fito, kyakykyawar budurwa wadda da zarar na dube ta ban iya hana kaina murmushi ban gajiya da kashe mata kudade ina ƙara fiddo ta, wani abokin Farhan ke neman aurenta, mun gama firarmu muka kamo hanya, saƙon Ahmad ne ya shigo, yana bayyana min irin matuƙar kewata da ya yi na kwanakin nan da bana nan, tare da bayyana zallar son da yake murmushi na yi idona na lumshe nake gode ma Allah bisa bani miji irin wanda ya bani me sona da ƙaunata da tattalin farin cikina.
TAMMAT BI HAMDILLAH. Godiya ga Allahu subhanahu wata’ala da ya bani ikon kammala rubutun littafin Canjin Bazata, abinda na yi daidai Allah ya haɗa mu a ladar, kuskuren da nayi kuma Allah ya yafe min, Godiya ga masoya littafin nan, a duk inda suke na gode da kauna Musamman jama’ar Dandalin karatu ina godiya da ƙwarin gwiwa, Sai yan Canjin Bazata Fans ina godiya da son littafin nan da kuke Ina barar ƙulhuwallahu Allah ya kai ladan kabarin mariƙiyata ya haskaka makwancinta ga duk wanda ya ji daɗin labarin nan. Nagode na gode na gode Sai Allah ya sake sadamu.