Skip to content
Part 6 of 28 in the Series Canjin Bazata by Maryam Ibrahim Litee

Maida kaina nayi kasa na ce “Ina kwana? Ya amsa kamar bai son yin magana “Kina iya shiga kitchen a duk sadda kike buƙatar hakan, akwai komai a ciki.”

A sanyaye na amsa da, “To.” Ina ƙara takurewa.

“Tonny yana gyaran gida ne da kula da shukoki, har falon nan yana gyarawa, da kuma kitchen. “To. ” Na kuma cewa sai ya juya. Sai da na tabbatar da barin shi gidan sannan na fito duk da falon ba shi da datti an daɗa tsaftace shi, sai tashin ƙamshi yake.

Kitchen ɗin na nufa kamar yanda na zata, kitchen ɗin ya tsaru da na’urorin zamani kala kala, Akwai manyan deep freezer guda biyu a ciki. Kayan amfani babu wanda babu.

Lallaɓawa nayi na jona kettle ta yi zafi, na haɗa tea mai kauri sai na koma falon nan na zauna ina kurɓa ina kallon tashar Aljazira da na samu tana yi, da na gama sai na koma kitchen ɗin na ɗauraye cup ɗin.

Window kitchen ɗin na leƙa in da na hango Tonny yana ta aikin sa na gyaran fulawoyi, Ɗakin na koma nayi wanka na gyara jikina. Sha biyu na rana Tonny ya kawo min wasu cooler guda biyu ɗaya shaƙe take da danbun nama ɗayar kuma cake ne Bayan ya gaishe ni cike da girmamawa ya ce,

“Saƙon daga mahaifiyar oga ne, ta ce a kawo min direban gidan ya kawo godiya na yi sai sannan na tuna da kuɗin da aka bani jiya dan jakar tawa ma a motar na bar ta da wayata ma a ciki, hango jakar nayi saman wani ɗan tebur, Na yi saurin ɗaukota na buɗe har da kuɗin duk suna ciki, Na ce “Ina direban? ya ce ya wuce. Dibar masa nayi yana ta godiya. Naira dubu na ba shi guda ɗaya, na ce ya sawo min katin MTN na kuma ba shi wata na ce ya sawo min na Etisalat. Shi kuma na ba shi ɗari biyar na ce ko zai sa. Ba’a ɗauki lokaci ba ya kawo min, na karɓa nayi zaman sawa, na sa MTN Etisalat ɗin kuma na tura wa innarmu.

Na yi ta try ɗin samunta amma wayar ta ƙi shiga ƙarshe na hakura. Na miƙe dan gabatar da sallar Azahar, danbun naman shi na ci a matsayin abincin rana Na ɗauko madarar hollandia na haɗa.

Cikin sati guda abinda ke faruwa kenan zai shigo da safe, idan zai fita ina kwana nake masa, ya ce lafiya. Daga nan idan ya fita sai kuma wata safiyar ni da kara ganin shi dan nima da na fahimci lokacin dawowar shi ina ganin ya kusa zan koma dakina in rife.

Tun ina tsoron kwana ni kadai har na saba ga kadaici na saba da gidan mu na yawa. Na hutar da Tonny gyaran falo da kitchen zan gyara ko ina fes tare da fesa room fresheners din da na ga yana fesawa. Na kan kira Innar mu da sauran yan’uwana lokaci lokaci, suma suna kirana har na wartsake. Na kan shiga kitchen in ta gwada girke girken da aka koya mana a makaranta dan littafi guda ne da ni. Sai in ga kuma ya yi fiye da zato na. Na’urorin kuwa da karanbani na iya amfani da su. Yin girkin ya kan dauke min zaman kadaici wa’azuzzukan malamai da ke cikin wayata suma ba kadan ba suke debe min kewa.

Duk bayan kwana uku Tonny zai same ni. Ya ce, madam oga ya ce idan akwai abinda babu ki fada min in je in sawo. Idan akwai abinda nake bukata sai in fada masa, Momi mahaifiyar sa tana kirana ta tanbaye ni ina da matsala? Sai in ce babu komai Kuma bata gajiya da yi min aike dan haka na cire komai a raina Iyaka dai jira nake ya gama wulakancin shi ya sallame ni ai dai shi kenan ko? Tunda ba kwantai nayi ba ni ba mummunar kama ba.

*****

Ranar da na cika wata guda da misalin ƙarfe takwas da rabi na dare, Kamar wasa na ji ana ƙwanƙwasa ƙofata sai da nasa hijab sai na buɗe kofar. Yana tsaye fuskar nan tashi ba walwala kamar kullun,

“Ki zo falo ana kira”

“To” kawai na ce. Sai ya juya na ɗan tsaya jim, sai kuma na bi bayan shi, Abdullahi ne abokinsa zaune, wanda na san ba shi da Aboki sama da shi, Sallama nayi a hankali ya amsa na gaishe shi ina tsaye rashin sanin abinyi, ya ce “Ki zauna mana In dai ba fushi kika yi ba, wata guda ban zo na kwashi gaisuwa wurin amaryarmu, Tafiya nayi saukata kenan ɗazu da rana.”

Ɗan murmushi nayi. “An dawo lafiya? Na faɗa ina zama a takure, “To ya gidan? Na ce “lafiya lau” “Ya amarci da baƙunta? Shiru nayi “Ko da yake kin zama ƴar gida.”

Ya kai glass cup ɗin da ke hannunshi kan wani ɗan stool ya dube ni. “Ba ku rage komai bane a gidan? shi wannan baƙin baturen sai lemo kawai ya kawo min?

Na ce “Ba za’a rasa ba” ina mikewa kitchen na wuce Tuwon shinkafa miyar agushi nayi, Miyar ta ji tantaƙwashi, Tuwon kuma ya yi danƙo kwarai, Na shiryo a babban tire na kawo masa zan juya, Ya ce,

“Zama za ki yi muyi hira.” Na sa ci kallon Ahmad wanda ya zura ma TV ido tamkar baya wurin. Yana ci yana cewa “Gaskiya ba kaɗan kika iya girki ba, In dai zan riƙa samun abincin gargajiya irin wannan, anan zan riƙa yin dinner, matuƙar ina gari kin san abin ka da gwauro.” Ganin ban tanka ba ya sa shi cewa, “Ni fa daurewa za ki yi ki saba da ni dan ni ɗin wan ki ne, daga Katsina nake kamar ke, ko ba ki san Masanawa ta katsina ba?

Na ce, “Ina jin sunanta dai, dan ban taɓa zuwa Katsina ba. ” Baki ya rufe “Ashsha ashe ki ce kifin rijiya ce, to yi shiru kar wannan ya ji ya yi mana dariya.” ɗan murmushi nayi ya ci gaba “Ko da yake na kusa barin gwaurantakar nan dan na kusa angwancewa saura watanni uku, duk da ba tarewa za tayi ba tana karatu ne.”

Na yi ƙarfin halin cewa, “Allah ya sanya Alheri.” “Amin, sunanta Khausar Sai ki bani lambarki in bata kwa riƙa gaisawa kafin ta iso.”

Na ce, “Zan bayar” Hamma na yi ya ce, “Ki je ki kwanta, na gode da hira da kuma abinci.”

Ɗan murmushi na yi sai na kwashe kayan abincin na kai kitchen, na je ɗaki na rubuta lambar, zan kawo masa. Tana bada baya ya dubi Ahmad, “Me nake shirin gani? A tsanake ya dube shi “Kamar me? Ya ce “Kamar komai ma, daga ganin yarinyar nan ba ka janye ƙudirinka ba, dan sam ba alamar ta saba da kai.”

Shima ranshi a haɗe ya ce Duk abinda ya kamata na ci ko sha ba wanda bana ƙoƙarin wadata ta da shi, to me kuma kake son in mata bayan haka? Ya ce “kwarai gaskiya ne baka da abin mata, dama wannan shi ne maƙasudin auren, Ka yi dai dai yanda ka yin… Katse shi ya yi “Kai malam abinda fa kake nufin in yin, ba fa zan yi ba, Ka san na gaya ma wannan ba irin choice ɗina ba ce, mace gajera maka malam, bagidajiya kullun a lulluɓe. Ina cikin raɗaɗi na rashin matata, dan rashin tausayi, sai kawai kamar wani yaro ace an bani ita ka…”

Cikin matuƙar ƙufula ya katse shi, “Dakata malam, ina me tabbatar maka yarinyar nan ta wuce ka ci mata fuska, dan ƙaryarka ka kira ta gajera, na dai yadda matsakaiciya ce, idanma ƴan hotunan da ake kawo maka talla ke ruɗarka, to ina me tabbatar maka duk ƙyaleƙyalen banza ne, ban ga kamar ta ba. Allah ya yi maka baiwa kana nema ka butulce, Yanzu gidanku ba matarka ake yabon halayenta ba? Ina ce akwai matan Kabir amma ta ka ake yabo ashe ba abun ka godewa Allah bane, Bayan ka rasata an ɗauki ƙanwarta an ba ka ka yi dace da gida na mutunci masu tarbiya. Wallahi abokina uba ɗan malumfashi ai ka dai san shi ? Ko wancan weekend ɗin mun haɗu a (Zone ll) muke maganarka Ya ke cewa ai ba ƙaramar sa’a kayi ba, dan mahaifinsu dattijo ne mutumin kirki Ƴaƴan shi suna da tarbiya, musamman ita wannan da aka ba ka. Ya ce ko a abokansa yasan da yawa masu san ta, Kawai kwarjini take wa maza saboda kamun kanta kullun za ka ganta cikin shiga ta kamala. Ka samu za ka wulaƙanta sai ka auro falwaya.”

Mikewa ya yi ya ɗauki key ɗinshi da ke ajiye ya bar falon, sanin ya yi fushi yasa ya tashi ya bi bayan shi. A ranar idan na ce nayi barci to sai dai ɓarawo ba sanin lokacinsa, dan tsabar baƙin ciki Kuka nayi tayi har na ji kaina yana ciwo, Na yi da na sanin tsayawa na saurari maganar Ahmad, zantuttukansa masu kama da zubar tafasashshen ruwa a ƙahon zuciya. Da safe ma key na sa ma ƙofata dan kar ya shigo to shi ɗin ma bai shigo ba.

Wunin ranar nayi shi ne cikin baƙin ciki da tunanin mafita, dai dai da wayata kashe ta nayi na kasa sa komai a bakina, Ko wanka ban yi ba sai biyar na yamma. Na yi tunanin Abdullahi zai zo cin abinci Sai na yi ƙoƙarin shiga kitchen, Dan ko ba komai ni kam ina girmama duk mutumin da ya nuna min mutuntawa, kamar yanda na tsani ka wulakanta ni. Lafiyayyen danbun shinkafa na yi Wanda dama shi na yi niyyar yi, Amma halin da na tsinci kaina Yasa duk ƙamshin da yake yi bai sa na ji sha’awar cin shi ba, sai kunun zaƙin da na haɗa masa nayi ta banka ma cikina. Tonny ma da na zuba masa da ya maido kwanonin sai faɗi yake “Madam abincinku na hausawa yana da daɗi” Murmushi nayi Sai da nayi sallar isha’i, kamar jiya yau ma haka ya zo, Sai dai ban yarda na zauna ba wucewa nayi nayi kwanciyata, tare da fatan barci ya dauke ni.

Yau da gobe sosai na saba da shi, sai dai megidan ne na kasa sabo da shi. duk da dai yanzu na tsinci kai na a wani hali na san ganin Ahmad da san jin muryarsa, randa duk ban samu ya shigo ba ko kuma Abdullahi bai zo ba da ƙyar nake samu barci ya ɗauke ni, Wani lokacin sai dai in ta kuka, ina me zargin zuciyata da san wanda bai so na. Sai in ce shi kuma san haka sharrin shi yake? Ya saka san wanda bai ƙaunar ka?

Mun saba da Khausar wadda Abdullahi zai aura ta waya, Idan mutum ya ji muna hira zai sha mun shekara da sanin juna ne.

*****

Ana gungurawa a haka nayi wata uku, ranar wata talata na kira Innarmu mun gaisa da su yayarmu da ummu, Yusuf ne wayar tashi a kashe take. Ina ajiye wayar a gefena na ji ana danna ƙaraurawa a falo daga in da nake zaune na amsa, Wata haɗaɗɗiyar budurwa ce ta shigo, doguwa ce baƙa irin black beauty ɗin nan, tafiya take kamar iska na kaɗa bishiyar turare, cikin rausaya ta karaso cikin falon.

<< Canjin Bazata 5Canjin Bazata 7 >>

1 thought on “Canjin Bazata 6”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×