A wannan karon ma, Asma’u bata ji me ya ce ba saboda komai nata ya d’auke in banda bugun zuciyarta dake ta ‘karuwa. A tsammanin Abbas miskilancinta ne ya motsa, don haka ya zuge bakinsa tare da maida dukkan nutsuwarsa ga tuki.
Ita kuwa bata farfad’o daga farfard’iyar kaunar Nas da ta bige ta a kan mashin din ba sai da ya juya stiyarin motarsa ya shiga U-turn din da zai kai shi gida, da raunanan idanunta ta raka bayan motar, yana ‘bace ma ganinta ta lumshe su tare da jike bushasshen makoshinta da yawu, a ranta ta ji ina ma ita ce a gaban motarsa, kai ko da a kan mashin din ne ina ma ya kasance shi ne a gaba ba Abbas ba. Wata irin kuna mai cike da rashin tausayi ce ta cigaba da azalzalar zuciyarta, domin ji ta rikayi dama mashin din ya kwace ma Abbas su fadi, kafin ya tashi kuma ‘katuwar mota ta bi ta kansa ta wuce, yayinda tuni ita ta’bille a gefe, idan ya so shi ya mutu, ita kuma ko karaya ce ta samu, bayan ta warke sai ta auri wanda take so.
‘Kiyayya kenan, shi yana ta yi mata fatan alkhairi a dare da rana, ita kuwa fatan bala’I da musiba take mashi. Toh ko da fatanta ya zama gaskiya, rayuwa ce zata bayyana wanda ke da asara, duk da ba a cikin hayyacinta take wannan fata ba, kawai ta yi gigan gaske ne a cikin haukan da so ya haifar mata.
Tana cikin sa’ke-sa’ken zucinta ne suka sauka daga kan titin. layin da zai kai su gidan sunan da zasu ne Abbas ya shiga, daga can nesa ta hango mata daga wajen wani katafaren gate, hakan ne ya tabbatar mata da nan ne gidan sunan, wanda ‘kanwar Umman Abbas ce mai jegon.
“Alhamdulillah”, Abbas ya furta lokacin da ya tsaida mashindinsa a gaban milk gate d’in. Saukowa ta yi, Abbas na saka idanunsa cikin nata ta d’auke kai, lokaci d’aya kuma ta kara murtuke fuska, ba tare da tunanin matan dake kallonsu ba.
“Ya dai madam?”, ya tambaye ta murya kasa-kasa, a dan tsiwace ta ce “Ka ga wani abu ne?”, ya ce “Eh, fuskarki na gani ba walwala, ga shi za ki shiga jama’a, ko kwaikwan ya motsa ne?”, cikin tsokana ya ‘karashe maganar duk don ta yi dariya, bai san a yanzu ba mutuwarsa ce kad’ai abin da zai iya sanya ta dariya. Ta bude baki za ta ya’bo mashi marar dad’i wata matashiyar causin din Abbas mai suna Hauwa ta nufo su tana fadin “Kai Abashe, yanzu duk soyayyar da kuka sha kafin ku fito bata isa ba, sai kun ‘kara shan wata a gidan suna?”, Abbas na dariya ya bata amsa da “Kwarai kuwa ‘yan sa’ido, don ba’a ‘koshi da ruwan ‘kauna”, duban Asma’u ya yi kana ya ce “Ko ba haka ba Sweety?”, kashe mata ido ya yi tare da fakaitar idon Hauwa ya langabe kai, alamun ta wasashe dan Allah.
Murmushin ya’ke Asma’u ta yi, lokaci daya kuma ta ce “Uhm! hakane”, Hauwa na dariya ta ce “Ke Amarya, ki ari bakin mijinki ki yi magana, don kika shiga gidan sunan nan fige ki zamu yi ni da dangina”, sosai ta ba su dariya, Abbas bai yi zato ba sai ji ya yi Asma’u ta ce “Kamar wata kaza?”, cike da jin dadin ‘yar sakewarta ya ce “Aikuwa ba.” Sosai suka tsokani juna, daga bisani Abbas ya damk’a amanar Asma’u wurin Hauwa, duk da ya san mahaifiyarshi da su Abida na cikin gidan, kuma ba zasu bari abokan wasa su titsiye mashi ita ba.
Tun daga manyan motocin dake faake a wurin ajiye motoci Asma’u ta tabbatar da mazauna gidan da’bensu ya ji makuba, suna shiga falo kuwa sai da ta raina kanta, domin manyan matan da ta baro a farfajiyar gidan ba komai bane idan aka hada da wadanda ke zaune a kan luntsuma-luntsuman kujerun da suka kawata falon, domin suturar kowace abin kallo ce. “Yoh dangin mai gidan ne”, ta fada a ranta, duk don ta kushe wani shashe na zuciyarta da ke fada mata dangin Abbas na da ‘kumbar susa. Sai dai suna kutsawa inda Umman Abbas ke zaune ta karyata kanta, don kusan manyan hajiyoyin da ke a rukuninsu duk suna kama.
“Hajiya ga ‘yarku nan da Abbas ya sanya ni dako”, Hauwa ta fada tana duban manyan Hajiyoyin, gaba daya suka dubi Asma’u lokacin da ta dukar da kanta katsa tare da gaishe su daga tsaye, da yake ba ba’kin tsanani ne ba suka amsa duk da fara’a a fuskarsu, ya jiki suka yi mata, daga nan kuma Umman Abbas ta tambaye ta “Abbas din fa?”, ta ce “Ya tafi”, jinjina kai ta yi “Ok, ku shiga ciki toh, su Abida na nan.” Jagora Hauwa ta sake yi mata suka fara zuwa wurin mai jego da adonta ya fi na kowa, baki Asma’u ta sake tana kallon kawayen maijegon da suka ci ado suna ta shewa, sosai ta ji tana muradin zama irinsu, wanda hakan ba zai tabbata ba sai ta auri Nas. Gaisawa ta yi da maijegon gami da bata hasahin suna, kin karba ta yi, wata kawarta ta ce “A’a Hafsa ki karba, kada ki kashe ma amarya zuciya”, dariya su duka suka sa, bayan ta karba ne kuma ta nuna ma manyan kawayenta Asma’u, aikuwa suka yi ta santinta, wata ta ce “Masha Allah, Abbas kam ya iya zabe”, Hauwa na dariya ta ce “A hakan? sai wani hura mata kai kuke har yana shirin fashewa”, da yake sun san abokiyar wasa ce sai suka kama dariya.
Daga dakin maijegon ne kuma sai inda su Abida suke, “Kun zo kenan?”, fuskar Abida ba yabo ba fallasa ta tambayi Asma’u, itama Asma’un daga kai kawai ta yi. Zama ta yi gefen gado kusa da Abidar, sai dai ta kasa sakin jiki, duk da tsokanarta da sauran dangi suke. Abinci ma da aka kawo mata ‘kin ci ta yi, kuma tana so. Abida da ta ga haka ma sai ta fice ta bar dakin. A zuciyar Asma’u kuwa ji take ita kamar ba mace ba, saboda yadda mata ke ta walwala sai take tunanin dukkansu mazan da suke so ne suka aura, “Allah ni ma ka bani kyautar damar auren wanda nake so”, ta fada a ranta bayan kaso mai yawa na matan dake cikin dakin sun fice.
Gab da Magrib ne Umman Abbas ta hada kansu suka tafi gida, saboda Abbas bai samu damar zuwa daukarta ba.
Da isarta gida ta cire kayan jikinta tare da maye gurbinsu da doguwar riga mara nauyi, katuwar tabarma ta shimfida a tsakar gida gami da abin sallah, daga nan kuma ta yo alwala domin gabatar da sallar magrib da tun suna a hanya aka fara kiranta. Ta gama sallar kenan tana azkar Abida ta kawo mata na’ukan abincin da ta’ki ci a gidan suna, ta ji dadi sosai a ranta, godiya ta yi ma Abidar, musamman da ta ga ‘kullin soyayyen ‘yan ciki mai yawa a farar leda. A ran Abida ta ce “Allah za ki godemawa da ya tsananta rabonki a wannan abincin”, domin ba dan Allah ya sa Ummansu ta jajirce ba, da Asma’u bata ci wannan abincin ba, saboda Abidar ta kife cikin wai ba za a kawo ba, tunda agidan sunan da aka bata gadara ce ta hana ta ci.
Asma’u na jin ficewarta ta kwance farar ledar, yawunta a tsinke ta dauki hanji ta kai a baki, wani irin dadi ne ya ratsa ta, wanda sai da ta ci kaso mai yawa na naman ba tare ta sani ba. Abincin kuwa sai da ta yi sallar isha’I kana ta je kitchen dauko plate, hadadden jallouf din dambun shinkafa ne, sai kuma sinasir da awara, wanda zai ishe ta zuba sannan ta rufe kwanon, ta fara kai loma kenan Abbas ya dawo, sannu kadai ta yi mashi ta cigaba da aikin gabanta, bai damu ba kamar kullum, sai ma ya wanko hannunshi daga bakin rjiya, zama ya yi akan tabarmar tare da duma hannu suka cigaba da afar dambun a tare, dadi na kai mashi karo ya tambaye ta “Yaushe zaki yi mana irinshi?”, kamar abin fad’a ta ce “Ban iya ba”, ya ce “Abida ta iya ai, sai ta koya maki”, cikin tsananin tsanar Abida ta ce “Wai komai ka ce Abida ta koya mani, toh bana so”, dariya kawai ya yi, dan ya fahimci tsuntsayen tsiyar basu sauka daga kanta ba.
Suna gama ci ya tashi ya sake wanke hannu, bedroom ya wuce ya rage kaya sannan ya dawo tsakar gidan, har a lokacin kuma bata tashi daga inda take ba. Kitchen ya kai komatsan da ke wurin sannan ya dawo kan tabarmar ya zauna, tana yunkurin tashi kenan Abbas ya ce “Ba ki tambaye ni ya aka yi ban dauko ki ba.”
Cike da gatse ta ce “Na tambaye ka”, cikin hasken fitilar da ya game tsakar gidan sakamakon maido wutar nepa da aka yi ne ya ce “Ina wannan d’an unguwar naku da muka gani a traffic light?”, da sauri ta ce “Alhaji Nas?”, ya ce “Eh, d’azu bayan na aje ki kawai sai ga kiransa wai yana son ganina, ni ban ma san inda ya samu numberta ba.” Ko da jin haka sai ta fasa tashi, a za’ke ta ce “Toh ka je ko?”, domin wannan ne karon farko da ta samu damar yin maganar Nas da wani, “Eh na je, wai contract din blocks zai ba kamfaninmu na ginin sabon gidan da zai koma shi da iyalansa.”
A daburce ta ce “Sabon gida dai, shi wancan me ya yi toh?”, Abbas ya ce “Ni kam ina zan sani, kila aure zai ‘kara. Kin san mu maza in dai muna jin dumus sai ‘karin aure.” Da Abbas ya san irin firgicin da maganar shi zata haifar ma Asma’u da bai yi ba, domin sai da ‘dan cikinta ya yi kwakkwaran motsi sakamakon muguwar faduwar da gabanta ya yi, hannunta dafe da mara ta nade kafuwanta, magana take son yi, amma ta kasa, saboda da alamun kwado na shirin yi mata kafa. Bata yi musun maganar Abbas ba, domin yadda ta ga Nas cike da annuri a dazu, ko shakka babu yana gab da samun wani farinciki a gaba. Kishi mai zafin gaske ne ya turnuke ta wanda take jin zamanta da Abbas ya zo gargara.
Shi kam bai san soki burutsun da take a ranta ba, sai ma ya cigaba da yi mata albishir din rayuwa mai yalwa idan har Allah ya sa contract din ta tabbata, domin kudade ne masu yawa. Ko kusa bata jin shi saboda ta yi nisa a tunanin shigewa a matsayin amaryar Nas ko ta halin ‘ka’ka.
Da ta ji zai cika mata kunne da magana ne ta tashi da nufin komawa falo, ruko hannunta ya yi “Ina zaki je muna hira”, idanunta a rufe ta ce “Bacci nake ji”, da yake yana son nutsuwarta sai ya sakar mata hannu “Okay, amma ki d’an bani pillow, nan zan rage dare”, ba ta ce komai ba ta shige daki, pillown ta miko mashi, bata jira jin godiyarshi ba ta koma dakin.
“Nas zai yi aure, kai ba zai yiwu ba”, maganar da ta yi ta juyawa a ranta kenan, wani irin kishinsa ne ya turnuke mata zuciya har ta tashi zaune ba da shiri ba, a hankali ta lumshe idanunta da suka cika da ruwa, lokaci daya kuma ta kwantar da bayanta ga kan gado, hannunta dafe da zuciyarta da ke zugi ta yi magana a ranta “Allah ka cika mani burina na mallakar Nas, idan ba haka ba mutuwa zan yi.” A hankali wani mayataccen son shi ya fara tsumar mata da jiki, sulalewa ta yi ta kwanta tare ‘kan’kame jikinta, fuskarsa ce ta rika yi ma gizo a rufaffun idanunta, yayinda muryarsa kuma ta shiga yi mata amo a kunne lokacin da ya ce “Barka dai Malam Abbas, ya iyali” a dazu, wani irin gardi muryar ta yi mata, kawai sai ta ji tana muradin sake jin zahirinta a dodon kunnenta, hanya kuma mafi saukin cikar wannan muradin nata ita ce number wayarshi wadda zuciya ta ruwaita mata dauka a cikin wayar Abbas.
Bata wani sha wahala ba wurin daukar number ba, domin babu shamaki a tsakaninta da wayar Abbas. Da Pyar ta yi save din number, ko da Abbas ya bar mata gidan sai ta sanya ma kofar key, falo ta dawo ta zauna a kan one seater, gabanta na dakan uku-uku ta shiga phone din wayarta, gano number Nas ta yi tare da kafe ta da idanu na wasu da’ki’ku. Tambayar kanta ta yi “Toh wai idan na kira ma in ce me?”, wani sashe na zuciyarta ya ce “Ai ba magana za ki yi ba”, hakan ne ya rage mata fargabar da ta cika mata zuciya. Dialing number ta yi gami da sanya wayar handsfree, tana fara ringing ta rumtse idanunta gam tare da kanga wayar a kunne, tsuma jikinta ya shiga yi saboda tsananin tsoro lokacin da muryarsa ta daki dodon kunnenta “Salam Alaikum”, a yadda ta firgita ko da ta yi niyyar magana, toh ba zata iya ba, bare dama bata yi niyya ba, sai da ya yi sallama sau biyu, a na ukun da ya ce “Hellooooo!” cikin jan murya ne ta katse kiran.
A je wayar a kirjinta ya yi daida da shigowar kira, aikuwa tana dubawa ta ga Nas ne, “Ya Salam” ta furta lokaci daya kuma ta girgiza kai, tana kallon wayar ta karaci ruri amma bata daga ba, domin sallamar da kadai ya yi a dazu sai da ta jijjiga mata zuciya. Yau kam misalta dadin da Asma’u ta ji abu ne mai wahala, ta dade zaune a falon tana tariyar muryarsa, ba ita ta shiga kitchen ba sai shabiyun rana.
A gurguje ta gama girki ta yi wanka. Abbas na dawowa ya ga fuskarta cike da annuri, ya so tambayarta farincikin me take, amma sai ya basar ya cigaba da cin abinci, abin mamaki sai ga ta zaune kusa da shi, tambayarshi ta yi “Kun je wurin contract din ko?”, sai da ya hade lomar bakinsa sannan ya ce “Mun je, ai gaskiya mutumin nan na da kirki, shi indai harkar samu ce, toh baya bakincikin ba wani”, tamkar wadda aka yabi babanta ta ce “Ai haka yake, shi ya sa yake da jama’a”, Abbas ya ce “Lallai dai kam, ai hali irin nashi abin so ne.” Tare suka ci abincin, lokaci daya kuma Asma’u na ta jan maganar Nas, nan ta ji unguwar da yake ginin, da ma wasu sirrika na arzikinsa a bakin Abbas. Wannan hira da suka yi ta sanya ta nishadi sosai, burin Abbas kenan ya ganta a farinciki, suna gama cin abincin ya jawo ta a jiki, bata kuma iya hana shi samun farinciki a tare da ita ba, domin dama kuncin zuciya ne ke hana ta bashi wata damar a kanta.
Gab da la’asar ya yi wanka, da zai fita ya tambaye ta “Me kike so na siyo maki”, dan langabar da kai ta yi daga tsayen da take a kofar daki ta ce “Data”, matsowa ya yi dab da ita “Data kadai?”, ta ce “Eh”, ya ce “Toh ba ki da damuwa”, sumbatarta ya yi a goshi, sannan ya ce “I LOVE YOU”, murmushi kadai ta yi, tare da raka shi idanu har ya fice gidan da mashindinsa, tana jin tafiyarsa ta ce “You love me. I love sweet Nas.”
Wurin karfe biyar Abbas ya kira ta ya ce ta yi checking data, tana dubawa ta ga 1GB, kai tsaye WhatsApp ta shige, ba inda ta zame sai contacts, wanda ta je nema ne ta yi sa’ar gani a sama, wato rabin ranta Nas, jikinta na bari ta danna dp dinshi “Masha Allah” ta furta a fili, domin ya yi kyawun da idan ba ta ce Tubarakallah ba kambun idonta zai iya taba shi. Kafe hoton ta yi da dara-daran idanunta. Tsaye yake a gaban mayyar motarsa cikin shigarsa ta kayan saurauta, sumba ta kai ma hoton, cikin sanyi murya ta ce “I love u Nas, Allah ka bani shi…”
Note: So ya makantar da Asma’u hart a fara ‘ketare iyaka, domin abin da ta tsira bai halatta ba a musulunci.