Wani irin masifaffen son shi ne ya cigaba da azalzalarta a zuciya, sake sumbatar hoton ta yi kafin ta yi save. cigaba da gamsar da zuciyarta ta yi da kallonsa, a fili ta ce "Mutumin nan ya had'u", a ranta ta 'karashe fad'in "In dai na mallake shi ba zan bar wata kofa da wata mace zata sake shigowa rayuwarshi ba."
Fitowa daga dp d'in ta yi bayan ta gama ba idanunta abinci, kai tsaye cikin chat ta shiga, zuciyarta na bugawa da sauri-sauri ta aje mashi "Salam", fitowarta ke da wuya nutsastsen 'bangaren zuciyarta. . .