Skip to content
Part 15 of 25 in the Series Cikin Baure by Hadiza Isyaku

Ko da lafiya lau Asma’u take abu ne mai wahala ta iya amsa kiran Abbas, bare kuma yanzu da take rai a hannun Allah. Ɗan bubbuga jikinta ya shiga yi, dan in ma bacci take ta falka, sai dai ko motsi bata yi ba, cike da kaɗuwa ya lumshe idanu, bakinsa kuma na cigaba da karanto “Inna li Llahi wa inna ilaihi raji’un”. Yana buɗe idanun kuma ya dire su a kan butar dake yashe gefenta, rashewa ya yi ƙasa tare da ɗago kan Asma’u ya ɗaura akan cinyarsa, butar ya ɗaga bisa ga yaƙinin samun ruwa ko da kaɗan ne a cikinta, yayyafa mata ƴan ruwan da ya samu a ciki ya yi, suna na ratsa jikin Asma’u ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, idanunsa tar a kan fuskarta da take ta yamutsewa ya ambaci sunanta “Asm’au.”

Haƙiƙa ta ji shi, sai dai tsananin ƙinsa ne ya sake kai ma zuciyarta hari, take ta sake sumewar baƙinciki.

 Sosai Abbas ya ƙara fita hayyacinsa, har ta kai ga ya manta da sake yayyafa mata ruwa, saɓar ta ya yi, bai dire da ita ko ina ba sai falo akan doguwar kujera, durƙushewa ya yi akan guiyawunsa yana kallon fuskarta da ta yi ramar dare ɗaya, hawayen tausayin kawunansu na fita a idanunsa ya shiga zargin kanshi, domin duk abin da ya samu Asma’u shi ne sila, saboda ta fito da ainahin abin da ke cikin zuciyarta na ƙin shi, amma saboda tsoron mawuyacin halin da zai faɗa ya ƙi fahimtar ta, bare ya bata damar samun farincikinta. Faɗa yake son yi ma zuciyarshi, sai dai bai san ta ina zai fara ba. Wayarshi da ya baro a tsakar gida ya tashi ya ɗauko, domin zuciya na umurtarshi da ya kira Ummansu ya faɗa mata halin da ake ciki, tun kafin Asma’u ta rasa ranta, daga dur’kushen da ya koma a gaban Asma’u ya kira number Ummansu tare da shaida mata Asma’u bata da lafiya. Cikin abin da bai fi minti goma ba sai gata ta zo ita da Abida, “Subahana Llah, kamar a some take ko?”, Ummansu ta tambaye shi hankalinta tashe, tun kafin ya bata amsa Abida ta yi waje ta d’ebo ruwa, mi’ka ma Ummansu cup ɗin ruwan ta yi kana ta ce “Wallahi wani lokaci kai kamar yaro, ta ya yarinyar mutane ta some amma ka kasa yayyafa mata ruwa”, idanunsa a kan Asma’u lokacin da ta sauke doguwar ajiyar zuciya ya ce “Na yayyafa mata mana”, ba wanda ya bi ta kan lusarancinshi suka cigaba da yi ma Asma’u sannu.

 Ita kuwa, ciwon kowace ga’ba ta jinta bai bari ta iya bu’de idanu ba, bare har ta amsa masu, jujjuya kanta ta shiga yi tana fad’in “Wayyo Allah”, lokaci d’aya kuma hannunta dafe da mararta da take jin kamar ana tsunkulinta, cike da tausayinta Ummansu Abbas ta ce mata “Sannu, me ke damunki?”, kukan da Asma’u ta fashe da shi ne ya amsa mata tambayarta, cewar akwai abin da ya samu cikin Asma’u, dan ta kasa janye hannu ga mararta, duban Abbas da kana ganinshi ka san yana jin rad’ad’in yanayin da Asma’u ke ciki a ransa ta ce “Abbas, asibiti za a kai yarinyar nan, ka je wurin Alhaji Sani ka nemi alfarma ya mik’a mu asibiti”, abin da shi ma ke ranshi kenan, “Toh” ya ce, jiki a mace ya fice gidan, cikin ikon Allah ana fad’a ma Alhaji Sani wanda ma’kwabcin gidansu Abbas d’in ne ya ce ba matsala, ba tare da ‘bata lokaci ba aka nufi FMC da Asma’u, domin a can ne take awo.

Emergency aka nufa da ita, karon karfo likita na mata Bp ya ga jininta ya hau, da ya dawo wurin cikinta kuwa kokwanto ya shiga yi, domin kamar abin da ke ciki bai da lafiya shi ma, scarning aka yi mata, aikuwa aka tabbatar masu da cewa ɗantayin mai watanni shida da ke cikin Asma’u baya da rai, dan haka za’a yi inducing d’inta ta haihu a yanzu, labour room aka nufa da ita.

“Ai dama ta rantse ba zata haifi cikin nan ba”, Abbas ya fad’a cikin ‘kunar rai, ba tare da ya san ya fad’a ba, cike da mamaki Ummansu dake gefenshi ta ce “Me kake fad’a haka Abbas?”, kasa bata amsa ya yi, zuciyarshi kamar zata faso ‘kirjinshi ta fito ya dafe kai, take al’kawarinsu da Asma’u ya fad’o mashi a rai na rabuwa da ita idan ta haihu “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” ya furta a firgice, domin akwai yiwuwar ya rasa ransa indai ya cika wannan al’kawarin.

“Abbas akwai wani abu bayan wannan ne?”, Ummansu ta tambaye shi, kai ya girgiza “A’a, kawai ina jin zafin rasa abin da Asma’u zata haifa ne”, ganin ƙwalla a idanunshi ne ya haifar mata da gagarumin tausayinshi. Ita d’in uwa ce, ko ba ita ta haifi Abbas ba dole ne ta tausaya mashi a kan rasa d’ansa da ya yi, domin itama ta ta’ba rasawa, bare kuma ita ta haife shi, sai abin ya zame mata biyu, “Ka yi ha’kuri, Allah da ya kar’ba shi zai baka wani”, maganganu masu tausasa zuciya ta yi ta faɗa mashi har ya ɗan samu nutsuwa. 

Wurin ƙarfe bakwai da rabi ne Aunty ta zo, dan ba’a faɗa mata ba sai da aka shigar da Asma’u labour room, cike da jimami suka gaisa bayan ta zauna a gefen Umman Abbas akan dandamalin varander labour room ɗin, “Oh! Ita kuma sai haihuwar ta zo da haka?”, Aunty ta fad’a cike da jimami, “Umman Abbas ta ce “Toh ya za’a yi, sai dai fatan Allah ya bata lafiya”, Abbas da Aunty suka had’e baki “Amiin”, shiru wurin ya yi, kowa na ta saƙesaƙen zuci, musamman Aunty da rikicin Abbas da Asma’u na jiya ya dawo mata rai.

Shi kam Abbas ya san idan ya zauna wurin toh zai cigaba da ɓarin zance ba tare da ya sani ba, hakan ya sanya shi tashi ya fita daga asibitin.

Asma’u kuwa sai da ta raina kanta saboda azabar naƙuda, tun kuwa kukanta na ba nurses d’in da ke labour room d’in tausayi har ta kai ga sun fara jin haushinta. Wata daga cikin nurses d’in ce ta zo wurin gadon Asma’u, “Asma’u dan Allah ki rage kukan nan, domin ba zai hana ki jin zafin da kike ji ba”, cikin magagin ciwo Asma’u ta ce “Baki san yadda nake ji ba shi ya sa”, dariya sosai ta ba kusan duk wad’anda ke labour room d’in, lallashinta nurse din ta yi, amma Asma’u bata fasa ba, haka ta rabu da ita ta koma kan sauran matan da su ke ta bauta su ma.

Doguwar na’kudar Asma’u bata bari hankalin kowa ya kwanta ba, rok’on Allah su Aunty suka duƙufa, cikin ikon Allah ɗayan rana sai gata ta sauka, barka su Aunty suka shiga yi ma juna, duk da a ‘kasan rayukansu suna jin ƙunar rasa jaririn, musamman Abbas da bayan rasa ɗa kuma akwai yiwuwar rasa uwar ɗan, shi dai bai daɗe Asibitin ba ma saboda kimtsa gawar yaro.

Itama Asma’u kwanta d’aya Asibitin aka bata sallama, domin bata da sauran damuwar komai a jikinta, sai ma murna da rabuwa da alaƙaƙai ɗin da take ta yi a ranta. 

Aunty ta so daga asibitin ta wuce da Asma’u , amma Umman Abbas ta ce a maida ta ɗakinta ta gyagije ko da na kwana bakwai ne, ta kuma yanke wannan hukuncin ne dan su bata kulawar da suke ganin za ta cire mata raɗaɗin rasa ɗanta, basu san ita ranta sawai ba. 

Abbas kuwa hidimar duk abin da ake yi wa maijego ya shiga yi, duk da ɗimbin fargabar da ke ransa. 

Dangin Abbas kuwa na kusa da na nesa sai zuwa suke, sai dai daga gaisuwa Asma’u sai ta ɗauke masu kai, amma danginta da ƙawayenta sake masu take su yi ta hira, Aunty na lura da haka ta yi mata magana a lokacin da suka keɓe a bedroom “Asma’u wai meke tsakaninki da dangin Abbas ne kike ta haɗe masu rai?”, shiru Asma’u ta yi kamar ba da ita take ba, a fusace Aunty ta ce “Magana nake maki”, turo baki Asma’u ta yi kafin ta ce “Ni fa ba haɗe masu rai nake ba”, Aunty ta ce “Toh shikenan, za a ga wa ke ƙarya tsakanin ni da ke”, faɗa sosai ta yi ma Asma’u a kan ta yi watsi da duk wani shashancin da ke ranta, dan ba zai haifar mata da ɗa mai ido ba. 

“Uhm! Na rantse ba dai Abbas da danginsa ba”, Asma’u ta faɗa a ranta, wannan faɗa ne kuma ya motsa mata da tijarar da ke ranta. Da daddare Abbas na shirin kwanciya ta tada mashi zancen da ya kusa tarwatsa mashi zuciya, cewar idan za ta tafi gida fa da takardarta zata tafi. 

Iska mai zafin gaske ya furzar, lokaci ɗaya ya tashi zaune daga kan gadon da ya ke, dubanta ya yi cikin hasken fitilar ɗakin ya ce “Asma’u meye ribarki na ɗaga mani hankali a yanzu?”, itama tambaya ta jefo mashi mai kama da wadda ya yi mata “Kaima meye ribarka na hana ni ƴancina?”, baki ya taɓe tare da faɗin “Babu riba kam Asma’u, tunda ke ba matar da hankalin mutum zai kwanta da ita ba ce”, Asma’u ta yi mamakin wannan magana, dan ta ɗauka zai marairaice mata kamar can baya. Cewa ta yi “Idan hakane ka rabu da ni mana”, ƙwafa ya yi, ba tare da ya sake magana ba ya kwanta, masifa ta shiga yi, tare faɗin “Wallahi ko ka rabu da ni, ko in iske mahaifiyarka in ce ta sa ka ka sake ni.” Da ita da banza duk ɗaya ya ɗauke su, fitowa ya yi ya bar mata bedroom ɗin. 

Washe gari Abbas bai bayyana mata ɓacin ransa ba, domin baya son jama’ar da ke zuwa gidan su san halin da suke ciki. 

Shawara ya shiga yi da ransa kan ya faɗa ma mahaifiyarsu halin da ake ciki ko kuwa?, rashin son ɗaga ma mahaifiyarsa hankali ne ya sa shi watsi da shawarar. 

Kwana bakwai na cika aka yi hidimar suna kamar a kwai ɗa, washe gari suna kimtsawa da shirin tafiya Aunty ta kira Abbas ya zo su yi bankwana da matar shi a ɗaki. Bedroom ya taras da ita ta hakimce gefen gado, wani kalar annuri ya gani a fuskarta, wanda ke fassara mashi idan ta tafi ba zata dawo ba, gabanshi na dakan uku-uku ya zauna gefenta, hannayenta da yake jin daɗin taɓawa ya ruƙo, murya can ciki ya ce “Asma’u, bana son ki yi nisa da ni, amma ba yadda na iya, dole na baki dama ki tafi”, shiru ya yi, ƙasan ransa yana jin tausayin kansa. 

Zare hannunta ta yi, cike da zaƙuwar barin gidan ta ce “Ka yi haƙuri, babu zamana a cikin ƙaddararka ta gaba, dan haka ka cika mani alƙawarina in tafi da shi.”

Ya san babu wata maganar da zai faɗa mata ta fahimta, don haka a taƙaice ya ce “Zan kawo maki har gida”, yana rufe baki ya yi saurin tashi ya fice. 

Ba dama Asma’u ta bi shi, saboda duk su Aunty na tsakar gidan. Da baƙincikin rashin tafiya da burinta ta fito ɗakin, Aunty ta lura da yaƙe take, amma ta basar. 

Mota Abbas ya samo, Inda shi da Abida suka yi ma su Asma’u rakiya har gida. 

Murna wurin Asma’u kamar ta taka dutsen arfa. Da Abbas zasu tafi ne ya miƙa ma Asma’u wata farar takarda cikin envelope, cike da zumuɗi ta buɗe takardar lokacin ɗakin ba kowa, inda ta fara karanta abin da ke ciki kamar haka “Sallama da fatan Alkhairi a gare ki matata Asma’u. A yau ni Abbas nake baƙincikin shaida maki na sake ki saki ɗaya, na yi haka ne domin na cika maki dogon burinki. 

 Amma ina neman alfarmarki da ki sakaya wannan sakin zuwa lokacin da zan dawo, domin ki ba su Aunty damar yin faricikin ganinki kusa da su….”, Asma’u bata ƙarasa karanta takardar ba ta ɗago kanta, murna take son yi, amma wani abu da bata san ko meye ba a ƙasan ranta ya hana ta, samun kanta ta yi cikin tambayar kanta a zuci “Me yasa ya sake ni a yau, bayan alamu sun nuna kamar ba zai yi sakin ba?

Mu haɗu nan da Sati biyu ko uku domin jin amsar tambayar Asma’u. Ina ba masu bibiyar wannan littafin haƙuri, saboda zan ɗan aje typing saboda wani uziri da ya sha ƙarfi na, nan da sati biyu ko uku Insha Allahu zan cigaba, Allah ya  sada mu da Alkhairi Amiin.

<< Cikin Baure 14Cikin Baure 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.