Ta ɓangaren Abbas kuwa, tamkar farincikinsa ne gaɓaɗaya ya ba Asma'u a cikin takardar sakin, domin tunda suka baro gidan yake jin wani kalar tashin hankali a ransa, don ma ya yi ƙoƙari sosai ta yadda wani ba zai gane irin wutar da ke babbakar masa zuciya ba.
Bai iya gane shayi ruwa ne ba sai da ya koma gida da daddare, tun a rashin samun mai amsa sallamar da ya yi ya san Asma'u na da muhimmanci a gidan, don kuwa ta kan amsa mashi ko da ciki-ciki ne don ta sauke. . .