Skip to content
Part 17 of 25 in the Series Cikin Baure by Hadiza Isyaku

Sosai maganar Umman Abbas ta saka Aunty cikin rudani, dan kuwa alamu sun nuna cikin tsananin fushi take, “Wata sabuwa kuma”, Aunty ta fada cike da jimami, lokaci daya kuma ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, Asma’u da gabanta ke dukan uku-uku ta ce “Aunty me ta ce maki?”, sai da Aunty ta nisa kana ta ce “Wai Abbas ne a Asibiti”, tsabar firgici Asma’u bata san lokacin da ta dafe kirji tare da fadin “Asiti! Me ya same shi?”, don kuwa ta san duk abin da ya faru da shi ita ce sila, “Ta ya zan san abinda ya same shi”, Aunty ta bata amsa cikin fada-fada, saboda abin ya hade mata biyu, jingina da bangon kitchen ta yi, saboda kafafunta neman rasa garkuwarsu suke. Hakika ta ji ba dadi a kan rashin lafiyar Abbas, amma da yake sawun giwa ‘badda na rakumi yake sai ta karkata a kan sakin da yayi ma Asma’u, cike da kullewar kai ta shiga magana da zuciyarta “Ashe har dama Abbas zai iya sakin Asma’u?”, duba da kusancin dake tsakanin mahaifansu, sanin halin mutum sai Allah ta ce “Ai shikenan, Allah ka iya mana.”

Asma’u kuwa duk da bata ji cikakkiyar maganar da Aunty ta yi da Umman Abbas ba, amma ko shakka babu a fusace take, kuma wannan ke nuna sun san komai game da azabar da ta gana ma dansu. Rasa yadda zata taro tsoron da ya mamaye mata rai ta yi. Zancen zuci ta shiga yi daga tsayen da take itama a kofar daki, “Allah ka hana Aunty ta gane ni nace a sake ni”, cike da firgici ta yi wannan addu’a a kasan ranta, dan kuwa muddin aka gane ita ce sila toh ta shiga uku, saboda kaf daginta suna ganin mutuncin.

Da ta juyar akalar tunaninta ga Abbas kuwa bata san lokacin da zancen zucinta ya fito fili ba, inda ta ce “Oh, ko mi ya same shi?”, da sauri ta kalli Aunty da har yanzu take jingine da bangon kitchen, gani ta yi ta kura ma wuri daya ido, alamun bata ji me ta ce ba. “Toh meye nawa ma da sanin abin da ya same shi?”, wani sashe na zuciyarta ya kwabe ta akan kada ta tilasta ma kanta sanin halin da Abbas yake ciki, koda kuwa mutuwa ya yi, tunda dai ta rabu da shi. Ta bangaren kashe aurenta ma da tsiya ta kawar da tsoronsu Aunty, dan kuwa ko sun dauki zafi ma zasu huce, kai ko basu huce ba in dai bukatarta ta biya shikenan. Domin ma ta samu sassauci sai ta shige ban daki, ta bar Aunty da tulin tashin hankali a rai. 

Acan asibitin kuwa likitoci sun yi kokari sosai wurin ba Abbas kulawar da ta dace. Allurar bacci aka yi mashi, sannan aka hana kowa shiga inda yake, in banda Ummansa da ta dage sai ta shiga, saboda gani take kamar Abbas ba zai tashi ba. ‘Kuri ta yi mashi daga tsayen da take a gefen gadon da yake kwance, idanunta cike da kwallan tausayin nagartaccen d’anta ta ce “Muddin baka yi zalunci ba, Allah ya tashi kafudunka kuma ya bi maka hakkinka Abbas”, rufe bakinta ke da wuya ta ji an turo kofar dakin a hankali, Abeeda ce da itama ta kasa nutsuwa har sai ta ga wane hali d’an uwanta yake ciki, tun kafin ta ‘karaso gaban gadon ta jefo ma Ummansu tambaya da “Umma ya jikin nashi?”, cikin dakushewar murya Ummansu ta bata amsa “Toh gashi nan dai”, cikin muryar kuka Abida ta roka ma Abbas lafiya a wurin Allah, don gani take kamar baya numfashi, likita na shigowa ya lallashe su da magana mai taushi, saboda shasshekar kukan da suke ba zata bari Abbas ya samu nutsuwar da ake so ya samu ba.

Wasu daga cikin danginsu Abbas kuwa cikin daren suka yi ta zuwa, kusan duk wanda ya ji dalilin rashin lafiyar shi sai ya zagi Asma’u. ‘Dan autan gidansu Umman Abbas kuwa,wanda shi ne zai kwana a asibitin ya ce “Ai dama da ganin wannan ‘yar banzar bata da kirki”, Abida da ke neman wanda zai taya ta zagin Asma’u ta ce “Wlh kuwa, ai ya rabu da masifa dai”, cike da ‘kuna rai suka yi ta lissafin miyagun halayen Asma’u da idanunsu suka gani, Ummansu kuwa sai dai ta ce “Hmm” kawai, don damuwar dake cike da ranta ta fi karfin baki ya furta ta.

Motsin da Abbas ya yi ne ya sanya su yin shiru suna dubanshi, cike da kulawa Ummansu ta dafa hannunshi mai daure da drip, lokaci d’aya kuma ta ce “Abbas”, a hankali ya bude idanunsa da suka yi mashi mugun nauyi, cikin sarkewar murya ya ce “Umma me ye aibuna dan na nuna ma Asma’u so?”, duk wadanda ke zagaye da shi sai da ransu ya baci akan farkawa da maganar Asma’u a bakinsa, amma kowa sai ya danne, saboda yanzu nutsuwarshi suka fi bukata, sai da Ummansu ta hade gululun da ya yi mata tsaye a wuya sannan ta ce mashi “Ba ka da wani aibu Abbas, kuma Asma’u ce ta yi asara ba kai ba, don haka ka yi hakuri, Insha Allahu zaka yi farinciki a gaba”, maganganu masu dadi suka yi ta fad’a mashi, wanda ba duka yake iya fahimta ba saboda duniyar ta yi mashi kuncin gaske. Goman dare na yi Umman Abbas da Abeeda suka tafi gida, sai dai yadda suka ga rana haka suka ga wannan dare.

Washe gari da yamma Aunty ta zo ganin Abbas, sosai ta ga chanji a wurin duk wanda ke da alaka da shi, kuma ta yi matuk’ar mamaki, duk da itama ya kamata ta chanja masu. Bayan sun keɓe da Umman Abbas a ƙarƙashin wata bishiya ne ta ce mata “Duk da baki bai furta ba, amma na fahimci abubuwa sun yi zafi Umman Abbas, ina fatan Allah ya ba Abbas lafiya, idan ya so sai a san abin yi a kan batun rabuwarshi da Asma’u”, sai da Umman Abbas ta sauke numfashi kafin ta ce “Ai ba wani sauran abin yi dangane da auren Asma’u da Abbas, tunda Asma’u bata son shi, kuma da kanta ta nemi saki, tare da ikrarin kisa idan bai rabu da ita ba”, Aunty bata yi zaton jin wannan maganar a bakin Umman Abbas ba, cike da mamaki ta dube ta tare da fad’in “Haba dai dan Allah, yanzu Asma’un ce ta nemi sakin da kanta?”, Umman Abbas ta ce “A yadda Abbas ya ce ba, kuma ko ba wannan tunda haka ta fara faruwa a hakura da auren kawai, muddin muna son ɗorewar zumuncinmu.”

Sosai maganganun Umman Abbasa suka sanya jikin Aunty sanyi, har ta nemi kwarin guiwar dake jikinta ta rasa, lallai tunda har Umman Abbas ta iya faɗa mata haka, toh munin abin ya fi gaban kwatance, jiki a mace ta ce “Toh shikenan, Allah ya kawo mafita”, a takaice Umman Abbas ta ce “Amiin”, shiru suka yi kamar waɗanda ruwa ya ci, kowa da irin ɗacin da yake ji a ransa, musamman Aunty da take ganin auren Asma’u na d’aya daga cikin hanyoyin da asirinsu ke rufuwa, saboda alkhairorin da Abbas ke yi musu basa lissafuwa, kuma ko ba wannan zawarci masifa ce mai zaman kanta a wannan lokacin na halin ni ƴasu, a ranta ta ce “Allah ka iya mana.”

Umman Abbas kuwa wasu maƙwabtansu na zuwa ta cigaba da hira da su, Aunty na ganin ba ta ita suke ba ta tashi, bankwana suka yi, sannan ta tafi gida.

Yanayin fuskar Aunty kad’ai Asma’u ta gani ta sha jinin jikinta, cike da kamun kai ta yi mata sannu da zuwa, ba tare da Aunty ta kalli kan kujerar da Asma’un take zaune a kofar d’akinsu ba ta amsa mata ciki-ciki sannan ta shige d’akinta. 

Dogon numfashi Asamau ta sauke tare da tambayar kanta “To ni ya zan yi ma”, dan ta ga alamun Aunty ta san gaskiya, ƙaramin tsaki Asama’u ta saki tare da ɗaga kafaɗa na nuna babu abinda ke damun ta, wanda a zahiri ita kanta ta san pretending take “As’mau!”, daga can cikin ɗaki Aunty ta kira ta. Rass! Ra-rass!! gaban Asama’u ya yanke yafadi, cikin sarƙewar murya ta amsa, sai da ta bata lokaci kana ta tashi jiki ba ƙwari ta nufi ɗakin Aunty. 

Kan kujera ta raɓe ta na fuskantar Aunty da ke kan gado, shiru na wucin gadi ɗakin ya yi kafin daga bisani Aunty ta ce “Asma’u, ki faɗa mani gaskiya, A kan me Abbas ya rabu dake??”, A daburce Asma’u ta ba ta answer “Ni, ni ma ban sani bah Aunty”, Kai Aunty ta girgiza tare da faɗin “Inaa! Wallahi kin san komai”, Don kuwa tafi kowa sanin yanayin Asma’u idan bata da gaskiya, Marairaicewa Asma’u ta yi tare da faɗin “Wallahi Aunty…” Dakatar da ita Aunty ta yi tare da fadin ” Bana son wata rantsuwa, ke kikace Abbas ya sake ki, koba haka bah?” Shiru Asma’u ta yi domin bata da bakin kare kanta, Faɗa Aunty ta shiga yi mata, ta inda take shiga ba ta nan take fita bah, kuka Asma’u ta shiga yi tana kokarin kare kanta.Tarar lumfashin ta aunty ta yi “Rufe mun baki, Allah ya rufa maki asiri muma ya rufa mana, Amma kika tona mana shi, in dai zaman gidan da kika zaɓa ne ga ki, ga shi, ai kin san yanda yake, sai kizo ki zauna mu dasa daga inda aka tsaya.” kuka Asma’u taita rizgawa, amma Aunty bata sarara mata ba, sai ma ta cigaba da faɗin “Ban yi maki baki bah, Amma samun miji kamar Abbas abune mai matukar wahala.”

 Fitowa Aunty ta yi daga ɗakin ta jingine da bangon kitchen ta cigaba da amayar da raɗaɗin dake cikin ranta. Maigidanta na shigowa ya nemi ba’asi a wurinta, yana kuwa jin abinda ya faru ya shiga zazzage ta cikinshi shima, daga ƙarshe ya leƙa ɗakin Aunty ya cewa Asma’u da har yanzu take kuka “Tunda kinƙi Abbas, to za mu maye masa gurbinki da Nafisa, don kuwa mun san ita ba zata watsa mana ƙasa a ido bah.” Juyowa yayi warin Aunty suka cigaba da furzas da takaicin dake cikin ransu. 

 Asma’u kuwa tun tana kuka mai sauti har ta kai ga muryarta ta disashe, tausayin kanta ta shiga y, domin kuwa ta san ko duniya zata haɗu ba wanda zai yarda da tsananin kiyayyar da takewa Abbas.

 Kiraye kirayen sallan magrib neh ya fito da ita daga dakin Aunty, Alwala ta yi ta shige dakinsu ta gabatar da sallah, tana gamawa ta roki Allah ya sa koda nan gaba ne a fahimce ta, saboda ta fahimci fushinsu Aunty data raina ya wuce gaban tunaninta,tana nan zaune tana addu’a har lokachin sallar isha’i ya yi, tashi ta yi ta gabatar.

Daga can tsakar gida kuwa babu wanda ya sake bi ta kanta har saida aka gama tuwon dare. 

Dan autan Aunty akaturo ya kira ta, don ta dauki nata, aikuwa ta ce ta ƙoshi, daga nan babu wanda yasake bi ta kanta.

 Rarrafawa tayi ta haye saman yar katifarta domin ta yi bacci, ƙaura baccin yayi mata, ahaka ta rinka juye-juye ta rasa mey ke mata daɗi, Alhaji Nas kawai ta ji zuciyarta na hasko mata, atake ta fara ganin fuskarshi a cikin idanun ta, juyi ta cigaba da yi, zuciyarta ta ji ta kasa nutsuwa tanason ganin sa at all cost, tunawa tayi tana da photunan sa a wayarta, hakan yasanya ta sami wani kuzari a jikinta ta tashi ta dauko wayarta da tamanta da ita kan sallaya, wayar ta kunna ta shiga kallon photunan, wani irin sanyi ta ji a ranta, murmushi ta shiga yi tana ƙara ƙure ma fuskara kallo, tana cikin wannan yanayin ne batare da saninta ba Nafisa ta shigo tare da yin tsaye akanta tana mata kallon anya wannan ƙalau take kuwa.???

Jin hucin mutum da ta yi asaman kanta ne ya sa ta dagowa da sauri, mummunan faduwa gabanta yayi, cike da kamun kai ta tambaya “ya akayi Nafisa ?” takaitacciyar amsa Nafisa ta bata da “ba komai” sannan ta dauki abunda ya kawo ta ta fice daga dakin. Komawa Asma’u tayi ta kwanta ta cigaba da kallon photon Alh.Nas, wata tsantsar kaunar sa ta rinka ji acikin ranta, zooming photon ta yi tare da sumbatar sa tayi, dora wayar tayi a saman kirjinta tashiga tunanikansa masu sanyaya mata zuciya ahaka har bacci barawo yasace ta. 

Ta ‘bangaren su Aunty kuwa ita da mai gidanta kwana suka yi suna sa’ka da warwara akan yanda zasu yi da lamarin Asma’u har asamu Abbas ya maida ta ba tare da kowa ya sani ba, daga karshe dai suka yanke shawara akan cewar idan Abbas yasamu sauqi, zasuje gidan su ayi sulhu. Koda kuwa suka samu labarin an sallami Abbas sai suka shirya tafiya gidansu da nufin gaisuwa da ro’kon Iri.

Da yamma, Abbas na tsaye a kofar gida ya hango dosowar mashin d’in su Aunty, da kyar ya iya shanye rad’ad’in ciwon da suka fama mashi, da dariyar yake ya tarbe su bayan sunyi mashi ya jiki yayi masu jagora zuwa cikin gidansu, A d’aki suka taradda umman Abbas, fuska a sake ta tarbe su har Aunty tayi mamakin hakan, gaesawa sukayi da juna har suka dan ta’ba labarin duniya, sosai su Aunty suka samu kwarin guiwar da mijinta yabayyana mata ku’dirinsu na son sulhuntawa tsakanin Abbas da Asma’u, da mamaki sai sukaji ta ce “Ni dai a bangarena a hakura da wannan aure shiyafi alkairi amma idan Abbas yanada ra’yi sai akirawo shi kuji ta bakinshi.”

Kiran Abbas d’in aka yi kamar yadda su Aunty suka bukata, tambayar shi ra’ayinshi suka yi. Shiru ya yi daga zaunen da yake a kasa, lokaci daya kuma yana nazarin tsananin ‘kaunar da yake ma Asma’u, wanda shi ne sanadin shigarshi mawuyacin halin da har yanzu yake ciki…

<< Cikin Baure 16Cikin Baure 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.