Miraran su Aunty suka ga tsabar raunin zuciyar Abbas, dangane da son da yake ma Asma’u, har suka yi tsammanin haƙarsu zata cimma ruwa, cike da zaƙuwa Aunty ta katse mashi tunani ta hanyar faɗin “Ka yi shiru Abbas.”
Murmushin da iyakar sa kumci ya yi, lokaci ɗaya kuma ya dube ta cikin sigar tausayin kansa, muryarsa na karkarwa ya ce “Ku gafarce ni Aunty bisa ga hukuncin da na san ba zai yi maku daɗi ba”, Sosai wannan magana ta Abbas ta ƙara saurin bugun zukatan da ke ɗakin, duk da ba su ji takamaiman hukuncin ba, a marairaice Aunty ta tarbi numfashinsa ta ce “Toh Abbas, duk abin da Allah yayi ai mai kyau ne”, Ummansa kuwa kasa cewa komai ta yi, don ta san ƙarfin hali ne kawai zai yi.
“Ina ganin a haƙura da aurena da Asma’u, saboda hakan shi ne mafita gare mu baki ɗaya.” Hausawa suka ce, abin da ya koro ɓera har ya jefa shi wuta, toh haƙiƙa ya fi wutar zafi, kamar yadda duk abin da zai sa Abbas ya haƙura da Asma’u, toh shi ne mafi alkhairi a kan zama da ita.
Cike da gigita Aunty ta ce “Haba kai kuwa Abbas! Auren nan naku da ko shekara bai yi ba, kuma sai ace saki ya biyo baya?, dan Allah a duba.”
Mijin Aunty ya san babu gyara a cikin hukuncin Abbas, sai bai furta komai ba.
Kamar Umman Abbas zata yi magana sai kuma ta danne duk da ta fahimci kallon da yake mata na ta sa baki ne, saboda ta fi son su ji komai daga bakinsa.
Tamkar mai jin bacci ya lumshe idanu, sannan ya ce “Asma’u bata so na, don haka mu barwa Allah komai”, yana rufe baki ya dafe goshinsa da hannu ya yi shiru.
Maigidan Aunty mutum ne mai saurin fahimta, ba tare da wahalar da sharia ba ya ce “Allah ya sa hakan shi ya fi Alkhairi”, baki suka haɗa tare da faɗin “Ameen.”
Umman Abbas ta fi kowa fahimtar tsantsar damuwar da ta addabi Aunty, saboda ta san abu ne mai wahala uwa ta iya jure raɗaɗin mutuwar auren ƴarta, cike da tausasa murya ta shiga ba su haƙuri da tabbatar masu da har yanzu zumuncinsu yana nan, asalima sunyi hakan ne domin basa son zumuncinsu ya yanke, kamar Aunty zata yi kuka ta ce “Ai babu komai.”
Abbas kuwa tashi yayi ya nufi gidansa don ya fashe gululun da ke ransa ba tare da sa idon kowa ba, da shigar sa ya maido ƙofar tare da sa mata key, ɗaki ya ƙarasa gami da zama kan kujera, lokaci ɗaya kuma ya dafe kansa da dukkan hannayensa.
“Allahumma laa sahla illa ma ja’altahu sahla, wa anta taj’alul hazna iza shi’ita sahala” kawai bakinsa ke furtawa, domin kuwa faɗin gobarar ta ke ci a ransa ma ɓanar baki ne.
Kuka yake son yi, amma ya kasa, a nan ya gane ƙaramar masifa ce ake yi ma kuka.
Cikin wata irin murya mai karya zuciyar mai sauraro ya riƙa furta “Ina ma ke kaɗai kika tafi Asma’u”, domin ko shakka babu da dukka farinciknsa Asma’u ta tafi, ɗorawa ya yi da faɗin “Ki dawo mani da farincikina, ki dawo mani da dariyata, ki dawo mani da nutsuwata, laffuzzana masu taushin gaske Asma’u, ko da kuwa ke ba zaki dawo ba.”
Kukan da yake fatan yi ne ya ƙwace mashi, har ya durƙushe a kan guiyawunsa ba tare da ya sani ba.
A wannan lokacin Abbas ya tabbatar da ya yi asarar duk wata siffa ta nutsuwa, har yana jin da wahala ya iya maida su. Kuka sosai ya yi har sai da hawayensa suka ƙafe.
A can gidansu kuwa, su Aunty na tafiya Ummansa ta shiga neman sa, don ta san duk inda yake a yanzu baya cikin nutsuwa.
Da kanta ta fita nemansa, saboda kaf yaran gidan suna islamiya. Daga ɗan nesa ta hango Zee, kuma da alamu gidan zata shiga.
“Umma fita ma zaku yi?” Zee ta tambayi Umman Abbas bayan ta ƙaraso, girgiza kai Umman Abbas ta yi “A’a, Abbas na fito nema”, sai da Zainab ta ɗan waiga ta kalli bayanta, sannan ta juyo ce “Aikuwa ɗazu na ga ya nufi gidansa, kamar ma jikin ya tashi ko?”, Umman Abbas da ta san za a rina ta ce “Ai komai ma ya tashi Zainab.”
Cikin gidan suka ƙarasa, nan Umman Abbas ta labarta ma Zainab komai, aikuwa buɗar bakinta ta ce “Wallahi ya huta Ummah, ni dama bana tunanin Abbas ya san daɗin aure.”, Umman Abbas ta ce “Ai dayawan mutane sun faɗi haka Zainab, duk da zurfin cikinsa kuwa”, ran Zainab ba daɗi ta ce “Allah ya zaɓa mashi wata matar ta gari”, Ummansa ta ce “Amiin”, lokaci ɗaya kuma tunaninta na kan wane hali Abbas ya ke ciki?, numbersa ta kira domin samun nutsuwar zuciyarta.
Kan Abbas na haɗe da guiwa ya ji wayarsa da ke kan kujera na fidda sautin da ya ware ma Ummansa, cike da tilasta ma kansa ya sassauta sheshshekar kukan da yake, duk da ya kasa ɗaga kiran.
Sai da ta kira a karo na biyu ne ya ɗaga daƙyal, cikin disashewar murya ya amsa mata tambayar ta da “Ina gida”, daga can ta ce “Ba wata damuwa ko?”, idan ya ɓoye mata ya yi ƙarya, cewa ya yi “Ki taya ni da addu’a Ummah”, ta ce “Insha Allah, Allah ya baka mafita ta Alkhairi”, ya ce “Amiiin Ummah.”
Maida wayar ya yi kan kujera bayan Ummansa ta tsinke kiran. Bai iya komawa gidansu ba sai bayan Magrib, har a lokacin kuma Zainab na nan, saboda mijinta ya yi tafiya.
Magana mai daɗi suka yi ta faɗa mashi, har Zainab na tsokanarsa da zata bashi ƙanwarta idan yana so, murmushin yaƙe kawai ya yi, don a yanzu babu wata mace dai zai iya ba amanar zuciyarsa.
Su Aunty kuwa ko da suka isa gida basu bi ta kan Asma’u ba, don sun bar ma duniya ta faɗa gaskiya, sai dai duk wanda ke da haƙƙi a kan lamarinta an sanar da shi, kuma babu wanda bai yi tir da Allah wadai da ita ba, saboda kaf illahirin danginsu sun san nagartar Abbas.
Babanta da ya haife ta kuwa saboda ɓacin rai ya ce ta koma wurinsa da zama, don ta ko yi zaman duniya a wurin matansa da kuma ƴaƴansu.
Allah ne ya tsaya mata, da kuma Aunty da ta nemi alfarmar a bar ta wajenta, don a nan ma sun shirya mata horo mai tsanani, kasantuwar rayuwar da suke ta tsanani bata chanja ba.
Asma’u kuwa ta ɗauka ta ci lalai, mafarin ta sake aka cigaba da rayuwa da ita, sai dai tafiya na miƙawa wahalar aikin gidan ta fara ankarar da ita ɗaurin talala ne Aunty ta yi mata, don kuwa aikin mutum biyu ko uku take yi idan har su Nafisa sun tafi makaranta.
Aunty kuma na lura da cika da batsewar da take idan tana aikin, musamman wanke-wanke da tsana, amma sai ta yi watsin karan mahaukaciya da ita, har sai lokacin da Asma’un da kanta ta samu Aunty a ɗaki ta ce “Dan Allah Aunty ki ce ma Nafisa ta riƙa tashi da wuri tana aikinta”, daga zaunen da Aunty take a bakin gado ta ce “Sai ki faɗa mata idan ta dawo”, yadda Aunty ta bata amsar a kausashe ne sanyaya mata jiki, kamar wadda bata da lakka ta saki labule tare da yin jugum a ƙofar ɗakin.
Nafisa na dawowa da yamma ta yi mata maganar ta riƙa tashi da wuri tana aikinta, da yake raini ya gama shiga tsakaninsu sai Nafisar ta yamutse fuska ta ce “Islamiyar daren da nake zuwa fa? Ko kin manta bata bari na falkawa da wuri”, cikin haushin yadda Nafisar ta maido mata magana ne ta ce “Toh me zai hana ki riƙa aikin kafin Islamiyar daren”, wani mugun kallo Nafisa ta watsa mata kana ta ce “So kike in wanke kwanuka a ɓata, kuma da safe a ce sai na sake wanke su ko, toh na rantse ba zan iya ba.”
Duk yadda Asma’u ta ɓullo wa Nafisa a kan ta riƙa aikinta, amma fafur ta ƙiya, hakan ne ya tunzura Asma’u har suka fara musayar maganganu.
Aunty na ɗaki tana jinsu, kuma har cikin ranta ta ji ba daɗin faɗan don basu saba ba, amma sai ta danne dan Asma’u ta fahimci ta rasa girman da aure ya bata, duk da kafin ta yi aure ma yaran gidan kowa girmamata yake, yanzu kuwa ba wanda bai ga wurin baccinta ba.
Washegari kamar kullum Nafisa ta yi tafiyarta ta bar kwanuka bata wanke ba, haka Asma’u ta shiga wanke su cikin ɓacin rai. Sanyi safiya na ratsata ta shiga zabga atisahawa, take zuciya ta tuno mata lokacin da Abbas ke taya ta aikin gida, wani lokaci ma sai ya ce ta kwanta ta huta zai yi aikin shi kaɗai.
Wasu zafafan hawaye ne suka gangaro mata a kumci, don kuwa duk wanda ya tuna bara, toh bai ji daɗin bana ba.
Haka ta yi ta aiki tana sharar hawaye, lokaci ɗaya kuma tana ta recalling zamanta da Abbas, Aunty na fitowa daga banɗaki shesshekar kukan Asma’u ta ɗauki hankalinta.
Tuni dama sanyin jikin Asma’u ya fara taɓa mata zuciya, cike da tausayinta ta zauna kan rijiya tana fuskantar ta, ƙuri ta yi ma Asma’un da ke ta ƙoƙarin haɗiye kukan da take, kai Aunty ta girgiza, a fili kuma ta ce “Hmm.”
Ƙasa Asma’u ta yi da kanta, inda kukan tausayin kanta ya ƙwace mata da ƙarfi, “Asma’u ya dai”, Aunty ta faɗa cikin sanyin murya, kasa ɗago kan Asma’u ta yi, bare ta iya bata amsa, ba tare da wahalda Shari’a ba Aunty ta ce “Ko baki faɗi abin da ke ranki ba, na san nadama ta fara shigar ki, don ba ki yi tsammanin za ki tsinci kanki a haka ba.”
Ɗan numfasawa Aunty ta yi, kana ta ɗora da “Kina zamanki lafiya da mijinki, mai ƙaunar ki, kawai kika biye ma wani banzan ra’ayinki kika kashe aurenki, yanzu tun ba a je ko ina ba na san kin tuna ɗimbin alkhairinsa a wurinki.”
Tabbas Asma’u ta sha tuna ɗimbin kyautatawar Abbas, amma har yanzu bata fara nadamar barinsa ba, kamar yadda Aunty ke tunani, sai dai ba zata yi musu da Aunty ba a kan duk wani faɗa da zata yi mata dangane da Abbas, saboda ta fi su sanin shi mutumin kirki ne.
Haka ta baza kunnuwanta tana sauraron faɗan Aunty, wanda take jin shigarsa kamar mashi a ƙahon zuciyarta.
Auntin na tashi ta ɗan ji sauƙi a ranta. Wani ƙarin sauƙin kuma Nafisa na dawowa Aunty ta tsara masu yadda kowa zai yi aikinsa.
Ta wani ɓangaren kuma Aunty ta jawo ta ajiki, dan sai da haka ne za a gyara mata babban kuskuren da ta aikata.
Wannan sassauci ne ya ba Asma’u damar tuna abin da damuwa ta mantar mata da shi, wato Alhaji Nas. Duk Lokacin da ta samu dama sai ta yi ta kallon hotunansa da take cirewa a dp kamar yadda ta saba, lokaci ɗaya kuma tana laluben hanyar da zata cusa kanta a wurinshi, tunda ba nisa suka yi da juna ba.
Abbas kuwa da ya ga tunanin Asma’u zai kashe shi a banza, sai ya tilasta ma kansa yakice ta a zuciyarsa, duk da hakan ba ƙamarar azaba yake gana mashi ba.
Sauƙinshi ma Abdull da danginsa suna kwantar mashi da hankali, uwa uba kuma aikinsa na blocks da ya maida hankali a kai, sai dai duk mai zurfin tunani idan ya sanya ma Abbas ido zai lura da sanyin jikinsa.
Daidai da Alhaji Nas wanda bai cika damuwa da sungulan mutane yayi ba, yana zuwa kamfaninsu sai da ya ce “Abbas ka yi sanyi sosai”, saboda komai yana yinsa ne kamar kazar da ƙwai ya fashe mawa a ciki.
Abdull ne ya faɗa ma Nas ɗin cewar Abbas yayi fama da rashin lafiya, kuma har yanzu bai ƙarasa murmurewa ba, sosai Nas ya tausaya mashi, tare da fatan masa samun lafiya mai ɗorewa.
Ummansa kuwa ta san kewa ce ke damunsa, maiyiwuwa idan ya yi aure ya samu kwanciyar hankali. Da daddare yana tsaka da cin tuwo ta ce “Abbas wai yaushe zaka yi aure?”
Wata irin faɗuwa gabansa ya yi, sai da ya haɗe lom ar bakinsa daƙyal kana ya ce “Aure Umma?”, ta ce “Eh”, ya ce “Ba yanzu ba…”