Cike da ƴar fargaba ta sake jefo mashi tambaya “Kamar ya ba yanzu ba Abbas?”, hannunsa ya fidda daga cikin plate ɗin tuwon, kana ya dube ta cikin hasken wutar lantarkin da ya game tsakar gidan “Sai nan gaba kaɗan Insha Allahu”, ya ba ta wannan amsar ne saboda bai son a ja maganar, bare rayukansu su ɓaci.
Cewa ta yi “Toh Allah ya nuna mana lokacin”, a taƙaice ya ce “Amiin”, a ƙasan ransa kuma yana tunanin anya ma zai iya sake wani aure?, don kaf matan da yake gani ba wadda ta taɓa birge shi kamar Asma’u, kuma tunda ita ta guje shi, toh ya haƙura.
“Ya Abbas wacece gwanar, don mu fara shirin tarbar ta?”, kamar daga sama ya tsinkayi tambayar Abida a saman kansa, dan bai ma san tana cikin gidan ba sai yanzu, ashe tana ɗaki, lokaci ɗaya kuma kunnenta na tsakar gida tana jiyo maganarsu, ganin zancen bai yi tsayi ba ne ya sa ta fitowa ta maida hannun agogo baya.
“Gulma ajali”, Abbas ya faɗa yana ƴar dariya, Ummansu ta ƙarasa mashi da “Wanda bai yi ba zai mutu”, daga bakin ƙofar da Abidar take tsaye ta ce “Daga tambaya, shi ne za a fassara ni”, dariya su duka suka yi, earpiece ɗin dake a jikin kunnenta ta cire, tare da kashe kallon da take a wayar, gefen Ummansu ta zauna a kan tabarma, suka cigaba da hira mai cike da sanyaya zuciyar ahalin. A nan ne Abida ta zuga Abbas da ya gaggauta yin aure, ko dan ya nuna ma Asma’u ƙarfin ikon da Allah ya ba namiji na yin aure a duk lokacin da ya ga dama, saɓanin mace da Idda kaɗai tana iya kawo mata tsaiko. Ta wani ɓangaren kuma yin auren zai tabbatar ma Asma’u da ba ita kaɗai mace ba a duniya.
Sai da ya yi ƙwafa kana ya ce “Wurin gaggawa in yi zaɓen tumun dare ba.”
“Ba wani zaɓen tumun daren da zaka yi, ni tsaf a cikin ƙawayena sai in samo maka ƴar ƙwalisa ka aura”, sosai maganar Abida ta bashi dariya, cewa ya yi “So ki ke a daɓa kenan, ni ba wanda zai kawo mani mata, bare a sake jin kunya”, Ummansu ta fahimci kandakon da yake masu, murmushi kaɗai ta yi, tare da faɗin “Ahaa! Faɗa mata dai, ni ma na fi so ka zaɓo matar da kanka.”, dan yadda zuciyarsa ta rugurguje, idan aka tilasta mashi ya auri wata, toh da wahala ya iya kyautata mata.
Tufka ya yi ma bakin maganar ta hanyar bayyana masu a yanzu babu macen da ke birge shi, don haka aure ba yanzu ba ma, kamar yadda a ɗazu ya faɗa ma Ummansa.
Rurin wayar Abida ne ya karkata akalar hirar a kan saurayinta wanda ke shirin turo iyayensa, bayan ta koma ɗaki dan amsa wayar ne Abbas ya tabbatar ma Ummansu da Abida ta yi dacen miji. Cike da jin daɗin wannan tabbaci ta roƙa ma Abbas shi ma Allah ya zaɓa mashi mace ta gari, shi ma cike da jin daɗin wannan fatan Alkhairi ya ce “Amiin Ummah.
Wata hirar suka dasa, ba shi ya koma gidansa ba sai goman dare. Tunga ya ja a ƙofar shiga bedroom kamar yadda ya saba, lokaci ɗaya kuma yana kewar kayan ɗakin Asma’u, dan sun daɗe da kwashe kayansu, sai ƴar katifarsa da akwatin kayansa kaɗai ke a cikin ɗakin, shiga ya yi ciki, bayan ya gama tausaya ma kansa, dan ɗakin bashi da banbanci da shago.
Kan katifa ya kwanta yana fuskantar sararin samaniya, zuciya na fara tuno mashi abinda zai haifar mashi da ɓacin rai ya sauko daga kan katifar, alwala ya fita waje ya yi, yana dawowa falo ya shimfiɗa abin sallah, nafiloli masu yawa ya yi, yana gamawa ya ɗaga hannu sama domin kai kukansa a wurin Allah maɗaukakin Sarki.
Farko Rahamar Allah ya fara nema ma mahaifinsu da ya daɗe da rasuwa, Sannan ya roƙa ma Ummansa dacen duniya da lahira a wurin Allah, domin kuwa yi ma Mahaifa addu’a na ɗaya daga cikin sabubban amsa addu’a. Sosai ya kai maƙura wurin addu’ar neman sassaucin damuwarsa da ke hana ruhinsa saƙat, tare da neman farincinkin da zai maye gurbin wannan damuwa, ko da kuwa ta hanyar da bai yi zato ba ne.
Yana gama addu’ar ya shafa tare da naɗe abin sallar, da Bismillah ya haye katifarsa, dan dama a gefenta ya yi sallar, jin babu nauyi a zuciyarsa ne ya ba shi damar ɗaukar wayarsa, kwanciyar ringingine ya yi, kana ya buɗe data, kai tsaye Whatsapp ya shiga, family group ɗinsa ya leƙa ya yi ƴar magana, daga nan ya dawo ɓangaren status yana buɗewa, ba tare da ya ankare ba ya faɗa status ɗin da ya haifar masa ƴar faɗuwar gaba, dan bai yi zaton yana da number ta ba.
Photonta ne ta sanya cikin shigarta ta social usterzher, sosai ta yi kyawu mai cike da ƙayatarwa, samun kansa ya yi cikin furta “Masha Allah”, lokaci ɗaya kuma ya yi capturing photon ba tare da sani ba. Reply ya yi mata da “Kin yi kyau Khadijah”, bai kai ga fita a contact ɗin ba ya ga ta buɗa, kamar wadda ke jiransa.
“Thank u”, ta rubuta mashi a taƙaice, inda shi kuma ya rubuta mata “U r wlcm.”
Bai zato ba ya ga ta ce mashi “Ya jiki, na so in zo gaishe da kai asibiti, amma ban samu dama ba, Allah ya kyauta gaba Amiiiin.”
Bai yi mamakin inda ta san bai da lafiya ba, tunda babbar aminyar Asma’u ce, godiya ya yi mata, daga nan suka taɓa ƴar hira.
Hausawa suka ce “Rana mai raba ma kowa aiki”, ni kuma na ce “Daren ma ba a barshi a baya ba”, dan kuwa shi ma gwanin raba ma zukata aiki ne, tunda a cikinsa ne suke da nutsuwar saƙawa da kwance abin da suke ganin zai kawo masu mafita.
Asma’u na ɗaya daga cikin waɗanda zukatansu basu da hutu a duk daren duniya, dan ta rasa ta ina zata cusa kanta wurin Alhaji Nas, duk hanyar da take gani mai sauƙi ce ta bi, amma bai ma san tana yi ba.
Ta yi maganar a whatsapp, ta yi a wayar, amma a hanza, mafarin ta shiga ruɗanin gaske, dan gani take da gaske aure zai yi, dan wannan katafaren gidan nasa da ta gano ya fi ƙarfin mace ɗaya.
“Ni dai ko wurin Malam zan kai shi a cusa mashi ni a zuciya”, daga zaunen da take kan katifarta ta yi wannan maganar a ƙasan ranta, dan zuciyarta ta gama ƙeƙashewa a kansa.
Rashin samun amsar da zata ba kanta ne ya sa ta komawa ta kwanta, dan ko wurin Malam zata kai Nas, toh bata da kuɗin da za su ishe ta. Wayar ta ce ta kawo hake sakamakon taɓa ta da ta yi, kai tsaye a a gallery ɗin wayarta ta shig tare da zarcewa folder photo grid, hotonta da ta haɗa da na Nas ne ta buɗe tana kallo, sosai haɗin pics ɗin ya yi kyau, “Allah ka tabbatar mani da ranar da zan ga kaina a jikin wannan bawa naka”, ta faɗa a ranta.
Zuciya ce ta ingiza ta da kira shi, har ta yunƙura za ta danna number shi ta ga bai dace ba saboda a dai-dai lokacin kowane mai gida na tare da iyalinsa, “Toh sai me idan yana tare da iyalinsa a yanzu?”, wani sashen na daban ya sake tunzura ta, farincikinta take so, dole ta danna number shi, bugu farko ta yi maza ta datse kiran, saboda tsoron da ya cika mata rai.
Tana cikin maida numfashi sai ga kira Nas ya maido mata, wani irin mamaki ne ya kama ta, har ta kasa ɗaga kiran sai gab da zata tsinke, tsoro ne ya hana ta yin magana, sai dai ta lumshe idanu tana sauraron sallamar sa mai daɗi a ranta.
Bayan ya katse ne ta shiga yi ma kanta faɗan tsoron da ta cusa ma kanta, don da alamu ba zai kai ta ga samun abin da take so ba.
Haka Asma’u ta samu kanta cikin ruɗani da magagin son wanda bai san tana yi ba, kuma sosai abin ya fara bayyana a jikinta.
Ta wani ɓangaren kuma har zawarawa sun fara kunno kai, dan tsaye ta ke da gyara, Aunty kuma na ta addu’ar Allah ya kawo mata miji na gari da wuri ta yi aure, saboda tausayi take bata.
Sai dai duk wanda ya zo, sai ta ce “A’a”, abin kuma yana damun Aunty sosai, wata rana da yamma ta same ta a kitchen ta ce “Asma’u wai me kike nufi ne, duk mazan da ke zuwa wurinki bakya so, ko Abbas ɗin dai?”, dan Aunty ta ɗauka ta fara nadamar Abbas.
Kamar Asma’u zata yi kuka ta ce “Aunty toh duka yaushe auren nawa ya mutu ne, da har zasu fara zuwa, ni makaranta ma zan koma”, Aunty ta ce “Makaranta dai?”, ta ce “Eh”, Aunty ta ce “Toh Allah ya kyauta.”
Jin zafin maganar ne ya sa Asma’u figar hijabi zata bar gidan, tambayarta Aunty ta yi “Sai ina?”, amsa ta bata da “Gidan Halima zan je”, Aunty bata hana ta ba, dan gidan Halimar kamar gidansu ne, mafarin duk faɗin unguwarsu can ne kaɗai Asma’u ke shiga.
Halima na zaune a tsakar gida Asma’u ta shigo, gaisawa suka yi, kana Asma’u ta jawo kujera taya ni gulma ta zauna “Ya dai mutuniyar?”, daga kan rijiyar da Halima ke zaune ta jefo ma Asma’u tambaya, dan ta lura da tsananin damuwar da ta bayyana a fuskar Asma’u.
“Wai Aunty ce ta fara yi mani maganar aure”, kamar Asma’u zata yi kuka ta bata amsa, Halima ta ce “Toh ai ba laifi ta yi ba, tunda zawarawa sun fara zuwa”, Asma’u ta ce “Toh ba sai idan ina son su ba?”, Halima ta ce “Kuma haka ne, Allah dai ya yi zaɓi na gari”, Asma’u ta ce “Amiiiin.”
Shiru suka yi, inda hakan ya ba Asma’u damar lulawa a duniyar tunani, kamar Halima ta karanta saƙon zuciyarta ta ce “Ke fa ba matar yara ba ce”, Asma’u ta ce “Ko?”
Halima na dariya ta bata amsa da “Eh, ina ma ki samu miji kamar Alhaji Nas, da kin huta wallahi.”
Wata irin faɗuwa gaban Asma’u ya yi, dan idan aka ce mata Halima na duba, toh zata yadda, cikin sarƙewar murya ta ce “Uhm, Uhm, wace ni da Alhaji Nas, ai ya fi ƙarfina”, Asma’u ta yi haka ne dan ta ɓoye maitarta ta Alhaji Nas.
Tabbatar mata Halima ta yi Nas bai fi ƙarfinta ba, Asma’u kuwa zancen take so, bayan ƴar gajeruwar jayayya da suka yi, daga bisani ta ce “Toh ta ya ma za’a yi ya san da zamana, bare har batun aure ya shiga.”
Akwai alaƙa tsakanin mijin Halima da Alhaji Nas wadda ita Asma’u bata sani ba, dan haka ta bata tabbacin shi zai iya haɗa su in dai tana so, cewa Asma’u ta yi “Ni dai ba ruwana”, a ƙasan ranta kuma sai godiyar Allah take da ya kawo mata mafita ta hanyar da bata yi zato ba.
Faɗuwa ta zo daidai da zama, kamar yadda Asma’u ke farautar Nas, haka shi ma mijin Halima ke farautar Nas, so yake ya samu hanyar da zai riƙa tatsar kuɗi a wurinsa, kuma tunda ga Asma’u, da ita zai fake.
Washe gari Asm’au na shigowa ya yi mata albishir ɗin zai haɗa ta Nas. A wannan karon kasa ɓoye farincikinta ta yi, tambayarshi ta yi “Ta ina ma za a fara, dan ni ma ina son sa.”
Cewa ya yi “Me kike ci na baka na zuba, ki bani lokaci.”
Halima na daga gefe ta ce “Toh kar mu ci amana fa”, baki Asma’u ta taɓe, dan ta daɗe da gama ɗaukar ma ranta cin amanar Aishar Nas, duk abinda duniya zata faɗa ba damuwarta ba ne.”
Mijin Halima kuwa cewa ya yi “Wannan kuma damuwarku ce ku mata, ni dai yanzu zan fita…”