Kara goge fuska na yi da hijabi gami da shanye idanuna ta yadda Nas zai gan su da annuri idan na yi arba da shi. Sai dai kash! Ban ankare da takun da na ji ba nashi bane sai da babbar 'yarsa mai suna Salma ta bude kofa, Sanye take cikin uniform na islamiyya mai ruwan blue.
Ba don na so ba na sakar mata murmushi lokacin da ta dube ni da girmamawa ta ce "Ashe Aunty Asma'u ce", a takaice na ce "Ni ce kuwa", kasan raina kuma cike da taikaicin faduwa kasa ba nauyin da na yi. . .
Ma sha Allah, muna biye.
Masha Allah