Skip to content
Part 20 of 25 in the Series Cikin Baure by Hadiza Isyaku

Yana rufe baki ya nufi hanyar fita, a ƙule Halima ta bi bayan shi har soro tare da dakatar da shi, murya ƙasa-ƙasa ta shiga roƙon sa akan ya bar maganar Nas inda suka yi ta. 

“Saboda me za a bar ta?”, ya jefo mata tambaya, tare da bin ta da kallon uku saura kwata, dan kuwa fasa maganar daidai yake da rushewar sabon tsarinsa na yin arziki, a marairaice ta ce “Ka ga muna gaisawar mutunci da matarsa, kuma idan ta ji daga nan gidan ne sanadin yi mata kishiya toh zata kalle ni a matsayin wadda ta ci amanarta.”

Ko kusa amsar da ta ba shi bata sa ya karaya ba, sai ma tambayar gatsali da ya sake yi mata, inda ya ce “Toh sai me idan ta kalle ki a haka? Ina ce Alkhairi ne kika haɗa mijinta da shi ba sharri ba.”

“Ni dai koma miye dan girman Allah ka bar wannan maganar, kuma ina Alkhairi acikin yi ma mace kishiya.?” Mijin Halima, ko kuma Sani a taƙaice, mutum ne mai tsayuwa a kan ra’ayinsa ko da zai cutar da wani, sai da ya nuna sama da yatsansa manuni kana ya ce “Ni kuma na rantse ba zan bar wannan maganar ba, ga hanyar da na cefanenmu za su ƙaru, shi ne zaki yi mana Katsinanci.?”

Kamar zata haɗiyi zuciya ta riƙa kallon shi, lokaci ɗaya kuma cikin raunin murya ta ce “Ni wallahi dama ban kawo maganar nan ba”, dariya ya ɓaɓɓake da ita kafin ya ce “Bakinki ya ja maki ai, kuma ko baki yi maganar ba, ni da kaina na yi niyyar haɗa shi da ita”, yana rufe baki ya raɓa ta gefenta ya fice daga gidan yana dariya. 

Cikin gidan ta koma, inda ta samu Asma’u jingine da bangon ɗakinta. Gaban Asma’u ta tsaya, kana ta barranta kanta daga wannan cin amanar da suke shirin yi ta hanyar faɗin “Asma’u ba zan hana faruwar abin da Allah ya hukunta ba, amma ki sani babu hannuna a ciki.”

Ko Halima ba ta faɗa ba, to fuskarta ta bayyana ma Asma’u komai tun a jiya da suka fara maganar, kuma har zuciya da bata da ƙashi ta ruwaita mata Halima na mata baƙinciki ne kawai, shi ya sa ta fake da bata son cin amanar Aishar Nas. 

Wayancewa Asma’u ta yi tare da nuna mata ta kwantar da hankalinta, dan ba lallai ne Nas ɗin ma ya karɓi tayin aurenta ba, idan kuma har ya karɓa, toh ba ta inda zargi zai faɗa kan Halimar.   

Sosai tsoro ya ƙara mamaye Halima, dan bata yi zaton Asma’u zata ƙi karɓar uzurinta ba, ƙwafa ta yi kafin ta ce “Hmm! Toh shikenan, in dai ta bi daga-daga”, Asma’u na dariya ta ƙarasa mata da “Na ƙurya ka sha kashi.”

Kukan Sadiq ne ya ja hankalin Halima zuwa cikin ɗaki, wanda shi ne ƙaramin ɗan da take goyo, ciki ta shige ba tare da ta sake tanka ma Asma’u ba. 

Baki Asma’u ta taɓe, a ranta ta ce “Ƴar baƙinciki”, lokaci ɗaya kuma ta ɗage labulen ɗakin ta ce “Na wuce”, Halima da ke saɓe da Sadiq tana shirin fitowa ta ce “A sauka lafiya.”

Ƙarasa fitowa ta yi daga ɗakin, zuciyarta cike da zargin kanta ta sanya Sadiq ya yi fitsari haɗi da wanke mashi baki, cikin ɗakin ta koma gami da zaunawa jagwab gefen gado, Mama ta fiddo ta ba shi, duk dan ya barta ta yi saƙar zucinta cikin daɗin rai. 

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, lokaci ɗaya kuma a fili ta ce “Na rantse ba za a yi wannan ɗanyen aikin a gidannan ba”, saboda yadda mijinta ya haƙiƙance a kan Asma’u ta auri Nas, toh shi ma idan ya samu wannan damar ko wace ɗiya ce zai iya auro mata a matsayin kishiya, ita kuma yadda ta tsani mutuwarta, haka ta tsani kishiya. 

Hanyoyin hana maganar tasirantuwa ta shiga bi, sai ta ga dukkanin su ba masu ɓillewa ba ne, daga wadda zata haddasa fitina a cikin unguwa, sai wadda za a zarge ta a matsayin ƴar baƙinciki, wani sashe na zuciyar ta ne ya yi ƙarfin halin tambayar ta “Toh da kuma a yi maki kallon ƴar cin amana fa?”, da ƙarfi ta cije leɓenta tare da faɗin “Taɓ! Na rantse duk abin da zai faru, ya faru! Amma sai na ɓata maganar nan, ko da zan rasa komai nawa”, domin kuwa kilbibin ƴan unguwarsu kaɗai ba zai bari itama ta zauna lafiya a gidanta ba. 

Kamar yadda Halima ta ɗaukar ma ranta hana maganar yin tsayi, itama Asma’u ta ɗaukar ma ranta ko ta wane hali sai ta auri Nas, dan ta fahimci da gaske Halima take wurin son kawo mata tasgaro. 

Tunda ta koma gida take godiyar Allah da ya sanya Sani ya tsaya mata, dan haka itama ta wani ɓangaren dole ta taya kanta yaƙi.

Toh ta ya ma zata taya kanta yaƙin? Saboda tunda ta shiga gidan Nas, matarsa ta murtuke mata fuska, ta ɗaukar ma ranta ita da sake zuwa gidan, sai an kai ma Nas ita a matsayin amarya. 

Kitchen ta faɗa ta fara haramar girki, don idan tana aiki ne zata samu damar yin tunanin Nas da kyau, ta yadda Aunty ba zata gane mata ba. 

Tana gamawa ta yi wanka da sallah, anan ta roƙi Allah da ya sa ta mallaki Nas ko ta wane hali, ba tare da ta roƙi Allah zaɓi ba, domin shi kaɗai ne ya san abin da yake Alkhairi ko akasin Alkhairin ga bayinsa. 

La’asar na yi ta shiga haramar yin ta, gamawarta ke da wuya kuma ta fice akan sa’a, domin Nas ne ta hango ya nufo motarsa, duk da akwai ƴar tazara a tsakininsu, amma hakan bai hana ta ganin kyawunsa ba, sosai shauƙin son sa ya makantar da ita ganin matarsa Aisha da ke tafe a bayansa. 

A hankali ta lumshe idanu tare da kwantar da kanta jikin bangon ƙofar gidansu, “Allah kada ka hana ni Nas”, ta faɗa cikin murya mai cike da shauƙi. 

Buɗe idanun kuwa sun yi daidai da bugawar zuciyarta da ƙarfi, dan kuwa a cikin na Aishar Nas ta dire ganinta, sosai ƙayatuwar Aishar Nas ɗin ta girgiza ta, kasantuwarta macen da ta iya ɗaukar wanka.  

 “Mayya! duk bala’inki sai na auri mijinki, kuma sai na fi ki fantamawa a gidansa”, cike da tsanar Aishar ta furta haka, lokaci ɗaya kuma ta bi bayan motarsu da idanu, dan har sun nufi inda suka dosa. 

Wani matashi mai suna Usman ne ya katse mata hanzari da faɗin “Ya dai, ko kin ƙyasa mijin wata ne?”, hararar shi ta yi “Usman bana son shisshigi”, kasantuwar suna wasa da juna. 

“Ba shisshigi ba ne”, ta ce “Toh me ye?”, ya ce “Meye fa, ni gani na yi ma kun dace da juna”, ta ji daɗin maganar, amma sai ta yi mashi hararar wasa, dariya kaɗai ya yi, saboda ya fahimci abin da ke ranta, kuma a kan idonsa ta riƙa yi ma Nas kallon ƙurilla. 

Ta ɓangaren Sani kuwa, bai samu damar kiran Nas ba sai da yamma liƙis, Nas ɗin ne ya faɗa mashi su haɗu a sabon gidan da yake gini, da sauri kuwa ya rufe shagonsa na sayar da provision.  

A chaɓa ya hau, cikin ɗan ƙanƙanen lokaci suka isa unguwar, ko da shigarsa center gidan sai wani kalar baƙin ciki ya taso mashi, don kallo ɗaya kaɗai mutum zai yi ma manyan gidajen da center ya tabbatar da mazauna cikinta manyan attajirai ne.  

Sosai ya danne jin zafinsa lokacin da mai acaɓar ya aje sa a bakin gate ɗin gidan Nas, kuɗinsa ya biya shi kana ya shiga. 

 Tsaye ya samu Nas da leburorin dake aikin gidan a ƙarƙashin wata ƴar rumfa suna magana. 

Hassada mugun ciwo!, Shi causin brother ɗin Nas ne, da mamanshi, da baban Nas suke uba ɗaya, kuma tazarar arziki Nas da ya yi masu ce ya sa yake jin haushi, kasantuwar duk a family ɗin babu wanda ya kai shi dukiya. 

Hakan ya sa Sani lasar takobin sai ya kwashi kasonsa mai yawa na arziki a wurinsa, duk da kyautatar da Nas ɗin ke ma danginsa daidai gwargwado, mafarin maganar Asma’u na zuwa ya ji shi tsaf.!  

Katafaren ginin benen ya kalla, lokaci ɗaya kuma bakin sa na faɗin “Ya Hajj, wannan gida ya ƙeru dai”, Nas na dariya ya ce “Ko?”, har a lokacin idanun Sani na kan ginin ya ce “Sosai wlh”, Nas ya ce “Ai ya samu ƙwararrun magina ne”, Sani ya ce “Lallai dai kam.”

 Gaisawa suka yi, sannan Nas ya ƙarasa maganar da zai yi da ma’aikatan su biyar, wadda duk ta kuɗi ce, take kuma ya je mota ya ba su kudaɗen cash suka tafi. 

Waɗannan kuɗaɗe sun daki zuciyar Sani, bai yi magana ba sai bayan da suka fara zagaya gidan yana ganin yadda tsarinsa yake. Cewa ya yi “Wannan gida dai ya ci kuɗi Ya Hajj”, Sai da Nas ya jinjina kai sannan ya ce “Kai dai bari Sani, gini ba wasa ba, yanzu haka a jeren blocks ɗinnnan kaɗai sai da na zuba milliyoyin kuɗaɗe”. 

Ido Sani ya zaro “Milliyoyi fa?”, Nas ya ce “Na rantse kuwa”, shiru Sani ya yi, a ranshi yana hasashen wace irin dukiya ce Nas ya mallaka haka?. 

Nas ɗin ne ya katse mashi tunani da faɗin “A ƙalla gidannan da na yi lissafi zai ci fiye da million Hamsin Sani”, a daburce ya ce “Na yarda! Ai na yarda, gini ya wuce tunanin mai tunani ai Ya Hajj.” 

Cigaba da zagaya gidan suka yi daga ƙasan benen har zuwa sama, Nas kuma yana nuna mashi tsarin ɗakunan, inda ya nuna mashi part ɗinshi, da na Aisha, da kuma na yara. Sai da suka je wani extra ɗaki ne Nas ya ce “Wannan ɗakin kuma…, da sauri Sani ya tarbi numfashinsa da faɗin “Na Amarya ne”, da mamaki Nas ya kalle shi “Haba Amarya dai?”, Sani ya ce “Amarya mana, ai wannan gidan ya fi ƙarfin mace ɗaya”, Nas ya ce “A ganinka ba”, Sani na dariya ya ce “A ganin kowa ma, babban mutum kamarka bai kamata a ce matarshi ɗaya ba.” 

Dariya maganar ta ba Nas, dan babu tsarin ƙarin aure a tare da shi. Shi kuwa Sani sai nanata maganar Amarya yake, har ta kai ga Nas ya ce “Toh idan ma auren ne ni ina zan samu mata?”, Zumbur Sani ya yi “Ni zan samo maka”, cike da gatse Nas ya ce “Na wakilta ka.”

Daɗi kamar ya kashe sani, yana cikin saƙawa da kwancewa ne wayar Nas ta yi ruri, duk da ba handsfree take ba, amma ya ji me aka ce a cikin wayar, ɗan ƙara duba gidan suka yi, sannan suka fito, mota ɗaya suka shiga, suka kama hanya. 

Unguwarsu Aisha suka biya suka ɗauke ta, a hanya ne Sani ya ke tsokanarta “Na ga gidanku ke da amarya ai”, Daga can baya Aisha ta ce “Amarya kuma?”, ƙin bata amsa ya yi, sai ma suka cigaba da magana shi da Nas. 

Cike da tsabar son abin duniya ya ce ma Nas “Alhaji ka ƙi ka ƙara mani jari”, Nas da idan bai ga damar bada kuɗinsa ba bai badawa ya ce “Duk naka fa, Allah kuwa Sani baka da godiya.”

Dariya su duka suka yi, ɗan waigowa ya yi ya ce ma Aisha “Madam ki sa baki a bani jari, idan kin ƙiya kuma amarya ta sa.”

Gaban Aisha na dukan uku-uku ta ce “Ai ka sanya amaryar dai ta sa a baka.”

Nas na da tsananin kishi, tufka ya yi ma maganar, inda ta dawo tsakanin su har suka isa unguwarsu. 

Aishar Nas kuwa maganar Amarya da Sani ke ta maimaitawa ta hana zuciyarta saƙat, Sai da ta bari Nas ya dawo da daddare, kuma ya kimtsa sannan ta same shi a ɗakinsa. 

A ɗarare ta zauna gefen gadonsa da yake kwance, tsawon mintuna ba wanda ya tanka ma wani, sai can ta yi ƙarfin halin fara yi mashi maganar gini, bayan ya bata amsa cikin sakewa ne ta ce, “Uhmm! Wai ni aure zaka yi ne?”, tambaya ya maido mata da “Inji wa?”, ta ce “Sani mana, ba na ji ɗazu yana maganar ba”, a inda suka yi magana da Sani, a nan ya barta, cewa ya yi “Rabu da shi dan Allah, shirmensa ne kawai”, shiru Aisha ta yi, sanin waye mijinta kuma ya sa ta ɗan ji sanyi a ranta. Ƴar hira suka taɓa, sannan ta koma ɗakinta cikin yara ta kwanta. 

Sani kuwa sai da aka yi kwanaki sannan ya kira Nas a waya, a lokacin kuma yana gida, daga cikin wayar yake faɗa ma Nas cewar “Na samo maka yarinyar fa”, da mamaki Nas ya ce “Wace yarinya kuma?”, Sani ya ce “Wadda ka sanya na samo maka mana, yau ma zan je gidansu in yi magana da mahaifanta.” 

Shigowar Aisha a ɗakin ta yi daidai da lokacin da Nas ya ce “Ban ce kaje gidansu wata yarinya ba Sani”, take hantar cikinta ta kaɗa, gefenshi ta zauna akan kujera, sai da ya gama wayar ta tambaye shi “Wa ce yarinya ce kuma?”, cewa ya yi “Ina na sani”, cewa ta yi “Ka sani mana, tunda ga shi har ana cewa za a je gidansu.” ƙwafa kawai ya yi, dan bai zaton haka daga wurin Sani ba, hakan ne ya ba Aisha damar cigaba da faɗin “Na fahimci dai so ake a tura ka ka ƙara aure.” 

Cike da gadara ya shiga nuna mata ba wanda ya isa ya sanya shi ya ƙara aure, kawai idan yaga dama ne zai yi, idan kuma bai ga dama ba, ba wanda zai sanya shi, bar mashi ɗakin Aisha ta yi, saboda bata son maganar ta kai su ga faɗa. 

Shima ficewa ya yi daga gidan, inda suka yi mahaɗa da Sani a bakin titi, cike da mamaki ya dubi Sani da duk suke jingine da motarsa ya ce “Haba Sani, ya za ka yi mani haka, daga gatse sai kawai magana ta zama gaske.”

Cike da son ɗaura Nas a keken ɓera ya ce “Dan Allah kada ka bamu kunya mana, na faɗa akwanaki, kuma a yanzu ma zan maimaita cewar, mutum kamarka bai kamata ya zauna da mace ɗaya ba”, sosai Sani ya nuna mashi babu wani aibu dan ya ƙara aure, hakan ma zai ƙara ɗaukaka darajarshi ta ɗa namiji ne. 

Da Nas ya nuna mashi rikicin mata ne baya so, sai shi ma ya nuna mashi ba wani rikici in dai namiji ya kasance adali a cikin iyalansa. A taƙaice dai sai da Sani ya cusa ma Nas son ƙara aure, har ta kai ga Nas ɗin ya ce “Toh wai yarinyar da kake magana ƴar ina ce?”, zuciyar Sani fal da farinciki ya ce “Ƴar nan unguwarmu ce, ko in ce maƙwabtanka ne?”, ɗan yamutse fuska Nas ya yi “Maƙwabtanmu kuma?”, dan bai tunanin akwai yarinyar da zai iya aure a kaf unguwar. 

“Eh, wata ƴar farar yarinya nan, ta taɓa aure, amma bata daɗe ba suka rabu”, Nas na jin ya ce ta taɓa aure ya ce “Kayya! Sani kada ka haɗa ni da masifa ina zamana lafiya.” 

Idan Sani maye ne, toh muddin ya kama kurwar mutum sai ya kashe shi, da salo da dubaru ya shiga yi ma Nas kwatancen Asma’u, tare da cusa mashi ita da tsiya, daga ƙarshe ba dan Nas ya so ba ya ce “Shin! Ya sunanta ma?”, Sani ya ce ” Asma’u”, ɗan shiru na wucin gadi Nas ya yi, kafin daga bisani ya ce “Toh! Ka je gidansu Asma’u..”

<< Cikin Baure 19Cikin Baure 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×