Skip to content
Part 21 of 25 in the Series Cikin Baure by Hadiza Isyaku

Ko kusa baki ba zai iya misalta irin farincikin da Sani ya samu kansa a wannan lokaci ba, bakinsa har kunne ya ce “Haba ko kai fa, tuni ya kamata a ce ka wuce wurin, amma sai ƙeƙƙega kake kamar wanda ya ke tsoron matarsa.”

Dariyar da iyakar ta kumci Nas ya yi, saboda ya ji zafin maganar Sani ta ƙarshe, kasantuwar sa mutumim da ya tsani a jefe shi da duk wata siffa ta gazawa, yanayin da yake ciki ne ya hana shi bayyana fushinsa, sai dai ya ce “Ba zaka gane bane Sani, na faɗa maka hayaniyar mata ce bana so, amma ba wai tsoron matata ba.”

“Insha Allahu ba wata hayaniya”, Sani ya faɗa duk dan ya ƙara cusa mashi nutsuwa, Nas ya ce “Toh Allah ya sa”, Sani ce “Amiin.”

Hanzari Nas ya kawo ma Sani, cewar ya fi son a yi komai a sirrance, idan ya so bayan magana ta tabbata sai a bayyana, idan kuma bata tabbata ba shikenan ba wanda ya ji. 

 Har ila yau kuma ba zai auri Asma’u ba har sai ya kammala gidansa, saboda tamkar bisa ƙaya yake a inda yake ciki. 

Duk wani hanzari da Nas ya kawo sai da Sani ya karɓe shi tunda dai bukatarshi ta kusa biya. Hotunan Asma’u masu kyau ya ƙara nuna ma Nas, daga bisani suka ƙara ƴan maganganu. Bayan sun fahimci juna sosai ne Nas ya shiga motarsa ya nufi cikin gari. Sani kuma ba inda ya yi tsinke sai gidansa, Halima na shigowa ɗaki kawo mashi abinci ta ce “Halan ta samu?”, dan fuskarsa bayyane take da labarin da ke cike da zuciyarsa “Tukunna dai”, ya bata amsa a taƙaice, abin da ke ta yi mata kai kawo a rai ne ta tambaye shi “Toh ya batun Alhaji Nas da Asma’u?”, cewa ya yi “Sai abin da hali ya yi”, ya zaɓi yi mata magana mai harshen damo ne duk dan ta bar shi ya yi shirinsa a natse. 

Ita kuwa ta ɗauka babu maganar, dan a hausance idan aka ce “Sai abin da hali ya yi”, toh da yawa zasu yi zaton akwai rauni cikin abin da ake son cimmawa ba, cike da jin daɗi a ranta ta ce “Toh Allah ya kyauta”, ya ce “Amiin dai.”

Abincin da ta kawo mashi ya ci ya ƙoshi, yana gamawa ya fice daga gidan, kai tsaye shagonsa ya nufa, ko da buɗewa sai ya shiga ƙare ma ƴan tsirarun kayan da ke cikinsa kallo, a fili ya ce “Insha Allahu ka kusa cika shagona, da sannu sai na fi Malam Mammada customers”, dan kuwa shagon ba wasu kayan a zo a gani ne cikinsa ba, kusan kaso goma na abin da jama’a ke zuwa siye, bai wuce a samu uku ba, shi ya sa sai ta ƙwaƙe mutane ke zuwa wurinsa siyayya. Shagon maƙwabcinsa Malam Mammada kuwa kullum cike yake da jama’a, mafarin hassada ke ta tilasta mashi a kan ya cika shagonsa shi ma ko ta wane hali. 

Sai da ya gama karance ma shagonsa wasiƙar jakin tas ne ya jawo ƴar kujerar katakon dake girke a tsakaiyar shagon, cike da zaƙuwa ya fiddo wayarsa dake gaban aljihu, Key ɗin ya cire, kai tsaye kuma sai dieler domin isar da albishir. 

Asma’u na zaune ɗakin Aunty kan kujera tana kallon film ɗin Jalebi kiran Sani shigo wayarta, ras! Gabanta ya faɗi, saboda saƙon ba zai wuce albishir ko gargarɗi ba. 

“Allah ka sa in ji Alkhairi”, ta faɗa a ranta, lokaci ɗaya kuma ta ɗaga kiran tare kai wayar a kunne. Duk wanda ya ji yadda ta amsa sallamar sai ya fahimci ba a natse take ba, musamman lokacin da ta lumshe idanu tana tsimayen me Sani zai faɗa. 

Daga can cikin wayar ya ce “Toh ki zuba ruwa ƙasa ki sha Madam, dan kuwa Nas ya amince zai aure ki.”

Kamar wadda aka tsikara ta miƙe, faɗuwar da gabanta ya sake yi ta nunka ta lokacin da kiran Sani ya shigo wayarta, cikin sarƙewar murya ta ce “Da gaske!”, lokaci ɗaya kuma hannunta dafe da ƙirji, cewa ya yi “Na rantse kuwa, bamu daɗe da rabuwa da shi ba ma.”

Kasa magana Asma’u ta yi, sai dai ta lumshe idanu, dan jin abin take kamar mafarki, daga cikin wayar Sani ya cigaba da cewa “Kin san me nake so da ke??”, kai ta girgiza kamar yana ganin ta, a can ƙasan maƙoshi kuma ta ce “A’a”, ya ce “Ki yi gum da bakinki, da kaina zan zo gidanku da maganar, dan ya fi son a fara magana da mahaifanki, kuma a sirrance.”

“Ok, na ji, na kuma gode”, kaɗai ta iya faɗa, dan duk wata lakka ta jikinta ta saki, ta kasa gazgata maganar Sani, saboda duk tsananin son da take ma Nas, bata taɓa zaton abin zai zo da sauƙi haka ba, ko da yake addu’a babu abin da bata sanya shi ya yi sauƙi. 

Bayan sun gama wayar ne ta koma kan kujerar jagwab da zama, murna da tausayin kanta ne suka haɗe mata, a can ƙarƙashin ranta kuma wata fargaba ce da ta kasa lura da ita. 

 Ƴar dariya da Kukan ba zato ne suka suɓuce mata, domin ta sha wahala a cikin son Nas, kasantuwar bata yi zaton zata same shi da sauƙi haka ba, lta kanta tana kallon mafarkanta kamar ba za su zama gaskiya ba, “Tsarki ya tabbata ga Allah Gagara Misali, a gareka dukkan godiya take Ya Mahaliccina, na gode sosai da cika mani burina da ka yi”, a fili ta yi wannan godiyar ga Allah, saboda ita kaɗai ce a gidan, lokaci ɗaya kuma ta goge siraran hawayen da suka malalo mata a kumci. 

A cikin wannan yanayin ne kuma ta shiga gallery ɗin wayarta, hoton Nas da ya fi yi mata kyau ne ta ƙura ma idanu, a zuci ta ce “Yanzu wannan haɗaɗɗen ne zai zama mijina”, wani shauƙi ne ya ɗebe ta, bata san lokacin da ta yi ta sumbatar hoton ba, ba don ta gaji da kallonsa ba ta sanya wayar sleep, zamewa ta yi kan kujerar ta kwanta, a gabanta ta aje wayar tamkar jariri sabon haihuwa. 

Rufe idanu ta yi kamar mai bacci, hakan ne ya bata damar lulawa duniyar yadda zata ji da Nas tun daga ranar da zasu fara haɗuwa, a ranta ta ce “Insha Allahu sai na baka kulawar da baka taɓa samun irinta ba my Nas.”

Hango kanta a sabon gidan da zai kaita ne ya tuna mata da Abbas, tunda da blocks ɗin companin su ne ake gina gidan “Wai ko yana ina ma?”, ta tambayi kanta, domin rabonta da shi anfi wata bakwai. 

Amsar tambayar Asma’u ita ce! Abbas na can yana rayuwarshi cikin magagin son Khadijah da ya kamu da shi ba tare da ya ankara ba. Tun da suka fara chat da ita ɗabi’unta suke birge shi, babban burinsa bai wuce su ƙulla alaƙar da zata kai su ga aure ba, duk da ita ɗin Aminiyar tsohuwar matarsa Asma’u ce. 

Babbar damuwarsa kuma ita ce ya kasa faɗa mata, saboda gani yake ba zata karɓe shi ba. Abdull ya tunkara da maganar lokacin suna wurin aikin block ɗinsu, ce masa ya yi “Abdull na samu yarinyar da nake so fa, amma tsoro ya hana ni bayyana mata”, wani irin kallo Abdull ya yi mashi tare da gyara zama akan bencin da suke zaune “Kamar ya tsoro?”, duba da ba wannan ne karon farko da Abbas ya ga mace yana so ba. 

“Khadija ce ƙawar Asma’u, bana son ace na ci amana”, dariya sosai maganar ta ba Abdull “Au har wata amana Asma’u ke da ita, wadda kake gudun ci, toh in dai ka yaba da halin Khadijar, kawai ka aure ta, muddin itama tana son ka.” Sosai ya ba Abbas shawarar kada ya ji tsoron komai wurin neman farincikinsa, mai yiwuwa Allah ya sa ta zama silar sharewar hawayenshi. 

Sosai maganganun Abdull suka tsuma Abbas, wayarsa ya fiddo gaban aljihu ya danna ma Khadija kira, sai da ta kusa tsinkewa ne ta ɗaga, shiru ne ya biyo bayan gaisawa da junan da suka yi, Abbas da ke a tsorace ne ya yi ƙarfin halin faɗin “Khadija, kina ji na?”, daga can ta ce “Eh, ina jinka”, idanunsa na kallon Abdull da ke ta yi mashi dariya ya ce “Uhmm, so nake ki ba ni iznin zuwa gidanku”, cike da mamaki ta ce “Gidanmu kuma?”, Abbas ya ce “Ƙwarai”, ɗan shiru ta yi, alamun tana nazari, daga bisani ta ce “Ok, toh Friday ne kaɗai nake da ishasshen time, idan ya yi maka sai ka zo”, Abbas ya ji daɗin yadda ta ba shi izini ba tare da jayayya ba, godiya ya yi mata, kana suka ɗan taɓa ƴar maganar karatun da take. 

Bayan sun gama wayar ne Abdull ya ce mashi “Ko da jin ta dai wayayyiya ce” Abbas da ke jin kamar shi aka yaba ya ce “Gaskiya kam ba laifi, dan ta fi Asma’u komai a rayuwa”, haɓa Abdull ya riƙe tare da faɗin “Inyeee! Yau Abbas ne ke faɗin wata ta fi Asma’u”, dariya sosai Abbas ya yi, dan shi kanshi bai san sadda maganar ta fito bakinsa ba. 

Rana bata ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, ya kama yau Friday, ranar da Abbas ya ƙudiri fallasa ma Khadija sirrin ziciyarsa na son aurenta. Da misalin huɗu da rabi na yamma ne ya hau sabon mashin ɗinsa Haijou ya nufi unguwarsu Khadija. Shotcut ya bi, dan baya son bi ta gaban gidansu Asma’u bare har ya haɗu da wani ɗan gidansu. 

Da isarsa ƙofar gidan ya faka mashinɗinsa gefe, ba tare da ya matsa daga wurin ba ya kira Khadija tare da shaida mata zuwansa, ba a jima ba kuwa sai gata ta fito cikin shigarta ta doguwar rigar material, sai ɗankwalin da ta yi rolling a kanta. 

Faɗuwar gaba ce ta riske su, sakamakon kyawu da suka yi ma juna, “Sannu da zuwa” Khadija ta faɗa lokacin da ta ƙaraso gaban Abbas, idanunsa a kan choculate colour ɗin fuskarta ya ce “Yauwa Deejah, na same ku lafiya”, a kunyace ta ce “Lafiya lau.”

Iso ta yi mashi har cikin gidansu, dan a ƙa’idar gidansu basa tsayawa da maza a waje, a falon mamansu da ya ƙayatu da kayan alatu ta kai shi. Tarba mai kyau ya samu a wurin mutanen gidan, dan kuwa sun nuna mashi su cikakkun masu kara da karamci ne. 

Bayan ya kasance daga shi, sai ita, sai kuma ƴar ƙaramar ƙanwarta mai suna Farha ne ya nemi ta ba shi dukkan nutsuwarta yana son su yi magana. 

Kanta na ƙasa ta ce “Ina jinka”, ɗan jim Abbas ya yi, saboda nauyin da bakinsa ya yi, shi ma kansa na ƙasan ya ce “Aam! Dama dai..”, sai kuma ya yi shiru, a yadda ya cije ne ya kusa sa Khadija dariya, dan ta gama gane a tsorace yake. 

“Aam! Dama ta yi ne na kawo maki na soyayya Khadija, idan ba damuwa ina roƙon ki da ki karɓa, domin mu haɗu ni da ke mu gina nagartaccen ahali, kasantuwar na daɗe da yaba kyawawan halayenki, har nake ji dama da ke na fara haɗuwa.” 

Tunda Abbas ya fara magana har ya kai ƙarshe Khadija ta ɗago kai tana kallonsa, wani irin kallon mamaki ta riƙa yi mashi, lokaci ɗaya kuma jikinta na ta ɓari. Ta daɗe da fahimtar Abbas na son ta, amma bata yi tsammanin zai iya tunkarar ta kai tsaye da batun aure ba, duba da kusancinta da tsohuwar matarsa. Sarƙewar idanuwansu ne ta sa ta kallon gefe, haƙiƙa Abbas yana da zubi da tsarin da mata zasu so shi, toh amma ya zata yi da Asma’u? Shin duniya ma ta kalle ta a matsayin wa??? 

Cikin yanayin rasa yadda zata yi ta lumshe idanu, a ranta ta ce “Allah ga ni gare ka, ka fitar da ni wannan tsomomuwar ba dan halina ya Allah.”

Abbas ma cikin ruɗanin yake, tsoro yake kada ta ƙi amincewa da shi, cikin raunin murya ya ce “Kin yi shiru Deejah”, bai zato ba ya ga ta ɗago ta dube shi, cewa ta yi “Al’amarin ne azimun, na ɗauka gaisuwa ce kaɗai a tsakaninmu, ashe ta ɓangarenka abin ya zarce haka”, cike da ƙarfin hali ta ƙarashe maganar, saboda bata son ya fahimci tsabar kiɗimar da ta baibaye ta. 

Cewa Abbas ya yi “Ni ma kwatsam na ji ina son ki, amma idan hakan laifi ne ki gafarce ni dan Allah, laifin duk na zuciyata ne da ta kamu da sonki.”

Maganganu masu kama da kare kai Abbas ya shiga zayyano mata, dan kuwa ta bullo mashi da batun Asma’u, nuna mata ya yi wannan duk ba wani abu bane, tunda Asma’un da kanta ta guje shi, dan haka babu dalilin da za ta ce an ci amanarta. 

Ba dan Khadija ta gamsu ba ta ce “Toh shikenan, ka bani time zan yi nazari”, cikin girmamawa Abbas ya ce “Na baki ranki ya daɗe”, murmushi kaɗai ta yi, ta gefen idonta kuma tana ta satar kallonshi, shi kuwa bai lura ba saboda ya shagala da yi ma Farha da ke gefensa wasa. Sai can ya ɗago ya ce “Madam, tafiya zan yi”, cewa ta yi “Toh.! 

Hannu ya zura aljihu ya zaro kuɗi ya ba Farha “Karɓi ku sha sweet ke da Aunty Khadija”, Khadija zata yi magana ya ce “Shhh!”, alamun baya son jin komai a bakinta, shiru ta yi tana hararar Farha da ta ce “Na gode Yaya”, dariya Abbas ya yi “Ba komai ƙanwata”, hannunta ya kama suka fito, bankwana ya yi da Maman Khadija da kuma ƙannenta, sannan ya fita, har waje Khadija ta raka shi, yadda take ta noƙe kai ne ya tabbatar mashi akwai son shi ko da kaɗan ne a ƙasan ranta. 

Cikin sigar lallashi ya ce mata “Dan Allah, ki yi nazari mai kyau Khadija, ki sama mana mafitar da zata haifar mana da farinciki kin ji”, kai ta ɗaga kafin ta ce “Insha Allah.” bankwana suka yi, sannan ya burka mashinɗinsa ya tafi.  

 Daddare wurin ƙarfe tara ne ya same ta online, ya so yi mata magana, amma sai ya danne, saboda baya son cika mata ciki. Bai zato ba sai ga saƙonta ya shigo “Fatan ka koma gida lafiya”, farinciki fal da ransa ya ce “Lafiya lau Deejah! Kin yi nazarin?”, a taƙaice ta rubuto mashi “A’a”, Reply ya yi mata da “Dan Allah toh ki yi, wlh a matse nake, aure kawai nake so.” daga ƙarshen maganar ya sanya haha emoji. 

Sticker wata mata mai riƙe da haɓa ta turo mashi, lokaci ɗaya kuma ta rubuta “Insha Allah.” reacting sticker da maganar ta ya yi, sannan ya fito yana duba status yana dariya. 

Status ɗin Asma’u ne ya yi masa shigar burtu ba tare da ya sani ba, dan ya dena buɗa status ɗinta sai a kan tsautsayi. 

Da ace ajalin Abbas a kusa yake, toh da abin da status ɗin ya ƙumsa ya kashe shi har lahira. Photonta da na wani mutum ne ta haɗa, sai dai ta rufe fuskar mutumin da logon heart ta yadda ba mai iy a gane shi, a ƙasa kuma ta rubuta “Amaryar New year Insha Allah…” 

<< Cikin Baure 20Cikin Baure 22 >>

1 thought on “Cikin Baure 21”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×