“Aure Asma’u zata yi?” cikin tsananin tashin hankali ya jefo ma kansa tambayar da ba mai amsa mashi ita. Take duk wata tsika ta jikinsa tashi, wani irin sanyi ne ya shiga ratsa shi har ya tsinke da karkarwa, kan ka ce me haƙoransa sun fara gugar juna, kamar wanda aka watsa ma kwanannen ruwa da asubahin lokacin hunturu.
Wayar kuwa bai san lokacin da ta ɓille kan katifa ba, lokaci ɗaya kuma tana ta ratsa status ɗin mutane ba tare da saninsa ba. A hankali ya lumshe idanunsa da suka ciko da ƙwalla, hannayensa rungume da ƙirji ya cigaba da karanto “Inna li Llahi wa inna ilaihi raji’un”, dan kuwa ji yake kamar zuciyar zata fito saboda azababben kishi.
Abbas na son Asma’u, son da shi kansa ya sadaƙas babu macen da zai iya yi ma irinsa, sai dai ta mashi nisan da ba zai iya bin bayanta ba, ko da bin zai kai shi ga nasarar cimma ta. A wannan lokaci kuma da zaka tambayi Abbas kwatankwacin yalwar duniya, toh zai amsa maka da a ƙuntace take, har babu inda mai rai zai raɓa ya ji daɗi, hakan ne ya sa shi jinginewa jikin bango tare da haɗe kai da guiwa, kuka ya yi ta rizga son ranshi, dan ya ɗaukar ma ransa in dai a kan Asma’u ne ba zai yi ma idanunsa ƙwabron zubda hawaye ba.
Sai da ya gama kukan ne ya lalubi wayarshi da ta fara zafi, alwala ya fita waje ya yi, yana dawowa ɗakin ya gabatar sallah tare da neman agajin Ubangiji, dan kuwa masifar Asma’u ta ishe shi, neman maraba kawai yake da ita, ba shi kuma ya kwanta ba sai ɗaya saura, wani irin wahalallen bacci ne ya tafi da shi, a cikin baccin kuma ya dasa da mafarkai marasa kan gado.
Washegari da Asubar fari ya hau WhatsApp, mute na status ɗin Asma’u ya yi, dan shi kaɗai ya san a zabar da ya sha bayan ya falka cikin dare. Chat ɗinsa da Khadija kuwa bai sake bi ta kansa ba, asali ma yanzun ba ita ke a gabanshi ba, burinsa kuma shi ne ya ji waye Asma’u zata aura.
Sai da gari ya yi haske sosai ne ya shirin fita aiki, gidansu ya shiga domin gaishe da mahaifiyarsa, a tsakar gida ya samu Ummansa tana gyaran cefane, plastic chair ya jawo ya zauna a gabanta, cikin dakushewar murya ya ce “Umma duk sanyin nan amma ku kuna tsakar gida.”
Cike da kulawa ta ce mashi “Toh Abbas ina na ga hutu, gashi yara sun koma makaranta”,
Idanunsa na kan kabewar da take sarawa ya ce “Kuma haka ne.”
Gaisawa suka yi, a nan Ummansu ta tambaye shi “Hala ma mura kake?”, ya ce “Wallahi wata irin mura ma Ummah”, ta ce “Toh ai sana’ar taku ce sai da taɓa ruwa, kawai dai sai an daure, tunda halak ake nema”, fatan nasara ta yi mashi, ya ce “Amiiiin”, shiru na wucin gadi ya yi, daga bisani ya bayyana mata abin da ke ta nuƙurƙusar mashi rai, cikin sigar tausayin kansa ya ce “Wai Asma’u aure zata yi Ummah”, a yadda ya ƙarashe maganar a raunace ne ya tabbatar mata da abin na soya mashi rai, duban shi ta yi tare da sakin wuƙa cikin robar cefanen, baki ta ɗan taɓe kafin ta ce “Toh Allah ya sanya Alkhairi”, ba dan Abbas ya so ba ya ce “Amiiiin.”
Da hanzari ta cigaba da yankan cefanen, saboda abin ya taɓa mata rai, lallai Asma’u kam ta sha dasu idan ta riga Abbas aure, toh amma Allah ke yi ai, fatanta dai Allah ya zaɓa ma Abbas mace ta gari.
Ganin Abbas ya yi jugum ne ya sa ta soko magana duk dan ya dayaye, cewa ta yi “Ai kai na ga alamar baka shirya auren ba.”
Da ƙyal ya iya bata amsa, “Insha Allahu ni ma zan yi Ummah”, ki dai taya ni da addu’a kawai, “Uhm” kaɗai ta ce, dan gani take kamar faɗa kawai yake.
Daga nan wurin aikinsu ya nufa, Abdull na ganin yanayinsa ya gane baya cikin walwala, tambayar sa ya yi “Jikin ko garin”, kamar Abbas zai yi kuka ya ce “Duka”, da ƴar damuwa Abdull ya sake tambayar shi “Me ya faru”, kasa faɗa ma Abdull ya yi, gudun kada ya gwalishe shi, sai dai ya ce “Ka dai ta ya ni da addu’a”, Abdull ya ce “Toh Allah ya kawo mafita”, Abbas ya ce “Amiiiin.”
Aikin haɗa block ɗinsu suka cigaba da yi, sai dai ko kusa Abbas ba ya jin daɗin aikin, sai can da ya ji ƙunci na shirin kashe shi ya dakata da haɗa blocks ɗin, idanunsa kamar garwashin wuta ya dubi Abdull “Kasan me?”, Abdull ya ce “Sai ka faɗa”, zuciyar Abbas iya wuya ya ce “Wai Asma’u ce zata yi aure.”
Take Abdull ya nemi ɗan tausayin Abbas da ya cika mashi rai ya rasa, a yatsine ya kalle shi, “Ikon Allah, Toh sai me idan Asma’u zata yi aure?”, ƙeya Abbas ya ɗan sosa “Ba zaka gane bane Abdull…”, a hasale Abdull ya katse shi “Indai a kan Asma’u ne ba zan taɓa ganewa ba Abbas. Wai kai dan Allah yaushe zaka raba kanka da wahala, Asma’un me da zata hana ka zaman lafiya?”, Shiru Abbas ya yi, a ranshi yana jin kamar ya haɗiye zuciya ya mutu, Abdull kuwa masifa ya cigaba zazzaga mashi, dan ya fahimci idan aka sassauta ma Abbas, toh hatta waɗanda ke tare da shi ba zasu zauna lafiya ba, tunda farincikinsa da ƙuncinsa duk nasu ne.
Har Abdull ya ƙaraci faɗanshi, Abbas bai ce komai ba, sai ma ya koma kan benci ya dafe kai, banza Abdull ya yi da shi ya cigaba da aikinsa.
****
Hausawa suka ce “Matar cushe bata daraja”, kuma sun faɗi gaskiya, domin tunda Aka haɗa Asma’u da Nas sau biyu suka haɗu, a wayar ma ba sosai yake kiranta ba, uwa uba kuma a chat sai dai ita ke ta aukin aje mashi saƙunan da bai buɗewa bare reply.
Abin na damunta, amma da yake ta makance a son shi bata jin zafi sosai, Aunty ma abin ya fara ɗarsa mata alamar tambaya, sosai take son ankarar da Asma’u, dan ba inda ake neman aure a haka. Har ɗaki Aunty ta same ta yammaci, lokacin Asma’u na karanta novel, daga jinginen da take da bango ta ce, “Asma’u wai ya batun mutuminki? Kuna waya kuwa.?”
Sai da ta gyara zama kan katifarta kana ta ba Aunty amsa “Eh toh, amma ba sosai ba”, mamaki ƙarara a fuskar Aunty ta maimaita “Ba sosai ba??”, kan Asma’u na ƙasa ta ce “Eh”, ɗan shiru Aunty ta yi tana nazarin lamarin, daga bisani ta ce “Anya Asma’u mutumin nan da gaske yake? Ta ina ake neman aure haka, ko kin manta irin zaryar da Abbas ke yi a gidannan lokacin yana neman aurenki??”, Asma’u kam bata manta ba, shiyasa itama lamarin Nas ke jijjigata, dan gani take ma kamar soyayyar ɓari ɗaya take.
Cikin sanyin zuciya ta shiga kare Nas da faɗin “Ai shi kinga unguwarmu ɗaya Aunty, idan aka ga yana zarya toh ƴan unguwa zasu fara tsegumi, shiyasa bai son zuwa.”
Aunty ba dan ta gamsu da hujjar Asma’u ba ta ce “Toh shikenan, Allah dai ya kyauta”, Asma’u ta ce “Amiin.”
Jiki ba ƙwarin da Aunty ta fita da shi ne ya ƙara tsorata Asma’u, wayarta dake gefe ta jawo, Number Nas ta danna ma kira, sai dai har ta ƙaraci ringin bai ɗaga ba, wani irin gwauron numfashi ta sauke, lokaci ɗaya kuma ta miƙe, ficewa ta yi daga ɗakin, dan kuwa zama wuri ɗaya tsautsayi in ji kifi.
Bata kai ga shiga Kitchen ba wayarta dake a hannu ta shiga ruri, tana dubawa ta ga Nas, wani irin daɗi ne ya taso mata, dan ganin sunan Nas na yawo a kan screen ɗinta na ɗaya daga cikin abin da ke haifar mata da farinci a yanzu.
Cikin taushin murya ta gaishe shi lokacin da ta ɗaga kiran, bayan ya amsa ne ya ɗora da “Na ga kira ne”, a yadda yake maganar ba zaka taɓa zaton da soyayyar ta a ransa ba,
murya a can ciki ta ce “So nake mu gaisa ai”, ya ce “Ayya, toh ya gida?” ta ce”Lafiya lau”, ya ce “Toh Madalla!”, Shiru ce ta ɗan ratsa tsakanin su, sai can Asma’u ta samu abin faɗa, inda ta ce “Uhm! Amma kamar baka damu da ni ba”, sosai maganar Asma’u ta bashi dariya, cewa ya yi “Saboda me kika ce haka”, a shagwaɓe ta ce “Ai baka son kirana, kuma a chat ma bama magana”
A wannan karon ta yi sa’a ya sassauta ta murya, cewa ya yi “Toh ba kya ganin bana zama”, cike da shuƙinsa ta ce “Ai ko yaya dai idan kana kira na zan ji daɗi”, ya ce “Toh shikenan, zan riƙa kiranki.”
Asma’u ta ji daɗin yadda ya saurari kokenta, suna gama wayar ta fito ɗaki, ranta fal da farinciki ta samu Aunty a ɗaki ta faɗa mata Nas ya kira, Aunty ta ce “Toh Allah ya sa a ɗore”, dan kuwa jikinta ya gama la’asar kan lamarin, musamman da take ta tsinto ƴan surutai a kan yadda Nas ɗin yake zaune da iyalansa.
Abbas kuwa tsawon kwana uku bai je wurin aiki ba, Abdull kuma ya kira shi amma bai ɗaga kiran ba, bare ya san dalili, hakan kuma ya taɓa zuciyar Abdull, a tunaninsa Abbas ko bai da lafiya. A rana ta huɗu ne da farar safiya ya nufi unguwarsu Abbas, dan zuwan ne zai ba shi tabbacin halin da Abbas ke ciki.
Abbas na kwance ya ji knocking ɗin da ƙarfinsa ya fi na yara, da hanzari ya yaye bargo tare da ɗaukar key ya nufi soro, lokaci ɗaya kuma bakinsa na tambayar “Waye.?”
Cikin ɗan fushi-fushi Abdull ya ce “Dallah Malam buɗe ƙofa, ka wani bar mutane sanyi na dukansu.”
Ƴar dariya Abbas ya yi tare da buɗewa, Abdull na kallonshi ya fahimci ba ƙaramar azaba Abbas ya sha ba, dan ya rame sosai, “Sannu! Majnuni Lailah, ko kuma in ce Majnuni Asma’u”, na ƴar dariya ya ce “Shigo dai, idan ya so da kowane suna ma ka kira ni.”
Gefe ya ɗan raɓe, Abdull na shigowa ya ɗan tura ƙofar. Har bedroom Abbas ya kai Abdull, dan can ne kaɗai ke da abin zama, sosai yanayin ɗakin ya taɓa zuciyar Abdull, dan saurayi mai jini a jika bai kamata a ce shi ke kwana a kan tsurar katifa ba kamar wani tsoho, cike da tausayin Abbas ya zauna kan katifar tare da naɗe ƙafufunsa saboda sany, Abbas na zama suka gaisa, ba tare da wata-wata ba Abdull ya ce “Lafiya kwana uku baka fita ba?”, cikin raunin murya Abbas ya ce “Wallahi Abdull bana jin daɗi, ko na fita ba zan iya komai ba”, Abdull ya ce “Toh wayar fa, ita kuma me yake hana ka ɗagawa?”, shirun da Abbas ya yi ne ya bashi damar ɗorawa da faɗin “Asma’u ko Abbas? Ta rabu da kai, kuma zata raba ka da mutane! So kake ta kashe ka, alhalin ita bata da asara? Wace irin zuciya ce gare ka, wadda ta ke da naci a inda ba a san darajarta ba.?”
Tamkar shigar mashi Abbas ke jin maganganun Abdull na ratsa mashi zuciya, a hankali ya rumtse idanu domin ya samu sassauci a ransa, shi kuwa Abdull wannan ne ya ba shi damar faɗa ma Abbas gaskiyar da ta kamata, inda ya nuna mashi idan ya mutu fa toh iyayensa da ƴan’uwansa ke da asara ba Asma’u ba. Sannan ya nuna mashi ba Asma’u ce kaɗai ta mallaki farinciki ba, dan haka ya dage da nema a wurin wasu matan, mai yiwuwa su ba shi fiye da wanda ya rasa.
Sosai Abbas ya tsunduma a kogin tausayin kansa, take Abdull ya biyo bayanshi lokacin da hawaye suka gangaro kumsa tare da faɗin “Abdull ka yi mani uzuri, nima so nake na rabu da wannan ƙuncin amma na kasa, Asma’u ta cutar da ni da yawa, ina roƙon Allah ya kawo mani sassaucin da zai mantar da ni ita, dan na tsane ta, so nake na goge ta shafin rayuwata”, kamar Abdull zai yi kuka ya ce “Allah ya yaye maka damuwarka, amma sai ka jajirce sosai wurin nisantar duk abin da zai tuna maka ita.”
“Wallahi Abdull cikin jajircewa nake, ka san duk abin da ya zama addicted rabuwa da shi bala’i ne mai zaman kansa, toh sakamakon cire Asma’u a zuciyata ne nake karɓa, Insha Allahu da na warke shikenan Abdull”, kai Abdull ya jinjina “Allah ya chanja maka da wadda ta fi ta”, Abbas ya ce “Amiin.”
Lallashi Abdull ya ɗaura da shi, tare da nuna ma Abbas shi namiji ne da babu macen da ba zata yi fatan ta aure shi ba, sai wadda bata da rabo irin Asma’u, murmushi kawai Abbas ya riƙa yi, dan Abdull ya iya kwantar ma mutum da hankali.
Ganin Abbas ya ɗan dayaye ne, sai Abdull ya samu damar tambayar shi “Ina Khadijah?”, ɗan shiru Abbas ya yi, dan rabon da ya yi ƙwaƙƙwaran tunani a kanta kwana biyar kenan, daga bisani ne ya ce “Tana nan”, Abdull ya ce “Toh ya ake ciki ne?”, Abbas ya ce “Na bata time ta yi nazari, toh ban dai sake tuntuɓarta ba”, Abdull ya ce “Toh gwara ka tuntuɓe ta, idan ta amince musha biki kwanan nan, idan bata amince ba kuma mu kai ka gidan tururuwa, tunda da alamun ba mai so”, yadda ya ƙarashe maganar da zaulaya ne ya ba Abbas dariya.
Waya Abbas ya ɗauka, kai tsaye Whatsapp ya shiga, tare da aje ma Khadija dogon voice, wanda ke nuna yana son jin matsayarsu. Fatan dacewa Abdull ya yi mashi ya ce “Amiin.”
Ɓangaren kamfaninsu suka koma, inda suka cigaba da tattauna yadda zasu bunƙasa kamfanin, tunda suna ta samun customers, tun bayan da suka gama kwangilar blocks ɗin Alhaji Nas. Abdull kuma bai samu tafiya ba sai ƙarfe tara.
Khadija bata samu damar leƙawa Whatsapp ba da rana, saƙon Abbas ne farkon wanda ta buɗe, cikin azarɓaɓi ta yi playing voice ɗinsa, so take ta ji, amma hayaniyar baƙi kuma ƙannenta sun cika falon. Earpiece ɗinta ta ɗauka tare da ficewa tsakar gida ta zauna kan plastic chair. A tsanake ta saurari voice ɗin Abbas mai cike rauni, inda ya roƙe ta a kan ta taimaka ta amince mashi, domin ita kaɗai ce macen da yake so a yanzu.
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke gami da faɗin “Oh ni Dije”, dan kuwa kanta ya kulle, ta kasa gane tana son Abbas ko bata son shi.
Tana cikin laluben hukuncin da zata yanke ne kiran Abbas ya shigo wayarta, kasantuwar ya ga alamun ta buɗe saƙonsa. Ƙin ɗaga wayar ta yi, sai ma ta tashi ta koma cikin ɗakin, ganin mamanta, da kuma ƙanwar maman mai suna Aunty Maryam da ta zo basa falo, sai ta nufi bedroom.
“Lafiya?”, Mamansu ta tambaye ta, saboda sanyin jikinta ya nuna akwai alamun wani abu, ɗan langaɓe kai ta yi “Wai Abbas ne ke son jin matsayata”, da mamaki Aunty Maryam ta tambaye ta “Wane Abbas?”, mamansu ce ta ba Aunty Maryam amsa “Abbas dai tsohon mijin ƙawarta Asma’u, kin san sun rabu, shi ne ita ya dawo mata”, ƙwafa Aunty Maryam ta yi tare da faɗin “Allah ya kyauta, toh ke me kika yanke?”, ɗan shiru Khadija ta yi tana nazari, daga bisani ta ce “Ni dai gudu nake kada a ce na ci amanar Asma’u, amma da na amince”, baki kawai mamansu ta taɓe, dan ta fahimci Khadijar na son Abbas.
Aunty Maryam ta san labarin Asma’u sosai, saboda Auntinsu Asma’u yayar mijinta ce, dan haka har Nas dake neman auren Asma’u ta san da labarin”, wani irin kallo ta yi ma Khadija kafin ta ce “Toh ita Asma’un da ta ci amana fa, Alhaji Nas fa maƙwafcinku zata aura”, kusan a tare Khadija da Mamanta suka haɗa baki wurin tambayar “Alhaji Nas??”, lokaci ɗaya kuma gaban Khadija na wata irin faɗuwar da za a iya kiranta kishi.
Aunty Maryam ta ce “Na rantse kuwa, wanda har iyaye sun shiga maganar, dan haka idan kina son Abbas ma ki aure shi, dan wallahi ya fi Alhaji Nas sanin darajar ɗan adam”, jinjina kai Maman Khadija ta yi “Faɗa mata dai, yoh ko Asma’u na gidan Abbas ai tsaf sai ta aure shi, bare basa tare, kuma wannan zamanin da aure ke wahala samun miji ɗan ƙwalisa kamar Abbas ai sai an tona”, Aunty Maryam ta ce “Wallahi kuwa”, nan ta shiga ba Maman Khadija labarin irin rashin mutuncin da Asma’u ta yi ta zubawa a gidan Abbas, sannan ta koma ɓangaren baƙin halin Nas ɗin, wanda ba kowa ya sanshi ba, dan haka akwai yiwuwar sakayyar cutarwar da ta yi ma Abbas ce zata haɗu da ita a gidan Nas.
Ita kuwa Khadija kanta ya kulle, dan ta gama gane Nas ne mutumin da Asma’u ke bata labarin tana so, take ta ji tana son ɗaukar ma Abbas da Aishar Nas fansa, kasantuwarsu na mutanen da Asma’u ta cutar.
A nan Aunty Maryam ta ƙara zuga ta, cikin ƙanƙanen lokaci ta ji ba wanda take so sai Abbas. Mamansu kuwa murna kamar ta taka dutsen arfa, dan ganin farko da ta yi ma Abbas ta ji tana son ya zama sirikinta.
Abbas na kwanace kan katifarsa yana jiran tsammani saƙon Khadija ya shigo wayarsa, “Salam, na amince na zamo matarka, kuma Insha Allahu zan share maka hawayenka”, zumbur ya tashi zaune, bai yi wata-wata ba danna voice button, inda ya naɗi “Nagode Khadija, Allah ya baki iko”, sai da ya sumbace ta sannan ya saki saƙon.
Allah ya kara basira aunty Hadiza Asmau ta debo ruwan dafa kanta