Skip to content
Part 23 of 25 in the Series Cikin Baure by Hadiza Isyaku

Khadija na gama sauraron voice ɗin Abbas ta maido mashi da “Amiiin, nima nagode”, haɗe da emoji mai nuna alamun jin kunyar sumbar da ya yi mata. 

Kai Abbas ya ɗan girgiza, lokaci ɗaya kuma ya yi dariya mai cike da jin daɗi, zama ya gyara kafin ya rubuta mata “Jin kunya kuma? Toh zaki dena ma”, yana aje mata saƙon ya fito daga WhatsApp, dialer ya nufa ya danna ma numberta da ke a sahun farko kira, a kunne ya kara wayar, dan ya fi son jin muryarta shi kaɗai, duk da ba kowa a ɗakin, sai da ya fara yanke tsammanin ɗagawarta ne ya ji muryarta mai daɗin gaske ta ratsa kunnensa da sallama, ƴar faɗuwa gaban Abbas ya yi, dan wannan ne karon farko da murya mai cike da shauƙin so ta taɓa ratsa zuciyarsa, kasantuwar Asma’u ce kaɗai macen da ya taɓa ba ma lokacinsa, ita kuma ga yadda tafiyarsu ta kaya. 

Idanunsa a lumshe ya amsa mata sallamar, daga nan kuma ya yi kasaƙe yana jiran ta sake magana, jin ta yi shiru ne ya ambaci “Deejah”, cikin murya mai taushin gaske, amsawa ta yi da “Na’am”, ya ce “Da gaske kina so na?”, murmushi mai sautin da ta yi ne ya amsa mashi tambayarshi. 

Cigaba da magana ya yi da faɗin “Nima ina son ki, Allah ya sa, tarayyarmu ta zame mana Alkhairi a duniya da lahira”, daga can ta ce “Amiin ya Allah.”

A kunyace suka taɓa ƴar hira, a nan Abbas ya faɗa mata kai tsaye wurin mahaifinta zai zo, tunda sun amince da soyayyar junansu, idan ya ba shi izini, toh zai turo waliyyansa su nema mashi aurenta, dan bai ƙi ba nan da wata uku an yi komai an gama. 

Khadija ta ji daɗin yadda Abbas ke son ɗaga darajarta, dan a wannan zamanin da muke ciki cikakkiyar daraja ce a wurin ƴa mace, wanda yake sonta ya furta mata kalmar aure, tare da yunƙurin aiwatarwa, daga can cikin wayar ta ce “Toh wane lokaci ne ka fidda zaka ga baba, sai a sanar da shi”, Abbas ya ce “Gobe ma idan yana nan zan iya zuwa”, cewa ta yi “Ai sai weekend ne kaɗai ake samunsa a gida.” Bayan sun tsaida ranar da zai je gidansu Khadijar ne suka yi sallama, saboda dare ya fara. 

Wannan ƴar waya da suka yi ba ƙaramin nishaɗi ta sanya Abbas ba, cike da son Khadija ya bi pics ɗin da ta turo mashi ya cigaba da ƙare masu kallo. Haƙiƙa Khadija tana da kyau, dan kuwa black beauty ce ita mai wushirya, a gefen kumatunta kuma ga wani dimple da ya ƙawata su, Abbas bai kwanta bacci ba sai ya tabbatar da kyawun Khadijah na daban ne. 

Washegari kuwa shi kanshi ya ji a jikinsa cewar ya samu nutsuwa. Ya so kuma faɗa ma ƴan gidansu, amma sai ya bari har sai ya je wurin baban Khadija, duk hukuncin da ya yanke, toh da shi zai yi amfani wurin sanar ma duk mai haƙƙin a sanar mawa. 

A wurin aiki kuwa Abdull ba ƙaramin farinciki ya yi ba da jin amincewar Khadija, zafafan hotunanta Abbas ya sake nuna mashi, aikuwa ya ce “Haba! Ko kai fa, wallahi yanzu zaka san ka yi mata”, Abbas na dariya ya ce “Ni ma na ji a jikina”, shawarwari masu kyau Abdull ya ba shi, daga nan suka cigaba da aikin gabansu.

Ta ɓangaren call da chat kuwa, Abbas da Khadija sun ƙara sabawa, har Abbas na mamakin anya shi ne ke iya kula wata? Saboda Khadija ta samu gurbi na musamman a ransa, har ta kai ga ya zaƙu Sunday ta zo ya je gidansu. 

Sunday ɗin na zuwa bayan la’asar ya chaɓa ado kamar sabon ango ya fito, a kan kwana ya yi kiciɓus da Abida ta dawo daga bakin titi. Kallo Abida ta ƙare mashi lokacin da ya tsaya da mashin ɗin, sosai kwalliyar yayan nata ta birge ta har ta furta “Kai ni Yaya Abbas sai ina?”, bata yi zato ba sai ji ta yi ya ce “Zance zan je”, idanu ta zaro “Da gaske”, ya ce “Ina yi maki ƙarya ne?”, ta ce “A’a, amma dan Allah wacece Gimbiyar?”, ya ce “Ki bari in dawo tukunna”, zuciyarta fal da farinciki ta ce “Toh shikenan”, ƴan maganganu suka ƙara sannan ya tada mashinɗinsa ya tafi.

Abida kuwa na isa gida ta kwarmata ma Ummansu cewar ta ga Abbas zai je zance, baki Ummansu ta taɓe, dan gani take kamar wasa ne maganar. 

Abbas kuwa sai da ya biya ya yi sayayyar kayan maƙulashe sannan ya nufi unguwarsu Khadija. Ba tare da ɓata lokaci ba aka yi mashi iso a babban falon maigidan, falo ne mai cike da kayan alfarma. 

Ƙasan carpet ya sunkunya zai zauna, babansu Khadija da suka shigo tare ya dakatar da shi da faɗin “A’a, ka zauna kan kujera mana”, cike da kunya Abbas ya ɗan ɗosana jikinsa kan kujera, dan shi a ganinsa rashin ɗa’a ne daidaita zama da surukai. 

Zama Babansu Khadija shima ya yi akan kujerar da ke opposite da ta Abbas, cike da mutunta juna suka gaisa, daga nan falon ya yi shir, baka jin sautin komai sai na ƙarar Ac, hakan ne ya babansu Khadija damar ƙara nazartar Abbas, inda ƙanƙan da kan ɗin Abbas suka birge shi, a ransa ya ce “Indai haka yake, toh Khadija ta yi sa’ar miji.”

 A zahiri kuma ɗorawa ya yi da faɗin “Toh Malam Abbas, na ji abin da ke tafe da kai, cewar kana son auren Khadija ko?”, a kunyace Abbas ya ɗaga kai “Eh Baba”, babansu Khadija ya ce “Toh madallah, a iya yau kaɗai na ƙara yabawa da halinka, saboda na daɗe da sanin waye mahaifinka wurin nagarta, dan haka na baka Khadija duniya da lahira, tunda kuna son juna, ina kuma da yaƙinin zaka riƙe mani ita amana.”

Abbas ya ji daɗi sosai, har a lokacin kansa na ƙasa ya ce “Nagode Baba”, babansu Khadija ya ce “Ba komai.”

Maganar lokacin da Abbas ya shirya auren suka yi, inda babansu Khadija ya nuna mashi baya son doguwar tarayya, idan ba damuwa toh nan da wata biyar ma zai iya ɗaura masu aure idan har Abbas ɗin ya shirya.  

A matse Abbas yake, kuma daidai gwargwado yana samun kuɗaɗe, dan har ya fara shirin siyen filin da ke kusa da gidansa ya haɗe, dan haka ba tare da ɓata lokaci ba ya amince da batun babansu Khadija. 

Bayan sun gama fahimtar juna ne Babansu Khadija ya tashi ” To bari in turo maka ita ku gaisa”, cike da kunya Abbas ya ce “Toh Baba, nagode.”

Khadija na bedroom ɗin mamansu ta shirya cikin doguwar rigar atamfa glitter, muryar babansu ta jiyo a bakin ƙofa yana faɗin “Ina Khadijar?”, daga can ta ce “Gani nan”, ya ce “Ki fito, ga Abbas ɗin can yana jiran ki”, sai da Mamansu ta ƙara gyara mata ɗaurin ɗankwali, sannan ta feshe mata jiki da turare mai sanyin ƙamshi. 

Gyale orange ta yafa, sannan ta zura flat shoe ta fito. Babansu Khadija mutum ne mai sakin fuska ga iyalansa, cikin wasa ya ce “Anya Abbas ɗinnan kuwa, na ga kamar an fifita shi a kan sauran”, cike da kunya Khadija ta rufe fuska tana dariya, dariyar shi ma ya yi, sannan ta kama hannun Farha ƴar rakiya suka tafi. 

Abbas kuwa tuni ya zuba idanu yana son ganin ɓullowar gimbiyar tashi, dan karramawar da babanta ya yi mashi ya ƙara tabbatar mashi da su mutanen kirki ne. 

Takunta da ya ji ne ya sanya shi faɗaɗa fara’arsa, tana shigowa kuwa ya ji wani irin sonta ya tafi da shi, domin ko a iya kwalliya kaɗai Khadija ta fi Asma’u, da idanu ya raka ta har ta je kan kujera ta zauna. 

Ita kuwa kamar zata nutse ƙasa, ta rasa dalilin da ya sa kullum kunyarsa ke ƙara mamaye ta. Farha ƴar rakiya kuwa tuni ta je gaban Abbas ta duƙa “Yaya inawuni”, Abbas na dariya ya dafa kafaɗunta ta miƙe “Lafiya lau ƙanwata, ina Mama?”, ta ce “Tana nan lafiya”, kumcinta ya ɗan lakata “Toh madalla”, zaunar da ita ya yi a gefensa. 

Cike da shauƙi ya juya akalar ganinsa wurin Khadija da ke ta wasa da yatsunta da suka sha ƙumshi “Barka da shigowa madam”, ya faɗa cikin muryar kulawa. Sai da ta yi murmushi kana ta ce “Barka dai, kun wuni lafiya”, ya amsa “Lafiya lau Deejah!”

Ƙuri ya yi mata, ita kuwa sai sussune kai take, a ranshi ya ce “Masha Allah”, saboda yana son mace mai kunya. 

“Khadija”, ya ambaci sunanta, a hankali ta ɗago tare da jifarshi da ƙayataccen murmushi, sosai salon ya birge shi, cewa ya yi “Yaushe kika fara jin kunyar Abbas?”, 

Sunansa da ya sako a cikin tambayar ne ya sanya ta ɗan nazari, tana ankarewa ta ɗan buɗe baki tare da yin dariya, shi ma dariyar ya y, haɗe da faɗin “Ko dan na ce ina sonki?”, murmushi mai sauti ta yi “Uhmm!”, 

Shima murmushin ya yi “Kin shiru”, dubansa ta yi, tana son yin magana amma bakinta ya yi nauyi, cewa ya yi “Shikenan, idan muka haɗe za ki manta da wata kunya.” 

Hira ya yi ta janta da ita wadda dole ta sanya baki, yana ganin ta fara sake mashi ya shiga faɗa mata irin tsananin son da yake mata, wanda har ta yi mamaki, dan a yadda ta ga yana ma Asma’u kuka, ta ɗauka ba zai sake son wata mace ba. 

Sosai itama ta ji son shi kamar ya fito mata a waje, kallon shi ta riƙa yi idan yana magana, yana lura ya ce “Ki faɗa mani matsayina a wurinki dan Allah.”

Wani kallo mai cike da ƙauna ta yi mashi, sai da ta yi murmushi sannan ta ce “Kana da matsayi na musamman a wurina, ina sonka sosai, Ina roƙon ka da komin daɗewa kada ka watsa mani kasa a ido”, kai ya jinjina yana dariya “Insha Allahu my love, Allah ya barmu tare”, ta ce “Amiin.” Sun daɗe suna hira, sai gab da magarib ya tafi, bayan ya basu tsarabarsu. 

Bai koma unguwarsu ba sai bayan Isha’i, gidansu ya nufa, ya kuma labarta ma Ummansu ya samu matar aure. 

Ita kuwa baki har kunne ta ce “Kai Masha Allah, ƴar ina ce?”, faɗa mata ya yi “Khadija ce ƙawar Asma’u”, cewa ta yi “Anya kuwa Abbas, ba za a koma ma ƴar gidan jiya ba?”, sosai ya nuna mata Khadija yarinya ce nutsatstsa, Abeeda ma ta ji daɗin haka, dan burinta Abbas ya yi abin da zai baƙanta ran Asma’u. 

Allah ya sa Alkhairi ta yi mashi, daga nan ya koma gida, sai da ya kimtsa sannan ya kira Khadija, dan ya faɗa mata kada ta yi bacci da wuri. 

Godiya ya yi mata a kan yadda gidansu aka karɓe shi hannu biyu-biyu duk da ba wasu kuɗaɗe gareshi ba, cike da soyayya itama ta gode mashi, dan tana jin a jikinta shi ne cikon farincikinta. 

Tun daga wannan rana soyayya mai ƙarfi ta dasu a tsakaninsu, hatta ƴan gidansu Abbas sun shaƙu da ƴan gidansu Khadija, saboda karamcin kowanen su. 

Hakan ne kuma ya sanyo duka waliyyansu a cikin maganar har aka sanya biki wata goma masu zuwa. An kuma sanya bikin nesa ne saboda Abbas ya gama gyaran gidansa a natse. 

Kamar kuma yadda Khadija ta tsinci maganar Asma’u zata auri Nas, haka itama Asma’un ta tsinto maganar Khadija zata auri Abbas, duk kuwa da bata son Abbas take ba, amma sai da ta ji wani irin ƙunci a ranta, har ta riƙa faɗin Khadija ta ci amanarta, Nafeesa na dariya ta ce “Shi fa gwano baya jin warin jikinsa ko?”

“Me kike nufi da wannan maganar?”, Asma’u itama ta jefo ma Nafeesa tambaya, duk da ta fahimci inda ta dosa, cewa Nafeesa ta yi “Yadda kika fahimta nake nufi, kuma kada ki ga laifinta fa, tunda ba wadda Abbas zai ce yana so bata amince ba”, wannan magana bata yi ma Asma’u daɗi ba, huce haushin Khadija ta shiga yi akan Nafeesa, har sai da Aunty ta dakatar da su, dan itama Nafeesar ba kanwar lasa bace.

Masu magana kuma suka ce idan an dafa ɓoye, toh ba za a ci ɓoye ba, domin kuwa magana ta daki kunnen Aishar Nas cewar zai auri Asma’u. Kowa ya san halin da mace ke tsintar kanta idan aka ce mijinta zai ƙara aure, toh amma yanayin Aishar Nas ya zarce na sauran mata, don kuwa har ta yanke tsammanin ita da farinciki har abada, duba da zaman ƴan marinar da suke ita da Nas ɗin, kuma a haka za’a ce zai ƙara aure.  

Kuka kam ta yi mai isarta, kuma ta ɗaura dukkan zargin Sani ne silar auren, duk da ta kama Asma’u dumu-dumu da son mijinta. Nas na dawowa ta same shi a ɗaki, shi kanshi yanayinta ya fahimtar da shi cewar ta ji labarin. 

Tambayar ta yake son yi, amma girman kansa ya hana shi, sai da ta gaji da jugum ɗinsu ne kana ta ce “Alhaji, me ye gaskiyar zaka auri Asma’u?”, a yadda ta yi maganar cikin taushin murya ya ci ace ya tausaya mata. amma sai ya kicincine fuska ya ce “Wace irin magana ce wannan daga dawowata?” kamar zata yi kuka ta ce “Yanzu dan Allah meye laifin tambayata?”, cewa ya yi “Kin yi ta ba a lokacin da ya kamata ba, hutawa nake son yi, amma kin zo mani da wani zance marar kan gado.”

Babban abinda ya fi ƙona ma Aisha rai a zamantakewarta da Nas shi ne rashin fahimtar juna, sannan ba ya sauraren kokenta, bare ya magance mata matsalolinta, shi ya sa da wahala su fara magana, kuma su ƙare ta ba tare rayuka sun ɓaci ba. 

Bayan ƙwafar da ta sauke ne ta ce “Yanzu har kana iya hutawa, alhali iyalinka tana cikin ƙunci”, tana rufe baki wasu hawaye masu kauri suka ɓuɓɓugo cikin ƙwayar idonta, wani mugun kallo ya jefe ta dashi, lokaci ɗaya kuma ya cigaba da danna wayarshi. 

Maganganu ne cike da bakinta, dan haka ta yi ta fesa mashi su, inda ta nuna a halin yanzu ma aure ba nashi bane, tunda yana da matsalolin da ita kaɗai da shi ne suka sansu, aikuwa a fusace ya ɗaga mata hannu, “Aisha, dan Allah fita ki bar mani ɗaki, bana son surutun banza da wofi.”

Kamar zata haɗiyi zuciya ta mutu ta ce “Zan bar maka ɗaki, tunda dama na fahimci ba so kake ina shigowa ba”, daga faɗin haka sai ya ce bata da ɗa’a, tana wulaƙanta shi, sai da ta kai bakin ƙofa ta ce “Ai dai aure zaka ƙara ko? Toh a nan ne lokaci zai bayyana idan wulaƙanta ka nake”, ta faɗi haka ne saboda tabbacin babu macen da zata iya zama da Nas, kuma a zauna lafiya. 

Cike da fargabar maganarta ya ce “Au so kike, in yi aure in wulaƙanta ko?”, ta ce “Ni bance ba, amma dai ka sani lokaci ne zai nuna”, shi kuwa sai gadara yake yana yi mata wulaƙanci. 

Shekaru goma kenan suna zaune, amma duniya ta shaida haƙuri kawai take da shi, haka ta bar mashi ɗakin tana kuka, kuma tun daga wannan rana suka dena kula juna. 

Duk wanda Aisha ke sa ran zai saurare ta faɗamawa, amma kowa cewa yake ta yi haƙuri saboda yaranta, dan ta ɗaukar ma ranta kashe auren ta huta da baƙinciki.  

Addu’a ta shiga yi ba dare ba rana, akan Allah ya kawo mata mafita, idan zamanta gidan ne Alkhairi, Allah ya daidaita su, idan ba Alkhairi Allah ya raba su, ya kuma yi mata zaɓi na gari. 

Allah maji roƙon bawa, da misalin ƙarfe taran safiya, tana cikin gyaran ɗakinta ya ɗage labulen falon “Kina ina?”, wata irin faɗuwa gabanta ya yi, a tsorace ta fito falon, kamar wanda aka wa tsa ma ruwan zafi ya miƙo mata takarda “Saki ne! ki je Allah ya haɗa kowa da rabonsa, dan na gaji.”

<< Cikin Baure 22Cikin Baure 24 >>

3 thoughts on “Cikin Baure 23”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×