Wata irin jijjiga zuciyar Aisha ta shiga yi, har ta kasa ko da motsi, saboda saki bala'i ne da duk taƙadarcin mace idan ta haɗu da shi sai ta girgiza, bare kuma kamilar mace irin Aisha.
Sosai ta yi ta maza wurin faɗin "Alhamdulillah, Allah ya sa haka ya zame mana Alkhairi baki ɗaya." Shi kuwa so ya yi ta firgice, saboda ya san tana son zaman gidansa duk da ba daɗinsa take ji ba, wata irin ƙwafa ya yi kafin ya ce "Amiiin dai."
Juyawarsa ke da wuya ta shiga furta "Inna li Llahi. . .