Skip to content
Part 24 of 25 in the Series Cikin Baure by Hadiza Isyaku

Wata irin jijjiga zuciyar Aisha ta shiga yi, har ta kasa ko da motsi, saboda saki bala’i ne da duk taƙadarcin mace idan ta haɗu da shi sai ta girgiza, bare kuma kamilar mace irin Aisha.

Sosai ta yi ta maza wurin faɗin “Alhamdulillah, Allah ya sa haka ya zame mana Alkhairi baki ɗaya.” Shi kuwa so ya yi ta firgice, saboda ya san tana son zaman gidansa duk da ba daɗinsa take ji ba, wata irin ƙwafa ya yi kafin ya ce “Amiiin dai.”

Juyawarsa ke da wuya ta shiga furta “Inna li Llahi wa inna ilaihi raji’un” a zuci, dan ji take kamar ƙasa zata dare ta faɗa a ciki. An ce “Idan aka yi saki Al’arshin Ubangiji na girgiza, saboda Allah ba ya son saki, duk kuwa da halal ne.” to a wurin Aisha zata iya cewa ƙasa ma girgiza take, dan kuwa kyarma ce ta tsinke mata, ba kuma komai ya jawo haka ba sai tunanin makomar ƴaƴanta mata.

Da ƙyal ta iya jan ƙafafunta da suka yi nauyi ta koma bedroom, jagwab ta zauna kan kujera tare da dafe kai ta fashe da kuka. Ita kuwa wace irin masifa ce wannan ke bibiyarta? Aure shi ne tushen duk wani farinciki idan an dace, amma ita sai ya zame mata silar ƙuncin rayuwa, dan rabuwa da ƴaƴa ciwo ne da ba ranar warkewarsa.

Cike da ƙasƙantar da kai a wurin Ubangiji ta ce “Allah ka ba ni ikon cinye jarabawar da kayi mani, ka sa kuma wannan sakin ya zame mani Alkhairi da kuma sila ta samun farinciki a gaba”, tana kai ƙarshen addu’ar ta haɗiye gululun da ya tokare mata zuciya.

A cikin wannan yanayin ta riƙa hango yanayin da yaranta zasu shiga idan suka dawo makaranta suka tarar da bata nan, domin kuwa suna da ƙwallafa, kai ta girgiza tare da faɗin “Wayyo Allah! Allah ka tausaya ma raunina.”

Kamar daga sama ta jiyo muryar Nas “Ki hanzarta ki fito, ni rufe gidana zan yi?”, tambayar kanta ta shiga yi “Anya Nas mutum ne?”, dalili da ko dabba ta san mai kyautata mata, toh da alamun dabbar ma ta fi Nas iya mayar da Alkhairi.

Kamar wadda aka tsikara ta miƙe, kayanta ta shiga haɗawa tana kuka, lokaci ɗaya kuma tana ta roƙa ma ƴaƴanta kariyar Ubangiji, dan bata tunanin Asma’u na da tarbiyyar da zata ba su idan ta shigo gidan.

Ɗan ƙaramin trolly ta cika da kaya, sannan ta kimtsa ta fito, a tsakar gida ta iske Nas zaune kan plastic chair sai huci yake, ba tare da kalli inda yake ba ta nufi ƙofa. Shi kuwa tsabar girman kai ya hana shi hangen kuskuren da ya tafka, da idanu ya bi ta har fice daga gidan.

Tashi ya yi ya shiga ɗakinta, haɗa ma yaransa kayansu ya yi, dan ya shirya inda zai kai su idan sun dawo, sannan ya bar gidan shi ma.

Aisha kuwa kamar wadda aka tullo ta shigo gidansu, a tsakar gida ta samu mahaifiyarta tana shara, ba ta yi sallama ba, bare ta iya gaishe ta, sai dai ta raɓa gefenta ta wuce ɗaki. Sosai jikin Hajiyarsu Aisha ya yi sanyi, wani gwauron numfashi ta sauke tare da sakin tsintsiyar, dan babu alamun lafiya a tare da Aisha.

Gabanta na faɗuwa ta shiga ɗakin itama, ganin Aisha ta rufe fuska da dukkan hannayenta ne ya ƙara taɓa mata zuciya, dan babu mahaifiyar da ke son ganin ɗanta cikin ƙunci, idanunta na kan trollyn Aisha ta tambaye ta “Me ke faruwa ne.?”

Kasa magana Aisha ta yi sai dai ta miƙa mata takarda, wadda dama jikin Hajiyar ya gama bata auren ya samu tangarɗa. Jikinta na ɓari ta buɗe ta karanta kamar haka “Ni Nasir, na saki matata Aisha saki Biyu.”

Dogon numfashi Hajiyarsu Aisha ta sake ja tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya “Ƙaaasa!” ta furta cikin tsananin tashin hankali, lokaci ɗaya kuma ta bi bayanta da “Tarji’i”, dan ba zata iya ɓoye tashin hankalin da ke ranta ba.

Wannan tashin hankali na Hajiyarsu ne ya ƙara ɗimauta Aisha, duƙar da kanta ta yi ƙasa ta cigaba da kuka, itama Hajiyar daurewa kawai ta yi, amma da ba abinda zai hana ta kuka.

Abbansu Aisha na shigowa ya riske su cikin wannan hali “Toh sai me; Daga kin huta da bala’i? Ya je, zai gane kurensa.” abin da ya faɗa kenan dan ya kwantar masu da hankali.

Cikin ɗacin rai Hajiyarsu Aisha ta ce “Nasir butulu ne Alhaji..”, tarbar numfashinta ya yi da faɗin “Aisha kuma mai biyayya ce, da sannu dukkansu zasu girbi abin da suka shuka”, ba tare da haufi ba Hajiyarsu Aisha ta ce “Allah ya sa”, dan duk wanda aka ce ma aniyarsa ta bi shi ya ji haushi, toh aniyar ba ta kirki ba ce.

Ƴan’uwa da abokan arziki ba wanda bai jajanta ma Aisha da mahaifanta ba. Fatan Alkhairi kuwa shi ne abin da kowa ke mata, dan ta yi haƙurin gidan aure. Nas kuwa ba wanda ke masa fata mai kyau, dan an ce “Allah sam barka ma idan ta yi yawa ɓarna take, bare Allah wadai.”

Batun yara kuwa, Allah ne ya tsaya mata aka maido mata yaranta gabanta, tare da sharaɗin Nas zai cigaba da kula da su har lokacin da za su dawo hannunsa.

Wannan ne ya sanya ma Aisha nutsuwa a ranta, har ta fara mantawa da wani Nas, dan dama damuwarta ta ƴaƴanta ce. Ibada kuwa ba kama hannun yaro, kasantuwar dama ita Sauwama ce kuma ƙauwama, fatanta shi ne Allah ya bata miji wanda ya fi Nas Alkhairi idan ta gama Iddah.

Ta wani ɓangaren kuma dangin Nas sun so ayi sasanci, dan sun san Aisha ce kaɗai zata iya zama da ɗansu, aikuwa babansu Aisha ya shafa kwallin audi ya ce “Aisha ta gama aure da Nasiru, ya je can ya auri mai tarbiyya, tunda ita bata da ita.”

Shi kuwa gogan ko da ya ga kewa na neman samun mazauni a ransa sai ya yi wuf ya kai kuɗin neman auren Asma’u. Ita kuwa kan ka ce me ta fara ji da kai wai ita zata auri Nas. Tsakaninta da Halima kuwa har faɗa suka yi, dan ƴan unguwa sai zagin Halimar suke wai ta ci amanar Aishar Nas.

Ƙawancensu da Khadija kuwa tuni ya zama tarihi, dan yanzu Khadija ba ta ita take ba, saboda aurensu da Abbas ya matso.

Shi kanshi Abbas ya yi ta maza wurin jure dafin auren Nas da Asma’u zata yi, dan bincike ya nuna Nas bai taɓa sanin Asma’u tsohuwar matar Abbas ce ba, saboda ba inda ya ga chanji wurin girmamawa da mutuntawar da Nas ke mashi idan sun haɗu.

*****

A kwana a tashi kuma a sarar mai rai, Abbas ya gama tsara gidansa mai kyau, biki kuma ya rage saura sati biyu masu zuwa.

Takanas ta Kano ya je gidansu Khadija dan jin nau’ukan Events ɗin da take son yi ita da ƙawayenta, tunawa Khadija ta yi da yadda suka yi bikin Asma’u ba tare da wata hidima ba ta ce “Ba baka son events ba?”, girgiza kai ya yi “Ai ke da ƙawayenki zaku yi shagalinku”, a shagwaɓe ta ce “Toh ai idan babu kai a bikin ba zai yi daɗi ba, ni ba abin da zan shirya.”

“Oh! So kike in zo bikin wata ta ƙwace maki ni; Ko so kike in gayyato friends ɗina su kalle mani ke?”, cike da tsokana ya jero mata waɗannan tagwayen tambayoyin.

Maƙe kafaɗa ta yi kamar ƙaramar yarinya “Uhm Uhm”, ya ce “To ki yi haƙuri ki shirya events da basu saɓa ma addini ba, ni kuma Insha Allah zan baki kuɗaɗen da zasu ishe ki kin ji”, kai ta ɗaga “Toh”, idanunsa na mata kallon so da ƙauna ya ce “Yauwa tawan! Ina son ki.”

Bayan tafiyarsa ne Khadija ta zauna ta yi nazari tare da yanke hukuncin wa’azi kaɗai zasu yi, saboda babansu shima mutum ne mai riƙon addini, bai son duk wata bidi’a da zata jefa shi ko iyalansa a cikin fushin Allah.

Bikin ya rage saura kwana biyu ne aka shirya gagarumin wa’azin da ya tara mata masu yawa, dangin Abbas ma duk sun zo, Asma’u kuwa kishi da hassada kamar su kashe ta, saboda an yi hidimar da ta tabbatar mata da Abbas mutum ne da Allah ke so, kuma mutanen gari ke so, dan kuwa an kashe kuɗaɗe masu yawa, an ci an sha, sannan an rabba litattafai da bags na zuwa Islamiya masu kyau, aikuwa bata kwana a unguwar ba, sai dai ta tafi gidan ƙanwar Aunty dan ta samu sassauci a ranta.

Ranar ɗaurin aure kuwa unguwar ba masaka tsinke, dan kuwa Baban Khadija babban mutum ne dake hulɗa da manyan mutane, kuma sun nuna mashi kara, saboda Khadija ce ɗiyar da ya fara aurar wa. Abbas kuwa bakinsa har kunne, a ransa ji ya riƙa yi kamar wannan ne aurensa na farko.

Da yamma liƙis aka ɗauki amarya Khadija zuwa ƙayataccen gidanta na aure. Danginta kuwa mutane ne masu zuciya, sun zuba mata kayan ɗaki na gani na faɗa, kamar yadda shima Abbas ya zuba kuɗaɗe wurin gyaran gidan da kuma lefe, wanda za a ce rabuwarshi da Asma’u gobarar titi ce.

A daren farko kuwa duk da kunya da tsoron da Khadija ke ji, amma bata hana Abbas samun farinciki daga gare ta ba. Kuka ta riƙa yi bayan komai ya kammala, aikuwa ya nuna mata shi kakken mijin novel ne. Da kansa ya kimtsa mata jiki, sannan suka koma kan gado da shirin bacci.

Tana maƙale cikin jikinsa ya ce “Sorry My Nanas”, saboda har yanzu bata bar ajiyar zuciya ba, maƙe kafaɗa ta yi alamun ba zata yi haƙurin ba, dariya mai cike da farinciki ya yi, kana ya ƙara matse ta, lallashinta ya riƙa yi da kalamai masu ɗauke da zallar soyayya, inda ya ce “Khadija ki yi haƙuri, idan ban kasance da ke ba a yau zan iya shiga wani hali, ki sani ke zaɓin Allah ce a gare ni, kin ga dole na kula da ke! Ina sonki my Deejah, ina ƙaunar ki, zan kula da ke fiye da yadda zan kula da kaina Nana.”

Kasaƙe ta yi tana sauraron kalmominsa da suka kashe mata jiki, lura da hakan ya sa Abbas ya cigaba da faɗin “Kin mani alƙawari kema za ki kula da ni?”, kasa magana Khadija ta yi, murya a disashe ya ce “Kin ji Nana?”, lokaci ɗaya kuma ya shiga yi mata abin da ke tsorata ta, sai da ta janye mashi hannu a jikinta kana ta ce “Uhmm!”, wanda ke nuna amsar tambayar shi ce. Albarka Abbas ya yi ta sa mata, daga bisani suka yi bacci mai cike da aminci.

Washe gari bayan sun yi wanka sun shirya ne Abbas ya shiga kitchen. Breakfast mai sauƙi ya haɗa musu sannan ya zo dining ya jera, ransa fal da tunanin amaryarsa ya nufi bedroom, kwance ya same ta a gefen gado ta takure jikinta, cike da kulawa ya duƙar da kansa saitin fuskarta, “Khady!”, ya ambaci sunanta cikin so da ƙauna.

A hankali ta buɗe idanunta da suka yi nauyi saboda zazzaɓin da ya sauko mata ta dube shi, sai da ya sumbaci kumcinta sannan ya ce “Muje dining ga breakfat can”, daga kwancen ta girgiza “A’a”, tambayar ta ya yi “Saboda me?”, kamar zata yi kuka ta bashi amsa “Bana jin daɗi fa”, cikin sigar tausayin ta ya lallaɓa ta akan ta daure ta yi breakfast ɗin tunda zata sha magani, ba dan ta so ba ta ce “Toh ka a kawo a nan”, da hanzari Abbas ya maido breakfast ɗin a bedroom, taimaka mata ya yi ta zauna a kan carpet, sannan ya haɗa mata tea mai kauri, da kansa ya riƙa bata wainar ƙwan tana ci, daga bisani ta sha tea ɗin. Sai da ya tabbatar da ta ƙoshi ne ya yi kalacin shi ma. Bayan sun gama ya kimtsa wurin, sannan suka koma kan gado dan rage gajiya.

*****

Toh Asma’u itama lokacin bikinta da Nas ya zo, sai dai a wata estate ya kama mata haya saboda bai kammala ginin gidansa ba. Dangin Nas mutane ne masu masifar son abin duniya, Asma’u kuwa ɗiyar Malam shehu ce, ko kuma ince ɗanwake ka fi babanka, duk da ƙoƙarin iyayen Asma’u wurin ganin ba a raina masu ba, amma sai da dangin Nas suka raina masu, gori da habaici kuwa sun sha shi daidai gwargwado.

Da Daddare kuwa Asma’u ta shirya sharɓar romon soyayyar ta da Nas, sai dai samunsa a matsayin raggon Namiji ne ya tuno mata da Abbas, saboda ba wata soyayya da Nas ya nuna mata, kawai ya jawo ta kamar mayunwacin zaki ya biya bukatarsa, shagwaɓa kuwa duk da ta ƙarya ce ta ƙirƙiro, amma kamar bai san tana yi ba.

Daga kwancen da Asma’u ke a gefensa ta yi jugum, saboda minsharin Nas da ya fara tashi sama na neman tarwatsa mata zuciya, a ranta ta ce “Shi dama haka yake?”, bata da mai bata amsa, dan haka ne ta tashi zaune, cikin ƴan daƙiƙu ta tuna daren ta na farko da Abbas, da kuwa irin kulawar da ya bata, duk da bata son Abbas, amma ita kanta ta san ya yi ƙoƙari wurin faranta ranta.

A daidai wannan lokaci kuwa Abbas ya kai ƙololuwar jin daɗin kasancewa da iyalinsa, bayan ya kimtsa ne ya kai matarshi ban ɗaki suka kama ruwa, suna fitowa ya rungume ta ta baya cikin muryar raɗa ya ce “Andijou nah”, amsawa ta yi da “Na’am angona”, saida ya sumbace ta a wuya sannan ya ce “Allah ya yi miki albarka”, ta ce “Amiin.”

Soyayya mai zafin gaske suka ɗan taɓa, sannan ya rungume abarsa cikin bargo, bacci mai daɗin gaske ne ya tafi da su.

Haƙiƙa ma’auratan sun dace da juna, rayuwa mai cike da so da ƙauna suke yi, dan sun ɗauki aure a matsayin Ibada. Mahaifiyar Abbas kuwa kullum sanya ma Khadija albarka take, dan ta riƙe mata ɗa da amana, kamar yadda su ma mahaifan Khadija kullum suke faɗin ta yi dacen nagartaccen miji.

Asma’u kuwa cikin ƙasa da wata ɗaya ta fahimci waye Nas da kalar shu’umcinsa, dan kuwa babu mafarkinta ɗaya da take tsammanin zai iya zama gaskiya. Zaune take a falo ta yi jugum, saboda tunda ya fice da asuba, bata sake jin ɗuriyarsa ba har shaɗaya saura, saɓanin Abbas da bai tafiya wurin aikinsa sai ya tabbatar da ta gama gamsuwa da zamansa a gidan. Tambayar takaici ta jefo ma kanta “Wai wane irin zama ne wannan.?”, tana cikin laluben amsar da zata ba kanta ta ji alamun tsayawar motarsa.

Ɗaukar ma ranta ta yi zata yi mashi magana, dan ba haka ta shirya zaman auren ba, fuskarta ba yabo ba fallasa ta yi mashi sannu da zuwa lokacin da ya shigo, bai kalle ta ba ya amsa, bare kuma ya karanci yanayinta.

Bayanshi ta bi lokacin da ya nufi ɗakinshi, suna kai wa bakin ƙofa ya dakatar da ita “Ina zuwa”, bata gama fahimtar inda ya dosa ba ya shige ɗakinsa tare da maido ƙofar ya sa key, sororo ta yi, lokaci ɗaya kuma ta ce “Ikon Allah”, zuciya ce ta ingiza ta buga ƙofar, dan ba zai yiyu ta tsaya waje kamar ƴar aikinsa ba.

Daga can cikin kaushin murya ya ce “Wai ya aka yi ne?”, zuciya iya wuya ta ce “Shigowa zan yi fa”, a gadarance ya ce “Toh da Allah yi haƙuri, ki koma can falo zan same ki.”

Tamkar Asma’u bata ji me ya ce ba, kasa magana ta yi, sannan kuma bata tafi ba, dan lamarin ya kwance mata. Ta fi ƙarfin minti goma a tsaye, amma bai fito ba, da ta gaji ne ta wuce ɗakinta ta faɗa kan gado.

Kuka take son yi, amma zuciyar ta ƙeƙashe saboda firgici, dan haka kawai ta fara zargin Nas, saboda haka kawai miji ba zai hana matarshi shiga ɗakinsa ba. Tana cikin wannan yana yi ne ta ji muryarsa a bakin ƙofarta “Ya aka yi ne?”, shiru ta yi kamar bata san da shi ba.

“Asma’u, ko bakya ji ne?”, ya faɗa tare da shigowa ɗakin ya zauna kan stool. Tashi Asma’u ta yi tana dubanshi, a ranta ta ce “Kallon kitse kawai na yi ma rogo”, a zahiri kuma kamar zata yi kuka ta ce “Wai haka zamu zauna a gidannan?”, cikin rashin fahimta ya ce “Kamar ya?”, cewa ya ta yi “Me yasa baka son zama gida, kuma ko ka zauna me yasa ba ka son na raɓe ka, yanzu ɗaƙinka ma dakatar da ni ka yi, kuma ba wannan ne na farko ba”, ɗan shiru ya yi, kafin daga bisani ya ce “Toh me ye haɗinki da ɗakina, kuma ba kina shiga ki yi bacci ba?”, cike da kallon mamaki ta ce “Ɗakinka ne miye haɗina da shi? ka dena faɗin haka ma kada ka sa na zarge ka.”

Baki ya taɓe tare da faɗin “Idan kin zarge ni ma kin yi a wofi Asma’u, dan bani da wani mugun abu a ciki, dan haka ma kada ki ɗaura ma ranki abinda zai wahal da ke”, musayar maganganu suka yi sosai, amma haƙar Asma’u bata cimma ruwa ba, dan ficewa ya yi daga ɗakin. Cefanen da ya baro cikin mota ya kawo mata, sannan ya bar gidan.

Haka rayuwar gidan Nas mai cike da ƙunci ta cigaba da kasance ma Asma’u, dan kuwa shi bai san wata soyayya ba, bare ya gwada ma wani ita. Hira kuwa babu ita a tsakaninsu, da ya dawo gida sai bacci kamar kasa, da ta sake nuna damuwarta kuwa sai da suka samu saɓani da shi.

Wani ƙarin haushin kuma kuɗinshi da take gani ashe shi kaɗai ke morar abinsa, sai wanda ya ga dama kawai yake ba, a nan ta gane Aishar Nas da suke kallon tana shanawa guminta ne take ci. Kankace me kuwa har ta fara ramewa duk da bata da matsalar abinci.

Abbas ɗin da ta tsana kuwa shi ne tunaninsa ya fara zame mata abin yi ba tare da ta ankare ba, hakan ne ya fara cusa mata tsanar Nas, har ta dena ganin duk wani kyawu da kwarjinin da yake mata a baya. Haƙiƙa Asma’u ta yi jifar gafiyar ɓaidu, kuma ta fara nadama tun ba’a je ko ina ba.

Ta ɓangaren Nas ɗin ma ba wani jin daɗin zama da Asma’un yake ba, saboda tun a girki ya san ya yi asarar rabuwa da Aisha, uwa uba kuma wurin haƙuri da kawar da kai, saboda duk dokar da ya sa ma Aisha bin ta take sau da ƙafa, Asma’u kuwa kai tsaye ni tsaye take mashi, shi ya sa mugun halinshi ya ƙarasa fitowa baki ɗaya.

Yanzu haka ma haushin juna suke ji shi da ita, saboda ya hana ta zuwa unguwa, kasantuwar shi ba ma’abocin son yawo bane, ita kuma wannan ne ya sa ta fara azabtar da shi a shimfiɗa.

Kwance yake ɗakinshi sai juye-juye yake, jira kawai yake ta zo ɗakin, amma shiru ba alamun ta har sha biyun dare. Tunda Nas yake bai taɓa kiran Aisha a shimfiɗa ba, sai dai ita ta kawo kanta, saboda ta san halinshi na girman kai, amma sai gashi yau ya ɗauki waya da zimmar kiran Asma’u, daga kwancen da yake ya danna ma number ta kira, sai da ta ga dama sannan ta ɗaga, cikin tsananin buƙatarta ya ce “Ki dawo nan ɗakin mana.”

Daga can Asma’u ta ce “In maka me? Ni a ɗakina zan kwana.”, yana shirin sake magana ta tsinke kiran, wani irin ƙuncin gaske ne ya taso mashi har ya riƙa ji kamar ya yi kuka, kwanciya ya gyara, tare da ba zuciyarshi haƙuri, dan idan ya biye ma abinda take zuga shi, toh zai iya sakin Asma’u a wannan dare, saboda dama ta ishe shi.

Washe gari da safe yana jin Asma’u na Knocking, amma ya ƙi buɗe mata, dan har yanzu a wuya yake. Ba shi ya fito ɗakin ba sai da aka kira shi a waya.

Asma’u na ɗakinta ta ji motsinsa, aikuwa da hanzari ta fito, lokacin kuma har ya zo falo, gaban shi ta sha ta ce “Ina ta Knocking ƙofa ɗazu amma ba ka buɗe ba”, wani irin mugun kallo ya yi mata, lokaci ɗaya kuma ya ce “Matsa ki bani wuri”, kanwa ba ta jiƙa bakin Asma’u, dan haka ta ce “Kamar ya in matsa in baka wuri?”, kamar Nas zai maƙure ta ya ce “Ba ki ji me na ce ba kenan?”, a yadda Asma’u ta ga idanunsa sun kaɗa ne dole ta matsa ta bashi hanya.

Murya can ciki ta ce “Can maka”, sannan ta koma ɗakinta, shi kuwa isarsa farfajiyar gidan ta yi daidai da Knocking gate ɗin gidan, ba tare da ya tambayi ko waye ba ya buɗe, ganin su Nafeesa ne su Uku ya ƙara murtuke fuska, saboda baya son mutane ko kaɗan, musamman dangin Asma’u da bai san ƙaddarar da ta haɗa shi aure da su ba.

Ɗaya bayan ɗaya suka gaishe shi, kamar wanda aka tilasta mawa ya amsa ma Nafeesa kaɗai, Hadiza da Ummulkhairi kuwa bar musu gaisuwarsu ya yi, waɗanda su ɗin babansu ɗaya da Asma’u. Jikinsu a mace suka shiga ciki, shi kuma ya ja motarsa ya bar gidan.

Asma’u kuwa ba ƙaramin farinciki ta yi da zuwansu Nafeesa ba, dan ko ba komai zasu rage mata kewa. Bayan sun gaisa ne Nafeesa ta ce “Wai ni mijinki kullum kamar wanda aka yi ma saƙon mutuwa”, Hadiza ta karɓe da “Ke ma kin gani”, baki Asma’u ta taɓe “Ku bar ɗan Iska, ni ban taɓa ganin matsiyacin mutum kamar shi ba wlh, ashe kallon kitse nake ma rogo.”, Nan Asma’u ta kwashe mugun halin Nas kaf ta labarta masu, Ummulkhairi na ƴar dariya ta ce “Wa ya ga CIKIN BAURE”, Kusan a tare suka ce “Wanda ba a sanin haƙiƙanin cikinsa sai an tona ba.”

Nafeesa da ta san sakayyar Abbas ce ta fara bibiyar Asma’u ta ce “Allah ya kyauta, dama auren wani mai kuɗin ko bala’i, gwara talakka mai muntunci wlh”, Asma’u ta ce “Wallahi na yarda, Abbas ya fi wancan shegen.”

Hira suka sha sosai, daga nan suka faɗa kitchen suka yi girki, suna cikin cin abincin a falo sai ga Nas ya dawo, ba inda idonsa ya dira sai kan tray ɗin abincinsu, ƙwafa mai ƙarfi ya yi sannan ya wuce, take kuwa suka sha jinin jikinsu, Nafeesa ta ce “Anya wannan mutumin”, Asma’u ta ce “Rabu da banza”, a wuwwurce suka ci abincin, sannan suka yi shirin tafiya.

Asma’u bata daddara ba ta je ɗakin Nas, a hankali ta tura ƙofar ta shiga, daga tsaye ta yi ta ce “Su Nafeesa ne zasu ta fi”, a gadarance ya dube ta daga gefen gadon da yake zaune “Sai aka yi yaya?”, cikin daburcewa ta ce “Kuɗin Napep zaka ba su.”

Ido cikin ido ya ce mata “Duk uban abincin da suka ci bai ishe su ba, sai na ƙara masu da kuɗi.?”

Asma’u ta ji maganar har cikin ranta, kawai bata son ta ja ma su Nafeesa ne, amma da ya ji amsa, “A’a, abincin ma ya wadatar”, tana rufe baki ta juya ta fice, da mugun kallo ya raka ta, saboda a buɗe ta bar mashi ɗakin.

A ɗakinta ta taras da su sun kimtsa, zuciyarta ba daɗi ta basu haƙuri, dan shi kaɗai ne abinda ta mallaka, basu wani damu ba, saboda suna da kuɗi.

Sai da suka bar gidan sannan ta iske shi a ɗaki, batun abinci ta yi mashi, ya ce ya ƙoshi, bata ankare da kuskuren rashin kawo mashi abincin da wuri ba ta fara koro mashi tarin damowoyinta.

Sai da ta gama karance mashi kaf damuwarta, sannan ya ce “Yanzu idan ke matar arziki ce zan kira ki a ɗakina ki ƙi zuwa; Ko kuwa ƙauyanci ne ke damunki da za ki manta da mijinki wurin abinci, sai sadda kika ga dama?”, wannan maganar ta mata zafi, cewa ta yi “Toh a irin zaman da muke kamar na gumaka ta ya zan zo wurinka? Ni da kai ba hira, sai zaman kallon kallo kamar kurame.”

Kalmar “Gumaka” da Asma’u ta sako a cikin zancen, ita ce ta ƙara tunzura Nas suka yi kaca-kaca, daga ƙarshe ya ce ta bar mashi ɗakinshi.

Tun daga wannan rana kowa ya yi ta kansa a gidan, a ranar cikon na bakwai ne Asma’u na kwance a falo ya shigo, inda yake bata kalla ba, bare ya sa ran sannu da zuwa.

Ɗakinsa ya  wuce, ba a fi minti biyar ba ya fito falon, “Ke!” ya furta cikin tsananin fushi, gaban Asma’u na muguwar faɗuwa ta tashi zaune tana dubanshi…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Cikin Baure 23Cikin Baure 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×